Showing 27001 words to 30000 words out of 43872 words
Chapter 10 - SURUKATA HORROR BOOK COMPLETE DOCUMENT 2025.txt
kansa ya bugu” ta faɗa cikin kuka ganin kan HAROON sai jini yake zubarwa,wasu samari suka taimaka mata suka saka shi a gidan baya yayin da ita kuma ta hau mazaunin direba ta tuƙa shi zuwa wata asibiti ta kuɗi.
Da isar su aka karɓe shi,duk da kuwa ba tada kuɗi a hannunta amma sai ta nuna musu katin ɗan ƙasarta cikin ikon Allah ma wasu sun santa.Abu na farko da aka soma yi wa HAROON shine tsayar da jinin kansa aka naɗe da bandeji,cikin ikon Allah kuma numfashin nasa ya dawo normal sai dai yana buƙatar hutu.
Sai a lokacin kuma ta kira mahaifiyarsa ta shaida mata ,babu jimawa kuwa sai ga Ammy.Ita ma kukan ta soma sai ya zamana babu mai rarrashin wani,ita sai faman faɗin “ HAROON kar ka mutu ka bar ni,kai kaɗai ne farin cikina a duniyar nan”
Ita kuma Malama Zainab cewa take “ duk laifina ne,da ace ban yarda ya sauke ni ba da ƙila hakan bai faru ba,saboda son kasancewa da shi yasa na aminta oh ni Zainabu na ga ikon Allah! ” sai kuma ta fashe da kuka.
Bacci nake mai kamar mutuwa, sama-sama nake jin sautin kukansu a hankali na ware idona ba tare da na buɗe su tarau ba.Ta ƙasan gashin ido nake hango yadda masoyana biyun ke kuka,sai na shagala yadda manyan idon Malama ke tsiyayar da ruwa ,pink leɓenta kuma duk ya jiƙe da yawunta yana rawa.Yatsun nan nata masu ɗaukar hankalina sai shafar hawaye suke,na dafe gefen kaina da ke sara min kafin na kira sunan Ammy.Da sauri ta matso kusa da ni tana cewa “ ka tashi? Mi kake ji? Ina yake ma ciwo?”
Murmushi na sakar mata tare da nuna mata saitin zuciyata da kuma yi mata alama da Malama Zainab,wacce ta yi tsaye tana kallona hawaye na bin kumatunta yayin da fuskarta ke ɗauke da ɗan murmushi.
Ammy ta ce “ za ka same ta in sha Allah kar ka wani damu” sai kawai na lumshe ido ina tuna abin da ya faru da ni, a daidai lokacin da mugun iskan nan mai ƙarfi yayi cilli da ni kaina ya bugu da dutse ɗigon jinina na farko ya ɗiga ga ƙasa Oganmu na gani a can gefe a tsaye yana kallona,bai samu damar ƙaraso wa inda nake ba sai da Malama Zainab ta ɗan yi nesa da ni,abin da na fahimta shi kansa yana shakkarta.Hakan kuma sai yasa na ƙara jin mugun sonta da ƙaunarta sun ƙaru a Wani farin abu ya saka min a inda kaina ya fashe kafin ya ɓace wa ganina.
Dakyar ta iya cewa “ ya jikin naka?”
Ammy ta ce “ bari na kira likita” sai ta fice.
Sai a lokacin na amsa mata “Da sauƙi! Na gode sosai”
Ta ɗan dube ni cikin ido kafin ta ce “ babu komai!” sai kuma duk muka yi shiru ,ni na ƙure ta da ido yayin da ita kuma take satar kallona lokaci-lokaci .A haka Ammy ta shigo ita da wata nurse,awon tension ta yi min kafin ta ce “ ka gyara zan yi ma allura ga cinya”
“Ga cinyaaa ?” Malama Zainab ta faɗa da sauri duk muka kalle dukkan mu ukun sai ta yi saurin wayancewa ta ce “ ina nufin wace irin allura ce za a yi ga cinya? A yi ga hannu ai zai fi”
Nurse ɗin ta ce “ saboda cinya ta fi tsoka,in ga hannu ne za ta iya yi masa zafi”
“Bai komai ai shi namiji ne,ki yi masa ga hannun kawai tun da dai ana yi” ta faɗa cike da kishin da ita kanta ba ta san ya fito ba,Ammy dai sai murmushi take.
Hannun rigar na cire sannan nurse ɗin ta yi min allura ga damtse,ni aka caka da allurar amma Malama Zainab ce ta yi ƙara har da rumtse ido.
Nurse ɗin ta yi dariya tana mai cewa “ ah Madam irin wannan tattali haka ? Ko duk don kar a yi miki kishiya ne?”
“Wace irin kishiya kuma ? Ai ...ai ba mij...” sai kuma ta yi shiru ƙila yadda muka haɗa ido da ita ne yasa ta kasa idawa.
“Zuwa an jima za a sallame ku in Dr ya hau aiki,sannan akwai gwaje-gwajen da aka yi ana jiran result” nurse ɗin ta faɗa kafin ta fice.
“Ni ma zan tafi Mama,am...ina nufin Hajiya Allah ya bada lafiya” shine abin da ta faɗa kafin Mama ta yi mata rakiya.
Suna fita Oga ya bayyana a cikin ɗakin fuskar nan tasa kicin-kicin,kamar zai fashewa da kuka ya ce “ ina mai yi maka gargaɗi akan ka bar sheɗaniyar yarinyar can.Sam tarayyarku babu alkhairi a tattare da ita,sannan ina so ka yi gaggawar barin asibitin nan kafin ta kwaso zugar ɗalibanta su zo duba ka”
Sam ban yi mamakin ganin nasa ba,amma na fi mamakin yadda yake so na bar asibiti alhalin banda lafiya.“ Amma Oga me yasa zan tafi? ”
“Za ka iya jurar addu'o'in da za su yi ita da zugar ɗalibanta? Kai ka rasa wacce za ka so sai babbar maƙiyiyarmu? Ko ba ka san manyan sheɗanu sun yi tirrr da halinta ba? In banda karatun littafinsu babu abin da ta iya,a haka ne kake tunanin haɗa wuta da ruwa wuri guda?”
“Ina son ta!” na furta kai tsaye ba tare da shakka ba,“ dole ka rabu da ita”
“Zan zauna da ita Oga,kai dai kawai ka zuba min ido” bai kai ga bani amsa ba Ammy ta shigo.
“ Da wa kake magana HAROON ?” ta tambaye ni.
“A'a ban yi magana ba Ammy ”
“Yanzun nan kafin na shigo na ji kana magana fa”
“To ƙila ko dai a ɗaya ɗakin ne”
“Ok to .Ka ga Malama Zainab na son ka ko? In sha Allah zan je can gidansu ni da Kawunka ” sam ban ɗauki maganar da wani muhimmanci ba na miƙe na shiga toilet saboda yadda na ji marata ta ƙulle,kamar jira ake ina shiga toilet ɗin na ga an zagaye ni na zamana a tsakiyarsu.Duka mutanen na gane su ahalin ƙungiyarmu ne,ban san da wane Siddabaru suka yi amfani wurin ɓatar da ni ba sai kawai na tsinci kaina a wani gun daban.
Cikin faɗa Oga ke faɗa “tun da ka ji za ka iya sai ka zo a ƙaddamar da kai ta yadda za ka samu power da yawa,sannan waccan abar ka sani lokaci guda ne kawai za ka iya kusantarta wato in tana period”
Cike da mamaki nake kallonsa kafin na ce “wannan ai ƙazanta ce! Ta ya zan kusanci matata da jinin al'ada?”
“Ba kada zaɓi” Oga ya faɗa yana matsowa kusa da ni hannunsa riƙe da wata ƴar tasa ,yatsana manuniyar ya kama ya sa reza ya tsaga shi nan jinina ya soma zuba cikin tasar nan har sai da ta cika duka.Ya ajiye tasar sannan ya saka wani abu ya rufe wurin da ya tsaga sai jinin ya tsaya.
Daga nan wani ɗakin sirri dukkanmu muka shiga ,ni dai ban san da zamansa ba amma su sauran da alamu sun saba shigowa.Komai na cikin ɗakin baƙi ƙirin yake sannan an yi masa adon zanen Cross da jan penti,gaban wata aba mai kamar halittar duniyar sama Oga ya je ya tsaya jinina da ke cikin tasa ya dangwala a yatsa ya shafa daidai bakin halittar ,wani irin girrrr na ji a yatsan nawa kafin kuma a sannu wani abu ya game dukkan gangar jikina.A gabana dukkan members ɗin suka dinga dangwalar jinina da yatsa suna lasa da alamu ma kamar daɗinsa suke ji saboda yadda kowa ke ta ƙoƙarin ganin ya fi ɗan uwansa sha.Bayan nan sai Oga ya ja mu izuwa wani katafafen capet duk kowa ya zauna amma ni ya hana ni,na buɗe baki da niyyar tambayarsa don me banda ni,kawai na ga abokan ƙungiyarmu sun shiga yin aman kuɗi sabbi dal da su wani irin tsoro ya kama ni har ban san lokacin da na saki ihu ba.
My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
Talla! Talla! Talla!!!
DULLAHZ CAKES AND MORE 💕
Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu,
Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki,
Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884
Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884
Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884
Call:09111648884
[26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
08
Tun da uwar da ta haife ni ban taɓa ganin inda mutum ɗan Adam yayi aman kuɗi ba sai yanzu,tamkar wasu ruwa haka takardun kuɗin ke fito wa daga bakin kowanne members har sai da suka kusan cika ƙaton capet ɗin.Ni kuwa banda kyarma babu abin da jikina ke yi,a nan take a inda nake tsaye kuma na ƙaryata fassarar da na yi wa sunan MAFIYA daga “cikar muradi ” zuwa “tsafi da shan jini”.
Ashe ban kai maƙura wurin mamakina ba sai da na ga kuɗin na ware kansu suna yin dunƙule-dunƙule na 100k ,kamar ƙyaftawar ido suka jeri rasss a hakan kuma kowace takardar kuɗi ta san wanda ya amayar da ita .
“ HAROON wannan ɗin duk kuɗinka ne!” Oga ya faɗa yana murmushi haɗi da bubuga gefen kafaɗata.
Na ce “ duk me zan yi da uban kuɗin nan?”
Sai duk suka hau yi min dariya,can suka tsagaita Oga ya ce “ ka manta akwai aiki jajur a gabanka? Ko da kanka za ka dinga bin maƙabartu kana ciro likafanin?”
“Wane irin likafani kuma?” na tambaya cikin tsoro.
Oga ya haɗe rai ya ce “ wanda zai taimaka ma ka yi tsawon rai nan gaba,ko ka manta ne?”
Murya na rawa na ce “ ban manta ba amma Oga ai sai nan da shekara biyar ko?”
“Bayan wannan akwai wasu sharuɗan! Kowanne ƙarshen wata za ka samo mana jinin period na budurwa,kar ka tambaye ni ta yaya .Ka fara tunanin hanyar da za ka bi ka kawo na wannan watan don yau muna ashirin da uku ga wata”
Wasu irin yawu na haɗiye masu mugun ɗaci,ido kawai na tsura musu da alamu ko a jikinsu sai harakar gabansu suke suna saka min uban tulin kuɗin a jakakuna.
“Amma Oga ina zan ajiye kuɗin nan? ”
“Bisa kaina”
“Ka yi haƙuri in na je da su gida Ammy za ta zarge ni ”
Ran Oga ya ƙara ɓace wa ya ce “ HAROON ka fita idona,kana yawan matsa min da zancen Ammynka in ba ka yi sa'a ba kai ne za ka yi silar mutuwarta ”
Gabana ya bada rasss jin wata lukutar masifa,amma na kawar da tsoron gefe na ce “ wannan shine babban kuskuren da za ka yi kuwa a duniya shine taɓa Ammyna,duk duniyar nan banda tamkar ta.Kar ka manta silar ta ne a yau nake cikin wannan ƙazamar rayuwar,Ammyna ita ce komai nawa in babu ita ban ma ga tsiyar da zan yi a duniya ba” duk wurin tsit yayi suna kallona shaye da mamaki,na sani sarai yadda duk ake tsoron Oga ni ma ina tsoronsa amma ba zan juri a taɓa Ammyna ba ko kaɗan ai gwara ya yanki fatar jikina ya fi yi min sauƙi.
Ban taɓa ganin Oga cikin fushi irin haka ba sai yanzu,tako ɗaya yayi ya isa inda nake idonsa sun kaɗa sun yi ja sosai.
“Ōgāfōr̃!” furucinsa kusan tsinke igiyar da ke saita mini numfashi yayi,na riƙe hannunsa tare da roƙonsa “ please Oga kar ka hukunta ni ta hanyar kai ni ɓoyayyar duniya” sai dai da alamu roƙon nawa a banza ne wai an tsikari kakkausa.Tuni ƙasa ta soma darewa ginin cikin ƙasa ya bayyana,idona na zubar da hawaye na tashi cikin iska kafin na yi nitso cikin dogon ramen a haka ƙasa ta rufe da ni ruf sai gani tsaye a gaban baƙar ƙofar nan a karo na biyu.
Yau ɗin ma Dōr̃anī ne suka buɗe min ƙofar tare da yi mini iso a ciki,sai dai fa wata jahar suka kai ni ba nan fara isa ba.
“Wannan karon kuma wane laifin ka yi mai yawa har Oga ya ce a kai ka sashen bauta ?” ya tambaye ni.
Ƙin basa amsa na yi sai ma tunanin yadda zan yi na fita na soma,“ fatan dai ba wani sirrin ƙungiyar ka fitar ba?”
“Ban fa iya surutun nan yau ka bar ni da abin da ya sha min kai” na faɗa cikin masifa,daidai nan muka iso wata duniyar mai cike da abubuwan ban mamaki mutum da jikin maciji,ko kifi,ko doki,mage mai ƙafa ta fi ɗari,ko kuma mage da kan mutum.Maciji mai magana,kare da shan sigari.
“Ina ne kuma nan? Me zan yi a nan?” na tambaya a firgice,banza suka yi da ni sai tafiya suke ina take musu baya har muka isa gun wasu tsofi.
“Ina ka samo mana ɗan saurayi kuma?” ɗayar tsohuwar ta faɗa tana wani kashe mini ido,yayin da wasu biyun suka taso suka soma shafa ta da sauri na soma ture su ina son guduwa.
Dōr̃anī ya ce “ ladabtar da shi za ku yi,shi ɗin yana da muhimmanci ga uwa MAFIYA don haka kar ku taɓa lafiyarsa”
Yana gama faɗar haka duk suka ɓata rai waɗanda ma suka yi min ƙawanya sun gusa daga jikina,su ma Dōr̃ānī tafiyarsu suka yi.
Wacce ta fi su tsufa duka ita ce ta miƙe tsaye ta ce “ ɗan samari biyo bayana ”
Dole dangin naƙi haka na take mata baya zuwa wani sashe mai cike da yana don ta cikinta ma muke bi muna wucewa,mun ɗan yi tafiya sosai kafin ta ja ta tsaya.
“Ruhinka nada ƙarfi sosai ta yadda har yanzu Octoba ya kasa karɓe shi duka duk da kuwa ka sayar da shi,uhum! Amma me yasa kake fusata shi haka? Ka san mene ne za a yi maka a nan ɗin?” tsohuwar ta tambaye ni.
“Mene ne zan yi a nan ɗin?” na tambaye ta tare da share duk sauran zancen da ta yi.
“Matso kusa ka gani” ta faɗa ,na ɗaga ƙafata na isa gare ta abun mamaki sai na hango duniyarmu ta Bil'adama.Wasu abubuwa ta dinga furta wa nan gidaje da ababen hawa suka dinga wuce wa kamar mai yin tariya har ta isa ga asibitin da aka shimfiɗe ni.
Wani irina na gani zaune kan gado Ammy na ɓare ayaba tana basa yana sha,gefe guda kuma direbana ne ya ƙura masa ido yana kallo.
“Ko ka san me yasa waccan mutumin yake kallon mai kama da kai?” tsohuwar ta tambaye ni.
“Eh saboda ba haka nake zama ba,sannan in zan ci abu da hannun dama nake riƙe shi ba hagu ba.Ban cika son mutum ya ƙure ni da ido yana kallo ba” ina gama faɗa sai na ga mai kama da ni ɗin ya mayar da ayabar a hannun dama yana cewa “ Ammy har yanzu hannun ga nawa ciwo yake,kai kuma lafiya ka tsare ni kana kallo? Fita ka ban wuri”
Direbana ya miƙe da sauri da ya kai bakin ƙofa sai da ya sake waiwaya wa,nan ɗin ma sai da ta tambaye ni “ me yasa ya waiwaya?”
“Saboda yi wa mutum tsawa da hantara ba tabi'ata ba ce” na bata amsa kai tsaye.
“To da zarar ka koma duniyarku ya zama dole ka kashe direban can”
Sai da na dafe ƙirji na ce “ saboda me?”
“Amsar na wurinsa” tana gama faɗa ta wani kamo hannuna muka yi suka tare da sauka can doron duniya mun iso bakin kwalta na ja na tsaya,ta wani ja hannuna tana mai cewa “ kai gara iya ruhinka ne kawai a nan gangar jikinka na can sama”
Haka motoci ke ratsawa ta cikinmu ba tare da mun kauce musu ba,wani gidan cin abinci muka je.Da murna take cewa “ tsawon lokaci kenan da ban shigo duniya ba ,ina son abincin nan ya kamata in nemi gangar jiki na shiga ta yadda zan ji daɗin abinci”
“Ta ya kenan?” ba ta bani amsa ba ta je jikin wata budurwa wacce ke tsaye jikin mota ita da saurayinta,a gaban idona tsohuwar ta shige jikin yarinyar.Ta ja hannun saurayin suka zauna ta yi odar kaji da lemun kwalba,“ yau sai na baka mamaki zan cinye dukkan kaji biyun nan” budurwa ta furta wanda a baɗini esprit ɗin tsohuwar nan ne.Aka kawo kaji biyu ta cinye su tasss ta sha lemun kwalba,tana gamawa ta fice daga jikin nata ta zo daidai inda nake tsaye tana dariya “ na tsani soyayya,yau na yi silar raba su” sai kuma ta ja ni muka tashi cikin iska muka koma can inda muka fito,gangar jikina na gani a tsaye tana zaman jirana sai dai ban san ya zan yi na koma ciki ba........
My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank,DM +22795045822 .Saura page biyu na gama free page kafin nan zan yi discount ga mai so ya biya 400 sai ya tura min shaidar biya ta WhatsApp.
Talla! Talla! Talla!!!
DULLAHZ CAKES AND MORE 💕
Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu,
Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki,
Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884
Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884
Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884
Call:09111648884
[26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
09
Wannan tsohuwar ce ta nuna min yadda matsafa ke yi wurin fitar da ruhinsu daga cikin gangar jiki da kuma yadda