Showing 42001 words to 43872 words out of 43872 words
Chapter 15 - SURUKATA HORROR BOOK COMPLETE DOCUMENT 2025.txt
kuka,na ja tsuki tare da tashi na fito na shiga ɗakin da na ware domin duba maras lafiya da kuma masu son a yi musu aiki.
Kamar yadda na tsara sai ranar asabar kawai zan dinga yin aiki,yayin da kuma Iliya direbana zai dinga karɓar kuɗin ganina sai ya bai wa mutum takardar shaida.
Yau ce ranar farko da zan soma kamar yadda na sanar a sanarwar da nasa aka yi,amma mutane ne masu mugun yawa suka taru.Ɗaya bayan ɗaya suke shigowa ,in na karɓi receip/reçu ɗin hannun mutum ni ne zan sanar da shi sunansa da kuma matsalar da ta kawo shi .Dukkan bayanin kuma Tony ne ke sanar da ni komai,yanzu ma layi ya kawo kan wata budurwa da ta shigo.Ta miƙa mini takardar hannunta na karɓa ina dubawa “ sunanki Shukuriya,kina son a yi miki aiki kan Salele don ya saki matarsa ke ya aure ki saboda ba ki son kishiya sannan shi ma ya faɗa miki bai da tsarin yin mata biyu saboda bai da cikakken lokaci a matsayinsa na soja” na faɗa ina mai kallon ta,a zahiri fuskarta ce nake kallo amma a baɗini ruhinta ne abin dubana.Sam ba ta da mutumci ga kuma muguwar zuciya,uwa uba rashin imaninta yayi ƙasa sosai.Bayan na gama ganin qualitynta sai na saki murmushi,yayin da kuma muryar Tony ke ce min “ HAROON wannan ɗin ma ka riƙe ta gam da alamu za ta kawo ma ci gaba a tafiyarka ”
“Eh haka ne malam,shine abin da nake so amma nawa zan bada?” ta tambaye ni tana wani sunne kai.Zama na gyara ina jawo tasar da na zuba ruwan tsafina na soma shafa su,sai na ce “ kina da hoton shi saurayin naki?”
“Sai dai a waya kawai” ta bani amsa,na ce “ nemo ki miƙo min” da sauri kuwa ta miƙo min wayar don hotonsa ne kan screen.Saitin tasar ruwan na kara hoton tamkar mai yin scanning nan take zanen hoton ya zauna raɗam kan ruwan,cikin abin da bai kai minti biyar ba na gama kwashe duk wasu bayanansa.
Na ɗago na dube ta na ɗan wani lokaci kafin na ce ,“me yasa kika yarda da shi har kika basa kanki? Cewa yayi zai aure ki ko? Yana son ki? To duk ƙarya ce kawai yana wasa da hankalinki ne,jikinki kawai yake so.Amma zan yi miki aikin da sai ya aure ki,fatan za ki bi duk sharuɗan da zan gindiya miki?”
“Eh malam in dai zai aure ni koma mene ne zan yi”
“Ina so ki kawo min maniyinsa” na faɗa .
Ta waro ido tare da cewa “ ta yaya malam?”
“Abu mai sauƙi,in za ku yi mu'amala ki saka condom ta mata ko kuma shi ki basa ya saka kin gane dai ko?”
“To malam zan yi,sai me kuma?”
“Shi kaɗai nake buƙata za ki iya tafiya,in kin samo shi ko yau ne ki dawo” na faɗa ta yi godiya tare da fita,wasu suka ci gaba da shigowa a cikinsu babu wanda na yi wa aiki sai dai cutarsu da na yi ina kwashe taurarunsu ina adanawa kaina domin ƙarin power a haka har dare yayi.
Ina shigo wa falo Ammy ta soma yi min sannu tare da addu'ar ci gaba akan aikin alherin da na soma yau.Ko abinci ban ci ba na shiga ɗakina,madubina na ga yau yayi kicin-kicin da fuska alamun akwai matsalar da ke tunkara ta.
Tony na duba na ce “ mene ne wannan?” sai kuma na yi tsaye gaban madubin.
“Ana shirin kai abar ƙaunarka ne gidan Ali” Tony ya bani amsa,wani ɓacin rai ne na ji ya sauko min na ce “ fatan ka yi duk abin da ya dace?”
“ Kar ka damu na aika masa da aljani mai juye hasken ido”
Na saki murmushi,kafin na shiga na yi wanka.Kamar wata tv haka na zauna ina kallon idon Tony waɗanda suke fitar da wani jan haske ta cikinsu ne nake ganin duk abin da ke wakana.Tun daga ƴan kan amarya har lokacin da Malama Zainab ta zuba maganin bacci da yadda shi Sheikh ya fita a guje babu kaya jikinsa,raina fari ƙal tsabar murna haka na jawo Tony na rungume tare da ja mana blanket.
Tunanin Malama Zainab ne ya addabi ruhina,yayin da muguwar sha'awarta ta yi min kamun kazar kuku.A haka dai na samu bacci ya ɗauke ni sai dai bai yi nisa ba na ji ana kiran sunana.
“ HAROON ? HAROON ?” a hankali na soma buɗe idona da suka yi min nauyi,ban gani sosai amma ita muryar tabbas na san mai ita sai dai na manta a ina.
“ HAROON za su kashe ni,ka cece ni HAROON ban bar gida ba don cutar da ku sai don na zaɓa wa kaina rayuwa mai inganci ” muryar ta sake faɗa ,a wannan karon zumbur na miƙe ina kallon madubina wanda hoton Abbana ya fito raɗau kuma yana motsi idonsa suna zubar da hawayen jini.Ko kaɗan ganinsa a cikin wannan hali bai sa na ji tausayinsa ba sai ma tuna min da yayi da tsohuwar rayuwata ta baya a ranar nan wacce na tarar da shi yana haɗa kaya ban manta ba abu na farko da na ce masa shi ne “ Abba ina kuma zaka je da kaya?”
Ya juyo a zabure kafin kuma ya haɗe rai ya ce ,“ zan tafi na yi nesa da ku,zan auri yarinya sabon jini wacce zata kula da ni.Wacce ta san darajata da ƙimata,wacce duk abin da na nemo na bata ba ta raina wa sai ma dai ta ƙara da nata kuɗin.Na gaji da zama Ammynka,mugun halinta sai ƙara yin gaba yake,ta hana ni na ƙara aure na ƙi hannuwa shine ta tsiro da faɗuwar ƙarya wai jininta ya hau.To can ku ƙarasa rayuwarku ni ma zan yi tawa ”
Cike da takaici na ce “ duk ƙoƙarin da take yi na yin ƴar ƙaramar sana'a domin ciyar da kai ba ka gani ba? Abba a wannan yanayin ne za ka ƙara aure? Ka manta nan gidan haya ne muke? In ka aure ta ina zaka kai ta?”
“Ita ai ba matsiyaciya ba ce irin uwarka,ita shahararriyar ƴar kasuwa ce mai ji da kanta .Ga tsafta ga gayu,ga cima mai kyau ka ga sai an jima ni zan tafi”
“Abba ka sani muddin ka bar gidan nan ka fita daga sawun masu rai a wurina” na faɗa sanin yana mugun sona.Amma ga mamakina sai na ji ya ce “ wannan ta fi nono fari a wurina” yana gama faɗa ya fice ya bar ni ina zubar da hawayen takaici.
Yanzu ma gumin hawayen ne ya dawo da ni daga duniyar tunanina,na dubi Abba da ke haɗe hannuwa yana roƙona yafiya.Ban ce komai ba haka kuma ban motsa ba,Tony da ke kan jikina yayi tsalle ya kai wa Abbana farmaki a gaban idona ya kafa haƙoransa ga wuyan Abba .
Na zabura na sauka daga bed ɗin,sai dai ko kafin na isa ga madubin duk hotunan suka ɓace ya dawo normal.Duk yadda na yi ƙoƙarin shiga ciki kuma abu ya cuttura,daga can bakin ƙofa na ji ana buga min ɗaki .Ba tare da na tambayi wane ne ba na je na buɗe,Ammy ce tsaye duk jikinta rawa yake da alamu a tsorace take.
“Ammy lafiya kika fito da tsakar daren nan?” na tambaye ta.
“ Tsoro nake ji HAROON ,yau ashirin da biyu ga wata Yulin ”
“Eh mene ne ?”
“Zagayowar sallar Lugnasad ” ta faɗa tana kuka,“ Ammy ni ban fahimci komai ba”
“Ai dai kanka bai ciwo ko?” ta faɗa tana tallabo fuskata,na ce “eh bai yi” sai ta ja ajiyar zuciya kafin kuma ta juya ta fita tsaye na yi cike da mamaki,tabbas na ƙara yarda Ammy na ɓoye min wani sirri.
Ɗakin na rufe tare da jingina jikin ƙofa,ina shirin rufe ido na ga saukar Oga tsudum.Da sauri na isa gare shi ina cewa “Oga kai ne a daren nan?”
Fuska ya ƙara haɗewa kafin ya ce “ HAROON na taɓa wasa da kai?”
“A'a Oga”
“Amma mene dalilinka na ɓoye min gaskiyar kai wane ne?”
“Ban gane ba Oga me kake faɗa haka?”
“Dubi madubinka” ya faɗa tare da yi min nuni da shi,na kai idona nan na yi arba da wata siffa marar kyawun gani kai tsaye za a kira shi da aljani ko kuma dodo.Tsaye yake cikin iska yayin da wata mata ke yi masa kirari wutar na ɓulɓulowa ta ƙasa .
“Wace ce ita?” na tambaya.
“Amsar da nake son ji kenan daga bakinka,ita ɗin ahalinka ce maganar da nake yi ma yanzu rigima ce muke don ta ce kai ɗin nasu ne ” Oga ya faɗa .
Na girgiza kai na ce “ban taɓa shiga ƙungiyar asiri ba”
“Abbanka fa?” Oga ya jefo min tambaya,na ce “ba na tunanin yana ciki,domin kuwa da ace haka ne da talauci bai yi wa duniyarmu ƙawanya ba ,har ta kai ga Abba ya guje mu ya koma wurin wata mata wacce ba Ammy ba”
“Yanzu na fahimta, wannan ɗin matar mahaifinka ce! Ita ɗin baya ga tsafi da take kuma ƴa ce ga ƙungiyar asiri,mahaifinka ya bayar da jininka matsayin sacrifice .Ya zama dole ka nemo mafita tun cikin daren nan,sannan ka tambayi ita Ammynka ta baka labarin ainahin abin da take ɓoye ” yana gama faɗa ya fice.Na dafe goshi ina shirin shiga toilet sai madubina ya soma fitar da wani haske,da mugun sauri na dafe gaban goshina saboda wani abu da na ji ya caki wurin kamar mashi sai kuma na zaro ido ganin kamar giftawar Malama Zainab,can kuma mijinta ya bayyana hannunsa riƙe da lakaɗeɗen belt.Da mugun sauri na isa bakin madubin,na kai yatsana manuniya na dakatar da mijin nata ta hanyar furta kalaman tsafi sai ya zube nan a yashe kan tile.
★MALAMA ZAINAB
Tamkar gawa haka ta yi ta sharar bacci,ba ita ta farka ba sai ukun dare.Kanta ta soma jin yana ciwo,ta tashi dakyar ta zauna.Duk abubuwan da suka faru ne suka soma dawo mata daki-daki,sai ta duba jikinta sam babu alamar an yi amfani da ita amma kuma ga jikinta babu sutura.Toilet ta shiga ta yi wanka tare da ɗauro alwala,ta saka jallabiya tana shirin ƙabarta sallah ta ji ihun Sheikh Ali,da sauri ta fito ta soma tafiya har ta isa cikin ɗakin nasa sai ta tarar ashe mafarki ne yake. “Subahanallah Sheikh lafiya kake?” ta faɗa tare da ɗan bubuga gefen gadon,daidai nan ya tashi suna haɗa ido da ita ya tashi tsaye tare da kwaɗa mata mari ko kafin ta tambayi dalili ya rufe ta da uban duka.Dole dangin naƙi ce ta sa ta fito a guje,shi ma Sheikh ya ɗauki belt ɗin da ya gani kan gado ya biyo ta a tsiyace sai dai aka yi rashin sa'a kafin ya isa gare ta ya ji wani abu mai kamar tartsatsin wuta ya naushe shi .Yayi ƙara tare da faɗuwa timmm a ƙasa,hakan ya jawo hankalin Malama Zainab ta juyo sai kuma ta ga abin da ke faruwa ta dawo da sauri tare da zubewa tana kiran sunansa “Sheikh? Sheikh Ali ?” sai dai shiru bai ko motsa ba saboda babu numfashi a tattare da shi,ta ɗora hannu saman kai tana mai cewa “innallilahi wa'inna ileyhi raji'un!” daga wannan page ɗin ba zan sake fitar da wata ba,duk mai son ci gaba za ta biya 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank sai ta turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
Mu haɗe a PAID group 🤗
NB: daga lokacin da ya zama Complete 1k ne farashinsa.