Showing 1 words to 3000 words out of 38502 words

Chapter 1 - BAWAN ALLAH COMPLETE DOCUMENT BY Maman Muhammad .txt

20 Dec 2024

2529

[12/12/2017, 5:59 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*




MRS NN ONE


*Bismillahir Rahmanirrahim*
Yaa Allah yadda ka bani ikon farawa lafiya Allah kasa na gama lafiya batare da na kauce hanya ba ALLAHUMMA amin


Bawan Allah labari ne da ke cike da tsantsar tausayi tawwakali talauci da kuma soyyaya wanda bawan Allah labarin wani matashine wan da iya yensa basu karfi yatashi shine ak'ark'ashin kulawar mahaifiyarsa, Ku biyoni domin jin ya labarin zai Kasan ce






® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_




# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com




Page1⃣




Zaune yake akan dakalin k'ofar gidan su ya jingina da jikin gini daganin alama yana cikin tsananin damuwa hakan yasa har wani yazo yaita sallama bai jishi ba sai da ya dafa kafad'ar sa sannan yace " Haba Abdallah wannan wani irin tunani ne ina ta sallama baka jini ba "




Wanda aka kira da Abdallah yace"uhum Umar kenan ba dole kaga ina tunani ba kafi kowa sanin halin da nake ciki dole nayi tunani "




"Hakane aboki na amma ya kamata ka rage Dan kar ka haifar wa kanka da wata matsalar "cewar Umar


"Ina k'ok'arin ragewa Umar abin ne yafi k'arfi na wallahi"


"Allah ka iya mana ka kawo mana mafita"


"Amin" cewar Abdallah




Umar ne ya ce"ya naga ka zauna ko ba muda wurin zuwa ne yau?




Murmushi Abdallah yayi Wanda da gani bata wuce fuskarshi ba yace" akwai gurin zuwa mana sai dai ba kud'i , dama tunani ni na idan na samu kud'i da safen nan in saima su inna abin da zasu CI , to gashi kuma duk k'ofofi sun kulle"




Umar shiru yayi yana nazarin abokin nashi sannan yace "tashi muje"


"Ina kenan? Cewar Abdallah


"Bakin titi zaka raka ni"


"to" kawai yace sannan ya mik'e sukA d'au hanya,


Suna tafe suna firarsu irin ta abokai kuma aminai suka k'arasa , k'ofar shagon wani me shayi Umar ya ja birki ,


Abdallah ya kalleshi ya ce"me za muyi anan?"


"Tsaya ka sha kallo "ita ce kawai amsar Umar, ya zagaya yayi ma mai shayin magana ya dawo ya ce mawa Abdallah "bismillah" ya nuna masa wata kujera da ba kowa akai ,.


Bai musa ba ya zauna suna zaune a wajen kusan minti biyar ba Wanda yayi magana cikin su , sai ga mai shayi ya kawo musu , tea ne aka had'a musu dai-dai shan talaka da bread ,


Abdallah ya bud'e baki zai yi magana kenan Umar ya katse shi"da kata ustazu bana son wani k'orafi CI abin cin ka" Umar ya k'arike maganar yana janyo nashi kofin


Ba yanda Abdallah ya iya domin baya son ganin b'acin ran abokin nasa Sam ya ja kofin shi tare da bismillah ya fara aikawa cikin shi Wanda rabon shi da abinci tun safiyar jiya ,




Bayan sun natsa ne Umar ya sallami me shayi tare da karb'ar wata Leda a hannun shi sannan suka kamo hanya




"Umar bansan da bakin da zan gode maka ba , nagode da taimakon da kake yi min Allah ya saka maka da alheri Allah ka Nuna min ranar da zan faran ta maka kaima "




"Amin , Abdallah bana buk'atar godiya daga gare ka taya za'a yi na samu kud'i har na iya kashe wa ba tare da kai ba wannan ba mai yuwuwa bane"




"Dole na gode maka aboki na daga kai sai mahaifiya ta kuke gane meke damu na"


"Uhum" kawai Umar yace domin ya san gaskiya Abdallah ya fad'i ,


Da haka suka k'arasa k'ofar gidan su Abdallah dukan su atare suka shiga gami da sallama ,




Mama ce a tsakar gidan tana zauna ita da wata matashiyar yarinya suna zaune akan tabarma kowa da hijab ajikin shi da alama sallah suka idar(salatul duha)




Yarinyar ce ta amsa musu domin Mama addu'a take yi




"Ina kwana yaya Umar?" Cewar. Yarinyar




"Lafiya lau hafsa ya gida?"


"Lafiya lau"inji yarinyar da aka Kira da hafsa




Dai-dai nan Mama tace" maraba da Umar" murmushi yayi sannan yace "yauwa Mama , kun tashi lafiya ?",


Mama ta bashi amsa da "lafiya lau "


Sannan ya juya ya ce ma hafsa " ke karb'a wannan kije Ki had'o"




Hafsa ta karb'a ledar ta wuce D'an k'aramin kitchen d'in su.


Sai alokacin Abdallah yayi magana " haba Umar kaima fa ba kud'in nan kake da shi ba amma sai kai ta wani wahala"




"Umar ya turb'une fuska yace "yan zun Dan nayi ma Mamana wani Abu shine wahala to ni Neman albarka nake nema " yadda ya k'arike maganar kamar yayi fushi basu yi aune ba sai jinshi suka yana fad'in " nabar Ku cikin amincin ubangiji"


Aiko Abdallah ya zabura ya bishi , da k'yar ya shawo kanshi ya tsaya ya saurare shi , nan ya bashi hak'uri tare da tambayar ina ya samu kud'i




"Acikin Raguna nane tun jiya d'aya bata da lafiya yau da safe da naga asara zanyi shine na yanka ta na kai kasuwa abanza mahauta suka siyeta dubu tara "ya k'arike maganar cikin takai CI




"To amma Umar ai kana da hidima"Cewar Abdallah


"Kaga gida uku na raba kud'in biyu naba umma narik'e d'aya nida aboki na "




Ajiyar zuciya Abdallah yayi sannan yace "Allah ya Sanya ma kud'in albarka"


"Amin" cewar Umar sannan suka bazama cikin gari






For comment 08165728746
[12/13/2017, 8:32 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*






*MRS NN ONE*💋


Dedicated to PURE MOMENT OF LIFE WRITERS


® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_




# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com








Page 2⃣




WAYE ABDALLAH




Abdallah d'ane ga Abdallah asalin mahaifin shi D'an wani k'auye ne ahanyar jos ya baro gida sakamakon rasuwar iyayen shi kuma shi kad'ai iyayen shi suka Haifa , alokacin da ya baro gida yana da matar aure me suna Hindatu itama auren zumunci akayi musu da ita , Abdallah ya tattara yan k'wandalolin da ya ke dasu ya taho garin zazzau domin Neman kudi , yasamu wani D'an k'aramin gida yasiya suka zauna shi da matarshi Wanda har zuwa wannan lokacin bata da ciki , yakan fita kullum ko zai samu abin yi amma babu rannan kawai sai ya yanke shawarar bari yaje bakin kasuwa ko dako yayi , to ahaka yake samu yana ciyar da matar sa duk da ba kullum ake samu ba,


Kasan ce warsa shida matarshi basu da hayaniya yasa suka zauna lafiya da mutanen unguwar , gidan da ke kallon gidan Abdallah gidan wani malami ne mai suna Malam Kabiru mai almajirai wani lokacin idan Abdallah ya dawo k'adugo yakan zauna yayi karatu awajen shi Kasan cewar shi mutum mai son karatu , akwana a atashi ba wuya sherar su Abdallah biyar agarin Zaria , suna rayuwar su yau samu gobe rashi , Akwai wani mak'ocin Abdallah wani tsanin gidan shi Dana mak'ocin gida biyar ne sunan sa Jafar shima dai rufin asirine kawai gareshi shiyasa abotar su tazo d'aya da Abdallah ,


Wata rana sai suka yanke shawarar suje su nemi aiki gidan bulo ko ruwa ne surunk'a d'ebowa , aiko basu sha wahala ba tunda sunsan me gidan bulo d'in ,


Kwanci tashi ba wiya har suma aka koya musu yadda Zasu had'a bulo wata ,


Wata rana Hindatu ta tashi da zazzab'i ciwon kai da jiri sai ranar sanyi take , akwai wani PHC asaman layin su nan ya kaita gwanjin farko aka tabbatar mai da tana da ciki murna kuwa ba'a fad'uwa tunda ga lokacin ya koma bata kulawa na musamman Dan duk wani aikin gidan shi yake yi




Alokacin da cikin Hindatu yakai wata takwas ya shigo mata da wani madai-daicin rago tayi murna sosai tare da godiya , bayan sati biyu Abdallah yaje gurin aikin shi sai man injin d'in ya k'are be jira kowa ba ya d'auko mai ya shiga d'urawa yana cikin haka ne wani noti ta k'asan injin d'in ya fita yana gama d'ura man ya cire rigarshi ya kwanta ta k'asa saida ya lek'a ya ga Ashe ma notin ba d'aya bane kafin ya gama tunanin da zai yi injin d'in ya fad'o masa a k'irji bai sake sanin inda kanshi yake ba sai dai ya farka ya ganshi gaban Hindatu ta na ta faman kuka k'irjin shi duk an d'aura mai su da farin bandeji da k'yar ya iya d'aga hannu ya bubbuga mata bayan ta , sai sannan ne ta juyo tace mishi sannu Malam d'aga mata kai yayi dan ya kasa magana k'irjin shi ya mishi nauyi sosai , tunda ga ranar baya iya komai idan ya fara tari haka yake fitar da jini guda guda , ranar wata juma'a kuwa Abdallah ya rasu , Allahu Akbar mutane sunji mutuwar shi sosai musamman ma abokan shi guda biyu Malam Jafar da Malam Kabiru,


Bayan rasuwar Abdallah da sati d'aya Hindatu ta haihu tare da taimakon matan Malam Kabiru da Jafar , matar Jafar lokacin tana da goyon yaron ta Umar D'an wata biyar ,




Hindatu ta haifi d'anta namiji yaro sak kamar shi da Baban shi dangin ta da suka zo sunso su maida ta gida amma fir ta k'i hakan yasa suka hak'ura suka barta mak'otan nan nata su ke ciyar da ita , ranar bakwai yaro yaci suna Abdallah .




Haka rayuwa ta cigaba da garama Hindatu idan mak'otanta sun samo su bata randa basu samu ba kuma kowa ya sha ruwa ya kwanta ,




Lokacin da Abdallah ya kai shekara bakwai Malam Jafar ya had'a shi da Umar ya sasu amakaran tar boko ta gwamnati ,




Abdallah da Umar sun taso cikin son junan su da tausayin iyayen su wani lokacin da Kansu suke zuwa bakin kasuwa suyi dako su sami 'yan kud'i su kaima iyayen mata sukuwa suyi ta sa musu albarka




Tun suna k'anana suke zuwa d'aukar karatu wajen Malam Kabiru har suka sauke bayan sun sauke sai ya sa musu littafai




Suna SS3 mahaifin Umar ya rasu anan karatun su na boko ya tsaya ,




Abdallah da Umar suna iyakar bakin k'ok'arin su wajen ganin sun ciyar da iyayen su amma abin yana fin k'arfin su wataran gwanda ma Umar mahaifin shi da aka raba gado Maman shi ta fara sana'ar k'ulla-k'ulle dashi suke rufa ma Kansu asiri




Lokuta da yawa Malam Kabiru yana musu nasiha akan suji tsoron Allah kada talauci ya sa su rasa imanin su da irin wad'an nan nasihohin kullum Malam ke musu




Da temakon Malam suka samu koyar wa a wata islamiya da ke wata unguwa babbar makaranta ce sai dai albashin ta mai K'aranci ne baya isarsu d'awai niyar su




Wannan shine BAWAN ALLAH kamar yadda mahaifiyar shi me kiran shi dan bats fad'in sunan sakamakon sunan mijin ta kuma sunan d'anta na fari






For comments
08165728746
[12/13/2017, 5:36 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*






*MRS NN ONE💋*


*I dedicated this page to you , masoyana a koda yaushe ina jin dad'in yadda kuke k'arfafamin gwaiwa na Gode Allah ya bar k'auna AMEERT Nd FATIMA (K'awwali)❤*




® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_




# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com








Page 3⃣




*CIGABAN LABARI*






Haka suka k'araci zaga gurare da kasuwwani ba su samu komai ba har la'asar ta gabato , hakan ya sasu koma wa gidan ba Dan sun so ba ,




Da sallama ya shiga gida Mama da hafsa ne suke hirarsu jefi-jefi , suka amsamai sallamar ne ya shiga




Cikin sanyin jiki ya nemi guri gefe ya zauna sannan ya juya ya kalli mahaifiyar sa ya ce




"Kun wuni lafiya Mama?"


"Lafiya lau ya k'ok'ari bawan Allah?" Ta kalli D'an nata cike da tausaya wa




"Alhamdlillah Mama" cewar Abdallah daya ke k'ok'arin tashi , domin kiran sallar da yaji ,




Bayan sunyi sallah shi da aminin nashi islamiyar da suke koyar wa suka je ,




Abdallah shine malamin k'ur'an da tajweed ,


Umar kuwa yana daukan ahdari da tauheed


Suna zuwa kowa yake shiga ajin shi




Bayan sun dawo daga islamiya k'arfe takwas na dare suke zuwa d'aukar karatu wurin Malam Kabiru ,




Yauma kamar kullum sunje karatu Malam ke musu fad'a




" wai yanzun Ku haka zaku zauna ba zaku yi aure ba Ai aure shike sa aga mutum da daraja kullum"




"Insha Allahu idan lokaci yayi za'a yi "cewar Umar


Shiko Abdallah shiru yayi


Malam ya ce "Bawan Allah baka ce komai ba "


Ajiyar zuciya Abdallah yayi sannan ya ce " yanzun Malam a yadda muke d'in nan wa zai d'auki d'iyar sa ya bamu , bayan bamu da abinda zamu ciyar da ita dashi balle kuma sauran buk'atu na duniya "




Malam ya ce "hakane Abdallah amma ai ba'a rasa na Allah"




"Hakane Malam " cewar Umar




"Kuma ni gashi har na fara nema muku aure Dan zaman Ku ahaka baya min dad'i "




Cikin sauri Umar yace " Malam kad'an yi hak'uri zuwa nan gaba kad'an"




Malam yayi murmushi ya ce "Allah ya kaimu "




Abdallah kuwa cewa yayi "duk yadda kayi Malam dai- dai ne"




Nan Malam ya sa musu albarka sannan suka tafi ,


Suna fitowa Umar ya kalli Abdallah ya ce


"Ustaz naga kamar kayi na'am da maganar Malam ne "




Kallon shi Abdallah yayi sannan ya ce " Malam tamkar Uba yake aguri na Dan haka babu zab'in da zai min na bijire masa dole Sana'a zannema "




Umar ya zaro ido"wace irin Sana'a kenan?"




" zanyi tunani idan na yanke shawara zan gaya maka zuwa gobe da safe" cewar Abdallah yana k'ok'arin shigewa gida




"Allah ya jisshemu alkhairi " Umar ya fad'a da D'an k'ar fi ,


Suka yi sallama kowa ya shige gida




*DA SAFE*


Yauma kamar kullum ba komai agidan suna zaune sai ruwa da suke D'an sha jefi-jefi ,




Shiko Abdallah yana can d'akin shi kwance kan shamulokin katifar shi yana ta tunanin sana'ar k'arfin da zaiyi , idan yace wannan ya ce A'Ah daga k'arshe dai ya yanke shawarar yin sana'ar wanki da guga , wannan shawarar ya tsayar Dan haka ya mik'e ya saka rigar shi ya fita tsakar gida




Bayan sun gaisa ne sai ga Umar ya shigo da kwanon sha , a hannun shi ya d'ire a gaban Mama ,bayan sun gaisa Mama tace




"Umar me muka samu ne?"


"Murmushi yayi yace "koko ne Mama "




Mama tace "an gode Allah ya saka da alheri"


"Amin " dukkan su suka ce




Bayan sun gama shan kokon ne Umar yace " Abdallah wai wace Sana'a zamu fara ne"




Abdallah yayi gyaran murya yace "wanki da guga"




Umar ya zaro manyan idanun nan nashi ya ce "wanki da guga?"




"Eh, Kasan dalilin da ya sa na zab'e ta?"


Umar yace "A'ah"


"Saboda ita kad'ai ce samu yi ba tare da mun kashe ko sisi ba "




"Hakane Abdallah Allah ya taimake mu "


Dukan su suka amsa da "Amin"


Mama ma fatan alheri ta musu ,


Cikin sa'a kuwa suka samu kasuwa , da yake gidan su Abdallah akwai rijiya kuma ba yara nan suke taruwa suyi sana'ar su ,




Da yake basu sa ha'inci a sana'ar suba hatta masu hannu da shuni na kewayen su suna kawo musu ,




Hafsa ce zaune tana tsintar wake zata dafa musu garau-garau , nan k'awarta Ummi ta shigo tare da sallama , Ummi akwai ta da son barkwanci ta cewa hafsa




"Ah k'awata yaushe aka fara shiga kitchen?"




Wata harara hafsa ta aika wa Ummi sannan ta ce "kefa 'yar rainin wayau ce wallahi yau kika fara ganina nayi girki?"




Ummi tayi dariyar mugunta tace "to aike hafsa abinshi naki ne na ganin dama sai Mama tace kiyi kike yi"




Hafsa ta tuntsire da wata dariya tace " kamar ko kin sani"




Suka tafa Ummi tace "AI na sanki ne k'awata, ina Mama ,"


Hafsa tace "Mama taje gidan su yata Umar Gwago ce bats jin dad'i"


"Subhanallah Allah ya bata lafiya "cewar Ummi


Hafsa ta amsa da "amin"


Nan Ummi ta taya ta suka gama sukayi shirin islamiyya
[12/14/2017, 9:58 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*




*MRS NN ONE💋*




*Dedicated to Rabi'atu Baba Paki😘 ina yinki mumcy irin dayawa d'in nan*




® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_




# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com






4⃣






Lokaci ya ja su Abdallah nayin wankin da guga suna samun na rufin asirin su , daga baya wani k'anin MAMAN Umar ya saman ma Umar tsaran shagon abokin shi acikin kasuwa , to daga nan Umar ya bar wanki da guga sai Abdallah kad'ai keyi , da haka idan ya cire kud'in da zasu CI abinci sai ya saka sauran a asusu saboda wasu idan yayi musu aiki over payment suke mishi,




Yanzun watan Abdallah shida yana wanki da guga wata , wata rana Malam ya aika a Kira shi , bai b'ata lokaci ba ya je,




Bayan sun gaisa Malam ya ce" Abdallah ya maganar aure?"


Wata irin muguwar fad'uwar gaba yaji amma sai ya d'aure ya ce"yanzun Malam akwai Wanda zai iya bani 'yarsa na aura yadda nake d'in nan?"




Malam yayi murmushi yace "sosai ma kuwa Dan an dad'e ma da baka sadaki kwai ake jira a d'aura aure"




Cikin firgici Abdallah ya d'ago ido ya kalli Malam


Malam yace " sosai ma kuwa idan kana da naira dubu bakwai ka kawo amatsayin sadaki , "




Gaba d'aya Abdallah ya diri-rice ya rasa me zai ce ,


Malam yace cikin sanyi murya "Abdallah dalilin da yasa na matsu kayi aure shine na dad'e ina lura da yanayin ka , sannan kuma ahalin yanzun da kake cike kana buk'atar mace ta gari da zata zamo natsuwa a gareka shiyasa kaga na damu"




Ajiyar zuciya Abdallah yayi Dan yasan zancen Malam gaskiya ne "Insha Allah bazai gagara ba , nagode Malam Allah ya saka da alkhairi ya k'ara girma "




"Amin "cewar Malam


Sannan sukayi sallama akan zai kawo sada kin gobe ,


Abdallah na koma wa gida ya sanar ma da Mama yadda suka yi da Malam , tayi murna sosai hafsa na d'aki na kwance ta fito tana "Mama lafiya?",


Abdallah ya turb'une fuska alamar be son raini yace" ke waye sa'anki a nan? dallah can koma d'aki"




"Haba Bawan Allah wannan ba 'yar uwar ka bace ai ya chanchanci taji abin alherin da yake shirin samun mu"




"Mama ni dai raini ne bana so" yana gama fad'in haka ya nufi k'ofar d'akin shi ya tura ya shiga ya fad'a kan shamulokin katifar shi yana tunani ,


"Shin ta ina za'a kawo wani mahaluki d'akin nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login