Showing 36001 words to 39000 words out of 43872 words
Chapter 13 - SURUKATA HORROR BOOK COMPLETE DOCUMENT 2025.txt
*MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
12
Cike da takaicin Illiya da matarsa na dawo gida,ina shigowa da sanyi idaniyata na fara cin karo wato Malama Zainab.Cak na tsaya a bakin ƙofa jin zazzaƙar muryarta na fitar da sautin karatun Alqur'ani wanda ya zama barazana ga ruhina,ji nake tamkar an watsa mini ruwan zafi.
Tamkar Ammy ta san halin da nake ciki ta dakatar da ita da karatun ,“ Malama gobe in sha Allah mu ci gaba ga HAROON nan ya dawo,ƙaraso ku gaisa ” Ammy ta faɗa tana murmushi,sai da na je na ɗauki gorar ruwa mai sanyi na sha sannan na ƙarasa wurin su.
Ammy na fara gaishe wa kafin na zuba wa malamar ido,ta ɗago a hankali ta ce “ ya ƙarfin jikin?”
“Ai na ji sauƙi” na bata amsa ina mai ci gaba da kallonta,da dukkan alamu kuma ta tsargu da hakan don sai wani takure jikinta take.
“Ka zauna bari na kawo ma wani abu” Ammy ta faɗa tare da nufar kitchen,nesa da Malama na zauna ina son tantance ta amma sam babu wata ƙofar tauraronta da ke buɗe wacce za ta bani damar ganin sirrin ruhinta.
Na ja ajiyar zuciya na ce “ ya aka yi yau kuka fara karatu da wuri haka?”
Kamar mai tsoron magana ta ce “ ina da wani aiki mai muhimmancin ne bayan sallar magrib ɗin”
“Mene ne shi?”
Sai da ta ɗan ƙara sunne kai kafin ta ce “ dama... Dama wanda aka yi mana baiko ne ya d...” sauran maganar ƙarar fashewar gilas ta maƙale ta.
Ammy ce ta yi ɓarin lemun zoɓo,hankali tashe kuma ta bi ta cikin kwalbar tana mai cewa “ an miki baiko?”
“Eh tun shekaru uku da suka wuce ni da Sheikh Ali,ba ki dai ji ciwo ba ko Ammy?” ta ƙarashe da tambayar Ammy wacce ta zuba min ido,ƙila mamakin ganin ban wani razana sosai ba ko na tayar da hankali.
“Allah sa alkhairi,je ki direba ya mayar da ke” Ammy ta faɗa tare da zubewa kan kujera yayin da ita kuma Malama Zainab ta fice.A hankali na tashi na tsuguna a gaban Ammy na kamo ƙafarta da ke zubar da jini.Kwalbar na cire sannan na ɗauko ɗan akwatin da ke da kayan magani na shafa mata tare da naɗe ƙafar da bandeji.
“ Ka kuwa ji abin da Malama Zainab ta faɗa ?”
“Eh Ammy na ji”
“Shine kuma baka ce komai ba?”
“Ammy a kullum fa ke ce da kanki kike min nasihar cewa duk wanda ya yarda da Allah to komai nasa zai zo da sauƙi,kin ga kar ki damu Malama ba ta da wani miji da ya wuce HAROON zan je har gidan nasu na fallasa mata sirrin zuciyata ”
Ammy ta shafi sumar kaina tana wani ɗan murmushi kafin ta ce “ haka take yarona” na miƙe tare da sakar mata murmushi sai kuma na nufi step,a cikin kwanyata na soma jin ana yi min magana “ HAROON lokaci yayi da za ka fara amfani da powerka domin sato taurarin mutanen kirki,ta wannan hanyar ce zaka samu Malama Zainab ”
Kamar wani zararre na tambayi kwanyar tawa “ ta ya kenan zan soma?”
“Je ka fara yin wanka tukunna,sai ka je madubinka zai sanar da kai”
Haka kuwa aka yi,bayan na yi wanka na je na shiga cikin madubina.Direct ajin nan da ake koyar da karatu na shiga,yau ma Mr Zulu ne ke darasi akan allo yayi zanen baƙar mage mai jajayen ido yana kuma yin bayani.
“Baƙar mage , waɗanda galibi ana lulluɓe su cikin sirri da camfi, koyaushe halittu ne masu ban sha'awa, musamman a duniyar mayu da ayyukan sihiri.
Baƙar mage a zahiri suna ɗaukar kuzari mai zurfi, kariya da sihiri. A cikin wasu al'adun arna da sihiri, ana ganin baƙar fatar mage a matsayin mai kula tsakanin talikai, mai tsaro na ruhaniya. Ya ƙunshi ma'auni tsakanin haske da inuwa, bayyane da ganuwa.
Wataƙila wannan duality ne ya sa bokaye da matsafa suka zaɓi baƙar mage tamkar abokan hulɗa masu mahimmanci a cikin aikin sihiri. Suna kawo hikimar dare da ikon kewaya wuraren ruhi na ɓoye.
A cikin gogewar kaina, baƙaƙen ƙuliyoyi sun kasance sau da yawa jagororina da masu kare ni a lokutan canji ko haɓakar ruhaniya. Suna tunatar da ni cewa inuwa ba abin tsoro ba ne, amma illa fahimta. Suna ɗauke da sihiri mai hankali amma mai ƙarfi a cikin su, ƙarfin canzawa wanda ke ingiza mu mu wuce fiye da kamanni don rungumar ɗaukacin halittarmu.
Baƙar ƙuliya kuma alamun sa'a ne a wasu al'adu, suna kawo albarka da kariya ga waɗanda ke maraba da su cikin gidajensu. Kasancewarsu na iya zama abin tunatarwa akai-akai game da sihirin da ke kewaye da mu, yana ƙarfafa mu mu kasance a buɗe kuma mu yi maraba da mutane wanɗada ba mu sani ba da gaba gaɗi.
Shin kun taɓa haɗuwa da su a cikin ayyukanku ko rayuwar ku ta yau da kullun? Menene ma'anar waɗannan sahabbai masu ban mamaki a gare ku? ”
Hannu na ɗaga hakan yasa ya ce “ ina jin ka HAROON ”
Na ce “ ta ya za a yi mutum ya mallaki ita baƙar magen? Sannan mutum ɗaya zai iya ɗaukar ƙuliyoyi biyu a lokaci guda don yin aiki da su ko kuwa sai ƙwaya ɗaya kawai aka yarje masa?”
Mr Zulu ya bani amsa da “ a'a in kana so duk launinkan ƙuliyoyin da muka lissafa zaka iya aiki da su muddin dai zaka iya ciyar da su.Bari na faɗa muku wani sirrin iya ƙuliyoyinka iya ƙarfin tasirin alƙalumanka,mai son baƙar mage ina da su da yawa na sayarwa ga su nan na kawo” ya faɗa tare da buɗe wani tsohon akwatin ƙarfe .Cike yake da jariran baƙaƙen ƙuliyoyi duk idonsu kuma jajur suke ,nan fa duk kowa ya soma cewa yana so ganin kamar za su ƙare yasa da sauri ni ma na isa gaban akwatin don zaɓar tawa.Akwai ƙwaya ɗaya wacce ta banbanta da sauran ta fi su girma haka yanayin fuskarta ma kicin-kicin yake babu fara'a.
“Wannan nake so” na furta tare da kai hannu na ciro ta,Mr Zulu yayi min kallo kafin ya ce “ HAROON ka tabbata ?”
Ba tare da tambayar dalilin da yasa sai ni kaɗai ya yi wa tambayar ba na ce “ eh yalaɓai ita nake so ” ya saki ɗan murmushi kafin ya ce “ shi yasa Oganku ya ce kai ɗin na musamman ne taurarinka masu matuƙar ƙarfi ne” ni ma murmushin kawai na sakar masa,magen hannuna ta yi wani zillo ta ruga da sauri na take mata baya kawai sai na tsinci kanmu a wajen madubi a tsakiyar ɗakina.
Da ido nake kallon magen wacce ta haye bed ɗina ta yi min ƙuri da ido,da sauri na nufe ta na ɗauko ta na rungume.Sai yanzu na lura ashe namiji ne muzuru,kansa na soma shafawa na ce “ daga yau sunanka Tony” daga bakin ƙofa aka soma buga wa tare da kiran sunana “ na'am Ammy gani nan zuwa” na furta tare da tashi na buɗe mata,da faɗa ta soma “ HAROON me yasa kake son zama da towel,to in ka shirya ka fito ina son ganin ka” har za ta tafi sai kuma ta yi saurin juyowa tana kallon gadona,sai na kai dubana na ce “ Tony ne fa”
“Yaushe ka fara son ƙuliya ban sani ba?”
“Na sosa ƴar ƙeya kafin na ce zan yi miki bayani daga baya”
Ta fice,ni kuma na rufe ɗakin.A tsanake na shirya na ɗauki Tony muka sauka ƙasa sai wani kuka yake “minyau!”
Ammy ta ce “ Laure zuba ma magen nan abinci ƙila yunwa take ji,kawai haka nan ka kama ka rufe ta a ɗaki”
Tony ya wani zille ya bi Laure mai aiki can kitchen,wani tsohon plate ta samu ta zuba masa abinci tana masifa ƙasa-ƙasa “kawai don mugun hali ka rasa magen da za ka kawo cikin gida sai baƙa mtsww!” ta ja tsuki,ƙafa ta sa ta bugi Tony ya tsaya yana kallonta “ ni bari kallona shegiya da wasu ido nata kamar mayya” sai kuma ta fito.
Na dube ta na ce “ kin zuba masa abincin?” yau ne karon farko da na taɓa yi mata magana saboda ni da ƴan aikin gidanmu gaisuwa ce ke haɗa mu ita ma sai na ga dama na amsa.
“Eh ga ta can tana ci” ta bani amsa.
Na ce “ namiji ne ba mace ba,sunansa Tony ”
“Sai kace dai wani mutum yalaɓai ai duk ƙuliya da sunan mace ake kiranta” Laure ta faɗa cike da jin haushi tana mai ɗaukar kwanon abincinta ta kama hanyar fita tana gunguni ƙasa-ƙasa sarai kuma kwanyata ta sanar da ni abin da ta ce.
“Tun da baƙin hali gare mu don muna da kuɗi da kuma jiji da kai ki je an sallame ki daga aikin” na faɗa cikin ɗaga murya,da wani mugun sauri ta juyo tana kallona kafin ta zo da gudu ta zube a gabana tana bani haƙuri,tsakiyar idonta kawai na kalla na fahimci Laure irin mutanen nan ne waɗanda akan kuɗi babu abin da ba za su iya yi ba,sannan tuni hassada da baƙin ciki sun gama gurɓata ruhinta.Jin daɗina guda da Ammy ta gusa ba ta falon,na saki makirin murmushi na ce “ zan maido ki aiki zan kuma ƙara miki da wani wanda ya fi wannan albashi na san za ki iya ”
Ai kuwa ta washe baki tana cewa “ sosai yalaɓai in dai zaka bani kuɗi”
Na ce “ yawwa yarinyar nan Salima ƴar gidan Yakubu soja kin san ta ne?”
Ta ƙara washe baki ta ce “ Salima mai mage ko? Ai har gidansu Hajiya ke aikina”
“Yawwa a kanta nake son baki aiki”
“Koma mene ne zan yi Alhaji in dai zaka bani kuɗi”
“Ok za ki iya tafiya,gobe zan faɗa miki bayanin aikin naki ” ta miƙe ta tafi da ƙarfin gwiwarta,sai lokacin kuma Tony ya fito daga kitchen yayi tsalle ya ɗare kan cinyata na soma shafa bayansa ina jin wani irin daɗi na mamaye ni.
Ina nan zaune sai ga Illiya ya shigo fuskarsa kawai na kalla na fahimci damuwarsa,ya zo ya gaishe ni tare da zama kan capet idonsa suka fara tsiyaya.
“Ai zata dawo ba za ta iya barin ka ba,sai dai ka sani ban janye ƙudirina ba ya zama dole na ɗanɗani zumarta” na furta ina cije leɓena na ƙasa.
Da sauri Illiya ya ɗago yana cewa “ yalaɓai dama baka kusance ta ba?”
Na kawar da kai gefe ina kallon cikin idon Tony da nake tsintar wasu abubuwa a ciki.
“Yalaɓai wannan muzurun fa?” Illiya ya jefo min tambayar da tasa na maido dubana gare shi na ce “ faɗa min Illiya ta ya aka yi a kallo ɗaya har ka san muzuru ne? Kana da wankin ido ne ko yaya?”
Ya ɗan washe baki ya ce “ yalaɓai lokacin baya fa na ɗan taɓa aikin tsibo sai kuma na bari saboda kusan haukata ni jinnu suka yi”
“Ita ma matar taka da tsafi ka aure ta kenan?”
“A'a wallahi auren soyayya ne ko rubutu ban taɓa bata ba”
“Ya ake samun costumer Illiya ? Ina nufin malaman tsibo ta wace hanya ce za su bi domin ganin sun samu mutane da yawa?”
“Ta hanyar shiga gidan rediyo da tv,ka yi musu alƙawarin aiki kyauta ne sai buƙata ta biya sannan mutum sai bayar da abin sadaka”
Na saki murmushi na ce “ to ka shirya min zama da manyan ƴan jaridu da kuma wasu mutanen da za su bayar da shaidun ƙarya akan na yi musu aiki ya ci sun zo godiya”
Ya saki baki yana kallona kafin ya ce “ yalaɓai kuma bayar da magani zaka koma?”
Na haɗe rai na ce “ tashi ka bani wuri,ka yi abin da na ce su kuma mutanen da zaka samo ka sanar da su zan biya su ne” da saurinsa kuwa ya tashi,ni kuma na kai baki na sumbaci Tony don wannan dubarar daga gare shi ta fito.
Bayan sallar la'asar kuwa sai ga mutane sun cika gidanmu,gefe guda ƴan jaridu biyu ne sai bayan na gama bayanan ƙarya kan cewa ina warkar da dukkan cututtukan duniya sannan mutane suka soma faɗin abubuwan alkhairin da na yi musu,na biya masu gidan rediyo da tv domin yi min talla da kuma lambar wayata da za a kira ni.Su kuma masu shaidun ƙarya Illiya na baiwa kuɗi ya raba musu,kuɗin da ace sun san sune ajalinsu to da tabbas ba za su karɓa ba amma ƴan magana na cewa kwaɗayi mabuɗin wahala......
NB:Ina ƙara yawan free page ne,niyyar kaina.
My book is only 500 via2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
Talla! Talla! Talla!!!
DULLAHZ CAKES AND MORE 💕
Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu,
Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki,
Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884
Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884
Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884
Call:09111648884
[26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
13
Washegari,afujajan Illiya ya shigo ofis ɗina ko neman izini bai yi ba.
“Yalaɓai ya haka? Dukkan mutanen da suka bada shaidar ƙarya a kan kai malamin tsibo ne sai ɗauki ɗaiɗaya mutuwa take yi musu”
Da wani mugun kallo na dube shi na ce “ au! So kake na bar su da ransu daga ƙarshe su tona min asiri? ”
“Yalaɓai kisan kai fa ne jinin wajen mutum goma” ya faɗa hawaye na zubo masa akan kumatu waɗanda suka sa na ji zuciyata ta yi mugun sanyi don tsabar daɗi,don a yanzu in ga mutum cikin baƙin ciki shi fi faranta min rai.
Ido na lumshe ina tuna yadda Tony yayi amfani da madubin tsafina ya dinga tsotse jinin duk mutanen da na bai wa kuɗi,sosai hakan ya ƙara mini ƙarfin power ta yadda a wannan karon har na yi nasarar toshe bakin Ammy ta yadda duk abin da zan yi ba za ta ga abunsa ba ko kuma ta yi min magana.
“Yalaɓai ciki fa har da mace mai ciki ” Illiya ya faɗa cikin gwanjin kuka,na buɗe ido jin furucinsa .Na ce “ ya zancen Salima ka kuwa fara wani shiri a kai?”
Ya saka idonsa cikin nawa yana zancen zucin da nake jinsa raɗau kwanyata na karanto min shi,‘ dama duk rashin imanina akwai wanda ya fi ni ? Anya akwai zuciya a ƙirjin yalaɓai? Wato duk wannan iftila'in da ya jefa mutane shi ko a kwalar rigarsa?...’
Tunanin nasa ne na katse ta hanyar cewa “ wani abun jin daɗi ma daga cikin wannan lamari shi ne kuɗin za su ci gaba da yawo a doron duniya,kuma iya masu son zuciya ne kawai za su je hannunsu haka kuma zan ci gaba da amfani da tataccen ƙarfin jikin mutane domin inganta gobena.Illiya ina so ka sa a ranka babu abin da ba zan iya yi ba yanzu,don haka kar ka kai ni bango yin haka ban kwana ne da rayuwarka.Je ka yi aikin da na saka,ka tabbatar Salima ta kasance cikin tsaronka sannan duk wani motsi nata ka sanar da ni”
Ba tare da ya ce komai ba ya juya zai tafi,na tsayar da shi “ mene ne sunan matarka?”
Ya juyo da sauri yana kallona tambayar ‘ me za ka yi da sunanta?’ shimfiɗe akan fuskarsa.Na ƙara haɗe rai ina juya idona zuwa na mage,murya na rawa ya ce “ Mariya ” na sakar masa murmushi,shi kuma ya fice.
Kan kujera na zauna ina tunanin hanyar da zan ɓullowa mijin da Malama Zainab za ta aura,wanda alƙaluman tsafina sun tabbatar min da tabbas auren babu fashi .Na ja tsuki ina jin takaici,kukan Tony na ji ƙarƙashin kujerar da nake zaune.Na duƙa na ɗauko shi na ɗora shi kan table,jikinsa na fara shafawa tare da soma yi masa magana ina neman shawara “ Tony a daren jiya na yi bincike akan Malama Zainab kuma an nuna min sai ta auri mijin nan nata,ban so ya kusance ta ya zan yi?”
“Turen aljani za ka yi wa mijin,tun da ita tana tsare iyakokin Ubangiji sosai babu ta hanyar da jinnu zai shiga jikinta.Amma kamar yadda ka yi bincike haka ni ma a jiya na yi bincike kan shi Sheikh ɗin,duk da yayi karatun addini amma fa bai amfani da shi in taƙaice ma dai fuska biyu ce da shi har da giya yake sha” Tony ya faɗa min da idonsa amma raɗam nake jin sautin murya na fita daki-daki.Tsabar murna ban san lokacin da na ɗauke shi na rungume tare da miƙe wa tsaye na soma yin rawa,“ ashe babban sirri ne da mage baƙa har haka? Hohoho! Wato shi yasa Tony ka kasance na musamman abin da ban saka ka ba yi kake yi domin sauƙaƙe min aiki”
Tony ya ce “ yalaɓai ka manta a daren jiya ka yi min sacrifice? Ai muddin zaka bani jini abin da zan yi ma sai ka yi mamaki” sam ban damu da cewa illata rayuwar wasu babbar cutarwa ce ba na ce “ in dai jini ne Tony kar ka damu”.
Ina nan zaune Illiya yayi min waya kan cewa Salima ta tashi daga makaranta,kuma shine ya kai ta gida da sunan ya rage mata hanya.Duk wayar da nake Tony ya buɗe kunnuwa yana saurare,bai ce komai ba ya fita da gudu.Na saki murmushi don na tabbata kuwa wani aikin ne zai yi min,wayata da key na ɗauka tare da ficewa .
Ina draving ina tunanin surar Mariya matar Illiya ,na lashi leɓena na ƙasa ina mai cewa “ ko fyaɗe ne sai na yi miki muguwa!” a haka na ƙarasa gida.Ina shiga na ga Salima a zaune kan kujera tana taya Ammy saƙar kayan