Showing 12001 words to 15000 words out of 43872 words
zaune a takure tare da tunanin wacce irin tarba zan samu a wurin mijin da haɗa mu aka yi ba soyayya ba na ji sallamarsa kafin kuma ta Hajiya Luba .
Abin da na fahimta ita ce ta rako shi a madadin abokansa kamar yadda al'ada ta tanada.
“Ki buɗe fuskarki mana” Hajiya Luba ta faɗa a daidai lokacin da na ji sun yi tsaye kusa da ni.Hannuna har rawa yake wurin bin umarninta,ina buɗe fuskar muka haɗa ido da Aliyu ,dogon namiji ne haka yana da ƴar ƙiba ba sosai ba fuskarsa sam babu walwala kamar ba ango ba.Da sauri na sunne kai ina jin zuciyata na ƙara ƙarfin gudunta,kamar wani yaro Hajiya Luba ta ce “ ka zauna kusa da ita” ko bakinta ba ta rufe ba kuwa ya zauna dab da ni har muna iya jiyo sautin numfashin juna.
Aka ƙara yin sallama aka shigo,da muryoyinsu na gane su wato ƙannan Aliyu ne waɗanda suka taɓa zuwa gidanmu.Su ma ɗin da alamu kamar uwar ke juya su yadda ta so duba da yadda komai sai ta ce sannan su yi,amanar Aliyu suka ban kafin su ajiye ledoji sai suka fice su duka ukun muka yi sauran ni da shi.
Kamar kurame haka mu ka zauna na tsawon lokaci kafin ya je ya rufo ƙofofin ɗakin ya dawo.Wata ƙofa na ga ya shiga can kuma na ji motsin ruwa ,da ya fito kamar wani mala'ika ya ce “ ki je mu yi alwala za mu yi sallah” sautin muryarsa kaɗai ya tsorata ni amma na aro jarumtar cewa “ Ni Kirista ce”
“Daga yau kin fita daga wannan sahun ki tashi” ya faɗa cikin bayar da umarni.
Wani tausayin kaina na ji,don kuwa ko giyar wake na sha ba zan yi masa muso ba.Jiki na rawa na sauka na shiga toilet ɗin,sai na tsaya ina kallon pampon tsaye don gidanmu babu shi.
“Me kike yi wai?”
“Ban iya ba” na basa amsa,ya kuwa shigo ya nuna min yadda zan yi kafin mu fita.Ban san inda ya samo dardumar ba,haka ya shimfiɗa muka yi sallah bayan mun gama ne ya jawo ledar tare da bani umarnin na ci a tsorace na ci na ƙoshi kafin kuma ya bani wani umarnin na wanke baki.
Ina fitowa daga toilet na nufi gado zan kwanta saboda mugun baccin da nake ji,“ keee!” ya wani tsayar da ni,na juyo muna facing juna.
“Da wannan kayan za ki kwanta?” ya tambaye ni yana mai tsure ni da ido ,kafin ya ja tsuki ya je ya buɗe wani trolly ya ciro min wasu kaya shara-shara.Haka na yi tsaye ina jujuya su,ina son ce masa ban iya saka su amma mugun kallon da yake watso min yasa a dole na shiga toilet na saka su sai dai fa na kasa fitowa.
Ya buɗe ƙofar toilet ɗin yayi tsaye yana kallona shi ma ya canza kaya,na sunne kai kawai ina hawaye.Mun fi minti biyar a haka kafin ya zo ya ja hannuna,kamar wata ƴarsa haka ya ɗora ni kan bed yana yi min wasu abubuwa da suka jawo maganin da aka bani jiya da yau ya soma aiki,kayan baccin da ya bani ma ya cire rigar ido kawai na rumtse ina jin takaicin yadda yake kalle ni ta hasken ƙaton ƙwan lantarkin ɗakin.Ban fargaba ya raba ni da komai sai a lokacin kuma na buɗe ido nan na yi tozali da shi ashe shi ma bai da sutura,a yadda na ga halittarsa kamar ta ƙaramin yaro yasa gabana faɗuwa rasss ashe akwai sauran mamakin da zai ban a gaba.Ƙoƙarin shigata ya soma,ko minti ɗaya ba a yi ba na ga ya koma gefe wai har ya gama ban san lokacin da na tashi zaune ina kallonsa ba sai mayar da numfashi yake kamar wanda yayi wani abun ƙwarai,rigarsa na sa na goge ƙazantar da ɓata min jiki ina ƙoƙarin sauka daga bed ɗin ya wani jawo ni ya rungume sai a lokacin kuma ya kashe ƙwan lantarki.Mugun riƙo yayi min kamar ƴar kaso wannan yasa ban ma gwada ƙwatar kaina ba,wani irin tausayin kaina ne ya ƙara luluɓe ni duk da na san an rina tun da har Mama ta yarda in aure shi amma ta hana wa ƴar gaban goshinta.‘ A haka zan zauna da shi ,ga baƙin rai da son iko,ga ƙaramar halitta ga kuma saurin inzali? Da wane zan ji ni Janiki? Wacce irin lukutar ƙaddara ce wannan ka ɗoro min ya abun bauta? Shin dama ka yi ni ne don kawai na yi ta baƙin ciki ina zubar hawaye?’ da ire-iren waɗannan zancen zucin na samu bacci ya ɗauke ni kafin kuma na farka cikin wata lukutar masifar,hannuna har rawa yake wurin danna maɓalin wuta.Haske ya kawo ɗakin,na dafe ƙirji tare da aron kalmar musulmi na ce “ Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” na dafe ƙirji ina kallon yadda shimfiɗar aurenmu wacce ta yi shaɓe-shaɓe da fitsarin Aliyu .
Daga nan zan tsaya duk mai son ci gaba zai biya 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank , sai a turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
*Na gama free page* in ya zama Complete kuma 1k ne farashinsa.
[21/12 à 08:37] MRS SADAUKI: My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822
Free 07
Hawaye ne suka soma yi min zuba, ‘ wannan wacce irin lukutar masifa ce mijina na fitsarin kwance ga kuma rashin lafiyar gamsar da iyali? Gaskiya abin yayi yawa shege da hauka sam ba zan iya auren ƙaddarar nan ba,da wane zan ji da ƙunci rayuwar da ya addabi ruhina ko da faman fitar da kafita kowacce safiya kamar mai yaron goye?’
Duk wannan tambayoyin na yi su ne a zuci ,yayin da na koma gefe ina kallon Aliyu wanda ke kwance cikin fitsarin sai sharara baccinsa yake da alamu ma sanyin lemar bai dame shi ba.
Toilet na shiga na cika bokiti da ruwa na soma yin wanka,don ban saba yi da shower ba.
Babu neman izini kawai na ga mutum shi ma ya shigo cikin toilet ɗin,da sauri yunƙura zan miƙe don kuwa ban ga dalilin da za mu yi wanka a tare ba.Ya cabko ni ya riƙe ni gam ko ƙwaƙwaran motsi ban iyawa,ƙoƙarin haɗe bakinmu yake ni kuwa na ƙi yarda saboda bai brush ba yanzu ya tashi daga bacci.
Wani gigitacen mari ya ɗauke fuskata da shi wanda ya sani ganin taurari,tuni fitilun idona sun ɗauke hankalina ya gushe na wucin gadi.Ƙazamin bakinsa na ji kan nawa yana kissing ɗina,ya haɗe ni da bango yana yin abin da ya so da gangar jikina.Banda wani zaɓi banda na yin kuka,sai da ya gaji don kansa kafin ya janye jikinsa daga nawa ya soma yin magana.
“Zo na nuna miki yadda ake wankan tsarki” ban ce komai ba,na dai zuba masa ido ina kallon yadda yake yi kafin ya bani umarnin yi.Har sai da na gama sannan ya ce “ ki yi alwala to irin na jiya ” jikina na rawa na yi sai sannan ya miƙa min towel na ɗaura.
Da muka fito bayan mun saka kaya ya ja mu sallah,muna idawa ya miƙe yana hararena.
“Na shiga uku ni Janiki yanzu kuma me na yi ?” na yi tambayar ina mai tashi tsaye.
Cike da masifa ya ce “ ita katifar can uban waye zai fitar miki da ita?”
“Yanzu zan yi” na faɗa tare da isa bakin bed ɗin na kwashe zanen gadon,sai da na ja ajiyar zuciya ganin ashe ba a fitar da ledar katifar ba sam fitsarin bai kai gare ta ba.
Bokiti na ciko da ruwa na saka towel a ciki ina matsewa ina goge ledar daga nan kuma na shiga toilet na wanke zanen gadon .
Ko da na fito har ya shirya cikin kakinsa na soja,sai na ji tsoronsa ya ƙara huda ruhina ya samu matsuguni.Fuskar nan tasa a murtuƙe ya ce “ abincin breakfast” murya na rawa na ce “ to” na faɗi haka ne gudun fitina sai na ɗauki bokitina na je na buɗe ƙofa.Allah yayi sa'a na ga igiyar shanya a tsakar gidan,sai na je na shanya zanen kafin na yi tsaye ina tunanin inda zan samo masa abincin .
Gidan na soma ƙarewa kallo har na fahimci ɗakin hajiya Luba,a hankali na soma cira ƙafata har na isa .Sallama na yi har sau uku ba a amsa ba,ina kutsa kai na ganta zaune ta luluɓe dukkan jikinta da jan ƙyalle a gabanta kuwa wata ƙwarya ce cike da nono.
Da sauri na juya zan fita don ina kyautata zaton ba ta gan ni ba duba da idonta da suke rufe,ina fitowa na yi kiciɓis da wata matashiyar mata.Ta sakar min murmushi ta ce “ amarsu! Fatan an tashi lafiya ya gajiya biki ya kuma baƙunta?”
“Lafiya lau an gode Allah, please ina zan samu abincin breakfast?” na faɗa .
Wani kallo ta yi min mai cike da ban mamaki kafin ta ce “ au! Har yanzu ba ki ɗora girkin ba?”
“ Ban san ma inda madafar take ba” na faɗa a sanyayye ,ta ce “ ok biyo ni” haka na take mata baya muka shiga wani ɗan lungu ai kuwa sai ga wata ƙatuwar ƙofa ta saki murmushi kafin ta ce “ ga kitchen ɗinmu,duk abin da kike buƙata za ki samu.”
Na marairaice murya na ce “ amma don Allah me zan dafa masa ban san me ya fi so ba”
Wata irin dariya ta yi kafin ta ce “ ai mu nan gidan girki ɗaya ake yi na kaf ahali,sannan Hajiya Mama ce ke zaɓar abin da za a dafa.Yanzu ai na ga daga ɗakinta kika fito,ba ta sanar da ke me za ki dafa mana ba?”
Na girgiza kai na ce “ ai ba mu yi magana ba”
“Ki je to ki tambaye ta”
Na sunne kai saboda har ga Allah ni dai tsoron komawa nake,“ ko kawai ki yi wainar ƙwai mai haɗi da fulawa na ga yau asabar kusan ita ake yi ”
“Yawwa ki taimaka min na yi please ” na faɗa cikin sigar roƙo,nan ta amince ta soma sauko abubuwan buƙata haka ta dinga ja na da hira na ga alamu ba ta da wuyar sabo sai dai akwai shishigi sai bugun cikina take tana son jin yadda muka yi daren farko.
Ban dai ce mata komai ba sai wainar da muke ta yi,“ wato kunya kike ji? Hum! Ai gwara ma ki cire ta don kaf gidan nan ni ce kawai zan saki jiki da ke,matan Umar ƴan ɗaukar kai ne ” ta faɗa tana wani kafe ni da ido .
Na murmursa na ce “ har yanzu ba ki sanar da ni sunanki ba.
“Binta ne sunana,ke kuma Janiki ko?” na gyaɗa mata kai ina mai cewa “eh haka ne,yanzu in mun gama girkin ya za a yi da shi? Kowa za a zuba masa nasa?”
“A'a akwai ɗakin cikin abinci,can babban falon Hajiya Mama ” ta bani amsa.
Cikin wani irin dogon faranti babba irin sosai ne muka zuba wainar kafin ta nuna min hanyar da zan bi na shiga falon cin abinci.Tun da na doshi ƙofar zuciyata ke tsananta bugu har na buɗe na shiga,babban falo ne sosai mai ɗauke da capet ja shi ma babba ne don ya cika ɗakin.Babu table ballantana kujerun cin abinci,sai wasu abubuwa masu kamar pilow da aka zagaye wurin da shi.Daidai tsakiya na ajiye farantin ina mai duba kowane bango da ke ɗauke da hotunan Hajiya Luba ,yadda duk idonta suke ƙurrr sai abin ya baka tsoro don tamkar tana kallonka za ka gani.
Ina nan tsaye duk mutanen gidan suka soma shigowa mata da maza da kuma yaran gidan ,amma banda Aliyu .Cike da ladabi na soma gaishe su suna amsawa kafin Hajiya Luba ta shigo sanye cikin wata alkyaba kai kace sarki ko matarsa,abin mamaki sai na ga duk sun miƙe tsaye suna wani sunne kai to ni dama a tsayen nake babu buƙata kenan.
Ido kawai na zuba mata ina kallo,a yanzu da nake tsaye a nan sam ba Hajiya Luba ƙawar Mamana ba ce nake gani wata ce ta daban mai abin ban mamaki.
Yadda ta zubo min idonta cikin nawa har ban san lokacin da ni ma na bi ayari ba na sunkuyar da kai.
Ta saki murmushi mai sauti,ban sani ba su ma sun ji shi ko kuwa ni ɗaya ce oho.
“ Ƴata Janiki je ki yi wanka ki canza kaya,sannan ki cewa Aliyu ya zo fadar cin abinci in ji ni” Hajiya Luba ta faɗa ,na amsa da “ to Hajiya ” sai kuma na nufi ƙofa fita,ina jin lokacin da ta ce “ kowa ya zauna”
Ko da na shiga ɗaki na tarar da Aliyu ya cika fam kamar zai fashe,har sai da ya ban tsoro .
“Ina abincina?” ita ce tambayar da ya jefo min.
“Yana..yana can ɗakin cin abinci kuma Hajiya ta ce ka je can fada tana nemanka” na basa amsa tare da yin wuf na shige toilet,a tsanake na yin wanka na fito cikin sauri na shirya saboda wata uwar yunwa da nake ji.
Ko da koma can sai na ga Aliyu zaune kusan Hajiya fuskar nan tasa har yanzu a muturƙe,rasa inda zan zauna na yi sai na je kusa da Binta na yi zaune ina sakar mata murmushi na buɗe baki zan yi magana kenan Hajiya Luba ta yi min wata uwar tsawa “ Janikiii???” na zabura tare da dubanta,yayin da na ga duk sauran sun sune kai banda Aliyu da ke jefo min mugun kallo.Murya a dake ya ce “ a nan babu mai magana sai ya tambayi izinin Hajiya Mama,kuma ki sauke wannan shegun idon naki ƙasa”
Ai kuwa ko baki bai rufe ba na yi ƙasa da kai.
Cikin muryar gadara take cewa “a jiya mun samu baƙuwa a gidanmu,kowa ya san a gidan nan Aliyu ne babba wannan yasa daga yau na naɗa matarsa shugabarku wacce za ta dinga kula duk abincin da za a dafa,a madadin ni na dinga faɗa ita za ku dinga tambaya a duk lokacin da ranar girkin ɗaya daga cikinku ya zagayo.In kuma nata ne to ita ke da alhakin zaɓar abin da take son dafawa.A ƙarshe kuma ina sake gargaɗar ku akan lamarin da bai shafe ku ba,ban son bin didigi da tambayar juna sirrin da bai dace ba” tana gama faɗar haka sai ta buɗe faranti abincin,tare da bada izinin kowa ya ci.
Kallo ɗaya na yi wa wainar na ga alamun canji,amma banda hujja ko kuma wata ƙofar da zan ce an saka magani .Haka na soma ci kamar kowa,har muka ida kowa ya watse amma Hajiya Luba ta tsayar da ni.
“Janiki yaushe kika fara yin sallah? Wa ya baki wannan izinin?” ta jefo min tambayar tana shafar ƙafafuna,sai na ɗaga kai na dubi Aliyu ba tare da na ce komai ba.
Ta haɗe rai ta ce “ daga yau kar ta sake yi,ka bar ta da addininta ban son jin komai kuma daga bakinka” kai ya jinjina alama ya ɗauka,kafin ta maido hankalinta a gare ni ta ce “ kar ki wani damu ƴata Janiki, Aliyu yayi kuskure da ya tursasa ki kan yin addininsa amma komai ya wuce,gobe ma zan sa ya kai ki Coci ki yi bauta ga Ubangijinku”
Na saki murmushi na ce “ na gode Hajiya ” duk a tunanina soyayya ce ta jawo haka ashe cutata ce ta yi,wani kofin zinare ta miƙo min mai cike da nonon shanu ,kamar wacce ta shekara ba ta sha ruwa ba haka na ji ƙishi da sauri na karɓa na kafa kofin a bakina....
Ki daure ki biya kuɗin karatu Hajiya a yi tafiyar nan da ke.
My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822
[22/12 à 21:39] MRS SADAUKI: My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822
Free 08
Wani irin abu ne na soma ji yana ratsa ruhina yana shiga,tamkar wacce aka juye wa tunani na wani ɗan lokaci haka na jin kwanyata ta yi wani lummm tare kuma da yin wani sauti kamar an buga ƙwai ga dutse.
Na ware idona a hankali kan SURUKATA wacce take yi min gizo kamar mutum kamar wata halitta.
“ Ƴata Janiki ?” ta kira sunana cikin wani sauti tamkar mai yin raɗa.
Sam ban motsa bakina ba,amma tabbas na ji a jikina na amsa da “ da na'am Mama” sai dai sam wannan ba furicin bakina ba ne,ƙila ruhina!
“Tashi ki je ki kwanta na san kin gaji,Aliyu yi mata rakiya zuwa ɗaki” ta faɗa tana wani murmushi .
Ya amsa da “ to Hajiya Mama” kafin ya miƙe ya ɗauke ni cak ya ɗora kan kafaɗa,sai ya zamana kaina ya sunne ƙasa yana reto.Idona ne suka soma nuna min wasu abubuwan da ke luluɓe a ɓoye a ƙarƙashin jan capet ɗin falon cin abinci,sai dai na kasa tantance na mene ne abu ɗaya na riƙe shine an ƙawata da wurin da jini.
A hankali Aliyu ya kwantar da ni kan bed ɗin,tamkar wata jaririya sabuwar haihuwa haka nake lumshe ido ina kuma ɗan buɗe su da zumar tantance wacce duniya nake sai dai sam na kasa .
Wani bacci mai kamar ido biyu ne na soma yi,gani nan ina gudu cikin daji yayin da wasu mutane masu rabi mutum rabi doki na take min baya a tsiyaci.Sosai nake gudu ina waiwayen su,suna dab da damƙo ni Prince Mahadi yayi min iyaka da su ta hanyar diro wa daga sama kamar wani aljani.A nan take kuma suka yi baya suka gudu,yayin da shi kuma ya jawo ni ya haɗe ni da ƙirjinsa.
Numfashi na yi ta saukewa saboda gudun fanfalaƙin da na yi,ya hura iska kan fuskata kafin ya matso da tasa fuskar dab da tawa kamar zai sumbace ni sai ya min raɗa a kunne “ ki tsaya ki lura da kyau,sannan ki kula da kanki” yana gama faɗa min haka na farka ina haƙi.Abun mamaki har zuwa yanzu ina jin wannan yanayin in mutum yayi gudu,maƙoshina ya bushe ƙamas .Na diro daga gadon,ina fitowa falo na yi kiciɓis da Hajiya Luba.
“Har kin tashi ? Ga ruwa na kawo miki ” ta faɗa cike da kulawa,hannuna har rawa yake na karɓi kofin na shanye ruwan tass ta ƙara tsiyaya min wasu na shanye,sai da na yi kofi huɗu kawai ƙishin ya gushe.
“ Halan kin kwanta da ƙishi ne? Ko kuma mafarkin shan ruwa kika yi?” Hajiya Luba ta yi min tambayar tana wani kafe ni da ido.
Mafarkin da na yi tsaf ya