Showing 27001 words to 30000 words out of 38502 words

Chapter 10 - BAWAN ALLAH COMPLETE DOCUMENT BY Maman Muhammad .txt

20 Dec 2024

2533

yake tambayar shi "Saifullah ina Baban naka?"




Saif cikin yanayin damu wa yace " yayi bak'i ne agida "


"OK muje muyi sallah Gashi har la'asar tayi ba muyi azahar ba "




Sai da suka d'anyi tafiya sannan suka fara tambayar inda masallaci yake akayi musu kwatance ,




Bayan sun fito daga masallaci ne ya Ciro wayarshi ya fara kiran wata number da aka rubuta "Bro" ajikin ta , acikin ringing na biyu aka d'aga kiran ,


Murmushi yayi sannan ya amsa sallamar da aka mai , bayan shiru da yayi na kimanin minti d'aya sai yace " duk naji k'orafin ka kafin nabaka amsa , kana school ne ?"




Shiru yayi domin sauraran me za'a ce mishi sannan yace "to ina ina cikin hospital naku ka sama mana abinci mare nauyi na mutum uku "




Nan d'in ma shiru yayi sannan daga baya yace "no don't worry ba ni bane friend d'ina na , kayi sauri fa na fara jin yunwa " kitt ya kashe wayar Dan yasan halin k'anin nashi ba k'i ma yatafi siyan abincin da wayar akunnen shi suna hira ba




Bayan sun aje wayar ne Dr Ahmad yace "AI da ka bari ma akwai restaurant anan waje da sai muci achan kawai "




"Wallah Sam bana son Barin cikin hospital d'in nan sai naga kamar wani Abu zai faru da Abdallah"


Dafa kafad'arshi Dr yayi yace "babu abunda zai faru dashi a hirar ma da mukayi da Dr yace yaji sauk'i yanzun ma bacci yake yi "




Ajiyar zuciya Saifullah yayi sannan yace " Alhamdulillah"




Suna tafe suna hira jefi jefi har suka k'arasa bakin d'akin da aka kwantar da Abdallah suka zauna a d'aya daga cikin kujerun dake aje wurin.




Bayan kimanin minti ashirin wayar Saifullah ta hau ringing ya d'aga tare da karawa akunne , k'anin nasa ya tambaye shi a inda suke , shi kuma ya mai kwatance , ba'afi minti Biyar ba sai gashi ya bayyana awajen .




(Ni mai d'aukan rahoto Wanda Nagani wajen saida alk'alami na ya fad'i k'asa saboda mamaki Saifullah ne ya mik'a min tare da fad'in " yes he's my brother " 🤪 AI ba shiri na cigaba da d'aukan rahoto Dan kar ayi show bani)




Aminullah ya k'arasa cikin sauri gami da ajiye ledar abincin kan d'aya daga cikin kujerun ya rungume D'an uwan sa cikin shauk'in bege yace " I miss you sweet bro "


"I miss you too little bro"


Sannan suka saki juna suna murmusawa .


Ahankali ya kai Cuban shi ga Dr cikin girmamawa ya gisheshi


Dr ya amsa tare da murmushi afuskarshi




"Bros ga abincin nan fa kuci "




Cin abincin suke amma kowa da abinda yake sak'awa a ranshi.




Wasu doctor's ne guda biyu suka fito daga d'akin , d'aya daga cikin su ya ce musu ya farka zasu iya zuwa su Ganshi , cikin sauri suka Shiga d'akin shiko Aminullah mamaki ne fal acikin shi yanda yaga har riga-rigen Shiga suke yi AI shima sai ya bisu abaya.




Akwance suka same shi hannun shi d'aya an samai drip tashi d'aya har yad'an fad'a kad'an ,




Cikin kulawa suka fara tambayar shi yajin nashi , kai kawai ya d'aga alamar da sauk'i , sannan ya kalli Saifullah yace.


"Saif baka tafi gida ba?"


Saif ya D'an harare shi yace " why should I go home when you are here"


Murmushi yayi ya kawai sannan ya juya kalli Aminullah kallon Neman k'arin bayani akan shi ,



Said ya janyo Aminullah kusa dashi yace " Aminullah da nake baka labarin shi, "


Sannan ya juya ya kalli Aminullah yace " Abdallah nasan ka gane shi "




Aminullah ya rab'a ta gefen Saifullah ya k'arasa kusa da Abdallah sannan yayi mishi ya jiki , suna d'an fira jefi-jefi dai-dai nan wayar Aminullah ta hau ringing sunan da yagani jikin wayar yad'an murmusa , Saifullah na kallon shi ya sakar masa dundu tare da fad'in


"D'an iska dariyar me kake "


"Ba komai sister na ce ta kira "


Zuwa lokacin kiran har ya katse D'an haka shi sai ya k'ara kira ,




Alokacin da aka amsa kiran yaji ance " haba Aminullah ka ce mujiraka kuma kayi shiru gashi har Aunty Ummi ta gaji ta tafi "


Dafe kanshi yayi tare da fad'in "ya subhannallah yan ke kina ina?"




"Ina inda ka barni "


"OK gani nan zuwa".




Ya juya ya kalli Saifullah yace "bros bari naje na dowa , kuna buk'atar wani Abu ne "




"Ah ah ka gaida k'anwar tawa"




Yamik'e tare da Sosa k'eya yayi musu sallAma har ya kai bakin k'ofa Dr yace " Aminullah kawuce da Saifullah gida ya D'an huta "




Saif zaiyi magana Dr ya dakatar dashi ta hanyar nuna masa yaje kawai ba wata damu wa,




Sai da suka Shiga mota sannan Aminullah ya juya ya kalli D'an uwansa yace "bafa gida direct zan wuce ba kuma kaga yamma tayi "


D'an tsaki yaja yace "muje"


Cikin makaranta suka koma , Hafsat na hango motar Aminullah ta taso ganin wani kyakkyawan saurayi cikin motar sai da yasa numfashin ta d'aukewa na wucin gadi , da k'yar ta iya Jan k'afafun ta zuwa kusa da motar , baya ta bud'e ta Shiga bayan ta rude motar sai nan ta gaida Saifullah a dak'ile ya amsa mata ya juyar da kanshi kan titi gami da d'aure fuska




Tunani yake yi wannan wace yarinya ce take tare da k'aninshi? Meye dangan takar su , yana cikin maganar ya tsikayi muryar abokin shi yana cewa "Hafsa nakira wayar Aunty Ummi bata d'aga ba ko tayi fushi ne?"




Sai da tayi dariya sannan tace " idan munje kaji"


"Is that what you said?"


Dariya kawai tayi domin tasan yanzun zai birkice Dan baya son ganin fushin Ummi Sam




*sorry for this one
[1/15, 1:55 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*




*MRS NN ONE💋*






® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_




# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com




*Readers bansan da me zan saka muku ba har kullum bakwa gajiyawa wajen sambad'o addu'oin fatan alkhairi agareni wallah har cikin raini ina ji daku ina k'aunarku Allah ya k'ara had'a tsakaninmu ya karemu daga sharrin dukkan abin k'i*🙏




*This page dedicated to you dearies*


*k'awalli*
*Maman hanan*
*Nafi khan*
*Fareeda*
*Ameenah*
*Mrs Abdulwahab*
*Rahma Isma'il*
*sa'adiya illa*
*Calz me nuccy*
*Maman Mimi*
*Umulkhairi Jibril*
*Ummulkhairi GJ*


*kai wallahi kuna da yawa you're uncountable amma kusani ni d'in taku ce har gaban Abadan*❤😘😍




3⃣5⃣




Shikam Saifullah ta kaici Duk ya cika shi , tun kafin su k'arasa aka fara kiran sallar magrib , dan haka suna k'arasawa Aminullah ya gyara parking dai dai k'ofar gidan su Hafsa , ta na fitowa tayi musu godiya had'e da sallama ,


Aminullah ya kalli yayan shi yace "bros ga masallaci chan muje muyi sallah "


D'an tsaki yaja sannan ya fito daga motar tare da fad'in " dama akan wannan abar ka b'ata min lokaci?"




Murmushi yayi yace "uhum bros ba zaka gane bane amana tace dole na kula da su "




Wata harara ya sakar mai sannan suka wuce masallaci .




Ummi kuwa tana shigowa unguwar su madadin ta wuce gidan su Hafsa sai ta wuce gidan su sai dai ta aika k'aninta da jakar makarantar ta , sai da ta yi sallar magrib sannan tayi sallama da gida tafito.




Dai dai lokacin su Aminullah suka dawo daga masallaci , yana ganinta yaja ya tsaya shiko sai tuni ya kame acikin motar




Takaici ne duk ya isheta bata so suka had'u ba tasan yanzun zai dameta da surutun shi , tamau ta had'e ranta sannan ta k'araso wurin ,




Hannun shi biyu ya had'a alamun banhak'uri sannan ya marai-raice yace " ayya Aunty Ummi Ki gafarce ni "


Dariya ne yakusa kufce mata dan yadda yayi maganar dole ne ma yabaka dariya,




"Is OK sai da safe " tana k'ok'arin shigewa gida ya tsayar da ita tare da fad'in


"Ga bros d'ina ku gaisa "


D'an lek'awa tayi ta window motar k'yarrr suka had'a ido dashi yana waya , d'agowa tayi tace ma Aminullah "ka gaishe shi nina tafi sai gobe "


Tana kaiwa nan ta shige gida , shi kuma ya bi bayanta da kallo yana murmushi


Yana Shiga mota Saifullah ya tallabe mai kai yana fad'in " D'an iska arasa gane wace ce budurwar taka aciki"


Tallabe k'eyarshi yayi yana cewa "wallah bro amana nane"


Ahaka dai yaja motar suka tafi suna hirar yaushe gamo






******************
Wasa-wasa dai Abdallah yau kwanan shi biyar a asibiti yana samun kulawa sosai wajen su Dr Ahmad da Saifullah , Aminullah ma ba baya ba idan ya samu chance yana k'araso wa su sha fira , Abdallah har ya gaji da nacin asallameshi dan shi babu inda yake mai ciwo sai uban gwaje gwaje da ake mai da tare tambayoyi wad'anda suke k'ok'arin birkita mai tunani,




Saifullah kuwa har yanzun baisan hak'ik'anin abinda yake damun abokin shi ba domin Dr Ahmad ya sakaye zancan daga shi sai likitoci suke aikin su,




Tun lokacin da Saifullah yaga Ummi Sam hankalin shi ya kasa kwanciya fuskarta sai gizo take mishi duk iya k'ok'arin shi ya daure amma ya kasa , sai kawai ya yanke shawarar ya nemi k'anin shi suyi magana , bayan ya dawo asibiti da daddare ya nufi part d'inshi wanka yayi ya ci abinci sannan ya nufi part d'in Aminullah a kwance ya sameshi yana game d'in criminal case a tab d'inshi da alama yana jin dad'in game d'in , motsin da yaji ne abayan shi ya sashi juyawa Saifullah yagani tsaye bakin k'ofa ya jinga ya zuba mishi k'ananun idanuwan shi da suke alumshe kamar mai jin baccin , dama idan ka Ganshi cikin wannan yanayin to akwai abunda ke damun shi .




Cike da kulawa Aminullah ya aje tab d'inshi sannan yace "what's up bro?"


D'aga kafad'un shi yayi alamar babu sannan ya k'arasa shigowa d'akin ya zauna kan kujera ya sake zubamai ido
Tasowa yayi yazo ya zauna kusa da shi yace " Bros wai meke damunka dan Allah ka sanar da ni idan zan iya taimaka maka idan ba zan iya ba kuma ko shawara na baka"




Ba tare da b'ata lokaci ba Saifullah ya sanar ma Aminullah da k'udurin shi akan Ummi daga k'arshe kuma ya nemi shawarar shi






Duk da Cewar Aminullah yaji wani iri akan maganar amma sai ya dake domin yana son ganin farincikin D'an uwansa , shima bai b'oye mishi komai ba game da wace ce Ummi ,


Tausayinta ne k'arara a fuskar Saifullah ya d'ago idanuwan sa da suka k'ara k'ank'ancewa yace "kana nufin har yanzun ba'a ga mijin nata ba ?"


"Had yanzun ba'aga Wanda yaga me kama dashi bama"


Jinjina kai yayi yace "gobe zaka rakani wajen mahaifin ta"


D'an zaro ido Aminullah yayi yace" me zakayi?".




With compidence yace "auren ta zan nema"


"Bro haramun ne fa Neman aure akan aure "


"Sam wannan auren nata bashida amfani kawai yarinya k'arama ana k'ok'arin d'aura mata wahala , yanzun haka ma wayasan inda yake ? Ko yana da rai ko bashida da rai oho?"




"Tab mai da wuk'ar , but you have to control your anger "


Bai cemai komai ba ya fita a d'akin , daren da k'ar ya samu yayi barci tunanin Ummi kawai yake yi dan yanzun wani tsananin sonta ke k'ara shigar shi duk ya k'agara gari ya waye


Kasan cewar yau Saturday ne ba makaranta dan haka da wuri suka shirya suka je gidan Malam kasan cewar safiya ce sun same shi yana ta koyar da almajiran shi wuri suka samu gefe suka zauna saida Malam ya sallami almajiran sannan ya kalli Aminullah yace " Amintacce bawa Kaine da sanyin safiyar nan ?"


Murmushi yayi yace "nine Malam"


Cikin girmama juna suka gaisai sannan Aminullah ya gabatar da D'an uwanshi Saifullah awajen Malam




Shikuwa Saifullah ya gabatar da k'udurinshi na son auran Ummi a wajen Malam




Shiru Malam yayi kamar ba zaiyi magana ba Dan maganar tazo mishi a bazata


Ya fara magana kamar haka , " kamar yadda D'an uwanka yayi maka bayani Ummi dai da aure a akanta sannan kuma bamu da ikon daura wani aure har sai an warware wanchan dan haka kayi hakuri duk yadda muka shawarta zan nemeka"


Godiya sukayi suka tafi duk da cewar sa Saifullah baiji dad'i ba Kasan cewar bai samu k'wak'waran tabbaci daga Malam ba haka ya koma gida cikin zullumi






Ranar wata talata ne wurin k'arfe biyar Ummi ta gama lectures d'in ta Hafsa kam bata samu zuwa va sakamakon wani irin ciwon kai da ta tashi dashi , hakan yasa yau ita kad'ai Aminullah zai mayar gida , bayan sun Shiga motar ya Tayar kenen wayarshi ta hau ringing Saifullah ne ya kirashi , bayan ya d'aga wayar yana sauraron me zaice bayan ya gama kawai sai ya ce "OK "ya kashe wayar




Juyawa yayi yace ma Ummi "Aunty Ummi kimin hak'uri kad'an zan amshi sak'o wajen bro acikin hospital "


Ta D'an b'ata rai tace "to"


Suna isa asibintin yayi parking inda ake parker motoci sannan yace "D'an Allah muje Ki gaida yaya na yana da mutumcin shi be cika d'aure fuska irin na Saifullah ba"




"Uhum muje"


Haka suka taka sunan jera wa kowa ya gansu sai ya sake kallon saboda tsabar marching da sukayi


Sai da sukayi tafiya me d'an nisa sannan suka k'arasa d'akin


Ummi kuwa nan take taji zuciyar ta na bugawa kamar zatayi tsalle ta fad'o k'asa




Tare da sallama ya bud'e k'ofar Kasan cewar gadon yana kallon k'ofar ya saya direct kana Shiga zaka hangi na kwance akan gadon yana baccin




K'iiii taja wani dogon birki sakamakon arba da tayi da wata fuska da ta dad'e tana marmarin gani duk da dai sauyin da ta gani hakan bai hanata gaskata ko wa ta gani ba




Aminullah ne ya juyo da niyar yi mata magana ita kuma alokacin ta juya ta kwasa aguje


"Ummi! Ummi!! Ummi!!!?" Haka yayi ta kwad'a mata kira amma bata waiwayo ba haka yasa shima ya kwasa aguje yabi bayan ta








❤❤
[1/17, 3:57 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*




*MRS NN ONE💋*






® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*


_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_




# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com








3⃣6⃣




Tun da ta runtuma bata tsaya ba mutane sai kallonta suke , duk iya k'ok'arin Aminullah ya tsaida Ummi ya kasa , aiko yana ganin sun kai wurin wani kwararo da ba mutane ya figo hijab d'inta ta dawo baya , kamar zata bangaje shi ,




Ganin yadda take kuka harda majina gashi sai wani tittirjewa take kamar sabuwar 'yar bori ya sashi daka mata tsawa " ke Zainab!!"


K'ara firgita tayi zata sake gudu sai ya sassauta muryarshi yafara magana cikin sanyi " Ummi Ki natsu mene ne ?, me ya faru ?, wani Abu aka miki,?"




Duk ya gama jero tambayoyin shi amma kawai da ido tabishi




Azuciyar ta ko fad'i take ina ma tana da halin amsa masa wad'an nan tambayoyi data amsa su


Shi kuma ganin shirun da tayi ga hawaye yana ta sintiri a fuskarta sai ya fara tunanin anya Ummi kam kanta k'alau ? Bai sake cewa komai ba yaja hannun ta har gurin motar shi sannan yace mata ta Shiga , tana Shiga ya rufe sannan ya zagaya shima ya Shiga , sannan ya tada motar har a lokacin kuka take shak'a ,




Haka yayi ta tuk'i amma Sam zuciyarshi bata mishi dad'i saboda yadda yake jin kukan Ummi a zuciyarshi kamar ana d'iga mishi tafasasshen ruwa.




Suna isa k'ofar gidan su ta hangame murfin motar ta fito ko tsayawa ta rufe batayi ba ta fad'a gidan su Hafsa , shi dai Aminullah kanshi duk ya d'aure ya rasa gane meke damun Ummi ayyah batada junnu, nan ya coge a k'ofar gidan.




Ummi kuwa tun da tasa kanta a zauren gidan ta fara k'wala ma Mama kira




Mama na d'aki abin da bata tab'a ji ba kenan afirgice ta fito tana "Ummi mene ne ?"


Amma ina zubewa tayi ta dasa sabon kuka , Mama duk ta kid'ime ,




Hafsa dake d'aki tana fama da kanta tafito ganin yadda Ummi ke kuka bilhak'i da gaskiya sai jikin ta ya k'ara sanyi domin duk runanin ta wani mummunan abun ne ya faru .




Duk suka rud'e da tambayoyi amma Sam Ummi tak'i magana sai kuka , cikin k'unci Hafsa ta koma d'aki ta d'auko hijab d'in ta ta fice , yanayin tashin hankalin da take ciki shi yasa bata lura da Aminullah dake zaune kan dakali ya zabga uban tagumi ba , shima kuma bai kula ta ba .




Direct gidan su Ummi ta fad'a ba'afi minti biyar ba sai gashi sun fito tare da Malam.




Malam ya ga Aminullah zaune turus ya zabga tagumi , shi kanshi Malam d'in sai da gaban Shi ya fad'i , cikin sanyi ya ce " Amintacce meke faruwa ne ?"




Aminullah ya kalli Malam cikin damuwa sannan ya labarta mishi sukkan abubuwan da suka faru d'azun ,




Bai yi wata wata ba yace ma Aminullah zo muje , suna suga gidan Malam ya hau fad'a yana tambayar ta me ya faru ? Ko tayi hauka ne duk ta tayar wa da mutane hankali,




Murya na rawa kamar ta mai koyon magana tace "Baba na...na..Ganshi"


"Wa kika gani?"


Zata k'ara wani kukan Malam ya yi jan ido yace takuma sai ya lallasa ta




Da k'yar tace " *ABDALLAH* "


Maman kam dab'as ta zauna a k'asa tayi zaman 'yan bori , tana tunanin to kodai mafarkin ta na jiya ya zama gaskiya ne?




Hafsa ma sai da ta Zabura,


Aminullah gaba d'aya ya firgice domin bai gane inda zancen ya dosa ba .


Malam ma kanshi duk ya d'aure ya kalli Ummi da keta wik'i-wik'i da ido dan yanzun kukan ya tsaya ya ce "Ummi kinsan me kike fad'a kuwa?".


With confidence ta d'aga kanta tare da fad'in "ku tambayi Aminullah AI shi ya kaini inda yake "


Nan fa kallo ya koma kan Amintacce wanda duk sun k'ara birkita shi , Malam ya kalli Aminullah yace " Amintacce mene ne hak'ik'anin wannan zancen?"


Cikin muryar rud'u Aminullah yace "kamar yadda na gaya maka a waje , abokin yaya na ne bai da lafiya shine yaya na yakirani na je na karb'i kaya na wuce mai dasu gida , shine na rok'i Ummi ta raka ni lafiya lau muka shigo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login