Showing 6001 words to 9000 words out of 38502 words
Chapter 3 - BAWAN ALLAH COMPLETE DOCUMENT BY Maman Muhammad .txt
addu'ar ,
Bayan ta fito ta gan shi yana alwala cikin sauri ta fara duk Dan gudun kar ya gama ya barta a wajen , shiko tsaya wa kawai yayi yana kallon ikon Allah , har ta gama ta shige d'aki , nan shima yayi ya koma d'akin Dan ya dauki hular shi
Ita kuma ta tada kabbara sai ce mata yayi " wato ni da na raka Ki Dodon ya cinye ni ko?"
Bata ce komai ba , shikuma ya d'auki hular shi , ustazu ka fiye naci ya saka ya fita ,
Bayan sun idar da sallah ne ya so ya D'an kwanta a massallacin ya D'an yi barci amma Umar Sam ya hana shi sai tsokanar shi ya ke yake " Ango Ango sai wani k'yalli kake kamar tauraro" haka dai yayi ta masa shak'iyyan ci,
Abdallah kuwa tashi yayi ya barshi nan zaune yana dariya da dai ya ga da gaske fita zaiyi sai ya taso ya biyo shi dai dai kunan shi ya rad'a masa "ya kama ta kaje ka ji d'umin 'yar k'anwar ka" ya k'ara sa da kashe ido d'aya
Abdallah ko da abun ya bashi haushi sai ya ce " ka manta ne ba d'umin ta zanji ba jikin ta Zan shige "
"Yauwa mutumi na Ashe ka gane "
Dai-dai nan Abdallah ya shige gida ya bar Umar a tsaye yana dariyar mugunta Dan shi gani yake kamar an had'a Abdallah da aiki ne ,
Yana shiga gida ya CI karo da Hafsa tana alwala , wata harara ya watsa mata sannan yayi sallama d'akin Mama suka gaisa take tambayar shi ya Ummi da jiki ya ce mata taji sauki suka Dan tab'a hira ya ji yana jin barci sai ya mik'e ya ce mata "Mama ina zuwa"
D'akin su ya koma , Ummi kuwa tana jin motsi tayi sauri ta rufe idon ta , ko da yayi sallama yaji ba Wanda ya amsa mishi , ya yaye labule kutsa kai ,
Yana shiga ya ganta tana barci , ya koma inda yaga dadduma a shimfid'e ya kwanta nan wani barci yayi awan gaba da su duka ,,
Mama kuwa da taga har takwas tayi Abdallah be futo ba , sai ta aiki Hafsa ta siyo kayan tea a bakin titi, ta na dawo wa ta d'aura ruwa zafi ta had'a citta da kaninfari da Lipton ya dahu sai k'amshi yake , , ta juye a wani tsohon plas d'in ruwan zafin su ta juye aciki ta d'iban musu nasu saura kuma ta had'a da bread tayi k'ofar d'in Ummi
Sai da tayi sallama sau uku taji ba Wanda ya amsa kuma ba ta ji motsin kowa ba , murmushi tayi sannan ta d'aga labulen kad'an ta ajiye kayan ba tare da ta kalli d'akin ba , gudun kar tayi mugun gamo,🤣🤣
Ummi ce ta farka lokacin Tara tayi cikin sand'a ta mik'e gudun kar Abdallah ya tashi bata San shima ya tashi ba baya son yayi motsin da zata ji ne ,
Jakar kayan ta ta bud'e ta Ciro brush da MacLean ta d'auki butar ta ta fita bata lura da kowa a tsakar gidan ba ta tafi chan inda suke wanke wanke tayi brush d'in ta sai da ta gama ne d'ago kai suka had'a ido da Hafsa , aiko me Hafsa za tayi in ba dariya ba , Ummi kuwa murtuk'e fuska tayi Mama ta gansu amma sai tayi kamar bata ma gansu ba .
Jiki a sanyaye Ummi ta k'araso ta zauna kusa da Hafsa , cikin jin kunya ta gaida Mama , ta amsa cikin sakin fuska Dan Mama tana son Ummi sosai
Hafsa ce ta ce"Aunty Ummi ya jiki"
Ummi da mamaki ta ce "yau kuma Hafsa nice Auntyn Ki?"
"Eh mana AI tunda kin auri yaya Abdallah kin zama Aunty"
Wata hara ra Ummi ta zuba mata ta gefen ido
"Ummi tashi Ki je Ki karya kinji Ki k'yale wannan "
"To Mama"
Ai sai Ummi ta d'auki kofin shayin Hafsa tana fad'in "Mama AI wannan ma ya ishe mu ni da k'awa ta"
"Malama bani shayi na naki na d'akin ku" cewar Hafsat tana zumb'uro baki
Mama dai bata tanka musu ba
Ummi ta ce cikin k'asa-k'asa da murya "K'awa ta je Ki d'auko min nawa tea d'in , zan aje miki naki,"
"Tab AI ko ba zan je b....." Bata gama fad'i ba Ummi ta make mata baki
Mama kuwa murmushi kawai tayi
"Ke hafsa nan matsalar Ki ba wayau je Ki d'auko min Ki zo musha fira"
"Eh sannu uwar wayau..." Ummi ta k'ara make mata baki
"Wallah Aunty Ummi kika sake duka na sai na...
." ta sake gwabje bakin ,
Hafsa ta mik'e "Mama kina kallon ta ko ?"
Mama ta ce 'ai ni na gode gwanda ta min maganin Ki , wuce ki je Ki d'auko mata"
Cikin zumb'ura baki ta tafi
[12/17/2017, 8:56 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONE💋*
*Wannan page d'in na sadaukar dashi ne ga masoya novel d'in BAWAN ALLAH aduk inda kuke Wanda na sani da Wanda bansani na gode Allah ya bar zumunci, ❤*
*BAWAN ALLAH fans wallahi ina matuk'ar jin dad'in comments d'in ku ku sani dani da ku muna mak'ale da juna🤞🤙*
*K'awwali ta da Ameenert gaisuwar ku da bance 💋*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
Page 8⃣-----🔟
Sai da tayi sallama sau biyu ba'a amsa mata ba , ana ukun ne ya amsa had'e da cewa,
"Mene ne?"
"Aunty Ummi ce tace na zo na d'auko mata shayin ta da magani"
Chan dai yayi shiru kamar ba zai bada amsa ba sai kuma yace "kije Ki ce mata tazo ta d'auka da kanta"
Har ta juya zata koma sai kuma yace "zo nan"
Ahankali ta d'aga labulen d'akin ta shiga ,
"Kwashe gasunan inda kika ajiye su"
Ba musu ta d'auka sannan ta fita jikin ta duk kyarma yake ,
Tana zuwa ta dangwarar da kayan a gaban Ummi " gashinan burinki ya cika kin tura ni wurin wancan zalimun mijin naki"
"Oho ko ma dai mene ne buk'ata ta tabiya tunda kin min abin da nake so" cewar Ummi tana murgud'a baki ,
"Idan kun gama wasan kwai-kwayon sai ku mayar mai da kayan shayin " Mama ta fad'i yayin da ta d'au buta tayi hanyar bayi
"To"dukan su suka ce ,
Mama na tafiya musu ya kaure tsanin Ummi da Hafsa akan Wanda zai mai da kayan shayi
Ummi na cewa "ke kika d'auko ke zaki mai da "
"Hafsa na cewa ke kuma ba mijin Ki bane ni ba runa wallah ba zan mayar ba"
Dai dai nan Abdallah ya fito ya , duk yaji me suke cewa , amma sai yayi kamar ma bai San suna wajen ba , Ya fara brush kenan Mama ta fito daga bayi , anan suka k'ara gaisawa alwala tayi ta shige d'aki shima alwalar yayi ya shige d'aki , duk da yana wurin musu tsakanin Ummi da Hafsa be k'are ba sai dai wannan karan a hankali suke yi , yana shiga ya tada sallar mai rabo (salatul duha),
Ummi ta gama tsumul- mulan shan shayin ta Dan Hafsat tuni ta gudu ta barta,
Hakanan tayi shahada ta d'auki kayan shayin ta nufi d'aki da shi sallama tayi sannan ta shi , ta same shi akan dadduma yana addu'a , kawai sai ta tsaya tana kallon shi da taga ya gama addu'ar sai tayi sauri zata fita kamar daga sama taji yace "ina zaki je?"
Sai ta hau kame kame,
"Yau ko gaisuwa ba zan samu ba kenan?" Yawani tsare gidan shi
Cikin sauri tace" yaya ina kwana?"
"Ah'ah Ki rik'e gaisuwar Ki indai sai na rok'a" ya sake murtuk'e fuska
Nan da nan ta tuna da nasihar Malam da ya ke cemata "ta guji b'acin ran mijin ta Dan zai iya kaita ga azabar Allah"
AI yana tuna wannan sai tayi sauri ta dawo kusa da shi ta zauna
Ta marai-raice murya "yaya Dan Allah kayi hak'uri , Malam yace idan kayi fushi dani zan iya shiga wuta"
Abin ya bashi dariya amma da yake bata so ya gane sai ya tsare gidan sa , azuciyar shi kuma cewa yayi "wato tanan kika b'ullo? Muje a haka game d'in zai fi dad'i"
Wani murmushi yayi sannan ya ce "idan kina so na daina fushi da ke kin had'a min shayi"
"Yo AI wannan mai sauk'i ne "cikin minti biyu ta had'a mai tea d'in ta bashi
Tana zaune a gurin ya gama karyawa sannan ya kalleta ya ce " ya jikin naki?"
"Alhamdulillah , naji sauki"
"To masha Allah , kinsha maganin Ki?"
Kai ta girgiza alamar bata sha ba
"Ummi Ki daina wasa da shan magani , tashi Ki d'auka Ki sha"
Ba musu kuwa ta mik'e ta d'auko maganin ta bud'e wata k'aramar randar ta ta d'ibi ruwa kamar abun arzik'i zata sha ,
Ga maganin ta Tara a gaban ta amma ta kasa sha ,
Shikuwa sai ya bita da na mujiya , wani abun mamaki bai wuce da ya tana zubar da k'walla ba , tana hawaye tana kallon maganin ,
"Lafiya? Ki sha maganin mana"
"Wallah yata magungunan ba dad'i "
"Ki daure Ki sha shi dama magani ba Dan dad'i ake shan shi ba"
Mik'e wa tayi tare da d'aukar ledar maganin zata fita ,
"Ina kuma zaki je Kuma?"
Cikin shagwab'a Ummi tace "zan je gurin Ummi name ita kad'ai zata iya bani nasha ba tare da nayi amai ba"
Shiru yayi na 'yan sakwanni sannan ya ce "zo na baki Ki sha"
"Ummi na fa lallab'ani take"
Wani murmushi yayi sannan yace" nima yayan Ki zan lallab'aki"
Jin hakan yasa Ummi kwasar ledar maganin tayi wurin shi ,
Zaman dirshan tayi a gaban shi sannan ta mik'a mai maganin , ya karb'a yace
"Ya Ummi take baki?"
Sai alokacin itama Ummi ta faki idon shi ta saki wani shu'umin murmushi azuciyar ta tace "anzo gurin ya ustaz"
"Ina magana kinyi shiru saifa kinsha maganin nan yau" yana magana yana d'aure fuska
"Dama sai ta gutsura maganin gida biyu sannan ta ta saka min d'aya a baki da ruwa , tana Shafa baya. Na har sai ta gama bani kuma tana yi tana fad'in , kiyi hak'uri Ummi na kisha , haka take ta fad'i"
😂😂😂😂😂
Bawan Allah sai da ya zaro ido sannan yace "to naji matso"
[12/18/2017, 1:47 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONE💋*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
Page
1⃣1⃣++++1⃣2⃣
Matso wa tayi daf da shi sannan ya bud'e ledar ya Ciro magungunan ya b'ab'b'alla su , ya ce "bismillah " D'an k'aramin bakin ta ta bud'e ya saka mata tare da bata suwa tana jira taji ya shafa bayan ta sai taga yayi mursisi , ai ba shiri ta fara kakarin aman k'arya fita waje tayi da gudu ta tofar da maganin , ta shigo tana fuskar tausayi, tace
"Yaya ka gani ko ba zaka iya bani ba kamar yadda Ummi na take bani"
"Me yarinyar nan ta mai da nine amma zan nuna mata nafi Ummin iyawa"wannan duk azuciyar shi yake fad'i
Azahiri kuma cewa yayi " ayya sannu na manta ne zo asake wani"
Ta sake zuwa ta zauna sai cewa yayi "cire wannan hijab d'in ko shima ya shak'e maganin yak'i wuce wa"
"Me ka ce yaya"ta zaro ido
Ya k'ara k'asa da murya dai-dai kunnan ta yace "nace Ki cire hijab d'in"
"Yaya ai ba zai hana ni sha ba"
B'ata rai yayi ya tura mata maganin ta , "shikenan tunda ba zaki cire ba, ni ba zan baki kije kiyi amai ba"
"Ayya yaya da gaske bana son Fushin ka bari na ciri"
Yaye hijab d'in tayi dai-dai wuyan ta sannan ta ce "na cire "
Hannu ya sa ya yaye hijab d'in , wata vest ce ajikin ta mai santsi da leshi agaban ta ta kwanta tayi luf ajikin ta , kayan arzik'i ne ya tsaya kallo har yana had'iye wani yawu mak'wat gaba d'aya imanin shi ya tafi awajen k'irjinta , ga dai su ba masu girma bane amma akwai d'aukan hankali,
Sai da Ummi ta kira Abdallah sau uku be jita ta ba , sam ita bata lura da inda yake kallo ba,
Tab'ashi tayi tana fad'in "yaya ina ta magana shiru"
Bece mata komai ba , ya sa mata maganin abaki dan gani yake ko magana yayi za'a gane halin da yake ciki
Ruwa ya sanya mata a baki sannan ya k'ara janyo ta jikin shi , tana jin ya tab'a ta tayi sauri taja baya , madadin ya kyale ta sai ma k'ara janyo ta da yayi ta kwanta a k'irjin shi yana shafa bayan ta ahankali cikin wani irin salo yana fad'in
Yazo dai-dai saitin kunnan ta ya na rad'a mata"k'iyi hak'uri Ummi kishanye ko kya samu lafiya"
Sai da suka kusa minti goma a haka Abdallah dauriya kawai yake yi amma ga ba d'aya notin jikin shi ya kwance
Ummi kam har ta fara bacci abunta bata ma San yana yi ba ,
"Ummi , Ummi"Abdallah yake kira a hankali
Cikin yanayin bacci tace "uwum Ummi na Ki barni ban gaji da jin d'umin jikin Ki ba " ta sa hannun ta biyu ta zagayo dasu ta bayan shi tare da dad'a cusa kanta cikin k'irjin shi
"Inalillahi wa 'inna ilaihirraji'un"abinda Abdallah ke mai-maitawa kenan
Acikin ranshi ko fad'i yake" wannan yarinyar zata kashe ni"
Sun jima a haka bai kwantar da ita ba domin zaman ta a jikin nashi na rake mai wata damuwar ,
Ana haka ya tsinkayi muryar Hafsa tana fad'in "eh yana ciki"
Sallamar Umar da yaji duk ta dagula masa lissafi shiko sai rafka sallama yake ,
A hankali ya lallab'a ya kwantar da ita , sannan ya fita,
Umar na ganin shi ya saki wani murmushin rainin wayau , yace "kayi hak'uri fa na katse maka hanzari"
"Ba hanzari ka katse min ba gudu" ya ja tsaki , yayi hanyar fita , binshi Umar yayi yana fad'in "ai dai ka tsaya kaji me ya kawo ni ko ?"
Cikin murtuke fuska Abdallah yace" Umar muddin kana son zaman lafiya tsakani na da kai to dole daina min shakk'iyancin nan naka , wallah har cikin raina bana jin dad'i shiya sa kaga gaba d'aya na fita harkarka domin b'ata min rai kake"
Umar yace "uhum Bawan Allah kenan indai wannan ne mai sauk'i ne , amma babu yadda za'ayi na ganka a cikin irin yanayin da na ganka a yanzun ban yi dariya ba"
"Mtsww yanzun dai gaya min meya kawo ka?"
"Dama Alhaji bello ne ya kirani yana ta Neman wayar ka be shiga shine ya bada wankin shi na kawo maka , amma wai gobe yake so da safe zaiyi tafiya"
"Shikenan ba damuwa , ina wanki suke?"
"Suna nan tsakar gida na barsu "
Nan dai suka D'an yi fira sannan Umar yace " bari naje kasuwar nan kaji"
Sukayi sallama , Abdallah ya koma gida , Mama da Hafsa ne keta kiciniyar d'aura tuwon rana , yayi musu sannu ya wuce d'aki , kaya ya chanja zuwa wata tsohuwar T-shirt , ya nannad'e k'afar wandon sa ya hau sana'ar shi ta wanki ,
Ummi kuwa ba ita ta farka ba sai d'aya saura , lokacin har Abdallah ya gama wankin shi yayi wanka yana shirin fita masallaci tana kwance tana kallon shi sai da ya gama shirin shi ya fita sannan ta mik'e ta d'auki bokitin ta da buta ta nufi rijiya , a nan waje ta tarar da Hafsa tana kwasar tuwo
Ummi cikin tsokana tace "yau manya ne a kitchen d'in "
Hafsa ta juyo ta watsa mata wata harara sannan tace " kuma dole aci ko be dahu ba ba"
"Yi hak'uri maida wuk'ar" ta duk'a ta d'ibi ruwan ta sannan ta wuce bayi tayi wanka da alwala tayi sallah sai da ta idar ne ma ta lura da kwanon abincin nan ta D'an yafita ta barshi ,
Hirar su Mama da Hafsa ne da taji ya sata fita don ta gaji da zaman shirun,
[12/20/2017, 9:27 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONE💋*
*Dedicated to*
*MAMAN Tahir*
*Maman Hanan*
*Maman mamy*
*Maman adhil*
*Meenat*
*Rukkaya maijega*
*Amne*
*Aisha Muhd Namadina*
*Sadiya Illa*
Agaskiya sunan ku ba zai lissafu ba I really appreciate your kind and support *Ina mugun k'aunar ku*❤💋
*Thanks for your well wishes*💋
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
Page 13___14
Shiko Abdallah tunda ya fita be dawo ba sai dare yana dawo wa ya shiga d'akin Mama ya gaishe ta sannan ya fita ya kwashe kayan wankin da yayi gashi yayi sa'a akwai wuta , kai tsaye d'akin su ya nufa , yayi sallama ya shiga , Ummi ya samu kwance tana baccin k'aryan da ta saba , be tanka mata ba ya shimfid'a sallaya ya hau gugan shi ,
Ita kuwa Ummi kallon mijin ta take yi cike da tausayi , azuciyar ta tace "shi ko gajiya baya yi?"
Abunda bata sani ba shine shima Abdallah hankalin shi yana kanta kuma sarai ya gane ba barci take yi ba kawai sai ya fuske yaci gaba da gugan shi , har wajen shabiyun dare ,
Ummi ce tayi wata mik'a tamkar me yin bacci sannan tace "yaya fitsari nake ji"
Fuske wa yayi ya ce "kije kiyi mana"
"Wallahi tsoro nake ji"
"Duk tsoron da kike ji da zaran kinyi addu'a zai tafi, ko baki iya addu'ar bane?" Ya k'arasa maganar kamar zeyi dariya
Zumb'ura baki tayi cikin shagwab'a tace"na iya mana"
" to sai kije kiyi kafin Ki min shi anan"
Ai sai ta hau shura k'afafuwa ita ala dole sai ya raka ta,
"Ya isa haka Sarkin shagwab'a tashi muje "
Zumbur ta mik'e tama manta da d'aukan buta Dan fitsarin ya matseta sosai , Abdallah ne ya d'auki butar ya bita da shi,
Bayan ta gama ta fito alwala ta d'auro sannan yayi gaba tana bin shi a baya kamar rak'umi da akala
Tana shiga d'aki ta hau katifar ta tayi addu'oi ta shafe jikinta dashi sannan ta kwanta , nan kuwa bacci yayi awon gaba da ita ,
Shiko Abdallah bayan ya gama gugan shi alwala yayi , yayi nafilfili sannan ya kwanta ak'asa , bayan ya kwanta kuma me ya tuna oho ya mik'e kamar an tsikare shi ya