Showing 1 words to 3000 words out of 43872 words
[10/12 à 13:05] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽
Na
*Chamsiya Laouali Rabo*
```{MRS SADAUKI}```💫✍️
*FCWA* ☀️
*SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊
___________________________________
01
A duniya akwai wata babbar illa wacce ba kowa ke fahimtar illa ba ce sai wanda abin ya faru da shi kamar dai ni da duniya ta yi juyin waina da ni.
Farinci;kalma ce da ban san me take nufi ba ballantana na more ta,na taso cikin matsin rayuwa mai cike da ƙalubale da rikitacen al'amari wanda da ace ba a kaina hakan ta faru ba da ko shakka babu ba zan taɓa yarda kan cewa Uwa na iya cutar da Ƴar da ta tsugunnai ta haifa ba.
Sunana Janiki,ƴar asalin ƙasar Yuganda ce a wani ƙauye da ake kira da Norobi,ƙauyen ya shahara wurin bai wa al'ada haƙinta.Ni ce ta farko wurin iyayena,sai ƙannaina uku Ayo mai shekara goma sha bakwai,sai Sarah mai 13years sai kuma ƴar autarmu Natasha mai shekara goma.Dukkansu baƙaƙe ne sai ni ɗaya tal ke fara sol kamar zabaya,da wannan jama'ar ƙauyen suke tsokanata da ƴar fara mayya.Tun ina da ƙanannun shekaru ake kirana da haka har zuwa yanzu da nake cikin shekara ta ashirin da biyar.
A hankali nake wanke kwanukan da zan zuba abincin rana,ina rera waƙoƙin da ake koya mana a Coci.Saukar dundu na ji a bayana kafin ashar ta biyo,“ to daƙunanna haihuwar asara,kin kama kwanuka kina shafa kamar mai yi wa jariri wanka sai sun sauko daga makaranta ba ki gama ba ko?” muryar Mama ce wacce a kullum nake fargabar jin ta.
Jikina na kyarma na ce “ na kusa ida wa Mam...” ko rufe baki ban yi ba ta gwaɓe mini haɓa tare da shure ni da ƙafa tana mai cewa “ don ubanki kar ma ki gama zauna nan ki yi ta shafar kwanukan in ƙannan ubanki ne” ban ce komai ba sai sauri da na ƙara ina mai ci gaba da tsiyayar da hawaye,ina gama wanke wa daidai ƙannaina na shigowa su duka ukun a tare kowacce riƙe da jakar makarantarta.
Kamar wasu jarirai haka Mama ta soma tarairayar su tana tambayar su makaranta, sai washe baki take tana fara'a kamar ba ita ce ta gama haɗe mini fuska tana zagina haɗi da dukana ba.
“Shegiya mayya ta wani zubo mamu shegun ƙattin idonta tana kallo,ba za ki je ki fidda abincin ba sai na kare miki ƙafa?” Mama ta faɗa a lokacin da na shagala ina kallonsu,sumi-sumi na wuce zuwa mafada.Kamar yadda na san kowa shi ɗaya yake cin abinci haka na ɗauki kwanuka ina zuba abinci har na fidda shi duka,haka na jera kwanukan kan ƙaton faranti na kai gaban Mama.
Nan kowacce ta ɗauki nata ni ma na ja nawa tare da komawa gefe na fara ci kenan sai ga Sallamar Hajiyar Lubabatu ƙawar Mama wacce a duniya in akwai wacce ta tsane ni bayan Mama to ita ce ta biyu.
Ina ƙoƙarin sunne kai don gudun mugun kallon da za ta watso mini,amma sai ta shammace ni ta sakar min murmushi har da tsarabar furuci mai daɗi.
“ Ah ƴata Jakini abinci ake ciki?” ta faɗa .
Da sauri na gaishe ta “ ina wuni Tanti?”
“Lafiya lau alhamdullah” ta amsa kafin su soma taɓawa ita da Mama,can kuma suka miƙe suka shiga ɗaki.Da wannan damar yasa na matsa kusa da ƙannan nawa ina mai cewa “ yawwa ku koya min karatun”
Ayo mai mugun hali ta miƙe ta shige ɗaki,sai Sarah ce ta fara koya min duk da ba a rubuce ne ba amma ina fahimta sosai.
“Janiki ashe har yanzu kina ta ƙoƙarin koyon karatu?” Hajiya Lubabatu ta faɗa bayan ta fito na tsawon lokaci da suka ɗauka ita da Mama a ɗaki.Na ɗan saki murmushi tare da jinjina kai,ta ƙara yin ƙasa da murya ta ce “ yawwa ki daure ki koya kin ji ai ana son mace ta waye ta fannin karatu,in kina so ma zan turo malami na Musamman don koy...” maganar ce ta yanke saboda fitowar Mama.
“Kin ga fa Ayo ce da rigimar da ta saba ashe ta ji hirar da muka yi” Mama ta faɗa tana murmushi kafin ta janye Hajiya su nufi ƙofar fita da alamu rakiya za ta yi mata.
Ina nan zaune sai ga Ayo ta fito tana hararena,wanda kuma ban san dalilin haka ba sai da Mama ta dawo.
“To Janiki sai a fara shiri lokacin aurenki yayi,yanzu nan Hajiya Luba ta zo min da shawarar arziki kuma na yi amanna da ita” sai kuma ta yi shiru tana kallona kamar yadda ni ma ita nake kallo.
“Ai kin san babban ɗanta Aliyu ko?” Mama ta tambaye ni,na jinjina kai tare da sunne kai ina jin zuciyata na mugun bugawa da sauri.
“To da shi muka yanke shawarar haɗa ki aure,tun da dama ba wani karatu kike yi ba sannan ba saurayi ne da ke ba” Mama ta ƙara faɗa .Idona ne suka kawo ruwa,na ɗaga kai dakyar na ce “ Amma Mama tsoho ne fa,ya kai shekara arba'in duka-duka nawa nake?”
“Yanzu na haifo ki Janiki!” ta faɗa cikin ƙaraji kafin ta ci gaba da yi min masifa “ wato kin samu zai rufa miki asiri ya aure ki shine za ki wani tsiro min da wani iya yi,a'a ba tsoho ne ba shine tuwo tashi ki bani wuri” ta yi min wata uwar tsawa tare da kai min duka.
Da mugun sauri na tashi na shige ɗaki,kan katifa na haye na ci kuka sosai har na gode ma Allah.A haka na samu bacci ya ɗauke ni,haniyar mutane ce ta tashe ni da bushe-bushe.
“Me kuma ake yi a gidan?” na tambayi kaina,shigowar da Abba yayi ce ta bani amsar tambayar hannunsa riƙe da alawa da goro.Bakinsa kamar gonar auduga tsabar murna,miƙo min yayi kafin ya ce “ kuɗin an gani ana so ne aka kawo miki Janiki,ina taya ki murna ke ma za ki je ɗakinki?”
“Duk yaushe aka tsara wannan ban sani ba? Yanzu fa na kwanta bacci” na yi furicin ina duba tsohuwar agogon ɗakinmu sai na ga ƙarfe wajen biyar har da rabi na maraice alhalin lokacin da na kwanta duka-duka ƙarfe ɗaya ne.
Abba bai wani damu da tashin hankalin da na shiga ba ballantana ya bani amsar tambayar da na jefo,kawai ya ajiye goro da alawar ya fice.Ban iya fita ba saboda har yanzu ina jin hayaniyar mutane da saura ba su watse ba,sai bayan gari yayi duhu ne gidan yayi tsit sai a halinsa kawai.Dakyar na je na yi wanka na sauya kaya na zauna tare da rabka uban tagumi ina tunanin zuciya ‘ yanzu dai gaske Umar za su aura min? Mutumin da kullum fuskarsa a haɗe take bai fara'a ? To shi ya ce yana sona ko shi ma dole za a yi masa?’ maganar Mama ce ta katse min tunani “ ki tashi kin yi baƙi” gabana ne ya bada rasss.....
[11/12 à 02:37] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽
Na
*Chamsiya Laouali Rabo*
```{MRS SADAUKI}```💫✍️
*FCWA* ☀️
*SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊
___________________________________
02
“Ba.baaa...ƙi kuma Mama?” na jefo mata tambayar muryata na ɗan rawa ,ƙwanda ta kai min ga kai tana cewa “ munafuka kamar ba ta son auren ,tashi don ubanki ki je suna jiran ki”
Wani kallabi na jawo na ɗora a kaina kafin na fita,a cikin rumfa na gan su a zaune kan kujera sun tsurawa ƙofar ɗakinmu ido.
Dakyar na aro nutsuwa na gaishe su“ ina wuninku?”
“Lafiya lau amaryarmu” suka amsa su duka biyun lokaci guda,a fakaice na ƙare musu kallo suna sanye cikin dogayen kaya amma babu wanda ya ɗora hulla duk da ƙwan fitilarmu bai da wani haske sosai amma hakan bai ɓoye min ganin kamanninsu da Aliyu ba.
“To mu za mu wuce dama mun zo gaishe ki ne,kasancewar ɗazu dandazon mutane yayi yawa ba mu samu muka gan ki ba ” ɗaya ya faɗa ,kafin su miƙe dukkan su.
“To na gode” shine abin da na faɗa ina mai shigewa ɗaki ba tare da jiran sai sun tafi ba ko kuma tunanin yi musu rakiya.
“Har sun tafi?” Mama ta jefo min tambaya,na gyaɗa mata kai ta ce “ mene ne suka kawo miki?”
“Babu komai Mama ” na faɗa a sanyayye.Ta ja tsuki kafin ta ce “ wannan shegen sanyin halin ki bar shi tun yanzu,don gidan yawa za ki je sannan mijinki babban mutum ne wanda kullum cikin yin baƙi yake dole ki yi tunanin zama da shi.Yanzu su baƙin kin basu ruwa ma?”
Cikin na dube ta na ce “ Mama ruwan me za su sha su da ba wani abinci suka ci ba?” ludayin miya ta jefo min aka yi rashin sa'a kuwa ya same ne ga ƙwandar ƙafa,na saki ƙara tare da soma yin hawaye.Nan Mama ta rufe ni da balbalin bala'i da masifa sai da ta yi mai isarta sannan ta yi shiru.
Haka na rakuɓe can jikin gini ina shafar hawaye,ƙafar kuma tuni ta ɗan kumbura tana min zugi. Tausayin kaina ne ya kama ni,ina daga gefe ina kallon ƙannaina suna lesson tare da yin hira jefi-jefi a tsakanin su amma ni tamkar wata mujiya sun maida ni gefe.
‘ Allah ke da magani,da wannan masifar ta Mama ai gara na yi auren na bar mata gidanta ’ na faɗa a zuci kafin na kwanta kan tsohuwar ledar ɗakin sai baccin wahala.
Washegari kamar yadda Mama ta sunnanta mini a kowacce safiya zan miƙe na haɗa wa ƴan makaranta abincin safe haka na tashi tun da sauran duhu na fita zuwa madafa.Dakyar na samu wutar ta kama,na ƙara wanke tukunyar kafin na ɗora kan murhu na zuba ruwa.
Garin ɗan wake na ɗauko na zuba kayan haɗi na kwaɓa,kafin na je na share tsakar gida tasss.Ko da na gama tuni tukunyata ta tafasa,sai da na wanke hannuna sosai kafin na jefa ɗan waken sai kuma na shiga yanka albasa da sauran abubuwan da zan soya mai da shi.
Ba ni na ida aikin ba sai ƙarfe bakwai da wasu mintina,sai na hau kuma wanke kwanuka.Ina nan a zaune ƴaƴan takarda suka fito duk kowacce ta yi wanka ta shirya.
“Janikiii?” Mama ta ƙwala min kira,jiki na ɓari na tafi a guje don amsa kiran hakan ya tuna min da ciwon ƙafata sai na tsangale ƙafar ina mai raba ta da ƙasa.“ Mama ga ni ?” na faɗa ina yamutsa fuska saboda zugin da ƙafar ke yi min,“ daga nan bakin ƙofa za ki tsaya ?” ina jin haka na san da akwai matsala amma na daure na ida shiga,kamar jira take ta kai min duka tana mai cewa “ da kika girka abinci ubanki ya kawo shi da za ki ce ba za ki zuba musu ba? Har da wani zaginta kina yi mata gorin cewa kin kusa bar musu gidansu”
Ina jin haka sai na ɗaga kai na dubi Ayo don kuwa na tabbata ita ce ta ja min sharri,ina hawaye na fito na shiga madafa na zuba musu abin karyawa na kai musu.
Wanke-wanken da na ƙare cikin kuka kenan,da za su tafi don tsokana har da ce min ta yi “ ƴar aiki mun tafi makaranta” ban kula ta ba sai Sarah ce ta shigar min ta hanyar bangazar ita Ayon.
Bokiti na cika da ruwa na je na yi wanka,ko da na fito sai na tarar da robar da na ajiye ɗan wake a tsakar gida alamu ya ƙare.
” Mama ina nawa?” ita ce tambayar da na yi ko da na shiga ɗaki don yunwa nake ji jiya ban ci komai ba na kwanta,duk da ba mu yi girki ba amma su sun ci wanda aka tarbi baƙi da shi.
“ Ba ki ci ba ne? To ya ida ” ta bani amsa tana mai ci gaba da cin nata wanda ta baɗe da yaji sosai har sai da yawuna suka tsinke.Ban ƙara cewa komai ba na je na buɗe jakar kayana na ɗauko mai na shafa kafin kuma na fita zuwa ƙofar gida.Kan dakali na zauna ina magana ni ɗaya “ Yesu kana dai ganin halin da nake ciki amma ka yi shiru,sai yaushe ne zaka amsa kokena?” sai kuma hawaye suka zubo min,na duƙe kai ina mai ci gaba da kukan haɗi da ɗaukar wata tsumagiya na soma wasa da ita ina yin zane.
Inuwa na gani kai gare ni,da wani mugun sauri na ɗago kai sai muka yi ido huɗu da wani kyakkyawan saurayi.Ya sakar min murmushi kafin ya miƙo min hankici,ban karɓa ba sai farin hannunsa da ƙure da ido ina kallon yadda jijiyoyin hannunsa suka fito sharrr da su tsabar hasken fatarsa.
Kan fuskata ya jefo min hankicin ya kuwa rufe ta ruf,da mugun sauri na lumshe ido tare da buɗe ƙofofin hancina ina shaƙar ƙamshin turaren da ke kan kyakkyawan farin ƙyallen. Can kuma na sa hannu na cire shi daga kan fuskata,sai dai wayam ban ga saurayin ba.Waige-waige na soma ko Allah yasa na gansa sai dai tsit layin yake babu kowa ,na miƙe tsaye ina mai cewa “ to ina kuma ya tafi? Amma ai bai kai ace har yayi nisa ba” sai kuma na maida dubana ga ƙasa inda sawun takalminsa ya fito raɗam har da wasu harufa,kamar wata zarariya haka na soma bin sawun takun takalmin ina tafe ina mamaki har na zo hanyar fita gari.Sai kuma na yi tsaye ba tare da na ƙara taku ɗaya ba,na ce “ cab! Ashe ba ɗan ƙauyen nan ba ne ai wannan da gani ma sai a babban birni” sai kuma na juya zan koma,abin mamaki sai na ga nisan komawa can gida ba kamar tafiyar ba.Sai ma a lokacin na yi da na sanin abin da na yi don da wuya har zuwa wannan lokaci ace Mama ba ta neme ni ba.Na kwashe sama da minti talatin ina tafiya kafin na isa gida,sai na tarar Mama ba ta nan sosai na ji daɗin haka kawai na shige ɗaki tare da kwantawa saboda muguwar gajiyar da na ji ta saukar min.
A firgice na farka jin sautin muryar Mama tana zagina tare da jefo min tambayar da ta hantsila hanjin cikina “ ina abincin da na ce ki yi kafin na dawo?”
Ido na shiga zarowa saboda ni na kasa tuna lokacin da muka yi da ita na yi girki,ga ƴan makaranta kuma sun yi tsaye sun zubo min ido da alamu sun kwaso yunwa.
“ Don ubanki ba magana nake yi miki ba? Ina dambun da na ce ki yi?” Mama ta faɗa tana zuba min dundu a baya,cikin azaba na ce “ yana madafa cikin tukunya” a yadda na yi maganar cikin haƙiƙanin gaskiya ƙila shi ya saka Mama fita,ni kuwa da na san ban yi komai ba sai na ƙara tsurewa na zauna zaman jiran ta dawo na karɓi hukunci.
“ Ke Ayo kika ce ba ta girka komai ba,je ki madafa ki zuba kan babban kwano a ci gaba ɗaya” Mama ta faɗa bayan ta dawo ɗakin.Sam ban yarda da abin da ta ce ba sai da Ayo ta shigo da dambu yana ƙamshi,duk suka kewaya suka soma ci suna santin yayi daɗi.Ni kuwa ido na tsura musu tare da yin saƙo ina ta son tuna lokacin da na yi dambun,“ Janiki ina kika samu kifi?” tambayar Mama ta katse min tunani,murya na ɗan rawa na ce “ Abba ne ya aiko da shi”
Cike da masifa ta ce “ don baƙin hali irin naki shine kuma kika saka shi a miyar dambu?”
“Na rage saura yana madafa” na sake sharo wata ƙarya ba tare da na san dalili ba,da wani irin sauri Ayo ta miƙe ta je ta ɗauko Kifin nan kuma suka shiga ci ban sani ba daɗin kifin ne ya shagaltar da su suka kasa ganewa kifi ƙwaya ɗaya sai ci suke ya ƙi ƙare wa ko yaya.
Amma ni kam na lura da hakan,sai ya zamana tsakanin ƙaryar da nake yi tana zama gaskiya da kuma wannan abin al'ajabi wanne ya kamata na fi jin tsoro......
[13/12 à 08:05] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽
Na
*Chamsiya Laouali Rabo*
```{MRS SADAUKI}```💫✍️
*FCWA* ☀️
*SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊
___________________________________
03
Abu dai kamar a mafarki ya tabbata gaskiya ne duk abubuwan nan da ke faruwa.Bayan sun ci sun ƙoshi suka ture Kifin wanda har yanzu kamar yadda Ayo ta ɗauko shi yake ko kaɗan bai ragu ba,“ ga shi nan ki ci ba don halinki ba” cewar Mama tana watso min mugun kallo.
Dakyar na iya ɗaga ƙafa na je na ɗauki kwanon da kifin yake ciki na fita can tsakar gida,kasa ci na yi sai aukin tunani da na fara.
‘ To duk wannan wa ya ajiye shi? Ko dai saurayin ɗazu? To in haka ne wane ne shi? Ko aljani?’ sai kuma na waro ido a take kuma na ji wani tsoro ya mamaye ni.
Ƙugin da cikina yayi shi ya fargar da ni da yunwar da ke ƙumshe da shi tun safe ban ci komai ba.Haka kawai na ji ban iya cin abin da ban san waye ya ajiye shi ba.Can madafa na kai na ajiye shi sannan na fita zuwa maƙwabta gun ƙawata Rahila,na kuwa yi sa'a ummarta ba ta gidan don sosai ta tsani ƙawancen namu duba da yadda na zama mujiya a cikin ƙauyen babu mai ƙaunar ya raɓe ni.
“ Laaa! Wai ke ce? Yanzu kuwa nake shirin zuwa gidanku na kai miki ɗan malele da na yi” Rahila ta faɗa cikin fara'a.Na saki murmushi na ce “ kamar kuwa kin san tun safe ban ci komai ba”
Nan take yanayin fuskarta ya canza ta ce “ ba ku yi abincin ba ne ko kuwa yau ma hana miki suka yi?”
Na ce “ bani da na ci na ƙoshi na baki labari” ba ta musa ba haka miƙo min shi cikin kwanon mai murfi,na buɗe tare da zauna wa na soma ci .
“Akwai sauran yajin ne ki ƙara min?” na tambaya,ta je ta kawo min kafin ta ce “ wane labari ne za ki bani?” ban ɓoye mata ba na labarta mata batun ɗan waken da Mama ta hana min har zuwa aljanin saurayin yau da kuma abubuwan mamakin da suka faru.
Rahila ta ce “ ki ce gamo kika yi da aljani na ƙwarai,kin san da cewa ita ma Asabe ta taɓa ganin wani ɗan albarka har ya taimake ta ?”
Na waro ido na ce “ wai kuma aljani da gaske?”
Maimakon ta bani amsa sai ta canza zancen da “ jiya wai bushe-bushen mene ne aka ta yi