Showing 9001 words to 12000 words out of 43872 words

Chapter 4 - SURUKATA HORROR BOOK COMPLETE DOCUMENT 2025.txt

27 Dec 2024

3502

ƙaru na buɗe baki da niyyar yi mata rantsuwa amma marin da ta sauke min yasa na yi yadda ta ce.Na rumtse ido gam,ina jin kamar zuciyata za ta fashe tsabar baƙin ciki yadda Mama ke duba ni har da gwada saka min yatsa ta yi kafin ta fita ta bar ni nan cikin banɗaki ina marayan kuka.


Sai da na yi mai isata kafin na miƙe na fito,Ayo ta bi ni da kallon tausayi kafin ta je kusa da Mama tana cewa “ Mama kin san halin Janiki ba za ta taɓa aikata abin da kike zargi ba,kuma sam hakan da kika yi gaskiya bai dace ba”


“Ki rufe min baki ko na ci mutuncinki,so kike na zuba mata ido ta je ta lalace?” Mama ta faɗa .


Madafa na shige ban ƙara jin abin da suka tattauna ba,haka na yi musu girkin duk raina a dagule.Bayan na gama na ɗumama ruwa na je na yi wanka,amma duk da haka zazzaɓin da nake guje ma sai da ya saukar min.Haka na je na shige ɗakinmu na kwanta kan katifata na duƙunƙune na soma rawar sanyi,har aka kira sallar isha'i ban fito ba.Ina jin muryar Natasha na cewa ga lemu da ayaba da Abba ya kawo amma ban iya ɗaga kai na dube ta ba ballantana na karɓa,tana fita kuma Ayo ta shigo tana tambayata.


“ Janiki ba ki sha ne?” dakyar na buɗe fuskata na ce “ banda lafiya ” sai ta matso kusa da ni ta zo ta ɗora hannunta kan wuyana kafin ta fita.Babu jimawa shi ma Abba ya shigo kafin ya ce na tashi ya bani magani.Haka ya ɗebo ruwa a kofi ya bani na sha cike da tausaya wa ,sai dai kamar ma an ƙara wutar ciwon sai abin ya ƙara ƙamari.Da gudu na fita na soma kelaya amai kamar raina zai fita,na zube nan cikin rumfa ina jan numfashi.




Ina jin Mama na masifar ita dai ba da kuɗinta za a kai ni asibiti ba,amma a haka Abba ya fito yasa na wanke baki ya kai ni asibiti.Ina tsoron allura hakan yasa sai da ya riƙe ni sannan aka yi min,bayan mun dawo ne na samu na ci ayabar sai na kwanta na lumshe ido babu jimawa bacci ya ɗauke ni.




Washegari na yi ranar tashi,ko da na farka har sun share ɗakuna da kuma tsakar gida.Girkin ma sun ɗora,haka na je na gaishe da Mama da Abba shi kaɗai ya amsa ita kuma banda saƙon mugun kallo babu abin da ta yi min.




“ Munafuka yanzu da aka gama aikin gida ai ga shi can ta fito,kuma wallahi ba za ki je coci ba gida za ki zauna” na tsinkayo furicin Mama ina ƙoƙarin shiga banɗaki.Daga nan ina jin yadda Abba ke cewa “ daga yau ba ta yi aikin ba shikenan ta zama munafuka? To nan gaba ayyukan gidan raba su za a yi ita da sauran danginta su rinƙa yi a tare,wankin kaya kuma kowa ya wanke nasa”
Ina jin Ayo na cewa “ Abba mu da muke zuwa makaranta”
“Ai ba ku yin ta maraice sabka guda kuke yi,don haka in ta yi aikin safe ku sai ku yi na maraice ke da Sarah.Ita ma da zarar an bani kuɗina zan mayar da ita makarantar ta ci gaba da karatunta”


“Auren fa?” wannan karon Mama ce ta yi maganar.
“Aure ai bai hana karatu”
“Amma dai ka san yanzu ta kusa shekara goma da barin makaranta ko? To wane aji za a saka ta?”
“Daga inda ta tsaya za ta ci gaba,ai shi karatu bai da girma ko ke yanzu kika ce kina son komawa sai na mayar da ke” Abba ya faɗa cikin tsokana.


Daidai nan na fito daga banɗaki sai na ga Mama na murmushi muna haɗa ido kuma ta gimtse fuska tare da kawar da kai.Ni kuwa ji na yi kamar na je na rungume Abba tsabar farin ciki,dama can mugun hali na Mama yasa na bar zuwa makaranta kawai don na kula da su Ayo ita kuma ta fice wajen kasuwancinta wanda a ƙarshe jarin ya karye ta zauna gida.


Abincin kari muka ci,yau na ci na ƙoshi saboda a gaban Abba ne.Bayan haka aka soma shirin zuwa Coci ni ma na shirya kuwa sai dai yau ba kaya iri ɗaya muka saka ba saboda banda irinsu su da Mama sai suka yi anko.
Da muka fito fuskar Abba ta nuna bai ji daɗin yadda aka ware ni ba,amma sai bai ce komai ba muka fita waje har muka shiga taxi Mama ba ta yi ƙorafin don me na biyo su ba.
Da muka je can coci sai na hangi Momy,gudun fitina yasa na zauna a nan gaba yayin da su kuma suka je can wurin ta.Da lokacin yin sallah da addu'a yayi haka na lumshe ido na ta kai kokena wurin Yesu cike da yaƙini.Bayan nan aka soma gwajin fasaha ,tambayoyi ne akan rayuwar Yesu duk wanda ya sani sai ya ɗaga hannu ya bada amsa,yau ma kamar waccan satin na fi kowa bada amsa wanda a ƙarshe har Father ya buƙaci na je can kan dandamali.
Lasifika ya bani tare da cewa na bada tarihin Yesu,ai kuwa haka na soma zayyanowa har ina haɗawa da wasu baitoci.Liƙen kuɗi aka soma yi min kamar ba gobe,Sarah ta zo tana tattare min har na kammala shi ma Father sai da ya bani kyauta ta musamman tare kuma da yin selfie da ni.




Bayan an tashi dukkan kuɗin da na samu sai na miƙawa Abba ,ina ganin Mama kamar ta fashe da alamu ta ji haushin haka.Da muka isa gida kuwa Abba ya sake jaddada alƙawarinsa na mayar da ni makaranta,a ranar ya sayo min uniform da kuma Books da duk abin da zan buƙata.




Washegari sai da na yi aikin da na saba yi kafin na yi wanka na shirya.Mama dai sai cika take tana batsewa amma wannan bai hana Abba kai ni makaranta ba,duk da ina da shekaru dayawa hakan bai dame ni ba musamman da na ga akwai wanda suka kai ni da girman jiki.Ina da ilimina dama,hakan yasa sosai nake fahimtar abin da ake koyawa wasu kuma dama tuni Sarah ta koya min su.Kamar a mafarki nake jin kaina haka na yi shawagi a filin makarantar da muka fito shan iska,abinci ma kasa ci na yi saboda shauƙi har muka taso na nufo gida.


Ina shigowa Mama ta ce “ sai ki ɗauki cefane ki ɗora girki tun da baƙin ciki ya rufe miki ido sai da kika koma makarantar” ban ce mata komai ba na ɗauki cefanen sai da na cire uniform na je na hura wuta ,babu jimawa na haɗa jalob ɗin taliya.Na sauke tukunya na shiga wanka,bayan na fito na ɗauki kasona wanda Mama ta zuba min na ci na wanke hannu ba don na ƙoshi ba.Amma na share tare da ɗauko kayan makaranta na soma dubawa,sallamar Hajiya Luba ta saka gabana faɗuwa.Kamar yadda na yi tunanin kuwa zancen auren ne ya ƙara kawo ta inda take shaidawa Mama ranar juma'a za kawo lefe kenan sai ta sanar da dangi waɗanda za su tarbi kaya.Tun kafin ta fita kuwa Mama ta soma kiran wayar na kusa da ita tana sanar da su za a kawo lefen Janiki,har wani murmushi take tana nuna tsantsar farin ciki wanda ni kuma tuni zuciyata ta aminta Mama ba za ta taɓa yin farin cikin akan abin da zan amfani da shi ba sai dai in wanda zai cutar da Ni ne.....
[19/12 à 04:41] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽


Na
*Chamsiya Laouali Rabo*
```{MRS SADAUKI}```💫✍️


*FCWA* ☀️


*SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊


___________________________________




06


Shirye-shiryen kawo lefena bai sa na ƙi zuwa makaranta ba,sai dai sam na kasa nutsuwa na yi karatun yadda ya kamata.Tsorona guda shine kar bayan auren mijin da za a aura min ya hana ni karatu, wannan na samu Abba na kai masa kokena ya kuma alƙarwanta min abu ne da ba zai taɓa faruwa ba.


Ranar juma'a ce suka tsayar don kawo lefe,yau ta kama Alhamis tuni kuwa dangin Mama sun cika gidan sai gyaran kayan da za a yi miya da su gobe suke.Abin da ya fi ban mamaki kuwa bai fi yadda na ga ana jiƙon ruwan lalle ba,wanda a al'adar garinmu ranar da aka ɗaura aure kawai ake yi wa amarya wanka da su.Amma sai na yi shiru na ja bakina,ina rakuɓe na kasa cin komai sai ga Rahila ta shigo.Kusa da ni ta zauna,kamar yadda ba na farin ciki da wannan auren ita ma haka.


“ Ashe har da ɗaurin duk za a yi a goben?” Rahila ta faɗa ,sai na yi rau-rau da ido amma na kasa cewa komai yayin da ita kuma ta ci gaba da cewa “ an ce gobe bayan sallar juma'a za a ɗaura a masallaci,irin na shari'ar Muslunci za a yi tun da wai mahaifinki ma musulmi ne” sai a lokacin na lumshe ido kafin na maimaita kalmar “ musulmi?” cikin wata irin murya Rahila ta ce “ eh wai! Kenan Abba ba shi ya haife ki ba?” na buɗe idona hawaye na masu surnano min na dubi Rahila da kyau na ce “ ni ma ban sani ba,ƙila hakan ne.Amma ke wa ya faɗa miki?”


“Umma na ji suna yin hirar ita da ƙanwar Hajiya Luba ” ta bani amsa,sai na sunne kai ina wani irin huci.“Mahaifinki Balarabe ne wai,kuma fari ne tasss kamar ke,sai yanzu ni ma nace ai sai larabawa irin wannan gashi naki tubarkallah ”


“ Kaina yana ciwo Rahila ki taimaka min da magani” na furta tare da yin kwanciya.
“To bari na je na siyo” tana fita na je na buɗe jakar kayana na ɗauko hankicin da Prince Mahadi ya bani na soma goge hawaye da shi ina shaƙar ƙamshinsa.Ba ta wani jima ba ta dawo ta kawo min maganin,na karɓa na sha sai kuma duk muka yi shiru.






Mama ta shigo ta dube ni kafin ta ce “ Rahila ko kuna da buƙatar yin wani ɗan shagali ne?”


“A'a Mama” ta bata amsa.
“To ki yi mata ko dilka ne kafin gobe a yi mata lalle,kitso dai kam sai dai ta zauna da gashinta don babu ƴar wahalar da za ta kitse mata wannan tulin gashin” Mama ta faɗa tare da jefo wata baƙar leda.Rahila ta ɗauka tare da buɗewa sai ta kalle ni kafin ta ce “ kayan gyaran jiki ne,bari na haɗa sai ki shafa a dukkan jikinki” kanzil ban ce mata ba har ta ɗauko wani ƙaramin kwano ta haɗa kayan sai da suka yi kamar minti goma kafin ta matsa min na tashi na shafa.




Wani tsohon zanena na ɗaura zuwa ƙirji kafin Rahila ta soma shafa min dilkan a kaf jikina.Sai da na yi kusan awa ɗaya kafin ta je ta kai min ruwan wanka,dakyar na iya fita saboda idon mutane.Bayan na fito daga wanka haka suka ta yaba yadda na ƙara kyau,ita kanta Rahila haka ta yi tsaye tana kallona kafin ta taɓe baki ta ce “ wannan ɗan tsamin ran ko an yi dilkan ma ai ga banza”


“In ma dai iya tsamin ran ne kawai da sauƙi,in ɗayar maganar ba ta tabbata ba” na faɗa kamar zan yi kuka.Rahila ta ja numfashi kafin ta ce “ to da yake an ce iya ƙarar alburushi ne ya taɓa masa ƙwaƙwalwa,ƙila haukan ba yadda muke tunani ne ba”


“Sani dai sai Allah ” na faɗa kafin mu soma yin hira jefi-jefi.Da Rahila ta tafi gida sai na ji kaɗaici ya ƙaru amma haka na daure,sai wuraren magrib su Ayo suka shigo gidan ashe wurin kitso da lalle suka je .Abin da na fahimta hatta su sun san gobe ake ɗaura min aure amma ni banda darajar da za a sanar da ni.


Natasha ta zo ta faɗa jikina tana nuna min kitson da aka yi mata har da duwatsu,yadda take murna da nishaɗi sai na ji sanyi a raina.


“Hum! Sai wani murmushi take kamar wani auren ƙwarai” Ayo ta faɗa wacce ita ma ta yi kitson da lalle,na ɗaga kai na dube ta kawai ban ce mata komai ba.Sai ta ja tsuki ta fita,Sarah ta matso tana cewa “ ki bar kula ta,so take ta ɓata miki daren aurenki ki kwana da baƙin ciki”


“Mu ga kitson naki ke” na faɗa na yi kamar ban ji me ta ce ba,ta cire hullar kanta na gani.Da na ga kitson sai na ji ina sha'awar ganin gashina a kitse sai dai kuma na yi saurin cire hakan a raina sanin abu ne da ba zai yiyu ba,rabona da kitso tun ina ƙarama shi ma dunƙule biyu ne Mama ke yi min sai ta yi ƴan tsoraye a sama.
Ina nan zaune aka kawo min abinci har da ruwan da zan sha,na tsurawa abincin ido ina kallo yau ce rana ta farko da aka taɓa yi min wannan gatan sai na saki ɗan murmushi tare da jawo kwanon na soma ci .Ina tuna gobe ne fa aurena sai na ji ya fita raina ba don ban jin yunwa ba sai don fargaba.Ƙawayen Mama da da danginta na ta ci gaba da yin hidima kafin ɗaya daga ciki ta kawo min wani tsimi ya fi kalar biyar,ban san na mene ne ba amma dai na yi biyayya na sha sauran kuma ta miƙa min ta ce na dinga sha har ya ƙare sai kuma wasu ƙullinka gari da kwalin madara su ma ta faɗa min yadda zan sha,ɗaya ne ta ware daga cikinsu ta ce “ wannan dole sai bayan sallar magrib za ki sha” kai kawai na gyaɗa tare da amsa.
Bayan fitarta ne na jawo sabuwar ƴar ƙaramar trollyn da na ajiiye domin saka abubuwana,na zube duk magungunan sannan na kwanta ina ta ci gaba da wahalar da kwanyata da tunani iri-iri.Duk gari yayi tsit ba ka jin sautin komai sai na karnuka,tuni kowa ya samu wuri ya kwanta amma ni sam bacci ya ƙauracewa idona.Haka na yi ta juyi ina jin kamar na tashi na fita amma sai na haƙura na ci gaba da bulaye a tunani a haka ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba.
Washegari hayaniyar mutane ce ta tashe ni tun asubah,kasancewar akwai waɗanda suka kwana gidanmu akwai kuma musulmi daga cikinsu.Daga inda nake kwance nake kallon yadda wata ke yin sallah cike da nutsuwa tana karanto wasu abubuwa da ban san na mene ne ba,har ta kammala ina kallon ta .Na ja ajiyar zuciya,ina sha'awar musulunci suna burge ni musamman in sun yi shigarsu ko ina a rufe.




“Ki tashi ki yi wanka,ki shafa dilka sannan kuma ki turare jikinki da wannan kafin mai lalle ta zo” Mama ta faɗa cike da sanyin murya,na dube ta sai na ga duk ta yi wani iri amma ban tambaye ta dalili ba na tashi na yi yadda ta ce .


Ko da na yi wanka na biyu tuni wacce za ta yi min lalle ta zo,doguwar riga na saka na zo na zauna kan tabarma kafin a soma sai da aka bani kunu mai zafi na sha.




Kusan awa huɗu ana yi min lallen kafin a ida, jefi-jefi muna taɓa hira da mai lallen har muka yi ɗan sabo.
Wuraren ƙarfe ɗaya na rana Abba da abokansa tuni sun taru da kuma dangi Mama maza.Tun a lokacin na soma jin gabana na faɗuwa,ina jin ƙarar cirawar motoci na sunne kai ina jin kamar zuciyata za ta fasa allon ƙirjina ta faɗo.Kamar minti talatin haka sai kuma ga su sun dawo ,wani maroƙi kuwa ya soma shela “ An ɗaura aure ya ɗaru,Aliyu Jafar ya zama mijin Janiki Al Haris ”


Duk da ina cikin tashin hankali bai hana ni maimaita sunan ‘ Al Haris ’ a zuciyata ba,wato sunan mahaifina kenan,don dai shi Abba sunansa ba haka yake ba .




Mata biyu ne suka ja ni zuwa banɗaki,kan wata kujerar katako na zauna bayan na cire doguwar rigar jikina kamar yadda suka ce.Haka suka yi min wanka da ruwan lalle,sai a lokacin kuma aka wanke min sumar kaina tasss har da saka min turare.Sai waƙe-waƙe suke har aka gama,sabbin kaya aka saka min haka ma takalmi sannan aka luluɓa min wata dara sabuwa dal aka fito da ni sai guɗa ake ta ko ina.




Ɗakin Mama aka kai ni har kan gadonta,wanda yau ne kawai zan ce na zauna shi.Banda kuka babu abin da nake yi,yayin da ƴan uwanta ke yi min nasiha gefe guda kuma Mama ce hakimce cikin shigar sabbin kaya sai amsar kuɗin biki take.




Dakyar na iya buɗe fuskata aka ɗauke mu hoto kafin na koma can ɗakinmu.Abun farin ciki sai na tarar da ƴan makarantarmu sun zo duk da kuwa ban gayyace su ba na san ji suka yi.Sai na ɗan saki raina muna hotuna,Rahila ita sai wuraren ƙarfe biyar ta shigo gidan ta rungume ni muka hau kuka sai da muka yi mai isarmu sannan muka yi shiru.An ci an sha amma ni kam ko miyar bikin ban lasa ba,mun yi hotuna ni da ƙannaina kafin motocin ɗaukar amarya su zo.


Tuni kuwa an sa na yi wanka an fitar min da kayan da zan saka,ban yi kwalliya ba sai dai Rahila ta yi min kalba guda biyu ta zubo min su a gaba.Haka aka zo aka ja ni aka kai ni gaban Abba da Mama don neman gafara da kuma yi min addu'ar fatan alkhairi akan sabuwar rayuwar da zan fara .Idona cike da hawaye nake kallon Mama wacce zuciyarta ta karye take goge ƙwalla,haka aka rufe min fuska tare da ja na zuwa waje har muka shiga mota kuka nake.
Babu wani nisa sosai da gidanmu,ko da muka isa ɗakin SURUKATA aka kai ni.Ana buɗe min fuska na ji wani ƙamshi marar daɗi ya daki hancina,ban sani ba iya ni ɗaya ce ke jinsa ko kuwa har da sauran mutane.Ni dai kam na matsu a fitar da ni,haka Hajiya Luba da danginta suka yi ta yin addu'a kafin a miƙar da ni zuwa ɗakina kamar yadda ta ce.Fuskata aka sake rufewa sannan aka ja ni izuwa can,ina zaune kan gado tare da dangina da kuma na shi mijin da aka aura min kafin abokan ango su shigo amma shi banda shi har suka gama karanto addu'o'insu bai zo ba haka suka fita dangin Mama na ta tsiyar gumin ƙin zuwan ango.




Sannu a hankali duk suka watse suka bar ni,ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login