Showing 3001 words to 6000 words out of 43872 words

Chapter 2 - SURUKATA HORROR BOOK COMPLETE DOCUMENT 2025.txt

27 Dec 2024

3495

gidanku? Na so na leƙa amma Umma ta hana”


Nan take na ji abincin ya fita raina,na fidda hannuna tare da sunne kai.“ Mene ne wai?” Rahila ta tambaya da sauri.
Dakyar na bata amsa da “ aure za su yi min da ɗan hajiya Luba aminiyar Mama”


“Wai Luba ƴar bori ?”
Na gyaɗa mata kai kawai,Rahila ta wani ƙara gyara zama ta ce “ cab! Wane daga ciki to? Ai na ga duk suna da aure”


“Aliyu” na bata amsa .
“Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” ta furta tare da yin shiru,sanin wannan furicin musulmi ba su yinsa ne sai in wani mummunan abu ya faru na yi saurin ɗago kaina na dube ta.Hawaye na gani tanƙam a idonta,hankalina sai ya ƙara tashi na shiga tambayar ta “ Rahila lafiya?”


“Janiki har ƙiyayyar da Mama ke yi miki ta kai haka da har ta yarda ta aura miki mahaukaci?” ta yi furicin hawaye na silalo mata.
Na daki ƙirji na ce “ mahaukaci kuma?”
Ta jinjina kai ta ce “ wane ne bai san Aliyu nada taɓin hankali ba? Tun bayan dawowarsa daga mission ya haukace an ce wai ƙarar alburushi ce ta taɓa masa kwanya,amma wai a hakan Mama ke son haɗa ki da shi?”


Jikina ne ya hau rawa kamar wacce aka zubawa ruwan ƙanƙara har sai da Rahila ta riƙe ni gam,“ na shiga uku Janikiii?” ta furta cike da tashin hankali.Da sauri kuma na ture ta tare da miƙewa tsaye ko hannu ban wanke ba na fita a guje zuwa gidanmu .




Cak na tsaya ganin Hajiya Luba zaune dirshen kan tabarma ita da Mama suna tsara yadda bikin zai tafi har da zanen kayan katakai.
“Ke lafiya don ubanki kika wani shigo a firgice kamar mai figar ruwa?” Mama ce da wannan furicin ,hakan ya bai wa Hajiya Luba damar ɗagowa ta dube ni.




“ Ƴata Janiki ƙaraso ki duba da kanki ki zaɓi kalar gadon da za a yi miki ” shine abin da ta ce ,kamar mahaukaciya haka na ƙara kwasa a guje na fita a tsiyace.Gudu nake ban tsaya ba sai da na kai bayan gari sannan na samu wuri na zauna na haɗe kai da gwiwa na soma kuka kamar raina zai fita.




Tsawon lokaci ina a haka kafin na ji tsayuwar mutum a kaina,ban wani damu ba na ci gaba da kukana.


“ Ke ba ki gajiya da kuka?” na tsinkayo sautin muryarsa,da wani mugun sauri na ɗago na dube shi .Saurayin ɗazu da safe ne,yayi wanka ya sauya kaya sai baza ƙamshi yake.


Ruwa ya miƙo min a gora ya ce “ ungo wanke fuskarki sai ki goge ta da wannan ” ya haɗo min har da sabon hankici.Kamar wacce ya yi wa asiri haka na karɓa na buɗe murfin gorar,ina soma wanke fuskata sai na ji duk wata damuwata ta gushe.Na lumshe ido ina mai ci gaba da watsa ruwan da nake jin su tamkar ruwan tsarki da father na Coci ke bamu labari.




Ina buɗe ido yanzu ma wayam ban gansa ba,“ to ko dai aljanin ne kamar yadda Rahila ta ce?” na tambayi kaina a fili kafin na miƙe na kama hanyar gida.


Kiciɓis muka yi da Hajiya Luba a ƙofar gida,ta dubi fuskata kafin kuma ta maida idonta ƙurrr kan hankicin hannuna.Yadda ta ƙure shi da kallo yasa ni ma na kai dubana,sai na ga a tsakiyarsa an zana masa wani hatimin masarauta.


Da sauri na jimƙe shi ina mai cewa “ har za ki tafi?” ta sakar min murmushi ta ce “ eh ai mun gama zaɓen komai” sai kuma ta raɓa gefena ta wuce .Na bi ta da kallon mamaki,sai na ga ta waigo muka haɗa ido da sauri na shige cikin gida.




“ Tun da kin dawo daga yawon gantalin sai ki zo ki fidda masara a ruwa ki je ki kai niƙa,yau tuwon laushi za a yi” Mama ta faɗa tana mai ci gaba da ƙirga kuɗin hannunta,na kuma yi imanin cewa Hajiya Luba ce ta bata.




Sai da na je can ɗaki na adana hankicina biyu har da na ɗazu kafin na zo na soma aikin da aka sani.Bayan na fidda masarar na je na kai niƙa na dawo sannan na hura wuta,na ɗora tukunyata sannan na soma tankaɗe garin.
Haka na yi aikin ni ɗaya ko ijin wuta babu wanda yayi min har na gama,na je na yi wanka .


Ana kiran sallar magrib Abba ya shigo a gajiye ,ni ɗaya kawai na gaishe shi ya amsa kafin ya ce “ ki kai min ruwan wanka”
“Toh Abba” na faɗa tare da fita na kai masa,kayan da ya cire kuma na ɗauko na fito da su don na wanke Mama ta tsayar da ni.


“ Me za ki yi musu?”


“Wankewa zan yi” na bata amsa.
“Kin manta gobe Lahadi? To ki ajiye su zuwa gobe da safe sai ki haɗa da na yaran duk ki wanke”


“Amma Mama gobe akwai zuwa Coci” na faɗa murya na ɗan rawa don ban son yin abun da za ta hana ni zuwa wurin bautar Ubangiji.


“Gara da kika tuna min Kirista ta ƙwarai ai ni kin san bani sallah sai ke”


Da sauri na sunne kai saboda a duniya ina tsoron mugun kallon Mama,na gwammaci ta dake ni a kansa.Haka ina ji ina gani na mayar da kayan,da kowa ya fara cin abinci ni kasa ci na yi saboda tunani biyu na farko na mahaukacin da zan a haɗa ni aure da shi don na san Rahila ba za ta taɓa yi min ƙarya ba,na biyu kuma sai aljanin saurayi.A haka bacci ya ɗauke ni tun wuri,hakan kuma sosai na ji daɗinsa don tun kukan zakara na farko na tashi na fita na zuba ruwa a manyan robobi tare da fiddo kaya na hau wanki.




Ƙarfe takwas na yi na ajiye wankin na je na hura wuta na ɗora ɗumamen tuwo,sannan na so na ci gaba da wankina ina yi ina waƙoƙinmu na Kiristoci.




Yunwar da nake ji ya sa na zuba ɗumamen na soma ci da sauri-sauri ina yi ina kallon kayan da suka rage ina addu'ar Allah sa na ida kafin ƙarfe goma ta yi lokacin zuwa Coci.


“ Shegiya ɗiyar asara bayan haɗiya tuwo babu abin da ta iya,ji kamar ƴar yunwa yadda take cin abinci ” Mama ce ta faɗa wacce sai yanzu ta tashi daga bacci ta ɗauki buta ta shiga banɗaki.


Idona ne ya soma zuba kamar wacce aka zuba wa barkono sai na ji tuwon ya fita raina haka na ajiye shi na wanke hannu na ci gaba da yin wankin.




Bayan ta fitowa sai ta ɗora daga inda ta tsaya ta ci gaba da zagina tana aibanta ni har da ce min irin tsiya irin masifa da dukiyarmu ba ta tare komai ba.


‘Wace dukiya Mama ke magana?’ na tambayi kaina a zuci sai dai ban da mai bani amsa haka ta gaji ta bari don kanta.




Zuwa ƙarfe tara da rabi tuni na gama wanki,amma dole na jira ƴaƴan gwal suka yi wanka sannan ni ma na yi daga ƙarshe.Dukkanmu shirin zuwa Coci muke har da Abba ,kaya masu kyau duk muka saka kuma iri ɗaya.Ta wannan fannin ne kawai zan ce muke kusan ɗaya da su Ayo,domin duk lokacin da Abba zai sayi kaya to iri ɗaya yake saya mana mu duka huɗun hakan yasa duk kayanmu kusan iri ɗaya ne sai in Mama ce ta ɗinka take banbanta mana wasu kuma su kaɗai take saya ma banda ni.




“ Hodar me za ki shafa?” Mama ta katse min hanzari,sai na ajiye na dinga kallon yadda Ayo ke cancara kwalliya amma ni babu damar in yi.Haka na haƙura ,har mun fito tsakar gida Mama ta tsiro da wata sabuwar fita “ wai dama ba ki wanke nawa kayan ba?”




Ƙyafƙyaf da ido na yi ina kallon ta kafin na dubi Abba,ai kuwa ya tare min faɗa “ Sulvi ki bari in muka dawo ta wanke wai yaushe ma kika fara bata wanki ban sani ba?” ba ta basa amsa ba ta cillo baki gaba kafin ta rufe ɗaki.


Duk muka fita ,taxi Abba ya nemo mana muka shiga aka kai mu babban Cocin garin namu.Tuni ya cika da mutane haka muka je duk muka zauna kan kujeru,muna sauraren waƙoƙin da aka kunna kafin Father ya shigo duk muka miƙe muka gaishe shi.Ya bamu izinin zama kafin ya soma yin wa'azi daga ƙarshe kuma muka miƙe muka ɗora hannu a ƙirji tare da rufe ido muka soma yin doguwar sallah kamar yadda muka saba.Bayan haka kuma ya nemi cikin yara wanda zai rera masa sabuwar waƙar da za mu yi a sallar ƙarshen shekara,na ɗaga hannu don kuwa tuni na hardace ta.




“Janiki matso,zo nan ki yi mana” ya faɗa yana murmushi,na tafi da sauri na je gaban mutane ya miƙa min sifika na soma rera ta kamar dama can ni ce na tsara ta,komai daki-daki nake yinsa.Tunk mutane sun fara yin kuka saboda kalmomin da aka yi amfani da su na ban girma da shugabanmu Yesu Almasihu.Cikin masu kuka har da Mama ,da Father ya cire Cross ɗin wuyansa ya saka min aka shiga taɓi nan ma ta zo ta rungume ni karon farko da ta nuna wa duniya ni ɗin ƴarta ce kuma kamar ta yi alfahari da hakan .Sai na ji zuciyata ta yi min sanyi wani daɗi ya rufe ni,na ƙanƙame ta gam ni ma ina hawaye.




Ita ce ta ja hannuna muka koma wurin zamanmu, autarmu Natasha sai taɓa Cross ɗin take tana murmushin jin daɗi,bayan an tashi daga darasi sai muka fita aka soma cin girkin rana wanda Coci ke shiryawa duk ranar Lahadi.


Da muka fito kowa sai nuna ni yake yayin da wasu iyayen ke yi wa ƴaƴansa huɗuba da su dage su zama kamar ni.Cross ɗin Father aba ce mai matuƙar muhimmanci, wannan yasa kowa ke sha'awar ina ma shi ne.Bayan cin abinci duk a soma watsewa,muka fito bayan Abba ya nemo taxi Mama ta ce “ Za mu wuce gida Mamy don ganin ko lafiya yau ba ta zo Coci ba,dama mun jima ba mu je”
Jin an ambaci sunan Mamy yasa da sauri na ce “ Ni kuma zan koma gida na yi wankin kayanki” ta jefo min wani mugun kallo ta ce “ in ma dai don ki saci kuɗina na jiya ne kin yi ga banza na san ko nawa ne,kuma a tare za mu je” tana gama faɗa ta shige taxi su ma ƙannaina haka,dole ni ma na shiga aka kai mu gidan mala'ika wacce na gwammaci matsatsin Mama kan nata.Muna isa su Ayo suka shiga gidan a guje suna ƙwala kiran sunanta,ni kuwa ina daga baya na yi tsaye ina kallon yadda take wani shafarsu kamar jarirai tana murmushi muna haɗa ido kamar ta ga mugun abu ta gimtse fuska ta yi kicin-kicin har sai da Mama ta juyo ta dube ni.


“Ina wuni Mo...m ” sai kuma na kasa ƙarasa wa tuna gargaɗin da ta yi min na kar in ƙara kiran sunanta ita ba Kakata ba ce.Ba ta amsa ba sai ma masifa da ta hau yi “ me kuma wannan abar ta zo yi Sulvi?” ta faɗa wa Mama cikin masifa.


“Dama yau ne Father ya cire Cross ɗin wuyansa shine na ce bari na zo ita ta nuna miki ” Mama ta faɗa cikin sanyi,saboda duk masifarta da mugunta da baƙin hali to Momy ta dame ta ta shanye don dama can ita ta gado.




“To shi ne me? Cross ɗin ce ban taɓa gani ba?” Momy ta tambaya cikin masifa.
Ayo ta ce “ ta wuyan Father ce wann...” ta katse ta da cewa “ to shi Father Yesu ne? Ni dai gaskiya Sulvi ba ki kyauta min ba na faɗa miki sarai ina baƙin cikin ganin mayyar nan saboda ita na kamu da hawan jini,a duk in na yi tozali da ita kuma in bai tashi ba sai na yi ciwon zuciya .Na bar zuwa gidanki saboda kar na gan ta na jaza wa kaina masifa,da kuma na hana ki kawo min ita shine kika wani kwaso ta yanzu kika kawo min in ma bindiga zuciyata za ta yi ke ko oho”


Tun da Momy ta soma masifa na tsure ta da ido ina kallo yayin da hawaye ke yi min zuba,na rasa daga ina wannan ƙiyayyar ta samo asali amma yau ji na yi ina so na sani .Hakan yasa na je na zube gaban Momy tare da tambayarta “ me yasa kika tsane ni? Me yasa sai ni kaɗai kawai ? Su su Ayo me suka fi ni da kike son s...” sauran maganar ce ta maƙale min jin saukar langa a kaina a zafafe Momy ta bani amsa da “ na saba! Ki dube ki sannan ki dube su kin ga kun yi kama ne?”


Duk da uban zugin da goshina ke yi bai hana sauke idona kan ƙannan nawa ba ina kallo,tabbas ta yi gaskiya ba mu yi kama ba ta ko wace siga sai dai ko kaɗan tunanina bai kai ya hango gaskiyar da take son nuna min ba.Ina shirin yin magana Momy ta soma yin wani numfashi kamar za ta shiɗe da alamu ciwonta ne ya tashi......
[15/12 à 05:36] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽


Na
*Chamsiya Laouali Rabo*
```{MRS SADAUKI}```💫✍️


*FCWA* ☀️


*SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊


___________________________________


04




Hankalin kowa a wurin tashe yake,ya tabbata dai hawan jinin Momy ya tashi.Bakinta sai fitar da kumfa yake,tuni Mama ita ma ta biyo sahuna ta soma kuka.Dakyar na yi jarumtar fita na taro mai taxi,ai kuwa ina zuwa tuni gidan ya cika da maƙwabta a haka na daure na je na shaidawa Mama mai taxi na waje.Momy irin matan nan ne masu ƙiba, wannan yasa sai da wajen mutum shidda suka ciciɓe ta zuwa ƙofar gida,dakyar suka cusa ta a taxi suka wuce asibiti .




A ƙofar gida na tsaya ina kallon taxi ɗin har sai da suka ɓacewa ganina.


“Duk laifinki ne mai baƙin jini,mayya kawai da ba ta da halin ƙwarai.In Momy ta mutu sai dai ki bar gida don wallahi ba za mu zauna da ke ba muna ji muna gani ki kashe mumu Mama don na san ita ma baƙin cikin ganinki ba zai bar ta ba.Yanzu da kika yi tsaye nan ƙofar gidan ubanki ne?” Ayo ce ke yin magana,ta wani zo ta yi tsaye a gabana tana zagina.


Ƙanwata ce,amma banda ikon ko da ɗaga murya ne a kanta ballantana na dake ta.Ban ce mata kanzil ba na kama hanyar gidanmu,tunani kawai nake na tushen ƙiyayyar nan amma ban iya samun hujja ko da ƙwayar zarra ba ce.A haka har na isa gida,nan ɗin ma a rufe na tarar da shi dole na zauna kan dakali na ci gaba da yin kuka.




Ƙamshin turarensa ne ya fara kawowa hancina farmaki kafin shi ya bayyana a gare ni.Banda zarrar ɗagowa na dube shi,haka na ƙurewa inuwarsa da ido ina kallo hawaye na masu ci gaba da yi min zuba.




“ Janaki !” na ji sautin muryarsa mai kamar busar sarewa,na lumshe ido ina jin zuciyata na tsananta bugu.Haɓata ya ɗago wannan yasa na buɗe ido taram cikin nasa,ya sakar min murmushi kafin yasa hannu ya miƙar da ni.


“ Zo mu je ki ga wani abu” ya ƙara faɗa tare da yin gaba,kamar wacce ya tsafe haka na take masa baya.Mun yi ƴar tafiya kafin mu ɓullo cikin wata gonar mangoro,sai a wannan lokaci ya juyo ya kama hannuna ya zaunar da ni kan wani ƙaton icce shi ma ya zauna.


“ Me yasa kike kuka?” ya jefo mini tambayar.
“Babu komai ” na basa amsa.
“ Ki zama jaruma a ko yaushe,yin kuka a kowane lokaci yana taɓa lafiyar ido”
“To zan bari” na furta ina sunne kai.Ya miƙe ya je ya ciro mini wani ƙaton mangoro sannan ya jawo ruwa a guga ya wanke shi sannan ya miƙa min “ ki sha” na karɓa tare da ɗora haƙorana akan mangoron na soma sha.




“ Wane ne kai?” na samu kaina da furta wa .
“Prince Mahadi ” ya bani amsa tare da juyowa yana kallona,muka ƙure juna da ido.
“Amma ba nan garin kake ba” na sake faɗa.


“ Ɗan Nijar ne ni ” ya bani amsa kai tsaye,sai na waro ido na ce “ Nijar fa? To me ka zo yi nan ?”
“Wurin ki na zo mana”


Na ɗan saki murmushi jin wani zance,na ce “ kafin nan mene ne dalilin zuwan ka ƙasarmu?”


Sai da yayi min wani kallo mai kashe ruhi kafin ya ƙara jaddada maganarsa “ na ce miki wurinki na zo”


Kai na sunne ban ƙara cewa komai ba,sai ya kamo hannuna na ɗago da sauri ina kallonsa.Shi ma tsakiyar idona ya kalla na ɗan wani lokaci kafin ya lumshe su ya ce “in baki wani labari?”


Ina kallon kyakkyawar fuskarsa na basa amsa da “ eh ina so”


Sai ya soma da “ labarin masarauta ne,akwai wani Yarima da duk cikin ƴaƴan sarki ya fi sonsa,ba wai don bai da ƴaƴa maza ba a'a shi ɗin sunan mahaifinsa ya ci daɗindaɗa kuma wannan Yarima ya kwaso kaf halin Sarkin na rashin girman kai da girmama al'umma.Wannan abu shi ya jafowa wannan Yarima baƙin jini a wurin saurin danginsa waɗanda suke uba guda da shi.Kwatsam Yarima wata rana sai ya bar Masarautarsu ya je wani gari domin cika umarnin mahaifinsa na taimakon al'umma ba tare da sun nemi haka ba,magautan Masarauta sai suka fara tsara hanyar da za su bi su kawar da Yarima ba tare da ya sake saka ƙafa a Masarauta ba.Shi kuwa a ɓangaren Yarima haka ya dinga zagaye duniya yana bi gari-gari yana bada taimako har ya zo wani ɗan ƙaramin gari ,su kuma al'ummar yankin nan babbar matsalarsu ita ce rashin ruwan da za su sha. A nan Yarima ya soma fafutukar ganin ya samo hanyar da pampon ruwa zai tsaya a kowanne gida da ke cikin yankin.Aiki ne mai matuƙar cin kuɗi,wannan ya saka bayan kuɗin mahaifinsa shi ma dole ya ƙara da nasa.Kafin soma aikin sai da yayi wa mutanen garin bayani tiryen-tiryen, shugabansu ya amince aka soma yin aikin.To nan ne fa su kuma al'ummar suka dinga bada gudunmawarsu ta hanyar dafa abinci suna kaiwa ma'aikata,irin haka ne kwatsam sai Yarima ya ga wata baƙar mace kyakkyawa wacce ya ji ta kwanta masa a rai” yana kawowa nan sai ya buɗe idonsa,da sauri na sunne kai cike da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login