Showing 33001 words to 36000 words out of 38502 words

Chapter 12 - BAWAN ALLAH COMPLETE DOCUMENT BY Maman Muhammad .txt

20 Dec 2024

2535

nata zuciyarta k'all.






Ummi kuwa duk haushi ne da takaici ya cikata wato yasan da zaman kowa amma banda ita? lallai ma meyake nufi ? badai jiran banza tayi ba?


Haka taita jero tambayoyi har Hafsa tazo ta sameta Cikin tsokana ta fara magana "Amarya angon naki ya dawo madadin na ganki cikin fara'a amma naga sai cin magani kike "




Wani kallon shatara shatakwas ta aika mata dashi , tsabar takaici ma ta rasa me zata ce.




Abdallah , Saifullah , Aminullah, tare da Umar suna tare har k'arfe Tara sannan Aminullah yayi hamma gami da salati yace "jama'a Bakujin bacci ne?"




"Subhanallah" cewar Saifullah yayin da ya kalli agogon hannun shi




Mik'e wa sukayi dukan su Mama na d'aki ta jiyosu ta lek'o cikin barkwanci tace " Amintacce inace pillows kawai zan mik'o muku".




Dariya kawai sukayi sai da suka rakasu har bakin mota sannan suka Shiga suka tada ita suka tafi , yarage daga Abdallah sai Umar .




Abdallah yace" kaima badai guduwar zakayi ba ko?"




Kallon shi yayi da idanuwanshi da sukayi fici-fici saboda tsabar bacci yace " jiyafa saboda tsabar k'osawa da nayi inganka Sam nakasa yin bacci"




Dariyar mugunta Abdallah yayi sannan yace " ayyah abokina "


Umar tsaki yaja ya k'ara gaba yana cewa" ajedai a rungumi pillow" gaba ya abinshi




Shikam dariya kawai yake yi ahaka ya Shiga gida .




Ummi kuwa tunda magrib tayi ta fara kwasan kayan da zata buk'ata adare ta maidasu d'akin Hafsa dan chan take so taje ta kwana .






Dai dai k'ofar d'aki taci karo dashi shikuma zai Shigo cikin hanzari ta fad'a d'akin Ummi kamar an wurgo ta , shikam abin ma dariya ya bashi d'akin ya nufa direct , yana ta k'are mai kallo komai nanan yadda yake da ba tarkace jakar kayanshi da Aminullah ya kawo mai ya tuna dashi fita yayi ya nufi d'akin Mama wadda har ta fara bacci a hankali ya d'auki jakar tare da sakayo mata k'ofa Kasan cewar yanayin sanyi ne , komawa yayi d'akin ya rage kayan jikinshi , sannan ya fito ya tunjumi ruwa arijiya ya nufi bayi ,






*kuyi hak'uri da wannan readers ina fama da ciwon kai*🤦‍♀🙏
[1/26, 4:53 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*




*MRS NN ONE💋*






® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_




# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com






Page 4⃣0⃣






Sai da ya watsa ruwan ajikinshi yaji wani sanyi yana ratsa shi , haka nan dai ya k'arasa wankanshi ya fito sai rawar sanyi yake yana Shiga d'akin ya fara Neman bargo chan gefen katifa yaga bargon Wanda da alama an ajeshine aka manta ba'a d'auka ba , aiko ba shiri ya d'auki bargon ya lullub'e har kai wanda duk da hakan bai hanashi jin sanyin da yake ji ba Wanda k'afafuwan shi da hannayen shi sukayi sanyi tarara sai wani kyarma yake.








A d'akin Hafsa kuwa Ummi keta k'orafi sai Hafsa taje ta d'auko mata bargon ta , ita kuma Hafsa tace bazata ba .




Da dai taga da gaske Hafsa take kuma ga dare yana dad'a yi ga sanyi yana k'ara sauka hakan ya sata fita ba shiri dan sanyi ya gama ratsata.




Da sallama ta Shiga d'akin idon ta duk ya rufe bargon ta kawai take hange bata lura da Abdallah dake ta rawar sanyi ba ta kai hannu tafara yaye bargon , bata Ankara ba taji an janyota an wurga ta cikin bargon tare da k'udundune ta , tafa ihu kenan taji an toshe mata baki , cikin muryarshi dake rawa yace


"Shhh ba abinda zan miki d'umin jikinki kawai nake so"




Ruk'on da yayi mata ya sata kasa k'wacewa a hannun shi , tana ji tana gani ya runk'a murza duk wata gab'a da keda d'umi ajikin ta Ummi tun tana 'yan k'ana nan kukan ta har ta daina domin ta fara jin dad'in abin , dukkan su basu San iya lokacin da suka d'auka awanan yanayin ba ita dai Ummi taji Abdallah shiru ne sai wata sassanyar ajiyar zuciya da yake hakan ya tabbar mata da cewar yayi bacci .




D'agowa tayi ta kalleshi yana ta sharar baccin shi azuciyar ta tace " kai maza kunyarsu ragagga ce " kayanta ta d'auka tasa sannan ta koma ta kwanta ajikinshi ta k'ank'ameshi tamkar zata farka taga bashi.






Tofa masoya ansha bacci Abdallah ne ya fara farkawa yaga da kyakyawar fuskar abar k'aunarshi ya fara tozali murmushi yayi ya furta a hankali " you are always beautiful my Queen" ahankali ya zameta ajikin shi ya mik'e sai alokacin ya lura da yadda gari yayi tangaras , dafe kanshi yayi yana fad'in "ya subhanallah"




Cikin hanzari ya zura jallabiya ya fita bokiti ya d'auka ya nufi kitchen dai dai lokacin Hafsa ta d'aga tukunyar ruwan zafi zata shek'a ma kama ya ce


"Ke! Ke! Tsaya"


tsaf ta gane me yake nufi dan ta d'ago ta kalleshi amma sai ta k'ara seta tukunyar da bakin bokitin


Cikin kirne fuska yace " ina mai tabbatar miki kika juye ruwan nan duk zafin shi sai kin shanye shi"


Yadda yayi maganar ya bata tsoro shiyasa ta aje tukunyar , aje bokin yayi yace" zubamin" ta d'auki tukunyar ta zuba ruwan rabi , ahasale yace " wai ke kinraina nine ko to duka zaki juye "




Sai alokacin tayi magana " to kokon fa?"




"Ki dafa wani ruwan dallah ni juyemin "




Ahaka tana k'unk'unai ta juye ruwan ba don ranta yaso ba .




Wani bokitin ya d'auka ya raba ruwan zafin biyu duka ya tafi rijiya ya surka su sannan ya aje bokiti d'aya a k'ofar d'aki ya tafi da d'aya bayi .




Hafsa ko baki ta saki kamar wawiya azuciyar ta tace "idan baka mutu ba baka gama ganin abun mamaki ba " hakanan ta sake d'aura wani ruwan kokon.




Ummi kuwa tunda ya fita ba dad'e wa ta farka kunya ce ta hanata motsi Sam tana zaune har Abdallah ya fito wanka tana jin motsinshi tayi sauri taja bargon tafe har fuskarta da sallama ya shigo tana ji bata amsa ba




A hankali ya fara magana " Ummi kije ga ruwa can a k'ofar d'aki kiyi wanka 8 ta kusa "


Zumb'ura baki tayi ta yaye bargon ko kallon inda yake bata yiba, yadda ta d'aga labulen ta lek'a ba k'aramar dariya ta bashi ba aciki yake dariyar .


Tunda ta lek'a ta hango ba Mama a tsakar gidan sai Hafsa da ke shara yasa ta fita ta d'au bokitin , me Hafsa zatayi inba dariya ba .




Lokacin da tagama wankan Mama ta fito tsakar gidan Ummi tana tsaye a bayan k'ofar bayin ta na lek'e ita ala dole sai Mama ta Shiga d'aki zata fito .




Kamar ance Mama ta kalli k'ofar bayin ta hango Ummi a tsaye ta d'aura hannu akai , murmushi Mama tayi ta mik'e ta Shiga d'aki Ummi na ganin haka ko tsayawa d'aukan bokitin batayi ba fella d'akin Hafsa .Hafsa ko sai shak'ar dariya take abinta .




Ummi na Shiga ta chanja kaya ta tada kabarar sallah.




Abdallah kuwa tunda ya jira Ummi bata shigo ba nan ya mik'e ya fito ba kowa a tsakar gidan hakan yasa kai tsaye d'akin Mama ya nufa ya sameta tana ta gyaran 'yar tsohuwar drower kayanta cike da tausayin mahaifiyar tashi ya gaisheta ta amsa mai fuska a sake , d'akin ya d'anyi shiru sai Mama ta katse shirun da cewa " abincin Ku nanan a k'ofar kitchen " to kawai yace ya mik'e dan gaskiya yana jin yunwa , yana bud'e kwanon yayi arba da d'umamen tuwon masara miyar busashen kub'ewa " oh my GOD" abinda ya fad'i kenan ya rufe kwanon ya fita machine ya hau yaje wani restaurant yaci abinci sannan ya kira number Umar ya tambayeshi yana ina , Umar yace" yana gida yanzun zai wuce kasuwa"




"Kajira ni ganinan zuwa " ya kashe wayar




Ko da yakoma gida yayi karo da motar Saifullah a k'ofar gidan su k'arasawa yayi ya gaida Malam da keta fama da almajirai , sannan ya bar gurin ya Shiga gida still bai ga Saifullah ba , nan ya kira wayarshi ringing biyu ya d'aga bayan sallama Abdallah yace


"Aboki ya naga motarka ban ganka ba?"


Dariya Saifullah yayi yace " gatanan aro na baka kafin kasiya taka amma ka sani idan ka tashi mayar min sabuwa zaka siyan mun"




Abdallah ma dariya yayi sannan yace " to waya gaya maka ina San kwancen wasu "


Haka dai sukayi ta barkwanci daga k'arshe Saifullah ya ce mai "key d'in motar yana bayan k'ofa a sagale a zaure "




Da haka sukayi sallama irin tasu ta abokai.




Fita ya sake yi dan so yake yaje ya siyo kayan abinci dan gaskiya ba zai iya cimar nan tasu ba ya saba da irin cimar turawa 😨




A b'angaren Ummi kuwa Sam tak'i fitowa saboda kunya sai da Hafsa ta kaimata abinci , sannan ta ce mata ta shirya suna da lecture anjuma , wannan dalilin ne ya fata mik'e wa daga inda take ta fara shiri , ahankali take fitowa sai da tazo dai dai k'ofar d'akin ta sukayi clashing da Mama ta fito band'aki , akunyace ya gaisheta Mama ta amsa sannan ta wuce ita kuma ta wuceta d'auko abunda take buk'ata ta fito ,






Lokacin da suka je makaranta suka samu lecturer yace bazai Shiga ba sai 4 kowa yana ta Allah wadaran halinshi , kowa ya fita ya kama sabgogin gaban shi ,




Hafsa kuwa Aminullah ta kira ya Zo shima suka zauna suka dasa shiriritar su , ita kuwa Ummi tsaninta dasu ido , ana haka suka tsinkayi muryar Saifullah yana cewa "to na mamajo"




Aminullah na had'a ido dashi ya d'aure fuska dan yasan yanzun zaizo ya takura mai




Zama yayi kusa da k'aninshi sannan ya ce ma Ummi" Madam d'in mu ina wuni?"


Akunyace ta amsa da taso ace ita ta fara gaisheshi , Hafsa ta gaidashi a dak'ile shima a dak'ilen ya amsa mata , juyawa yayi ya kalli Ummi yace


"Wai wannan k'anwarki ce "


Ummi tambayar ya bata dariya amma sai ta kalli Hafsa taga yadda ta d'aure fuska itama sai ta tsare gidanta tace "eh k'anwa tace "




Hafsa dan takaici kamar tayi kuka .




Sai kuma ya sake jefo mata wata tambayar " k'anwarki ta jini ko kuwa"




Tsaki Hafsa Hafsa tayi ta tashi tabar gurin , Aminullah me zaiyi inba dariya ba




Ummi tace "ah ah k'anwar yata Abdallah ne shima kuma y'ar wan Mama ne"




"That's great ina jin nan zan maida shek'ata"




Da sauri Aminuallah ya juyo yace " what do you mean?"


"Abinda kunannan ka yaji "




" to da sakel inji Fulani , wai kai yayan nan duk abunda nace ina so sai ka yi k'ok'arin rabani dashi " ya ko had'e rai ya juyar da fuskarshi gefe




Saifullah gyara zamanshi yayi yace " mekake nufi ?"




" ina nufin ina son Hafsa haka sanda ina tsak'a da son Ummi ka fara k'ok'arin rabani da ita wannan kam bazan barma ita ba I have already win her heart , go and find your own"


Ummi kam rufe fuskarta tayi ta runk'a shek'a dariya abinta....






Follow me readers*


*Maman Muhammad d'inku ce*😎
[1/27, 9:12 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*




*MRS NN ONE💋*






® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_




# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com




*Nafi khan Nd k'awalli wannan page d'in nakune zamuga Wanda za'a yi ma gwalo kwando kwando*😜😜


*Amma fa kar ace nayi nayi son kai ehe*😉




*ina gefe ina cin daria*😁🤭


*edited by husnah beauty love you sis*😉


*page* 4⃣1⃣






Wani bak'in ciki ne ya tokare Saifullah amma sai ya dake ya ce " zo muje D'an k'anina musa contains kar Madam tayi mana dariya"




Nok'e kafad'a Aminullah yayi yace "nak'i wayon "


"Haba my little bro my best friend ever "


Da k'yar ya lallab'eshi suka matsa gefe kad'an .




Ita dai Ummi tana gefe tana cin dariya




Can sai taji Aminullah ya na cewa " asshhh da zafi fa " ko da ta juya ta kalleso sai taga suna ta dariya har da rungumar juna , nan suka canja salon hirar tasu .


Sai da sukayi sallar la'asar sannan suka Shiga lectures .






Ba su duka Shiga gida ba sai k'arfe 7:30 , ga wahala ga yunwa agurguje sukayi sallah sannan kowa ta mik'e awurin don jiran sallar isha Ummi kuwa wani wahalallen bacci ne yayi awon gaba da ita Hafsa da taga tayi bacci saita fita ta tafi d'akin Mama , tana d'akin Abdallah ya shigo yana shigowa bayan sun gaisa yace ma Hafsa


"Ke kira min Ummi"


"Tayi bacci "


"Baccin gaske ko baccin k'arya ?"


"Wallahi tayi bacci tun d'azun "




"Go and call her for me my Friend!"


Sumi sumi ta mik'e ta fita , Ummi na bacci taji ana jijjigata ana kiran sunan ta , tana bud'e ido taga Hafsa ce taja wani wawan tsaki ,


Hafsa abun ya bata haushi tace "oh ga marainiyar wayaunki ko , to bani ke kiran Ki mijin Ki ke kiranki "




Cikin muryar bacci tace "baki ce mai ina bacci bane ?"




"Na gaya miki Malama Ki tashi kije kafin ya gaya wa mutane a matse yake dan naga yana gab"




"Bafa inda zanje idan kinga na tashi awajen nan to Tara tayi "




Baki a sake Hafsa tace " eyyeh haka kika ce , ni 'yar sak'oce , kar ya huce a kaina "




Hafsa ta fita taje d'akin Mama baya nan sai ta tafi d'akin su sallama tayi ak'ofar d'akin sai da ya amsa sannan yace "ya akayi kuma ?"




Kai tsaye tace " tace ba zata zo ba"




Shiru yayi sannan yace "tana da waya?"


"Eh"


"Bani number ta"


Nan da nan ta rattafo mishi numbers din sannan yace mata "jeki " ta tafi tana sauke wani nannauyan ajiyan zuciya,.




Tana kwance taji wayarta na ringing da kamar ba zata d'auka ba sai da kiran ya kusa katsewa sannan ta d'aga tare da sallama ,




Amsa sallamar kawai yayi sannan yace " kizo Ki sameni ad'aki ina jiranki minti biyar kawai na baki" k'itt ya kashe wayar ,




Wata zuciyar tana cemata taje wata zuciyar tana cemata kije ya sake rik'e Ki irin na jiya Ki kwashi abun kunya da safe shi ba ruwan shi🤷‍♀


Can kuma dai me tatuna oho sai ta mik'e ta fita , tana zuwa bak'in k'ofar tayi ta jero sallama bai amsa ba sai da ya mula ya mulmule sannan ya amsa be ce mata ta Shiga ba ita ma kuma bata Shiga ba takai kusan minti biyar awajen sannan ya ce


"Idan baki gaji ba to kiyi ta tsayuwa " ba shiri ta banko labulen ta shigo ta nemi gefe ta rakub'e kamar wata bak'uwa,




Juyawa yayi ya kalleta cikin tsare gidan shi yace mata " Ummi na lura Sam bakya murna da dawowa ta "


Cikin sauri ta d'aga ido ta kalleshi kallo me tattare da alamar tambaya




Shima kallonta yayi yace "yes da kin damu dani da zaki nuna farin cikinki gareni amma dayake ba damu wa da ni kikayi ba sai wa wasan b'oyo mukeyi "




Ita dai ta kasa magana Wanda tasan har ga Allah ko mahaifiyashi da wiya ta kaita zumud'in ganin shi , tana cikin tunani taji muryar shi yana cewa " shikenan tunda ni ba bazaki iya magana ba kije kawai "




Ba tare da tayi tunanin komai ba tayi waje abinta .




Abdallah kam bak'in ciki ne ya isheshi wato ma ba zata iya zama kusa dashi ba me take nufi ? Irin wannan tunanin yayi tayi har dare ya raba sannan ya fita ya d'auro alwala .






Ummi kuwa d'akin Hafsa ta koma ta k'udun dune cikin hijab d'in ta tana ta kuka azuciyarta tana fad'in " ina ma ace zan iya fad'a maka sirrin zuciyata , ina ma ace zan iya fad'a ma irin kewarka da nayi ina ma ace zan iya fad'a maka irin farin cikin da nashiga lokacin da ka bayyana agareni amma bazan iya ba dan duk sun wuce gaban kwatance sai dai a aikace mijina "


Irin wad'an nan kalaman tai ta fad'i cikin mayan shauk'in soyayya har Hafsa ta dawo daga d'akin Mama ta same ta wajen tana kuka ,




A hankali Hafsa ta zauna gefen Ummi tace " Aunty Ummi lafiya ?, me ya faru?"




Kamar jira take dama akulata sai ta zauna ta dasa sabon kuka , da k'yar Hafsa ta lallesata sannan ta sake tambayarta me ya faru cikin kuka take sanar da ita yadda sukayi da Abdallah .


Hafsa ko mai zatayi inba dariya ba Ummi kam had'e rai tayi tace " saboda wulak'anci kice na gaya miki damuwata madadin Ki bani shawara sai tsaya kina yi min dariya ?"




Cikin dariya Hafsa tace " yo Aunty Ummi AI ke d'in ce sai a hankali"




"Da nayi me fa?"




Murmushi tayi tace "Aunty Ummi yaya Abdallah kulawar Ki yake nema kin kasa ganewa yanzun haka ma k'ila ko D'an welcome kiss d'in nan baki mishi ba , au ko dayake bari nayi shiru naga jiya kun kwana d'aki d'aya " ta k'arasa maganar tana dariyar mugunta .


Ummi kam abin ya k'uleta ta d'auki pillow ta makawa Hafsa tare da fad'in " wallahi baby bakiyi ba"




Duk suka kwashe da dariya daganan Ummi ta mik'e ta d'auro alwalar sallar isha da batayi ba sai da tayi sannan 'yan hanjinta suka fara Neman agaji , ba shiri ta nufi kitchen shinkafa da miya ta tarar miyar taji soyayyen nama sai buga k'amshi take nan tazubo taci sannan ta koma ta kwanta.








*DA SAFE*


Kamar yadda Umar yake yi yanzun kafin ya tafi kasuwa sai yazo sunsha hira da Abdallah sannan ya wuce , yauma suna tsaka da fira sai Umar yace


"Aboki nima fa na kusa Shiga daga ciki "




Cikin sauri Abdallah yace " Allah mutumi na "


"Wallahi kuwa , yau saura sati biyu"




Had'e fuska Abdallah yayi sannan yace " amma gaskiya bana kyauta min ba sai yanzun kake gaya min"




"Kayi hak'uri abokina na bari ka samu natsuwa ne sai muyi maganar "


Ajiyar zuciya yayi sannan yace " shikenan Allah ya Santa alkhairi , a ina ka samu matar?"




"A funtua 'yar k'anwar Mama ce"


"Hakan yayi kyau , to ya maganar kayan aure an had'a ?"


"Eh an gama komai "




"Masha Allah na tayaka murna sosai , a ina zaku zauna?"




"A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login