Showing 6001 words to 9000 words out of 43872 words
kunya don tun ɗazu shi nake kallo.
Sai yanzu na lura ashe tun ɗazu hannunmu na cikin na juna,na so na janye hannuna sai kuma na tsinkayi muryarsa “ ba ki so na ci gaba da baki labarin ne?”
“Ina so amma ka sakar min hannu”
“Ta ya zan baki labarin to in na saki hannun naki?” ya faɗa ,ni kuma na dube shi cike da mamaki kafin na ce “ ta hanyar riƙe hannuna shi labarin zai badu?” kai ya jinjina min ,ba tare da ya sakar min hannun ba ya ƙara lumshe idonsa a karo na biyu sai ya ci gaba da cewa “ soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin Yarima da ƴar baƙar budurwarsa,sama da watanni biyu kenan kullum in ta kawo abinci sai ta zauna sun yi ta hira.Sannu a hankali ma sai abincin da take kawo wa iya shi ɗaya ke ci,ganin haka sai ta soma bai wa wata muguwar ƙawarta labari wacce ita kuma ta bada gudunmawa baƙar shawara shine su dinga zuba masa maganin mallaka da wanda zai hura wutar sonta a zuciyarsa,don su duk a tunaninsu ba zai aure ta ba.Ƴar baƙa ta bi gurguwar shawara,kullum tana kai wa Yarima abinci,adadin kwanakin kawo abinci adadin yadda magani ke aiki a jikinsa.Kan kace wani abu Yarima ya kamu sosai,kin san ƴan magana na cewa duk inda mugun so yake to sha'awa ce ke yi masa sanɗa.Sai Yarima ya soma bijiro wa ƴar baƙar budurwarsa da muradinsa da farko ta ƙi yarda a ƙarshe kuma ƙawarta ta bata shawarar kawai ta amince ta yadda in yayi devirgin nata ba zai taɓa suɓuce masu ba.Ita kuma babu wani tunani ta amince suka soma keɓewa da Yarima,tun daga wannan lokaci kuma suka fara tatsar shi kuɗi ita da ƙawarta.Kafin kuma su farga Yarima ya bar gari saboda kiran ujila da ya samu cewa Sarki bai da lafiya,bai san gidansu budurwar ba,sannan ita duk tsawon lokacin nan ba ta da wayar hannu haka ya bar ta cikin halin ƙaƙanikayi domin kuwa tana ɗauke da ciki har na wata biyu.Babu jimawa ta soma laulayi,wanda hakan yasa mahaifiyarta ta gane da ta tambayi ba'asi ne ta koro mata bayanin cewa ciki na Yarima ne.A al'adar garinsu duk wacce ta yi kuskuren ƙin kai budurci a gidan mijinta ta zama abar kwatance,to ina kuma ga cikin shege? Hanyar da suka samu mai ɓullewa ita ce aura mata wani saurayi da yake nacin sonta amma mahaifiyarta ba ta so saboda talaka ne.Shi kuwa so hana ganin laifi ya aminta da auren bisa yarjejeniyar ko da ɗaya rana kar ya taɓa nunawa abin da aka haifa banbanci tsakanin ƴaƴan da za su haifa a gaba.Ya riƙe alƙawarin da ya ɗauka,sai dai kash shi wannan ciki da aka haifa na farko yarinyar ta banbanta da sauran ƙannanta...” da wani mugun sauri na fizge hannuna yayin da jikina ya ɗau kyarma,na miƙe tsaye ina kallonsa kamar yadda shi ma ɗin ni yake kallo.
Ko ƙaramin yaro aka baiwa labarin nan zai fahimci komai ballantana ni da nake cikin hankalina.Da gudu na bar wurin ko waiwaye babu har na shigo cikin unguwarmu,daidai ƙofar gidanmu na yi tsaye dafe da zuciya.
A buɗe na tarar da shi,hakan yasa na shiga kamar wata munafuka aka yi sa'a kuwa Abba da ƙannaina duk suna zaune cikin rumfa yana yanka musu kankana.
Ɗaya bayan ɗaya na soma kallonsu,dukkansu kama suke da Abba kana gani ka san ƴaƴansa ne.
Kamar wata mahaukaciya haka na wuce ɗaki ko gaishe da Abba ban yi ba,madubi na ɗauka na soma ƙarewa farar fuskata kallo wacce ke ɗauke da zankaɗeɗen hanci har baka,ga gashin gira wanda yake baƙi ƙirin kamar na wanda ya ƙawata manya idona.Laɓana pink ne sirara,a hankali kuma na ture kallabina kyakkyawar sumata ta bayyana baƙa ƙirin da ita wacce tsabar yawanta yake sa ban yi kitso sai da na wanke na naɗe ta a tsakiya sai ya zama kamar na yi acuci maza.Karon farko da na ji sha'awar baje ta amma sai ban yi haka ba.Da gudu kuma na sake fita zuwa gidansu Rahila,aka kuma yi sa'a ummarta ba ta nan yau ma.
Ɗakinta na shiga na yi tsaye gaban ƙaton madubinta sannan na warware gashina na cire ribob ɗin.Nan ya zube a gadon bayana da na jawo shi ta gabana har ya wuce ƙirjina,sumar kaina tana ɗaya daga cikin sirrin da Rahila ba ta san da zamanta ba .
Tana tsaye tana kallona cike da mamaki tun shigowar da na yi ban mata magana ba sai yanzu.
“A cikin ƙabilu wace ƙabila ce kika san masu yawan gashi Rahila? Dubi gashina kamar aljana har ya kusa taɓo mazaunaina ” na faɗa cikin rawar murya idona da ba su gama bushewa ba suka daɗa kawo ruwa.
“Fulani ne,sai kuma buzaye” ta bani amsa kai tsaye.
“Amma a Yuganda ba mu da ƙabilar nan,wacce ƙasa ce mai irinsu?”
“Sai in ko Nijar kin san suna da kusan duk ƙabilun da kika sani,amma wai da gaske gashinki ne dama ba hulla gashin doki ba?” ta faɗa tare da zuwa tana shafawa.A garinmu kusan ƴan mata suna saka hullar gashin doki,don haka ba sabon abu ba ne ko da a ce na fita a haka.
Maimakon na ba Rahila amsar tambayarta,wai kawai na toshe kunnuwana ina jin amon muryar Prince Mahadi suna yin gwaro da kalaman Mama wani sa'in yadda take tsare pampon ruwa ta yi ta zagi tana cewa “pampon tsiya,pampon ƙaddara ban ga amfanin kawo ruwa a wannan gari ba dama a haka aka bar mu muka ci gaba da ɗebo su a rijiya” wani sa'in kuma ta kan ce “ duk in na ga pampo takaici nake ji,sai na ji kamar duk na bi kowanne gida na cire shi”
Wata uwar ƙara na saki na soma shure-shure rabin hankalina dai ya gushe amma ina ganin wasu abubuwa.Yadda Rahila ta ruɗe ta fita waje da gudu sai ga ta sun dawo da Abba,da lokacin da ya kiran pasto ya zo yayi min ruƙiya yana karanta abubuwan cikin Bible.
Na yi tsit ina jan ajiyar zuciya,Abba ya kamo hannuna muka koma can gidanmu.Ya zaunar da ni kan kujera yana kallo,cike da tausayi ya ce “ Janiki tun yaushe kike da Aljanu ban sani ba? Sun taɓa taso miki?”
Kai kawai na girgiza masa,su kuwa su Ayo sai kallona suke .Abba ya fita ya kawo cefane,ya miƙa mata ya ce ta yi girki .
“ Abba ni ban iya ba” ta faɗa .
Cike da masifa ya ce “ ki koya” sai kuma ya fice daga gidan.
Bokiti na cika da ruwa da kuma buta uku na shiga banɗaki na yi wanka na wanke dogon gashina wanda a ƙa'ida sai wata-wata nake wanke shi.Ban bari ya wani bushe ba na yi parking nasa tare da laulaya shi ya tsaya tsab kamar tayar mota.
Cefanen na karɓa na ɗora mana girkin dare,duk yadda na so na cire tunanin Prince Mahadi na kasa .Na yi wa kaina tambayar ” kenan ni shegiya ce ba da aure aka haife ni ba?” ya fi shuren masaki.
Ban gama girkin ba har sai da aka yi kiran sallah,haka na zuba musu sai Ayo ta kawo wani kwano ta ce “ ki zuba wanda za a kai asibi” ba tare da na ce komai ba na karɓa na zuba.
“ Shi ne ko jikin Momy ba za ki tambaya ba saboda mugun hali” ta faɗa tana mai ficewa,na bi bayanta da kallo ko kaɗan ban ji haushinta ba saboda a gidan ubanta nake ni nawa mahaifin a tsallake mahaifiyata yayi ya bar ta tun ina ciki.
Na goge ƙwallar takaici ina jin tsanarsa na ɗarsuwa a zuciyata,bayan na fidda abincin na kai kwanukan can ɗaki na jera.Na miƙawa Sarah da Natasha nasu suka fara ci uwar iya yi kuma ta ɗauki na ƴan asibiti ta wuce.
Kan shimfiɗa na kwanta tare da yin lamo,na ma rasa wane tunanin zan yi.
Sallamar Rahila na ji a tsakar gida,da sauri na tashi zaune ina amsawa tare da bata izinin shigowa.
Bayan ta shigo ta zauna sai ta miƙo min wani ƙaton kofi na roba mai murfi ta ce “ kunun madara ne na san kina sonsa shine na yi miki,ki sha tun da zafinsa ƙila ma ba ki ci komai ba”
“Na gode” na faɗa tare da buɗewa na soma sha a hankali,yayi daɗi sosai hakan yasa na sha rabi sannan na ajiye.Rahila ta dafa ni kafin ta ce “ don Allah ki cire damuwa a ranki,kin ga ba isashiyar lafiya ce da ke ba”
“Na gode sosai Rahila” na furta ina goge ƙwalla.
“Ya Salam! To kuma mene ne na kuka? Ina Mama?”
“Tana asibiti , Momy babu lafiya ”
“Ok to ni zan koma gida kar Umma ta neme ni” har zan yi mata rakiya amma ta hana ni.
Bayan fitarta ne na bai wa su Sarah sauran kunun suka sha,ni kuma na ci gaba da tunanina har bacci ya ɗauke ni.
Washegari tun safe na tashi na yi aikin gida kamar kullum,suka ci abinci kafin su wuce makaranta Abba ma tuni ya fita kasuwa.Kayan da na wanke jiya na kwashe na ninke su sannan na sakawa kowacce a jakar kayanta,na Abba ma haka.Sai kuma a lokacin na ɗauko na Mama na wanke,bayan na gama komai na fita na zauna kan dakali da tunanin Prince Mahadi zai zo sai dai wayam sai duban hanya nake shiru.
Taxi ce ta tsaya ƙofar gida,Mama ce ta dawo fuskar nan tata kicin-kicin kamar wacce ta dawo daga zaman makoki.Ni kuwa sosai na yi kewarta duk da kuwa tana takura min amma sai na ji gidan yayi min girma da ba ta nan.
Na miƙe da saurina na ce “ sannu da zuwa Mama ” kanzil ba ta ce min ba ta wuce ciki,na take mata baya.
“Jiƙa-jiƙar mene ne nan kika yi? Don iskanci wannan har wanki ne? Haka ake wanke kaya duk ba su fita ba sai uban datti? Don ubanki zo ki kwashe su ki ƙara wankewa” Shine abin da ta ce min tana hararena,na sunne kai na amsa da “ to” ta wuce ciki ni kuma na kwashe kayan haka na ƙara tsoma su a ruwa na wanke ba don ba su fita ba sai don tsiyar gumin Mama da ba ta ƙaunar ta gan ni zaune ina hutawa.
Daga can cikin ɗakin ma ban tsira ba sai saƙon zagi take jefo min tare da aibanta farar fatata da ɓakar kala mai hasken tsiya da bai tare komai ba.
Ni dai banda hawaye babu abin da nake yi,ban ga dalilin da zai sa a kama ni da laifin da ba ni ce na aikata ba....
[17/12 à 08:08] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽
Na
*Chamsiya Laouali Rabo*
```{MRS SADAUKI}```💫✍️
*FCWA* ☀️
*SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊
___________________________________
05
Sati guda currr Mama ta ɗauka tana azabtar da ni da yunwa,ba wai ba ta bani abincin ba ne a'a sau ɗaya tal nake da damar cin abinci a wuni a maimakon sau uku.Kuma wanda ake bani ɗin ba wani ba ne,ƙarin haushi kuma ni ce ke girka musu abincin wani sa'in ma ita Mamar sai na yi mata nata daban saboda juna biyun da ya bayyana gare ta mai kwaɗayi.
Yau ta kama asabar,gobe kuma ranar zuwa coci in na tuna da goben zan kai wa abin bautar tamu kokena a ɗakinsa har wani sanyi nake ji yana ratsa ni.
Tun wuri na yi dukkan ayyukana har da wankin kayan ƴan gidan,sannan na yi musu girki.Ina zaune gefe ina kallon su suna cin girkin rana,shinkafa da miya ce na yi musu sai ƙamshin kifi take.
“ Ko a zuba miki tun yanzu?” Mama ta jefo min tambayar,na jinjina kai alamun eh.Sai ta ɗauri wani ƙaramin faranti ta zuba min tare da turo shi gabana tana zagina “ don ubanki gobe ma ki sake yi min laifi,azabar da zan yi miki sai ta fi wannan.Kuma ki bar kallona da shegun idanun naki masu kama da na aljanun ruwa ”
Ban ce mata komai ba na ɗauki abincin na fara hannu baka hannu akushi,ko minti biyu cikkake ban ɗauka ba na cinye kuma ban ƙoshi ba.Sai na soma kallon su Ayo da har yanzu suke cin abinci suna hira hankali kwance,ni kuma yatsuna na soma siɗewa ina jin hanji cikina na yin ƙugi alamun dai abincin bai ishe su ba.
Mama ta tashi ta ɗauki buta ta shiga banɗaki,da sauri Sarah ta cika hannu ta zuba min a farantina har sau biyu.Jikina har rawa yake wurin soma ci.
“Tukunyata kika buɗa kenan?” Mama ta faɗa cike da masifa,na girgiza mata kai.Uwar masu mugun hali ta ce“ cikin namu ta damtsa ta ƙarawa kanta”
Mama ta sa hannu ta buge farantin abincin ya juye ga ƙasa,ta dungure min kai ta ce “ ke da baki jin kunya abincin ƙannan naki za ki ci?”
Sarah ta ce “ Mama ni fa na zuba mata na ga ba ta ƙoshi ba”
Da sauri Ayo ta ce “ ƙarya ce Mama Janiki ce ta ɗeba da kanta kin ga sawun ƙaton hannunta ma”
Da harara Mama ta bi ni kamar idon za su faɗo kafin ta shige ɗaki,ni kuma da sauri na kwashe abincin na je wurin pampo na wanke shinkafar.Yunwa ce ta saka ni na ci haka nan,sai kuma na sha ruwa na fita na zauna kan dakali.
Tunanin abubuwan da Mama ke yi min na soma,hawaye suka zubo min na ce “ ban san me zan yi don na faranta ranki ba Mama da tabbas sai na yi shi” sai kuma na goge hawayen kafin na ci gaba da cewa “ duk kai ne ka ja min da ace ba ka kusance ta ba da tabbas ba za a samu cikina ba,na tsane ka! Ban sonka!” na furta kamar ina gaban shi mahaifin nawa.
Idona na ji an rufe min ta baya,na saki ɗan murmushi na ce “ Rahila ce” da sauri ta buɗe min idon tare da dawowa gabana ta yi tsaye.
“ Kukan mene kike?”
“Babu komai daga ina kike da tsakar rana?”
“Umma ta aike ni na karɓo ɗinkunanmu,bari na nuna miki ” Rahila ta faɗa tare da ajiye ƙatuwar ledar kan dakali ta buɗe ta soma nuna min ɗinkunansu kala uku ita da Mamarta duk zanuwan iri ɗaya ne gwanin sha'awa.
Ban san lokacin da na ce “ kin ji daɗinki Rahila ke Umma na son ki”
Ta ce “ haba Janiki wace irin magana ce wannan? Ke ma ai Mama na son ki kawai dai don kuna da yawa ne shi yasa kike ganin kamar tana nuna banbanci ni kuma kin ga ni ɗaya ce kawai mace ga Umma”
Na girgiza kai na ce “ wannan bai isa yasa Mama ta ƙi ni ba,kullum tana hantara ta.Kin ga mu bar hira nan zuciyata na ƙara ciwo”
“Ya maganar aurenki?”
Na taɓe baki na ce “ har yanzu dai Hajiya ba ta sake zuwa ba”
“Shi Aliyun ya zo?”
“A'a fa,Rahila ga Umma can ta leƙo ki je kar ta yi miki faɗa ” na faɗa ,da sauri kuwa Rahilar ta tafi saboda in ka ga Umma na yi mata faɗa to a kaina ne kawai kwata-kwata ba ta so ta gan mu tare.
Ni ma tashi na yi na koma gida,masarar tuwo na fidda a ruwa kafin na je ɗaki don karɓo kuɗin niƙa.Mama tana kwance na kira sunanta,shiru ba ta amsa ba sai a na biyun ta tashi da ta yi min wata uwar tsawa har sai da na firgita.
“Na ce mene?”
“Kuɗin niƙa” na bata amsa.
“Saboda kuɗin niƙa sai ki tashe ni ina bacci? ”
“Ki yi haƙuri ban san bacci kike ba” na faɗa tare da fita waje,Ayo wacce suke exercices ita da sauran ta tuntsire da dariya kafin ta yi min gwalo sai ta miƙe ta shiga ɗaki.
Babu jimawa ta fito tare da cillo min kuɗin niƙan,na duƙa na ɗauka tare da zuwa na ɗauki robar masarar na fice.Ina isa mashin na tarar da layi,na ajiye nawa kafin na koma can nesa da mutane na zaune.Idona suka ciko da hawaye,tunanin shan maganin ɓera ya zo min a kwanya na mutu kowa ya huta.
“In kin gama kukan ungo ki ci” na ji muryarsa kamar daga sama,na ɗaga na dube shi kafin na dubi abin da yake miƙo min.A take yawuna ya tsinke,hannu na rawa na karɓa ba tare da jira ba na soma ci.
Ya ja ajiyar zuciya tare da zama kusa da ni,bai ce min komai ba har sai da na ci rabin abin da ya kawo min wanda ban san taƙamaimai mene ne ba amma a tsakiyar akwai niƙaƙen nama.
Gorar ruwa ya miƙo min na karɓa na sha,na yi ajiyar zuciya tare da dubansa cikin ido.
“ Shikenan sai kika gudu kika bar ni?” ya faɗa .
Na sunne kai kafin na ce “ da gaske wannan shi ne tarihina?”
Ya saki murmushi mai sauti ya ce “ eh sosai”
“Amma kai ya aka yi ka sani?”
“Saboda ba ki san ni ba shi yasa har kika yi wannan tambayar,amma ni da nake yarima mai jiran gado jinin masarauta ai wannan ba abin mamaki ba ne?”
“Kenan tsafi kake?” na samu kaina da tambaya.Bai ce komai ba ya miƙe tsaye,“ ina za ka je ?”
“Zan koma gida mana” kafin na kai ga cewa komai mai yin niƙa ya kira sunana na waigawa don na amsa masa kawai ban farga ba Prince Mahadi ya ɓace.
Niƙana na je na ɗauka tare da biya sannan na wuce gida,ragowar abincin da ya bani sai na kaiwa Natasha ta karɓa cike da murna ta shiga ɗaki.
Ina tsaka da hura wuta Mama ta shigo madafar ta yi tsaye kaina,“ gidan uban wa kika samu gurasa da nama?”
Gabana ne ya bada wani rasss ,na dubi Mama kawai ina zarar ido ga kuma Natasha gefenta tana cin abincin.
“Da ke nake!” ta ƙara faɗa a dake tana haɗe rai.
Murya na ɗan rawa na ce “ bani aka yi ”
“Na sani ai,uban wa ya baki shi nake son sani?”
Idona ya kawo ruwa na ce “ sadaka aka ban” ban rufe baki ba ta shure ni da ƙafa tana cewa “ almajira ce ke ballantana a baki sadaka? Wato daga jin za a yi miki aure shine kika fara biyar maza? ” nan ta rufe ni da duka kafin ta ce “ taso ki biyo ni don ubanki sai na duba ki” haka na tashi ina kuka na bi bayanta har banɗaki.
“ Ki cire pant ɗinki na duba ki” ta faɗa ,jikina ne ya ƙara ɗaukar mazari yayin da kukan da nake ya