Showing 24001 words to 27000 words out of 38502 words
Chapter 9 - BAWAN ALLAH COMPLETE DOCUMENT BY Maman Muhammad .txt
shi duk biyu akai sai abin ya d'aure mata kai
Shiko Aminullah duka biyu ne Ummi tamai ga mummunar fassara gashi ta ce mishi ita matar aure ce ,
Cikin sauri Hafsa ta k'araso kusa da Aminullah tana fad'in meke faruwa ne ?"
D'ago jajayen idanuwan shi yayi ya fara magana cikin sark'ak'yar murya "wai dagaske Zainab na da aure?" Ita ce tambayar da ya watsa mata. .
With confidence Hafsa tace "Eh matar yayana ce"
"To ina mijin nata yake ? Meyasa bata sanar masa matsalar ta da D'an Asabe ba?" Yasake jeho mata wata tambayar
Ajiyar zuciya tayi tace " is a long story"
Katseta yayi da cewar "I need to know"
Bada b'ata lokaci ba tayi mishi briefing wace ce Ummi,
[1/11, 1:06 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONE💋*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*HAPPY ONE YEAR ANNIE PURE MOMENT OF LIFE WRITERS❤*
*Dedicated to REAl PURE MOMENT OF LIFE WRITERS sisters we're the best ever , let's continue shining like a ster in the sky🌠🌠😍*
*Readers ina mai Baku hak'urin rashin jina da kukayi kwana biyu wani uziri ne na musamman ya tsayar da ni amma insha Allah zaku rink'a jina akai akai*❤
*godiya mai tarin yawa gareku masoya na da fatan alkhairin da kuka yi agareni nagode Allah ya bar k'auna,*😍
*BAWAN ALLAH fans kullum burina shine nishad'an tar daku , Allah ya barmu tare*🤝
❤ *k'awalli*🤪 ❤
3⃣2⃣
Ummi kuwa bata zame ko ina ba sai gida , tana shiga gida Mama ta kalle ta da mamaki tace " a 'ah Ummi har an da wo?"
"Eh Mama"
Mama ta sake tambayar ta " ina 'yar uwar taki take ?"
"Tana chan baya ni nayo gaba ne " Ummi ta fad'i tana tura k'ofar d'akin ta ,
Mama ta girgiza kai cike da al'ajabin hali irin na Ummi
Ummi kuwa koda ta Shiga d'aki wurgi tayi da jakar makarantar ta fad'a katifar ta tana ta tuno kalaman Aminullah tabbas tasan da babu Abdallah ikon Allah ne kad'ai zai iya sa bata auri Aminullah ba domin yafi Abdallah'n' da ta sani had'uwa sai dai kuma bata San ya zuciyar shi take ba ga kuma zargin da take mishi , haka tayi ta juyi tana tunani ,
koda Hafsa ta shigo class Neman ta suka ce bata dawo ba tayi Neman har ta gaji daga baya dai ta yanke shawarar komawa gida ko ta koma ,
Ta fito dai dai bakin gate taga motar Aminullah yana ta zabga mata horn da dai kamar zata wuce sai kuma ta tsaya ,
Fitowa yayi daga cikin motar da kaganshi zaka gane hankalin shi ba'a kwance yake ba Dan har idon shi yayi ja cikin sanyin muryar shi yace "Hafsat ina zuwa ne ?"
"Gida " ta bashi amsa atak'ai ce
"To muje na sauke Keki mana kinga ana wuyar mota "
"A ah ka barshi zan jira "
"Hafsat kenan saboda na b'ata ma k'awarki rai shine zaki hau fushi dani ?"
"Ko kad'an yanzun muka je gida dakai kuma Kasan laifin kaina zai dawo "
"Babu Wanda zaisan Nina maidoki Idan kuma baki yarda da ni ba I can't furse you"
Shiru ta yi na D'an lokaci tasan dai indai bata bishi ba to batasan ranar samun abun hawa ba nan tace mishi "shikenan muje"
Nan da nan yaji zuciyar shi tarage suyar da take mai domin yasamu hanyar ba Ummi hak'uri ,
Bud'e mata motar yayi ta Shiga sannan ya rufe shima ya zagaya ya Shiga sai da ya hau titi sosai sannan ya juya yace mata " sis ina zamu je ne ?"
Kwatan chan tamai cikin 'yAr dariyar shi da iyakarta fuska yace "Ashe ma bamu da nisa"
"Uhum" kawai tace ta maida kallon ta titi , daga nan kuma babu Wanda ya k'ara magana ,
Dai dai sanda ya Shiga unguwar su ana ta kiraye kirayen sallar issha , agurguje yayi parking motar a k'ofar gidan da ta nuna mai ta fito daga motar kenan sukayi ido biyu da Malam yana ta sauri zashi masallaci , kallon da taga Malam ya mata ya sata shigewa gidan aguje , Aminullah ma nan bar motar shi ya wuce masallaci ,
Yadda Mama taga Hafsa ta shigo ba natsuwa yasa gabanta fad'uwa "ke lafiyarki kuwa kinwani shigo kamar an koroki "
Hafsa ko sai zare ido take ,
Mata ta daka mata tsawa"ke Dan gidanku!?
Zumb'ura baki tayi tace "ba komai fa Mama"
Ta d'aga labulen d'akin Ummi ta fad'a ganin Ummin na sallah ne ya sata fita domin itama ta sauke nata faralin ,
Malam kuwa banyan sun idar da sallah ya tsaya bakin masallaci domin jiran saurayin da ya ganshi da Hafsa domin yana son yasan mene ne tsakamin su?
Bayan Aminullah ya fito daga masallaci ya fara tafiya kenan sai yaji sallama a bayan shi , cikin natsuwa ya juya tare da amsa sallamar Dattijon ya k'ara da cewar "ka wuni lafiya Baba?"
"Lafiya lau D'an samari , amma kai bak'o ne a unguwar nan ko?"
"Eh Baba "
Shiru ya biyo baya sai Malam ya sake cewa "na ganka tare da 'yata lafiya dai ko?"
Aminullah shiru yayi sannan daga baya ya ce "ni D'an makarantar su ne ganin yamma tayi gashi babu abun hawa shi yasa na dawo da ita"
Duk da cewar Malam ya yarda da nutsuwar yaron amma sai yaji hankalin shi bai kwanta ba musamman ma da yagan su su biyu ba tare da Ummi ba ,
Ya kalle shi yace" to ina 'yar uwarta?"
"Baba Zainab ta dad'e da barin school ina tunanin yanzun haka tana cikin gida "
Dai dai lokacin suka k'araso k'ofar gidan su Hafsa
Aminullah ya juya cikin kulawa yace "Baba ni zan wuce a huta lafiya"
"Ah d'ansamari ko ruwa baka sha ba bari nasa akawo maka ruwa "
D'aya daga cikin almajiranshi ya yafito , sai gashi cikin sauri ya k'araso Malam yace " Shiga ciki kace Hafsa ta kawo ma bak'o ruwa" ya fad'i yana nuna gidan su Hafsa
Sannan ya juyo ya kalli Aminullah ya ce "Bawan Allah zauna mana"yanuna mishi dakalin k'ofar gida sai da yazauna sannan yace "Baba suna na Aminullah"
"Masha Allah suna me daraja "
Alokacin da d'an Aiken Malam ya Shiga Mama ce kad'ai a tsakar gidan Hafsa na d'akinta tana shimfid'a Mama ta k'walla mata kira bayan ta fito taji sak'on Malam sai da gabanta ya fad'i nan dai ta daure tace "Mama ina Aunty Ummi ?"
"Taje gida duba Sani yana zazzab'i "
Jiki a sanyaye ta d'auki wani jug a d'akin Ummi ta kamfato ruwan randa a fita tana ta sak'e sak'e azuyarta,
Tana fita tayi kicib'in da Malam da Aminullah suna ta hirarsu kamar dama sunsan juna ,
Gaban tane yayi mummunan fad'i amma sai ta daure ta gaida Malam tare da aje ruwan , ta juya kenan zata Shiga gida ta ga Ummi a k'ame tana mata kallon tuhuta ,
Ahankali ta furta "Aunty Ummi?" Cikin tsoro ta k'arasa maganar
Sai lokacin su Malam suka lura da ita awajen , Malam ne ya kalleta ya ce " ke Ummi mekike awaje a irin wannan lokacin ?"
Murya na rawa tace "Baba Sani naje dubawa "
"Maza Ki shige gida "
Zata wuce kenan Aminullah yayi zumbur ya mik'e "tare da cewa Baba Dan Allah ka min izini nayi magana da Ummi"
Ummi najin haka ta fad'a gida aguje , kamar zai bita sai da Malam ya rik'oshi , Malam ya kalleshi cike da takaici yace
"Bata gaya maka ita matar aure bace?"
"Hafsa ta gayamin komai Baba laifi na mata shine nazo na bata hak'uri ne"
Malam dai abin ya d'aure mai kai kawai sai ya daure ya tambayeshi "wani irin laifi ?"
Nan dai Aminullah ya kwashe labarin farkon had'uwar shi da Ummi har zuwa yanzun ya fad'a ma Malam ,
Malam hankalinshi ya tashi jin wani yana farautar mutuncin 'Yarsa nan ya fara fad'a har yana cewa ma makarantar ta daina zuwa ,
Sam Aminullah baiji dad'in zanchan Malam ba nan ya fara fahimtar da Malam amfanin karatu da illar rashin sa ga al-umma musamman ma d'iya mace mai bada tarbiya Dan wani b'arayin dole anabuk'atar mata ,daga nanan yayi mishi alk'awarin kula da su matuk'ar yana numfashi ,
Gaba d'aya jikin Malam yayi sanyi da jin kalaman Aminullah kuma yayi na'am da zanchan shi Malam ya kalli Aminullah ya ce
"Yakai *AMINTACCAN BAWA* na baka amanar Zainab da Hafsa kamar yadda ka buk'ata duk abinda ya faru da su dakai zanyi kuka"
Duk da cewar gaban shi ya fad'i amma sai ya dake yace "insha Allah Baba babu abinda zai faru dasu sai alkhairi"
Hafsa da Ummi dake mak'ale a zaure suka kalli juna sukayi tsuru tsuru
Cikin mutumci da girmamawa Malam da Aminullah sukayi sallama bayan Aminullah ya ba Malam dubu biyu amma firr Malam yak'i amsa ahaka sukayi sallama
[1/12, 5:43 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONE💋*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*k'ungiya ta abin alfahari na😘*
*DEDICATED TO ALL HAUSA NOVELs WRITERS ina mana fatan alkhairi Allah ya bamu ladan fad'akarwa ya k'ara mana hazak'ar tunatar da masu karatu Amen*🤞
*Readers ban manta daku ba muna godiya bisa soyayyarku ga littafan mu*😍
*Masu cewa na manta da Abdallah, ku sani ba yadda za'ayi na manta da Abdallah domin shine jigon labarin ku biyobi a hankali Dan jin ya zata kasance*❤
*Page*3⃣3⃣
Kwanci tashi ba wuya yanzun su Ummi suna Hutu Wanda da zarar sun koma zasu 200level , ba laifi tad'an saki jiki da Aminullah amma duk da haka bata tab'a bari suyi fira , sai dai Hafsa ce k'awarshi.
*Umar*
Umar kuwa ko da mahaifiyar shi taga yana D'an samun rufin asiri tace lallai sai dai ya fara Neman aure , da taga bashi da niyya sai ta had'a shi da Malam , nan Malam ya kirashi yayi mai nasiha sannan ya amince , zai yi auren amma D'an k'ara mishi lokaci domin ya d'anyi shiri, mahaifiyar tace ta amince .
Wannan kenan
Ummi da Hafsa kuwa yanzun ankoma makaranta karatun su suke tuk'uru basuda matsalar komai , Aminullah shi yake kula da al'amuran su na makaranta , lokuta da ma shi yakan maida su gida duk da Ummi bata son hakan amma idan Aminullah ya nace mata da magiya dole take binshi su tafi.
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Yau shekara biyar kenan da b'atan Abdallah , Wanda ko me kama dashi ba'ace angani ba tun ana zuba idon ganin shi har an hak'ura da wannan *RUTACCEN ALAMARI* sun fawwalawa Allah komai .
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
To masu karatu bari na lek'a birnin London Dan ganin meke faruwa .
*W*asu kyawawan matasa ne na hango d'aya akwance d'aya kuma yana tsaye gaban wardrobe yana ta cillo kaya sama Dan k'areren gadon dake d'akin sai da ya d'ibi mai isarsa sannan ya rufe wardrobe d'in ya hau kitsa kayan shi awani kyakkyau sky blue d'in trolley , yana gama wa ya juya ya kalli na kwancen da keta faman lumshe idanuwan shi yace
"Friend Kodai bayau zaka bar k'asarnan bane?
Wanda aka Kira da Friend ya mik'e zaune tare da jingina da bango yace " Saif wallah bana jin tafiyar nan bansan mai yasa duk lokacin da naji sunan 9ja gabana ke fad'uwa ba , amma kuma wani b'arin na zuciya ta yana son koma wa ta bansan mai yasa hakan ke faruwa ba"
Ajiyar zuciya Saifullah yayi domin ya fahimci abokin nashi Dan tunda yake dashi be tab'a jin yayi hirar Nigeria ba ko wani relative nashi sai yai yana ganin kamar akwai wani *B'OYAYYEN AL-AMARI*da abokin nashi yake b'oye mai .
Cikin sanyi ya taka zuwa kusa da abokin nashi ya dafa shi tare da fad'in " ka kwantar da hankalin ka abokana mai yuwa wani alkhairi ne shiyasa zuciyarka ta aminta da komawar"
Cikin yanayin damu wa Abdallah ya d'aga k'ana nan idanuwan shi ya kalli abokin nashi kallon ban fahimta ba amma kuma sai bai ce komai ba .
Cikin tausasawa da lallashi Saifullah ya kwantar ma da Abdallah hankali yaryaji yana son tafiyar , nan ya mik'e suka cigaba da shirin su Kasan cewar yau zasu koma kuma flight di k'are hudu zasu bi .
Cikin dare suka sauka a Abuja Dr Ahmad da kanshi yaje taryar D'an nashi cikin sauri ya k'arasa ya rungume Abdallah yana fad'in "welcome to Nigeria son "
Da murmushi ya amsa masa sannan suka rungume juna .
Saif kuwa dama agida yace karsu zo tarbar shi su bari sai gobe sabo rashin kyawun hanyar .
Cike da fara'a Dr ya jawo Saifullah yana mishi sannu da zuwa .
Daga nan ya jasu zuwa gurin motar shi suka Shiga suka wuce gidan shi dake maitama.
Kusan raba dare suka yi suna hira Wanda Kasan firar Dr ne da Saifullah suke yi Abdallah ko jefi-jefi yake sa musu baki da ga baya dai ya gaji ya mik'e ya Shiga toilet ya d'auro alwala ya fara jero nafilfili , idan da sabo Saifullah ya saba da ganin hakan wannan d'abi'ar Abdallah Wanda shima yake k'ok'arin koyi da kyawawan halaye irin nashi .
Bayan Dr yayi musu sallama ya koma d'akin shi tunanin Abdallah ne suka addabe shi Wanda ba tun yau ba yake jin hakan , yanzun kam dole ya nemi mafita don baya son hak'k'in 'yan uwan shi ya kama shi wata k'ila ma yana da mata da yara idan ko hakane ya zama azzalumi kenan , da irin wad'an nan tunanin yayi barci Wanda sun zame mai jiki duk in yazo kwanciya sai ya yisu , .
*DA SAFE*
Bayan sunyi wanka sun shirya sukayi break 9:30 suka d'auki hanya bayan Saifullah ya kira mahaifin shi ya sanar masa da Dad d'in abokinshi zai dawo dashi .
Saifullah ne ya k'arb'i tukun suna tafe suna hira cikin nishad'i tun lokacin da suka doshi Zaria Abdallah yake ganin hotunan wasu abubu a idon shi sunan mai flashing tamkar video black white rutse idonuwan shi , duk wani moving d'in shi Dr yana gani sai bai kula shi ba Dan yana ganin wannan wani sign ne da Abdallah zai fara sanin koshi waye .
Ko da suka Shigo Zaria Abdallah duk ya gama zaucewa musamman ma da suka biyo ta kasuwar tudun Wanda Kasan cewar Saifullah D'an cikin tudun wada ne abun da k'ara d'aga mai hankali bai wuce da yaga shagon ogan Umar ba nan kam gaba d'aya durkushewa yayi a waje nan take zufar da yake yi ta k'ara yawaita , shi kanshi Dr abin ya bashi tsoro matuk'a , janyo shi yayi jikin shi yana shafa bayan shi.
Motsin da Saifullah yaji ana yi ne yasa shi kallon su tajikin mirror , yaga yadda abdallah jikinshi ke wani irin b'ari afirgice ya ce "Dr lafiya"
Shi kanshi Dr ya firgita kawai sai cewa yayi su wuce asibiti, mik'e titi yayi street *SHIKA* yake son kaisu domin nan ne yake ganin za'a ba abokin shi kyakyawan kulawa.
Kasan cewar basu had'u da cinkoson ababen hawa ba yasa acikin minti ashirin da biyar suka isa asibitin emergency aka kab'e shi aka wuce dashi wani private room nan likitoci suka duk'ufa akanshi .
Iya k'ololuwar tashin hankali Saifullah ya Shiga mostly yana ganin Abdallah a irin wannan halin amma nayau yafi gigitashi , ringing d'in wayarshi ce ta katse mai tunani da ya keyi ahankali ya zaro wayar cikin pocket d'in shi sunan da yagani ajikin screen d'in wayar ya fad'i a hankali "DAD?"
A nutse ya d'aga wayar gamida sallama bayan Anas sallamar maifin ke tambayar shi lafiya shiru har yanzun basu iso ba?
Cikin natsuwa Saifullah yake sanar ma dad d'in shi abunda ke faruwa .
Cikin mamaki dad d'in yace gashinan zuwa,
[1/13, 8:00 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONE💋*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Wannan shafin rankatakaf naku ne masoya Bawan Allah na mallaka muku shi aduk inda kuke fad'in k'asar nan Allah yabar zumunci da k'aunar juna Amin ❤🤞*
*Dedicated to Faty Axland🤪*
3⃣4⃣
Banda *SAFA DA MARWA* babu abunda Dr da Saifullah suke yi , sun d'ibi kusan minti arba'in a haka sai ga Dadyn Saifullah ya Iso cikin girmamawa suka gaisa da Dr sannan yayi masa ya mai jiki sai wurin ya d'auki shiru , chan Dr ya juyo ya kalle Saifullah yace "Saif kaje gida ka huta mana "
Cikin sanyi yace " no Dr bazan iya zuwa ko ina ba har sai nasan halin da abokina yake"
Dadyn Saifullah yace "gaskiya ne bari mu tsaya muga jikin nashi "
Ana cikin haka k'ofar d'akin da aka kwantar da Abdallah ta bud'e wani Dr ne ya fito daga cikin ta cikin ta ya k'araso kusa dasu yace " ina Baban Abdallah?" Dr yace" gashinan "
"Ina son ganin ka"
Cikin sanyin jiki Dr Ahmad ya bi bayan shi suka D'an tab'a tafiya kad'an sannan suka k'arasa office d'in shi bayan sun Shiga sun zauna Dr ya fara yima Dr Ahmad tambayoyi akan rashin lafiyar Abdallah ,
Ba tare da b'ata lokaci ba ya sanar masa da duk abunda ya faru har zuwa yanzun ,
Ajiyar zuciya Dr yayi yace "this is serious, but Dr meyasa baka yi k'ok'arin dawo masa da tunanin sa ba kuma ka k'asa sashi cikin wata rayuwar rud'ani ? Wannan serious case ne amma da tun farko ne da yanzun memory d'inshi ya dad'e da dawo wa "
Shi dai Dr Ahmad shiru yayi Dan duk abinda zai fad'a ya gama fad'i ,
Dr ya sake cewa "kuma abinciken da mukayi muna da tabbacin yana da connection da garin nan , Dan haka indai ka shirya nema masa lafiya to lallai sai dai ka barshi a nan zuwa wani D'an lokaci"
Bayan guntun nazarin da Dr Ahmad yayi yace" shikenan ba damuwa indai zai samu lafiya komai me sauk'i ne"
Dr yace "akwai yuwuwan hakan insha Allah"
"Zan iya zuwa na gashi ?"
"No har yanzun likitoci basu gama aikin suba ku k'ara musu lokaci"
Nan dai suka k'ara tattaunawa akan matsalar sannan suka rabu , alokacin da Dr Ahmad ya koma wajen Saifullah shi kad'ai ya tarar a wajen nan