Showing 30001 words to 33000 words out of 43872 words
Chapter 11 - SURUKATA HORROR BOOK COMPLETE DOCUMENT 2025.txt
ake yi a koma.
Cike da jin daɗi na isa inda gangar jikina take a tsaye kamar saƙaƙo,yadda ta koyar da ni ɗin da shi na yi amfani na koma ciki.Daga nan sabbin abubuwa ta soma koya min,irin yadda zaka juya tunanin mutum,kashe mutum ba tare da kaca masa wuƙa ko bindiga ba,yadda za ka cutar da wani normal mutum ba tare da shi kansa ya san an cuce shi ba.
Daga wannan kuma sai ta soma yi min wani bayani da ya tafi da ruhina.
“ HAROON ita duniyar MAFIYA da kake ganinta kowanne members yana samun power ne daga aikin da yake yi,wato iya yawan sacrifice iya adadin yadda ƙarfin ikonka zai ƙaru.Samun power ƙwaya ɗaya ya fi a baka miliyan ɗari,saboda su kuɗin za su ƙare ita kuwa power zaka iya sarrafa ta sosai ta yadda za ka samu dubban abubuwa marar ƙirguwa.Ka ga ko ita wannan wacce kake so ko? To tabbas kana iya yin galaba a kanta muddin dai ka samu power dayawa.Bari na nuna maka wani sirri na musamman da ba kowa ya san da shi ba” sai kuma ta miƙe ta ɗauko wani tandun kwalli ta miƙo min.Na karɓa ina dubanta,ta ce “ shafa shi da idonka sai ka sanar da ni me ka gani”
Ban musa ba sai kawai na bi umarninta na shafa kwallin ga dukkan idanuwana,sanyi ne ya ratsa su kamar na ƙanƙara wannan ya sa na ɗan lumshe su.Ina buɗe su kuma na yi tozali da tsohuwar matar nan ta zama tamkar lagwami duk jikinta tattakaken ƙwarangwal ne babu kyawun gani.
Ta ce “ wannan kwallin yana taimakawa wurin gane taƙamaimai asalin mutum da kuma niyyarsa a kanka,sannan zai ƙara ma ƙwarjina ta yadda babu wanda ya isa ya kalle ka cikin ido ciki kuwa har da Ammynka”sai ta yi shiru na wani lokaci kafin ta ɗora da “abubuwan da suka fi kawo maki a Mafiya sune mata da ƙananan yara,sai kuma mahaukata.Kowanna daga cikinsu da tasa rawar da yake takawa,in kana son a kowace irin jarabawa ko sabga taka ka yi nasara to da buƙatar ka yi sacrifice na ƙaramin yaro da bai balaga ba...” da sauri na katse ta da tambayar “ amma saboda me?”
“Saboda ƙwaƙwalwa yaro a wanke take babu komai cikinta na tunanin wata matsala,sannan zuciyarsa ma haka fara ce fesss babu baƙin cikin kowa .Bakinsa kuwa gaskiya ce tsagwaron ta,irin haka ne zaka samu wasu mutanen da daɗin baki in sun yi magana sai ka ji tasu ta fi ta kowa”
“Su kuma mata me yasa ake son sadaukar da su?” na tambaya.
Ta yi wani murmushi kafin ta ce “ akwai wanda ya fi mace wuyar sha'ani a duniya? Ita fa kamar sawun keke take baka gane gabanta ballantana bayanta ,wannan ya saka Mafiya ke da buƙatar mata.A sassan jikin mace akwai waɗanda in aka yi tsafi da su aikin ya fi kyau ,daga ciki akwai al'aurarta da kuma mamanta,abu na ƙarshe kuma shine ana yi mata wankan ƙaddamawar sai namiji yayi amfani da ita irin haka ne ke janyo farin jini da dukiya mai tarin yawa”
Na jinjina kai na ce “ su kuma mahaukata fa wane dalili ne?”
Kai tsaye ta bani amsa da “ a gaskiya sabbin members na MAFIYA waɗanda suke son yin kuɗi sun fi amfani da mahaukata,dalili kuwa shine shi hauka launin cuta ce da ke zuwa daga ƙwaƙwalwa wasu ta jinnu ce wasu kuma haka aka haife su da ita,to ita kanta wannan launin cutar tana da matuƙar muhimmanci a mafiya tana sa member ya ji gamsuwa fiye da in da mutum mai hankali ne ka kusanta”
Shiru na yi ina nazari,abin da na ƙara fahimta game da Mafiya wani rikitacen al'amari ne marar kyau.Duk abu na ƙwarai a wurin su ba mai kyau na ne sai gurɓatace,“ to amma yin mu'amala da mace yayin jinin al'ada fa me yake ƙarawa?” na jefo mata tambayar.
“Yin haka tamkar rufe ƙofofin taurarin ita macen ne,sannan duk wasu lamurranta za su iya kwaɓe mata yayin da shi kuma namijin rayuwarsa ta ɓoyayyar duniyar za ta yalwanta ”
Kasaƙe na yi ina zancen zuci ‘ kenan so ake duk na disashe taurarin Malama Zainab?’
“Bari ka ji HAROON ,babu abin da sheɗanu suka fi ƙauna irin warin jini musamman na al'ada yana da matuƙar muhimmanci a duniyarmu”
“Wane irin sheɗanu kuma?” na tambaya kamar wani gara.
Sai da ta sheƙe da dariya kafin ta jefo min tambayar ta saka zuciyata tsananta bugi,“ kai a tunaninka kai mutum ne? Bani amsa kai mutum ne?” shiru na yi na kasa cewa komai.
Ta ci gaba da cewa “ ka sani tun ranar da ka kwashe kayanka a gaban Manzo ka fita daga sawun mutane,kai sheɗani ne HAROON !” ta faɗa cikin wani sauti wanda ya saka yanar da ke yaɓe ta ko ina ta soma kaɗawa kamar ana iska.
“ Tashi ka bani wuri” ta faɗa cikin fushi,da sauri na ce “ na fita na je ina? Ki yi haƙuri amma ni ban ga abin ɓacin rai ba” ina gama rufe baki ta ja hannuna ta matso ni kusa a nan take madubina da ke can gida ya bayyana a nan.
“Wannan ita ce siffar mutum? ?” ta tambaye ni tana nuna ƙwarangwal ɗin da ke cikin madubi ,na girgiza kai na ce “ a'a ba mutum ba ne fatalwa ce”
Madubin ne ya ɓace ita kuwa sai ce min ta yi “ ai HAROON gwara fatalwa da kai,saboda kai sheɗani ne na musamman.Wai ma mene ne dalilin Oga na zaɓar ka alhalin ga dukkan alamu baka san muƙamin da ke jiran ka ba?”
“Muƙami?” na maimaita.
Dōr̃ānī ne ya shigo yana mai cewa “ lokacin komawar ka yayi” haka na bi bayansa muka fita.
Sai da ya kai ni wani sashe aka yi min wanka da wasu korayen ruwa sannan na ci na sha kafin yayi min rakiya zuwa bakin ƙofa.Yau ɗin ma kamar kullum haka ƙasa ta dare na fito sai dai fa wani uban canji na ji,jin kaina nake yana hayaƙi yayin da kuma zuciyata nake jin tamkar an yi min musanyar ta,sauran tausayin da ya rage min ya kau a yadda nake ji ko wuyan jinjiri zan iya murɗe wa ya mutu.Ban gama mamakin kaina ba sai da na ga sauran members sun miƙe suna gaishe ni cike da girmamawa,yayin da shi kuma Oga yayi kicin-kicin da fuska haɗi da nuna min wata kujera da aka ƙawata ta da ado.A yau sai na yi wa Oga dubin uba mahaifi wanda kuma ban san dalilin yin haka ba,zuwa na yi na zauna nan ɗin ma wani sabon canji na ji amma dai na yi shiru ina ta nazarin komai daki-daki.
“Daga rana irin ta yau na wakilta HAROON matsayin mataimakina wato shugabanku,in ba ni ga wuri shi zai ɗaukar matsayina sannan duk wani hukuncin ƙungiya da za a zarta ko ya shige muku duhu shine zai bada umarnin ƙarshe” Oga na gama faɗa suka shiga taɓa min kafin ya sallame su wurin ya zamana sai mu biyu kawai.
“Wannan ɗin duk na mene ne Oga?” na samu dakyar na tambaya.
Ya bani amsa da “ tun da aka kafa ƙungiyar nan kai ne na farko da ke iya maida min martani, wannan yasa na baka wannan muƙamin kana iya tafiya” ban sake ce masa komai ba na soma yin tsafin da zai kai ni inda mai kama da ni yake,aka yi katari kuwa yana cikin mota direba na tuƙa shi.
Bayyana ta cikin motar yayi daidai da lokacin da direbana ke ƙara saita madubin gaba na mota,yayi ƙara tare da sakin sitiyarin motar sai a lokacin ɗayan ya ɓace saura ni.Na tashi da sauri na tsayar da motar tare da zama gefensa,direba ya dafe zuciya yana kallona kafin da sauri ya maido dubansa gare ni sai na fahimci tabbas ya ganmu mu biyun duka.
Na saki murmushi na ce “ shi yasa bin didigi da ganin ƙwaf bai da kyau,duk yawan sa idon bai yi maka ba sai da ka nemo yadda za ka yi ka tantance shin mu biyu ne ko a'a .To ka tuƙa motar nan izuwa wani wurin cin abinci na ga alamun har da yunwa kake ji daga nan sai na aika ka barzahu”
“Yalaɓai don Allah ka yi haƙuri!” ya furta tare da ƙoƙarin fita sai dai tuni na ƙargame dukkan ƙofofin yayin da kuma na saka motar ta soma tuƙa kanta da kanta .......
My is only 500 via2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822 saura page ɗaya na gama free page in sha Allah.
Talla! Talla! Talla!!!
DULLAHZ CAKES AND MORE 💕
Ina jamaata mutanen kirki ji'bin arziki? Yan kurna, rijiyan lemo,bacirawa,da duk abunda y jibanci Nan Ina mutanena mutanen Kano kanawan dabo mutanen kirki mutanen da sukasan Kansu,
Ina mata yangayu wadanda basaso gayu y wucesu,biki gareki? Suna? Ko kwarya kwaryan liyafa qawata? Kinji labarinmu ko yenzu batun ke tafe gareki,
Munayin cake me dankaren dadi cake hadadde a musulmin farashi,akway cupcakes,samosa, spring rolls,Muna gashin kaji da kayan kwalam d maqulashe kala kala,09111648884
Yayata Muna girkin biki,suna,ko tarbon baki komi kikeso,inma grkine bakijinyi Dan Allah ki kira dullarz zatamaki shi nantake a gyaremaki cikin warmers me delivery ykaimaki,09111648884
Yar uwata inkinyadda d Allah kibamu yardarki bbu cuta babu cutarwa b ha'inci zaa mki komi fiyeda yenda ke zakiyi 09111648884
Call:09111648884
[26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
Last free page
10
Ni kaina ban san taƙamaimai ina ne motar za ta je ba,gudu take tamkar aljani ne ke tuƙa ta.Cikin abin da bai wuce minti biyu ba har mun fita daga cikin garin Yamai mun shiga ƙasurgin daji sai a lokacin kuma motar ta tsaya cak tare da buɗe kanta.Na fito zuciyata na sake azalzala banda wani buri baya da na kashe direbana wanda har izuwa yanzu bakinsa bai gushe da bani haƙuri ba.Finciko shi na yi da sauri ya zube kan gwiwansa tare da kama ƙafafuna ya ce “yalaɓai ka yi mini rai ,na yi maka alƙwari zan kasance bafaɗenka mai yi maka hidima.Zan zama tamkar Kare da mai ikonsa,ka yarda da ni zan yi maka duk abin da kake so amma kar ka kashe ni ina da buruka masu tarin yawa da nake son cikawa kafin na bar duniyar nan!”
Cikin ƙaraji na ce “ Illiya ka tabbata duk abin da nake so za ka yi shi?”
“Eh yalaɓai koma mene ne zan yi” ya amsa mini cikin haƙiƙanin gaskiyarsa.
“Za ka zama mataimakina kamar yadda ka ce akwai ayyuka masu tarin yawa da za ka yi min,in ka kuskure kuwa ka sani daidai yake da fitar numfashinka ”
“Na gode sosai yalaɓai” ya furta tare da tashi har yanzu jikinsa bai bar rawa ba,haka muka shiga mota na lumshe idona ina jin wani matsayi ya hau kaina saboda na fara samo wa ƙungiyarmu member sannan duk wani wanda ya shigo ta sanadiyar ka to a ƙarƙashin kulawarka yake kamar yadda doka ta tsara.
Ko da nake buɗe ido sai na tsinci kanmu a tsakiyar babban titin Yamai,na ɗan saki murmushi na ce “ Illiya na tambaye ka mana”
“Eh yalaɓai ina ji tambaye ni” ya faɗa murya na rawa.
“Matanka nawa?”
“Matata guda yalaɓai da kuma yaronmu ɗaya” ya bani amsa a tsorace.
“Zuwa gobe ka kawo min ita a babban ofishina ina son ganinta” na faɗa cike da gadara.
“Yalaɓai ai ba ta yi makaranta ba”
“Yaushe na ce ma zan ɗauke ta aiki ?” na yi masa tambayar a tsawace.
Ya ce “ka yi haƙuri yalaɓai”
Na juyar da kai ina kallon titi har muka isa gida,ina fita sai da na tsaya ina ƙarewa Illiya kallo gajere ne shi baƙi yana da ƴar ƙiba amma ba sosai ba,idonsa irin na munafukan mutanen nan ne masu son sanin sirrin wani.
“Yalaɓai na faɗa ma zan yi duk abin da ka ce,ka yarda da ni ” ya faɗa cikin tsoro,na shafi sajena kafin na ce “in ma ba ka yi ba ai ka san meke jiran ka! Sannan duk faɗin duniyar nan ba za ka taɓa ɓoye min zan lalubo ka” ina gama faɗa na wuce ciki.
Yau Ammy ba ta falo ban kuma nemi na san inda take ba kawai na shige ɗakina,wanka na soma yi kafin na fito ɗaure da towel.Kai tsaye kusan madubina na je na tsaya,ina son sanin abubuwa da dama game da MAFIYA wacce a yanzu garɗinta nake ji.Kamar wanda zai shiga ɗaki haka na yi na ratsa ta cikin madubin na shiga ciki,yau ɗin ma kamar waccan lokacin yanayin duniyar hazo-hazo ce sai dai hakan bai hana ni ganin abin cikinta ba.Wani aji na gani inda aka rubuta “TSAFI DA MATSAFI” babu wani tunani ai kuwa na je na tsaya sai na ga wata malama a tsaye tana koyawa wasu karatu,ba tare da neman izini ba na je na zauna ina kallon darasin . Tana gamawa kuma sai ga wani shi ma malamin ya bayyana kamar daga sama,kamar wani rediyo kuma ya soma yin magana.
“Sannu Matsafana da kuma Mayuna!A yau za mu gano abokiyar sufi da muka fi so wato: cat da turanci,wacce a Hausa za mu kirata da mage ko kuma ƙuliya.Wannan halitta ko da yaushe tana da alaƙa da sihiri da mayu.Za ku ga a gidajen Mayu,matsafa ko malaman tsibo suna ƙawata shi da mage ko kuma ƙuliyoyi wanda normal mutum zai ɗauka iya soyayya ce kawai amma yanzu zan muku gwanjon sirrikan.Bari mu fara da labarin da zai burge ku!” sai ya tsaya da magana tare da soma yin rubuta a ƙaton allon da ke cikin ajin.
# Cat da Bokaye: Tsohuwar ajiya a cikin kundin Labari na ƙarni biyu.
Shine abin da ya rubuta kafin ya soma yi mana bayani dalla-dalla.
“Tsawon ƙarnoni, ƙuliyoyi sun kasance abokan bokaye. Masarawa sun bauta musu a matsayin alloli. Indonesiya sun yi imanin cewa ƙuliyoyi na iya gani fiye da mayafi. A takaice, abokanmu na sirri sun fi dabbobi kawai.
Abu na gaba shine :
# Ikon Sufanci na Mage
A naku hange me yasa mayu suke son kyanwa sosai? ” Mr Zulu na kawowa nan sai ya tsaya yana tambayar mu,wato ya bamu damar tsoma baki a ciki kamar yadda malaman makaranta ke yi.
“ HAROON ko za ka faɗa mana dalili?” ya jefo min tambayar,duk sai hankalin kowa ya dawo kaina.
Na ce “Domin suna da ƙarfin ikon sihiri”
Yayi alama da babban yatsansa irin na jinjina kafin ya ce “ba shakka! HAROON yayi gaskiya a cikin halittun da duniyar Ruhaniya ta aminta da su mage nada kaso casa'in na ƙarfin tsafi yayin da sauran halittun kuma nada ƙarancin rinjayen.Daga cikin quality ɗin mage akwai:
* Hankali, Cats suna jin kuzari da ruhohi mara kyau. Mafi dacewa don kiyaye gidanku.Ma'ana a duk lokacin da wani mummunan abu zai faru cikin gida mage tana sani kuma za ta iya kare mamallakinta daga wata cutar wa ita abin ya same ta.
* Kariya :suna tunkuɗe mugayen ruhohi da munanan kuzari.Daga lokacin da mugu ya shigo gida zai ji ya kasa zama a ciki saboda wanzuwar ƙuliyar.
* Warkarwa : Tsaftace su yana da tasirin warkewa, cikakke don rage damuwa.In mutum na cikin wata damuwa ta dalilin yadda yake mu'amulantar magensa zai iya samun sauƙi daga abin da ya shige masa.
Sannan ku sani bayan wannan ɗin akwai wani ɓoyayyen sirri a tattare da kowacce mage.Abu na gaba da nake son ku sani shine TASIRIN LAUNI,kowacce mage da kuke gani da nata tasirin sannan ba haka kawai ake mallarkarsu ba sai an cika sharuɗa.Amma kafin nan bari na sanar da ku tasirin kowacce daga cikinsu.
Kowane launin yana da ma'anarsa ta sihiri da tsafi.
_Baƙar fata: Yana nuna kariya da sihiri. Saɓanin camfi suna kawo sa'a.
_Fara: Yana wakiltar tsarki da waraka.
_Grey: Yana jawo hikima da hankali.
_Ja: Yana jan hankalin sa'a da kuzari.
_Tiger: Yana wakiltar sassauci da daidaitawa, cikakke don lokutan canji.
Zan tsaya a nan sai wani lokaci ” Mr Zulu ya faɗa tare da yin ɓaton dabo.Ina zaune dai cikin mamakin wannan lamari sai ga kuma wani tsoho shi ma ya shigo ajin tare da rakiyar dog.Na gyara zama don jin wane darasi ya zo mana da shi kawai na tsinkayo murya Ammy na faman kiran sunana,a dole na tashi na fito abun mamaki har yanzu jikina na ɗigar da ruwa kamar yanzu ne na fito daga toilet.
Ƙofar na buɗe ina ƙirƙiro murmushi na ce “ Barka da maraice Ammy!”
Ta dube ni da kyau kafin ta ce “ HAROON wai meke damunka ne? Ka dawo daga aiki amma ba za ka zo ka gaishe ni ba? ”
“Yi haƙuri Ammy na gaji ne sosai,kaina kamar zai tsage haka nake ji shi yasa na soma yin wanka.Amma kina zuciyata ” na yi ƙaryar ciwon kai saboda shi ne abin da ke sa hankalin Ammy gusashe wa a duk lokacin da ta kama ni da wani laifi ni kuma ina gudun ta yi min faɗa .
“Tun yaushe ka fara jin ciwon kan?” ta faɗa hankali tashe,na ce “ bai wuce minti goma” ba ta ce komai ba da sauri ta fita sai kuma ta dawo da ruwan ƙanƙara da towel,kamar ƙaramin yaro haka ta zaunar da ni ta soma yi min tausar kai har sai da na ce mata ya daina na bar ji.Wata irin wawuyar ajiyar zuciya ta sauke wacce har sai da na ɗora ayar zargi da tambaya na ce “ Ammy me yasa hankalinki ke tashi in nace kaina na yi min ciwo?”
Ɗan daburcewa ta yi kafin ta ce “ ka saka kaya ka sauko ƙasa na yi maka girki mai daɗi” tana gama faɗa ta fice,na bi ta da kallo ina cewa “ tabbas akwai wani ɓoyayyen sirri da Ammy take ɓoye min” haka na miƙe na kimtsa sannan na sauka zuwa ƙasa.
Ammy ta zuba min abinci amma na kasa ci,ta zauna kusa da ni tare da soma bani a baki tana mai cewa “ zama da yunwa bai da kyau yana haifar da cutar olser,ka yi niyya ka yi aure HAROON ko hankalina zai kwanta na san matarka za ta kula da kai” ban ce mata komai ba sai murmushi.
Da sauri na juya bayana jin kukan mage yau a gidanmu ,magen fara ce sol ko tabo ɗaya ba tada kuma dumul-dumul da ita kana gani ka san ba ta da yunwa.
“Ammy