Showing 33001 words to 36000 words out of 43872 words
Chapter 12 - SURUKATA HORROR BOOK COMPLETE DOCUMENT 2025.txt
ina kika samu mage?” na yi tambayar ina kallon magen sam na kasa ɗauke idona a kanta .
“Ka jira yanzu mai ita ta shigo ” cewar Ammy tana dariya,babu jimawa kuwa sai ga wata kyakkyawar budurwa fara tas da ita har da wani ƙaton baƙi a goshinta na sallah .Sallama ɗauke da bakinta sannan kuma ta gaishe da Ammy,kafin ta soma kiran sunan magen “ Mira! Mira! Zo mana” kamar uwa da ƴa haka magen ta je da gudu wurinta,ita kuma ta duƙa ta ɗauke ta kafin ta zo ta miƙawa Ammy key ta ce “ ga shi in Mama ta zo ki bata ni zan koma makaranta” Ammy ta karɓa ita kuma ta fita,da sauri na yi jarumtar tattara nutsuwata na share zancen magen na ci abinci.
Kiran sallar magrib aka soma,“ HAROON je ka yi alwala ka wuce masjid ni zan shiga daga ciki” cewar Ammy,a dole na amsa mata da “ toh” sai kuma na fita can harabar gidan.
Da hannu na yi wa Illiya alama da ya zo,da sauri ya ajiye butar da yake alwala ya zo jikinsa na rawa .“ Ga ni yalaɓai”
“Yarinyar nan da ta fita yanzu Mai mage wace ce ? Ka san ta ne?” na tambaye shi .
Ya ce “ Eh yalaɓai Salima ce ƴar gidan Yakubu soja tana karatu a babbar jami'a ne”
“Ina son ta ne,ka san yadda za ka yi ta yarda da hakan” na faɗa kai tsaye.
“Amma yalaɓai Malama Zainab fa?”
Har sai da ƙarar rawar zuciyata ta motsa jin an ambaci sunanta,na saki wani murmushi na farin ciki kafin na ce “ ita wannan ta musamman ce” sai kuma na bar shi nan na koma ciki.
ILLIYA POV
Bin bayan HAROON kawai yayi da kallo yana mamakin wane irin rikitacen mutum ne shi,a haka ya koma yayi alwala ya je masallaci.Har aka yi sallar isha'i yana ta tunanin hanyoyin da zai bi ɗin ya sanar da Salima,da kuma ya tuna zancen Yalaɓai na ya kai masa matarsa gobe sai hankalinsa ya ƙara tashi.Haka dai ya samu ya fito daga masjid ɗin ya je bakin hanya ya samu taxi ta kai shi can gidansa,yau ko motar bai tafi da ita gida ba kamar yadda ya saba.
Yana shiga kuwa ɗansa Abdul ya rugo yana tara masa hannu,sam ya manta bai shigo da komai ba kamar yadda ya saba musu ba.”Yi haƙuri Abdul na manta ban sayo ba ka bari har zuwa gobe” yana gama faɗa yaron ya fashe da kuka,hakan ya jawo hankalin matarsa Mariya ta fito tana kallon mijinta ta fahimci ba ƙalau ba,gaisuwar da ta yi masa ma dakyar ya amsa.
Ruwan wanka ta kai masa,haka ya je yayi ya fito ya zo ya shige can uwar ɗaka ya rabka uban tagumi.
“Baban Abdul” ta faɗa cikin Hausarta da ba ta dafu ba.
Ya zabura ya ɗago ya dube ta,sai kuma ya haɗe rai ya ce “ lafiya kike wani kirana haka?”
“Kai dai zan tambaya lafiya duk ka bi ka sauya haka?”
“Mariya haka ya dace a tarbi miji in yana cikin damuwa? Ko abinci fa ba ki bani ba” ya faɗa wannan karon ya sassauta murya.Ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce “ ka yi haƙuri bari na kawo ma” sai ta fita ta je ta kawo masa.Ya ce “ ina Abdul?”
“Ya gaji da kuka har yayi bacci ” ta basa amsa tare da zuba masa abinci a plate ya karɓa ya soma ci yana ƙare mata kallo,bafulatana ce ita kyakkyawa ba ta da ƙiba hakan yasa ƙirjinta har yanzu a cike suke kuma tsaye daram .
“Lafiya kake ta ƙare min kallo kamar yau ka fara gani na?”
“Kin san ke ɗin ce kullum kyau kike ƙarawa” ya faɗa tare da kashe mata ido ɗaya yana murmushi,ita ma dai ta ɗan saki ranta ta soma yi masa surutunta da wannan ta ɗan sassauta zuciyar Illiya har suka yi bacci,amma tsakar dare ya tashi a firgice saboda mummunan mafarkin da yayi.Sam kasa komawa yayi sai yayi zaune yana ta saƙa da warwara har garin Allah ya waye,suna tsaka da cin abinci kiran HAROON ya shigo wayarsa,gabansa ya faɗi rasss haka yayi ta kallon kiran har ya yanke wani ya sake shigowa amma shi ma ya ƙi ɗauka sai ana uku ne yayi ƙarfin halin tashi ya fita can tsakar gida sannan ya ɗaga idonsa na kawo ruwa ya ce “ yalaɓai ina zuwa yanzu nan zan kawo ta” yana gama faɗa kuma aka kashe kiran daga can ɓangaren.Illiya ya goge ƙwalla kafin ya dawo ɗaki,Mariya ta kafe shi da ido sai dai bai bata damar yin magana ba ya ce “ Ogana ne bai da lafiya yanzu nan aka kira ni,tashi ki saka hijabinki mu wuce”
Ganin yadda mijin nata ya shiga tashin hankali yasa ta bi umaninsa kawai,Abdul ta kimtsa ta goya shi sannan suka fito bakin titi ya tsayar musu da taxi ya faɗa masa sunan babban kamfanin da za su je.
HAROON
Da abu uku na kwana daren jiya,na farko soyayya da ƙaunar Malama Zainab,na biyu kuma son mallakar magen Salima,na uku kuwa shine son ganin matar Illiya . Wannan yasa gari na wayewa na yi wanka na shirya,shayin Ammy kawai na sha kafin na fito sai kuma na tarar Illiya bai zo ba na yi tunanin don kar ya cika umarnina ne ya ƙi zuwa wannan yasa na soma jera masa kira domin yi masa gargaɗi sai kuma ga shi ya bani tabbacin zai kai ta.
Ɗaki na koma na ɗauko key na mota,da kaina na yi draving na isa can kamfanina.Ko sauraren gaisuwar mutane ban tsaya ba na shige ciki,babu jimawa kuwa sai ga Illiya ya shigo shi da matarsa wacce idonta ƙurrr a kaina masu cike da mamaki da tambayoyi.
Kujeru na nuna musu ,ta kwance goyonta kafin ta zauna shi kuwa Illiya ya ma kasa zama da alamu jira yake ya ji dalilin zuwan nasu.
Rigar rashin mutumci na sake yaɓawa kaina kafin na ce “ Illiya karɓi yaron nan ku fita waje ina son yin magana da ita” jikinsa na rawa ya ɗauki yaron da tun da muka haɗa ido da shi ya soma kuka,Illiya ya je bakin ƙofa ya waiwayo yana kallona na banka masa harara da sauri ya fice ina mai ganin ƙwalla na zubo masa.
Daga inda nake zaune na baiwa ƙofar umarnin rufewa,da sauri ita matar Illiyan ta juya tana kallon yadda key ke murɗa kansa handle kuma na motsi.Tana juyowa ta gan ni a zaune kan table gabanta har ƙafafuwanmu na gugar na juna,cikin ido na dube ta na ce “ ki cire hijabinki”
Idonta ya kawo ruwa amma na san tabbas ba za ta iya musa min ba,haka ta cire shi nan na yi arba da siffarta mai ɗaukar hankali.Rabon da na yi mu'amala da mace har na manta, wannan yasa jikina ya ɗau rawa har ban san lokacin da na kai hannuna na zuge zip ɗin rigarta ba.Nan na yi arba da ainahin surarta,hawayenta da suke ɗiga sam ba su dame ni ba haka na yi mata sintiri ina shafar dukkan sassan jikinta.Daf da zan cimma burina na ƙarshe na ji sautin muryarta mai kamar tafasasshen ruwa,cak na tsaya ina sauraren amon muryarta wanda kuka ya gurɓata shi “ ka sani ni ma mace ce mai daraja kamar uwar da ta haife ka! Yadda baka son wani ya keta mutumcinta haka ni ma yarona da ke can waje yana kuka bai son a keta nawa” da sauri na yi baya ina dafe zuciyata ina kallonta ta soma mayar da kayan jikinta.Daidai nan na gama page na kyauta mai so sai ya biya 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank sai ya turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 .Kawai ki tura in na zo zan saka ki group,wacce ta san ba biya za ta yi ba ta yi wa girman Allah kar ki yi min magana.
Littafin MAFIYA labari ne ya cakuɗe da true life da kuma wanda na ƙirƙirar,sannan wannan duk shimfida ce ba mu ma shiga cikin zallar labarin ba.
Talla! Talla! Talla!!!
DULLAHZ CAKES AND MORE 💕
Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu,
Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki,
Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884
Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884
Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884
Call:09111648884
[26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
11
Tun da nake babu wata ƴa mace da na taɓa rabawa da kayanta kuma ban kusance ta ba sai wannan.Har ta kai bakin ƙofa na dakatar da ita “ keee!” ta wani juyo a firgice jikinta na rawa,idona na kafe ta da su ina son sanin ko tana ɗauke da wani sirri ne na daban amma ban gansa ba.Na dafe goshina cike da takaici kafin na kwashi kayana na shige Toilet,gaban shower na je na tsaya na buɗe shi duka ruwan na soma sauka a kaina tsohuwar rayuwata ta baya ta fara zuwar min kamar wanda aka kunna wa video.
Wannan labari yana ɗaya daga cikin mafi ruɗani da na samu. Yana da gami da madubi. Ba wai kawai kowane madubi ba, amma ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da ake ganin suna ɗaukar wani abu fiye da kawai tunaninsu.
A ƴan shekarun da suka gabata, na ci karo da wata kasuwar kayan gargajiya a wani gari da nake wucewa.Kasancewar ni ɗin direban babbar mota ne,ina son yawo a cikin waɗannan wuraren koyaushe suna samun abubuwa masu ban sha'awa tare da labari. Ina zagawa wani tsohon madubi ya kama idona tamkar mayen ƙarfe. Yana da ban sha'awa, tare da firam ɗin katako da aka sassaƙa, an ƙawata shi da ƙira. Wani katon madubi ne, kusan girmansa kamar ƙofa, ga fuska kamar ya ɗan dusashe da shekaru.
Dillalin kayan tarihi ya gaya mani cewa wannan madubin ya fito ne daga wani tsohon gidan da aka yi watsi da shi kuma ya kasance a wurin shekaru da yawa, ba tare da wani ya so ya saya ba. Ya ce wasu mutane in sun ga wannan madubin suna cewa “yana tattare da damuwa” ba tare da sun iya bayyana dalilin da ya sa ba.
Tabbas, a matsayina na mai son abubuwan bazata da na ban mamaki sai na yanke shawarar saya. Na kai shi gida da tunanin zai dace da duniyata.
Tun daga ranar farko da na rataye shi, na ji wani abu mai ban mamaki. A duk lokacin da na wuce nakan ji kamar tunanina yana kallona ta wata hanya mai ban mamaki. Ba kamar wani tunani mai sauƙi ba, amma kamar wani sigar ni a cikin madubi yana kallona ta baya, ko da kuwa bayan na kawar da kaina.
Da farko na ɗauke shi a matsayin gajiya ce da na yi, tunanina kawai hankalina ne ke wasa da ni. Amma da yawan kwanakin da suka wuce, wannan jin yana ƙara tsanantawa. Abin da ya fara damuna da gaske shine lokacin da na lura cewa tunanina yana motsawa.
Wata rana da yamma, ina wucewa gaban madubin , sai na ga tunanina ya ɗan juya kaina kafin in yi haka. Tsawon daƙiƙa ne kawai, amma a fili yake. Har na yi gwaji, ta wurin tsayawa a gaban madubi ina motsi a hankali. A wani lokaci, tunanina ya lummm a gabana ya kasance da dabara irin ya ɗan jinkirta abin da na yi .
Na fara firgita sosai, amma na gaya wa kaina tabbas tunanina ne. A daren nan na yi bacci a kan kujerar falo, kuma madubin yana can hangen nesa na. Da tsakar dare na tashi ba zato ba tsammani, sai na ji wani yana kallona lokacin da na buɗe idona, sai na ga inuwa a bayana a cikin madubi, kamar a mafarki amma gaske ne.
Na juyo ba zato ba tsammani sai dai ba komai babu kowa a cikin ɗakin .Zuciyata ta fara bugawa ba zato ba tsammani na sake duba madubin, kuma wannan lokacin ya fi muni,inuwar ba ta da kyau, yana can a cikin tunanina can tsakiyar madubi amma ba a cikin ɗakin ba. Ita wannan inuwar irin siffata ce da ita amma jikinta duk ko ta ina jini ne ke fita,yadda na ƙure ta da ido ita ma haka take kallona babu motsi. A yadda ake son na fahimta wannan na cikin madubi ni ne da kaina kamar yadda kowanne mutum in ya tsaya a gaban madubi zai ga kansa,amma ni nawa ya sha banban da na sauran.In na yi motsi shi na cikin madubin bai motsa wa yana nan a daskare kamar saƙaƙo,in kuma ni na tsaya ɗam ba tare da na yi wata alamar motsi ba sai na ga shi ya motsa. A firgice na bar ɗakin a wannan ranar ban dawo ba sai da safe.
Washegari, na yanke shawara mai tsauri. Na rufe madubin da farar ƙatuwar zanen gado. Tun daga wannan lokacin, ya kasance a can a ɓoye. Amma kuwa duk da na rufe shi har yanzu ina jin kasancewarsa. Wani lokaci ina tsammanin ina jin ƙararrakin hayaniya suna fitowa daga wajensa kamar surutu da sautin faɗuwar wani abu kamar tasa ko kuma an cilla dutse a rijiya.
Kamar wanda aka yi wa dole haka kuma na ƙi fitar da madubin,na ci gaba da rayuwa da shi har wata baƙar rana ta zo wacce ba zan manta ba.Ina kwance ina baccin bayan la'asar aka kira ni a waya Ammyna ta zame jiki ta faɗi babu hannu babu ƙafa ga kuma zuciyarta ta kumbura.Ko wanke fuska ban yi ba na ɗauki makullin mota,a ƙa'ida sai jibi zan yi jigilar dabbobi kamar yadda tsarin yake in na zo asabar sai kuma ranar Laraba zan koma can gida Agadas.Kwana ɗaya da wuni na yi a hanya kafin na isa,direct kuma asibitin da aka sanar da ni take na nufa,a yadda na tarar an banzatar da Ammyna sai na ji takaici ya rufe ni don babu wata kulawa ta musamman tsabar wulaƙanci ma kan tabarma take ba a gado ba.
Ba ta iya yin magana ,bakinta ya juye yawu na yi mata dalala,motsin kirki ma ta iyawa sai idonta da ta kafe ni da su masu cike da rauni da neman agaji a gare ni.
A wancan lokacin da na tambayi nurse dalilin ƙin bai wa mahaifiyata taimako yadda ya kamata sai ce min ta yi “ sai kun biya kuɗi na gwaje-gwaje,na gado,da kuma alluran da za a dinga yi mata tausar ƙafarta da ta sandare ” ƴan kuɗaɗen da na samu waɗanda sun kasance na uban gidana ne da su na yi amfani na bayar aka ba Ammy gado ,sannan da taimakon da ba a rasa ba.Dandanan goshinta ya fara fitar da zufa sai bacci,ganin haka sai yasa na wuce can gidanmu domin yin wanka.Mahaifina na tarar wanda shine silar duk halin da Ammy ke ciki,kayan jikinsa na tarar yana haɗawa da alamu garin zai bari.
Ina kawo daidai nan na kashe shower saboda a duk lokacin da nake tuna rayuwata babu gaɓar da na tsana irin ta Abbana.Cike da takaici na kimtsa na fito na zauna kan kujera,ina jin tabbas ya zama dole na mallaki matar Illia direbana.
ILLIA POV
Babu wani tashin hankali da ya taɓa shiga wanda ya wuce wannan,babban takaici ne yau ace ya miƙar matarsa ta aure ga wani namijin da yayi imanin cewa imani bai wanzu a ƙirjinsa ba ballantana ya sa ran ba zai keta haddinta ba.
Kamar wani marayan uwa da uba haka ya takure jikin katanga ya rungume Abdul gam a ƙirjinsa wanda tuni ya gaji da kuka yayi bacci,ido kawai Illiya ya ƙura wa ofis ɗin HAROON tunani iri-iri na ta zuwar masa .Ya san halin Mariya da tsoro tun a tashin farko za ta sallama kanta ko da kuwa bai yi amfani da tsafinsa ba.Yana nan jibge kamar kayan wanki ya ga ta buɗo ƙofa ta fito,da sauri ya nufe ta yana cewa “ me yayi miki?” ba ta basa amsa ba ta karɓe ɗanta ta yi gaba.Ya take mata baya yana kiranta,duk mutane na kallonsu amma ta ƙi tsayawa haka suka dinga yin tafiyar ƙasa su biyu har suka isa gidansu duk da kuwa uban nisan da ke da kwai.
“ Mariya mene ne haka? Ina tambayar ki amma kin yi shiru” Illiya ya faɗa bayan sun shiga ɗaki.
Ta dube shi da idonta da suka yi jajur tsabar kuka ta ce “ abin da ka kai ni dominsa shi yayi! Wato Illiya ban taɓa sanin cewa baka ƙauna ta ba sai yau amma ka sani wallahi na gama aurenka!” sai kuma ta wuce can uwar ɗaka ta soma haɗa kayanta.
Shi kuwa zaman ƴan bori yayi jin HAROON wai kusance ta,kukan baƙin ciki ya soma yi kamar ransa zai fita yana da kishi sosai amma yau yana ji yana gani an ɗauki abunsa mafi daraja an tozarta shi .Wata irin tsanar HAROON ce ya ji ta ɗarsu a ransa,ya ƙudiri aniyar zai yi masa aiki amma kuma tabbas shine ajalinsa......
My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
Talla! Talla! Talla!!!
DULLAHZ CAKES AND MORE 💕
Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu,
Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki,
Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884
Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884
Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884
Call:09111648884
[26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: