Showing 39001 words to 42000 words out of 43872 words
Chapter 14 - SURUKATA HORROR BOOK COMPLETE DOCUMENT 2025.txt
sanyi,na saki wani murmushin jin daɗi ganin Laure ta fito daga kitchen hannunta riƙe da kofin zoɓo ta kai wa Salima.
“Ga wannan ki sha Madam yana ƙara gani musamman gare ku masu kallon zare” Laure ta faɗa amma kafin Salima ta kai ga amsa Ammy ta ce “ Laure miƙo min ganin zoɓon nan har maƙoshina ya bushe,je ki kawo wani”
Da sauri na ƙarasa ina cewa “ haba dai Ammy ya za ki ce haka? Ita fa wannan baƙuwarmu ce ita ya kamata a fara karramawa,kuma kin ga ke kina da mura.Laure je ki kawo wa Ammy marar sanyi,ki dinga kula don Allah ko ta ce ki bata abu mai sanyi kar ki biye ta”
Laure ta miƙa wa Salima kofin,za ta ajiye shi ita ma na tari numfashinta “ Hajiya ƙyanƙyamin mu kike shine ba za ki sha ba?” da sauri ta girgiza kai ta ce “ a'a wallahi bari na sha to” sai ta kai kofin bakinta har sai da ta sha rabi sannan ta ajiye sauran.Laure na fitowa na yi mata nuni da ido kan ta tafi da ragowar wanda Salima ta ajiye,ai kuwa tana miƙawa Ammy nata sai ta ce “ bari na ɗauke sauran kar ya zuba ga capet”
“Laure wane irin abu ne wannan? Ta sha abu ta ajiye shine za ki tafi da shi? In kuma tana son ƙara sha?” Ammy ta faɗa cikin faɗa ,a doli Laure ta ajiye kofin tana kallona ta koma kitchen.
Hira suke tsakanin Ammy da ita Salimar ni kuma ina gefe ina danna waya,hannun Ammy na gani ya ɗauki kofin zoɓon ban san lokacin da na ce “ Tonyyyy!” ban ida rufe baki ba ji kake Ammy na salati haɗi ƴar ƙara tuni Tony ya saka bindinsa ya buge kofin daga hannunta ya faɗi ƙasa ya zuba a ƙafarta.
Laure ta fito tana tambayar lafiya,na soma shafa bayan Tony da tuni ya zo ya ɗare cinyata kafin na ce “ zo ki tsabtace wurin nan please ”
Jikinta na rawa ta zo ta goge wurin da ya ɓace ita kuwa Ammy sai faɗa take,a ƙarshe dai na tashi na bar wurin na koma part ɗina.Ta cikin madubina na ga hanyar da Tony ya bi ya bai wa Laure maganin da ta zuba a zoɓon Salima,ya ajiye mata shi ne a kitchen da kuma ƴar guntuwar takardar da yayi bayani daki-daki.
★MALAMA ZAINAB
Matashiyar budurwa ce ƴar kimanin shekara ashirin da bakwai a duniya,ta mallaki hankalin kanta.Duk wata cikar halitta da ƙima da ake nema wurin cikakkar mace mai ƙima duk ta mallake su.Mace ce ita wacce ta riƙi bautar Ubangiji matsayin abu na farko a rayuwarta,duk sauran abubuwa suna biyo wa baya ne.Tausayi,kyauta,jinƙai su ne suka luluɓe duniyarta suka ƙawata kyakkyawar fuskarta mai cike da hasken ni'imar imani.Tun da take ba ta taɓa soyayya ba,duk da kuwa maza dayawa sun nuna ra'ayin haka amma ita ba ta ji wanda take so ba.Sheikh Ali ya kasance cousin nata,tun da ta tasa ya ga tana da addini ya ɗauki son duniya ya ɗora mata tare kuma da zage dantse wurin nuna mata abin da zai kawo ci gaban karatunta.Wannan yasa ba tare da wani tunani ba ta amince za ta aure shi har aka yi musu baiko,bayan haka ne ya tafi Misira wurin karatu.Tun da ya tafi kuma ba wata gamsashiyar waya suke ba kasancewar shi da ita ɗin duk ba su da wani isasshen lokaci.Kwana biyu da dirar shi a ƙasar Nijar ya nemi a yi walimar aurensu,wacce kuma tuni aka soma shawarwari tsakanin ahalin biyu kafin shi ma angon ya nemi su keɓe domin tattaunawa.
Ko da ta fito daga gidansu HAROON direct gida direba ya ajiye ta,zuciyarta cike da fargabar abin da take gudu take kuma zato kar ace gaskiya ne wato tana son HAROON .
Ɗakinta ta shiga ta yi wanka ta canza kaya,bayan ta yi sallar magrib sai ta shafa mai.Tana nan zaune tana saƙa da warwara Innarta ta shigo tana cewa “ Zainabu ki fito ga Ali nan ya zo”
Sai da gabanta ya faɗi,amma ta daure ta ce ” to Inna gani nan” sai kuma ta miƙe ta zaɓo wani farin hijabi ta saka tare da fesa turare marar ƙamshi.
Sai da ta yi jarumta sosai sannan ta ƙaƙalo murmushi ta yaɓawa fuskarta mai cike da damuwa.Da sallama ta fita falon,yana ganin ta ya kafe ta ido ko ƙyaftawa bai yi.Ta zauna ƙasan capet ta ce “ ina wuni Imam?”
“Alhamdullah malamata fatan kin wuni lafiya?” ya faɗa ba tare da ya janye idon nasa a kanta ba,cike da tsarguwa ta ce “ Imam babu fa kyau kallon mutum haka”
Yayi murmushi mai sauti ya ce “ haka ne ! Amma kar ki manta saura ƙiris ki zama tawa na yaye duk wani hijabin kunya a tsakaninmu”
Ba ta ce komai ta miƙe ta je ta kawo masa ruwa da abin da Innarta ta gyara mata domin tarben baƙon.Tana zuba masa ruwa ya kafe hannunta da ido,nan take jikinta ya soma yin rawa ta ɗaga kai ta banka masa wata muguwar harara.
Ya ja ajiyar zuciya ya ce “ sai da na ji wani yarrr ” ruwan ta ajiye masa ya ɗauka ya sha,sannan ta zuba masa abinci har da su cewa ta zo su ci amma ta ƙi.
Bayan ya gama ne ya ce “ Malama Zainab yau muna wace rana?”
Ta basa amsa kai tsaye da “laraba”
Ya ce “to rana irin ta yau kin shiga lalle da yardar Allah,sai a yi ɗaurin aure juma'a,taron biki kuma asabar”
Shiru ba ta ce komai ba sai ma duniyar tunani da ta lula,ranar farko da suka soma ganin juna da HAROON ,yadda suka yi baya ta faɗa kan ƙirjinsa,yanayin yadda yake kallonta cikin tako da kuma salo,yadda yake mata murmushi...
“ Zainab ?” Sheikh Ali ya katse mata tunanin,a ɗan firgice ta ce “ na'am HAROON !”
“Haroon kuma?” ya tambaya da mamaki,sai ta diririce ta soma kame-kame,ita ɗin ba ma'abociyar yin ƙarya ba ce shi yasa ya gane.
“Kar ki yi min ƙarya Zainab,wane ne HAROON ?”
Ba tare da ta basa amsa ba ta tashi da sauri har da ɗan gudunta ta shige ɗakinta tare da faɗawa kan bed ta fashe da kuka.......
My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822.
Ki zo ki yi payment domin a yi tafiyar nan da ke, wannan karon salon na daban ne salo ne da ban taɓa yin irinsa ba.
BONUS! BONUS! BONUS!!!
Ina makaranta kuma ma'abotan son littafan soyayya ko kuma na tsafi? To ku zo MRS SADAUKI ta yi muku gwanjon Books ɗinta akan farashi mai sauƙi,duk book ɗin 500 za ta bar muku shi ne a 300 kacal,wanda kuma yake 700 ko sama da haka za ku same shi a 500 kawai .Me kuke jira kawai ku tuntuɓe ta WhatsApp +22795045822. Domin ku kwashi garaɓasar.
[26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
14
Sai da Zainab ta ci kuka ta ƙoshi sannan ta shiga toilet.Tana shiga ƙarƙashin shower tunaninta ya soma nuna mata ga HAROON nan tsaye tare da ita suna wanka tare da wasanni irin na ma'aurata.Murmushi ne yayi nasara bayyana a kyakkyawar fuskarta wacce a ɗazu take shimfiɗe da baƙin ciki.Tamkar wata zautata haka take murmushi na wasar ruwa da niyyar nan HAROON ne take watsa ma su haɗi da yi masa shagwaɓa.Towel ta ɗaura ta fito ,sai ta tarar da Inna zaune bakin gado.Ta ƙara sakin ranta kafin ta ce “ Inna?”
“Ungo wannan ki sha,su kuma waɗannan ki dinga zuba a abinci kina ci yaji ne” cewar Innar tana mai miƙa mata kofi.Karɓa ta yi ta zauna tare da yin Bismillah ta soma shan madarar har ta shanye,sai da Inna ta ƙarara jadadda mata kar ta saki ta yi wasa da su kafin ta fice.Ita kuwa tsaf ta shirya cikin riga da wando na bacci ,ta yi sallar isha'i sannan ta zauna ta soma duba takardun jarabawar da ta yi wa ɗalibanta.Sai dai sam hankalinta ya kasa kwanciya sai aukin tunanin HAROON ,wayarta ta ɗauka ta kira Ammy bayan sun gaisa sai ta yi shiru.Can dai ta ce “ ina HAROON ?”
“Yana ɗakinsa,ko na baki shi?”
“A'a turo min dai lambarsa” sai kuma ta yi saurin kashewa tana dafe saitin zuciya haɗi da waro ido.“ Zainab mi kika yi haka?” ta tambayi kanta,ƙarar shigowar saƙo ta ji da sauri ta duba sai ta ga lambar ce aka turo mata sai da ta yi ta kallon lambar kafin ta yi saving da “ NAWAN” sai ta ɗora love daga ƙarshe.
Data ta kunna tana addu'ar Allah sa yana WhatsApp,tsawon lokaci kafin a nuno mata lambarsa mai ɗauke da hotonsa da Ammy su duka biyun suna murmushi.Da sauri ta ɗauki hoton sai ta yanke daidai nasa kawai ta tsura masa ido can kuma ta rungume wayar tana mai jan numfashi.Duba takardun da ba ta yi ba kenan ta je ta haye bed,MP3 ɗinta ta kunna ƙira'ar Sudais ta soma tashi tana biyar karatun tana kallon hoton HAROON a haka bacci ya ɗauke ta.
Washegari sai da ta tsarkake jikinta kafin ta gabatar da sallah saboda mafarkin da ta yi.Bayan ta gama ta yi shara da gyaran ɗaki sannan ta ɗumama abincin kari,sai kuma ta je ta yi shirin makaranta.Cikin ƴar ƙaramar kula ta zuba abincinta kafin ta yi wa Inna sallama,sai da ta zo bakin titi sannan ta samu abin hawa .Tana isa makaranta ɗalinta suka fara gaishe ta ita kuma ta wuce cikin aji,sai a lokacin ta ci abincinta cike da tunanin mafarkinta na jiya.Sai da ta yi da gaske sannan ta hakice tunanin HAROON daga ranta ta gabatar da darasi wanda shine ya zama na ƙarshe.Tana komawa gida aka shafa mata lalle,don dole ta haƙura tuni kuma aka fara shirye-shiryen biki kamar yadda abin ya zo mata a bazata haka su ma dangin da abokai amma duk da haka sai da aka fitar da anko.Har aka kawo lefe aka yi ɗaurin aure ko sau ɗaya Sheikh Ali bai kira ta ba haka ita ma ta share shi ko saƙo ta kasa tura masa.Yanzu ma da ake ta hidimar biki babu abin da take sai tunanin da ya daɗe da aurenta,na masoyin da igiyar aure ta yi mata iyaka da shi .Da zarar ta tuna cewa yau ɗin nan wani zai karɓe budurcinta sai hawaye su yi ta mata zuba,mutane kuwa tunaninsu kukan rabuwa da Inna ne kasancewar ita ɗaya ce tal ta rage musu a duniya duk ƴan uwanta sun rasu tun suna jarirai.
Har aka yi kiran sallah magrib Malama Zainab na kuka,da aka ce ta je ta yi wanka domin shirin kaita ɗakinta ji ta yi kamar ta fasa ihu ta yadda kowa zai fahimci tsananin damuwar da ta luluɓe sirrin zuciyarta.
Da ta yi wankan sai da ta yi sallar isha'i sannan mai kwalliya ta soma yi mata simple make-up ba irin tarkacen nan ba.Doguwar rigar less fari sol ta saka sannan ta ɗora alkyaba sama a haka ma sai da aka ƙara ɗora mata darar amare.Sai da aka yi hotuna da bidiyo da abokan arziki kafin a ƙara yi mata wata nasihar,daga nan aka ja ta zuwa can waje inda motocin da ango ya turo suke jira.Banda kuka babu abin da Malama Zainab take yi amma hakan bai hana aka kai ta ɗakinta ba,har aka gama addu'a kuma ba ta buɗe fuskarta ba.Nan mutane duk suka watse yayi sauran ƙawarta guda tal Hafsat wacce sai yanzu ta samu damar yi wa Zainab ɗin nasiha “ kukan nan ya isa haka don Allah! Abin da muke ta jiran ranar nan amma ta zo sai kuka kike”
Malama Zainab ta buɗe luluɓin ta ce “ Hafsat tsoro nake ji,wallahi zuciyata kamar za ta fashe don fargaba don Allah ki taimaka min ki bani shawarar da zan yi amfani da ita wacce za ta hana Sheikh ya kusance ni”
Shiru ta yi kafin ta ce “ caɓɓɓ! Batu wuya,gurguwa da aure nesa! Amma kin san wannan ba mai yiyuwa ba ne,wallahi sai ya kusance ki sai in magani bacci za ki basa ya sha” da sauri Malama Zainab ta ce “ yawwa ko hakan yana yi,don Allah je ki karɓo min ” sai ta zuge zip ɗin jakarta ta bata kuɗin,sai da Hafsat ta yi ta juya kuɗin kafin ta fita ta je ta siyo mata sai a lokacin hankali Malama Zainab ya kwanta.Babu jimawa kuwa ango ya shigo tare da rakiyar abokansa,bayan sun gama tasu nasihar Hafsat ta bi su don su sauke ta gida.
Ido Sheikh ya tsura wa Malama Zainab wacce tun da suka haɗa ido sau ɗaya ta sunne kai.Ya ja wata ajiyar zuciya kafin ya ce “ amincin Allah ya tabbata ga ma'abociyar ado da kyawu”
Dakyar ta amsa masa da “ wa'aleykum Salam!” sai hawaye shaaa,ya kamo dukkan hannuwanta ya sauko da ita daga bed ɗin yana mai cewa “ mu je ki yi alwala”
“Ka bari zan yi ni ɗaya” ta furta,sai ya bar ta ɗin ta shiga toilet ta ɗauro alwala bayan ta fito shi sai ya shiga.Da sauri jikinta na rawa ta ɗauko maganin baccin ta je buɗe ledojin da ya shigo da su ta zuba maganin cikin lemu sai dai aka yi rashin sa'a tuni Sheikh ya fito daga toilet ya ga kwalbar sirop ɗin kuma ya fahimci na mene ne.Yayi saurin komawa toilet ɗin ya bata lokacin da za ta yi rashin gaskiyarta ta gama.
Yana fitowa a karo na biyu ya sakar mata murmushi kamar bai ga komai ba,ya ja su sallah bayan nan yayi musu addu'o'i ya miƙe ya ɗauko ledojin da sauri ta karɓe ta ce “ bari na zuba mana” bai ce komai ita ta ɗauko plate da kuma kofinan shan ruwa.
Da ta zuba haka ta daure tana cin kazar shi kuwa tunani ne fal zuciyarsa ‘ mene ne ribar Zainab in ta bani maganin bacci? Wato ba ta son na kusance ta sai kace ba sadakina na biya na aure ta ba .Ko dai tsoro ne take ji? A'a ba shi ba ne inda shi ne da tabbas da magiya da kissa irin ta mata zata ɓulo min’ yayi tambayoyin duk a zuci amma ya kasa samo amsa,ya ƙure ta da ido lokacin da ta cika masa kofi da lemun ya karɓa a nan take kuma ya tuna da sunan HAROON wanda y'zuciyarsa ta yanke masa tabbas saurayinta ne.
Kofin ya kai bakinta yana mai cewa “ namijin kirki shine wanda ke fara shayar da matarsa kafin shi ya sha”
“A'a ka sha ni ma zan sha ai ga nawa nan sai na gama ci na sha” ta faɗa tana zarar ido, Sheikh ya saki murmushi ya ce “ in dai ba ki sha to ni ma ba zan sha ba sai da na sha ruwan pampo”
Malama Zainab na jin haka ta yi saurin karɓa ta sha ,da tunanin can su yi ta baccin su biyu .Shi kuwa Sheikh haka ya tsura mata ido har sai da ta shanye tass,ta cika masa kofi ta ce “ saura kai” ya laƙace mata hanci ya ce “ ai ni bana shan kayan zaƙi saboda suna da illa, dama dai wayo na yi miki ”
Tamkar wacce cutar sanƙarau ta kama haka ta sandare ta kasa motsi sai idonta da ke tsiyayar da hawaye tana da na sanin haƙa wa ramen muguntar da a ƙarshe ita ce ta faɗa .Ba a ɗauki lokaci ba ta ji fitilun idonta na disashewa,sai a lokacin ta miƙe da hanzari ta shiga toilet ta wanke fuskarta duk don kar bacci ya ɗauke ta sai dai ina tuni ta soma jin jikinta ma na saki.Da sauri ta fito kamar wata makauniya tana lalube, Sheikh ya je ya kamo ta tare da ɗora ta kan bed yana mai cewa “ shi yasa aka ce in za ka gina ramen mugunta ka gina shi gajere” sai kuma ya soma cire mata suturar jikinta.Sai da yayi mata zirr kafin ya cire nasa,jikinsa har rawa yake wurin ƙoƙarin haura gadon sai dai cak ya tsaya saboda yadda idonsa suka fara nuna masa ba daidai ba.Malama Zainab yake gani ta rikiɗe masa ta koma lakaɗeɗen maciji sai wani haske take fitarwa......
My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
[26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
15
Jikin Sheikh Ali ne ya ɗau wata irin muguwar rawa ganin amaryarsa wacce aka kawo masa yau ta rikiɗe ta zama lakaɗeɗiyar macijiya sai wani kaɗan bindi take.
Da gudu ya dawo falo ba tare da ya tsaya ɗaukar ko da wando ba ne,ɗakinsa da ya ware tun can a matsayin baraya ya shiga.Duk uban sanyin da ake zufa ce ke yi masa tsiyaya,tunani ya soma kamar wani zautace haɗi da suratai.“ Aljana ce aka kawo mini ko kuwa Jinnul ashiq ne da ita banda labari? Kaicona ni Ali ,ni kam banda rabo a duniya duk yadda nake mararin ganin wannan daren amma ya zo min ta wata mummunar siffa? Ai kuwa ba zan zauna da ke ba wallahi dole ki tafi gidanku” sam bai rumtsa ba haka yayi ta zagayen ɗakinsa yana tubka da warwara.
★HAROON
Tun bayan da Salima ta sha lemun zoɓon nan sai ya zamana a kullum kafin na fita aiki sai ta shigo gidanmu.Haka za ta yi ta kallona amma ta kasa yin magana,gefe guda kuma Laure mai aiki na ci gaba da bata maganin da Tony ya ajiye a kitchen.
Yau ma kamar kullum ina zaune ina duba takardun da nasa aka buga min irin wanda in kana son ganin likita patients ke cira,da sallama Salimar ta shigo.Ammy ba ta falo sai ni kaɗai,ido na zuba mata sai na ga ta soma kyarma yayin da bakinta ke ta rawa.Na fahimci kalmar so take son furta mini amma ƙarfin zuciyarta ya hana ta faɗa ,ni kuwa ta wannan hanyar ce kawai zan cimma ƙudirina a kanta.
Idonta ne ya soma kawo ruwa,da sauri na kawar da kai gefe ina jin wani haushin ta .Sai ta fita a guje tana