Showing 57001 words to 60000 words out of 70663 words
Chapter 20 - WACECE NI BOOK COMPLETE BY UMMUH HAIRAN.txt
don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
*WACECE NI?*
*(SANADIN KUKANA!)*
_typing✍🏻_
*Mrs Dr M.A...*
*48-49*
Dagowa tayi da sauri ta dubeshi shima ita yake kallo ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa “ina kwana" bai amsaba sai miqewa da yayi ya fita yace “kada ki batamin lkc inada abinyi zankai matata airport zata tafi Rasha" jikinta a sanyaye ta miqe ta shiga bathroom tayi brush ta fito ta dauki doguwar rigarta ta zura ta dauke mayafinta ta yafa ta fito yana tsaye har ya quta saboda takaicin jiran da yayi mata.
Tana fitowa ya zafga mata hararar da saida yayan cikinta suka juya ya fuzgi dansa dake hanunta ya fice ya shiga motar itama ta fito ta bude ta shiga yaja a guje suka fita ya nufi gdansu Ummuh duk bacin ran da take ciki tana shiga gdan sai taji ya goge.
A parlour suka iskesu tana zuwa ta shige jikin Abuha tana dariya shima murmushi yayi yace “Bintun kina lfy ya jikana?" Shigowar Colonel Marwan ne yasasu dagowa suka kalleshi ya qaqalo murmushin da baikai zucci ba yace “jiya bata barni nayi bacci ba har mafarki ta rinqayi da ku shiyasa nace yau asubanci zamuyi muku" kallonsa takeyi da tsananin mamakin yanda ya karkace yake sharara qarya a gabanta itama Ummuh shi take kallo tace “aikuwa kayi qoqari sosai Bintun ya jikinki"
Murmushi tayi tace “wlh Ummuh zazzabin dare yasani a gaba yau kinga harda ma na safen yanzun ma a kwance nake yace na taso muzo" taba jikinta Ummuh tayi taji zafi zau tace “jiya ta hanaka bacci amma hakan baisa ka fahimci batada lfy ba ko?" qasa yayi da kansa cike da kunya yace “dama idan muka gama danan zamu wucce asibiti" qwafa tayi sukaci gaba da hirarsu shi hankalinsa yafi karkata wajen yiwa dansa wasa inda ita kuma take kwance jikin Abuha tanata zuba masa shagwaba. Miqewa yayi da Mu'azzam a jikinsa ya fice.
Basu dawoba sai dare sosai lkcn Mu'azzam yayi bacci sukayi sallama da Abuha ta tafi akan cewa zasuzo da Ummuh, suna zuwa gda ya shige dakinsa da Mu'azzam a hannunsa itadai batace masa qalaba itama ta shige nata dakin ta kwanta saboda bacci takeji sosai.
Hakanan sukaci gaba da wata quntatacciyar rayuwa har tsayin watanni biyu kalma bata shiga tsakaninsu ko gaisuwa tayi masa bai amsawa hakanan yakejin bayason ganinta ko motsinta bayason ji a inda yake wannan dalilin yasa sai suyi sati guda basu hadu ba zuwa wannan lkcn ciwo yaci qarfinta sosai kullum cikin zazzabi amai da ciwon kai take gashi Allah ya dora mata wani mugun kwadayi kullum abinda zataji tana sha'awa daban gashi ko tasa an nemo mata bata iyacin na kirki sai taji ta qoshi idan ta cika takurawa kuma ta kama sheqa amai.
Kullum Baba Zulai cikin tuhumar ta takeyi meye yake damunta haka amsa daya ce babu komai yau dai abun yaci tura don tunda ta tashi take murqususun ciwon ciki dole Baba Zulai ta kirashi a waya take fada masa budar bakinsa sai cewa yayi “to kiyi mata abinda zaki iya kibarwa Allah sauran" yana ida fadi mata haka ya kashe wayar ta saki baki sororo da tsananin mamaki jikinta yayi mugun sanyi saboda bata taba lura da abin yakai hakaba a matuqar sanyaye ta koma dakin nata ta tarar da ita tadan samu relief ta hada kanta da gadon tanata sharar hawaye ta zauna a gefenta tace “waini meye yake faruwa tsakaninki da mijinki ne yar nan?"
Hawaye ne ya zubo Mata tace “yace bazaizo ba ko?" Kallonta Baba Zulai tayi tayi murmushi me ciwo tace “shiyasa nace kada ki kirashi nasan amsar dazai baki kenan bansan abinda nakeyi masa ba yake daukan wannan matakin akaina ba" kallonta Baba Zulai tayi tace “gsky bazai yuwuba yar nan dole asan abinyi ki fadawa iyayenku asan matakin da zaa dauka bantaba ganin rashin imani irin wannan ba matarka qanwarka batada lfy amma kace babu ruwanka"
Girgiza mata kai tayi tace “kada ki fada musu don Allah wlh bana fatan shiga tsakaninsa da iyayensa musamman Ummuh" miqewa Baba Zulai tayi tace “nasan baki da kudi ki tashi ki fito muje a dubaki akwai albashina na wannan watan bantaba ko sisi ba" miqewa tayi suka fita jiri da dibanta Baba Zulai ita ta riqeta Mu'azzam yana bayanta suka fito Jabir drivensu tajasu zuwa wani asibiti dake cikin unguwar suna zuwa babu bata lkc suka bata gado tare dayin gwaje²nsu cikine da ita wata biyu harda sati daya sosai Baba Zulai tayi murna tare da gdy ga Allah bata daddara ba ta sake kiransa ta fada masa yakuwa nuna farin cikinsa harda tambayarsu suna wanne asibiti, ta fada masa yace su jirashi kafin wani dogon lkc sai gashi a asibitin ya shiga dakin da take tana kwance yaje ya rungumeta yanata murmushi yace “na gde sosai everlasting kin gamamin komai" bata iya cewa dashi komai ba likitan ya shigo yace.
“Baba jikar nan taki akwai damuwa a ranta don Allah ku rage sanyata damuwa mace me qaramin ciki bata daukar damuwa jininta zai iya hawa" kallon Colonel Marwan tayi shima itan ya kalla ya kawar dakai tare da cewa “me kikeso kici everlasting?" Kawar dakai tayi ji takeyi kamar ta shaqeshi saboda takaici.
Kallon da yaga tanayi masa ne yasashi shiga hankalinsa likitan ya miqa masa takardar magungunan ya fice shima ya tashi ya fita tashi tayi ta dubi Baba Zulai hawaye na zubo mata Allah ya sani batayi farin ciki da samun cikin ba Mota suka shiga Jabir yaja suka tafi gdan suna shiga yayi parking babu kowa a cikin masu gadin gdan su uku sai Ostin shi daya tanata yan waqoqinsu na sojoji bude qofar tayi ta shiga ta haura saman saboda baccin dake idonta.
Bude qofar tayi ta shiga ta fara cire kayanta ya rage daga ita sai under siket da bra taji an bude qofar bathroom din an fito ta kalli qofar da sauri cikin firgici wani gajeran mutum ta gani baqi ya fito dagashi sai boxes ya nufota taja baya da sauri tare da qwallah ihu, a lkcn Marwan ya hauro saman da sauri ya bude qofar ya shigo yaga yanda mutumin ya damqi nononta yana qoqarin cire bra dinta yana cewa haba Baby shekara nawa muna harkar nan da zaki tayarmin da hankali ki gujeni yanzu ki barni na jiyar dake dadi yau har magani nasha saboda kince wannan banzan kodadden mijin naki baya kulaki har yanzu nasan kin tara ruwa sosai tun haduwarmu ta qarshe ana danasha gindinki har yanzu zaqin ruwan durinki nakeji a bakin..."
Wani uban ihu Colonel Marwan ya saki tare kaiwa mutumin damqa amma saiya hankado masa Marwah da tuni ta sume saboda tashin hankali ya tureta yabishi a guje ya bangaje Baba Zulai dake fitowa da tire a hannunta ya fice haka suka keta da gudu yana qoqarin zaro bindigar pistol din dake qugunsa yaji sautin harbin ya tashi mutumin ya fadi riqe da qafarsa Emmah ne yayi harbin ganin yanda uban gdan nasa yakecin uban gudu shida wani qato shikuwa Ostin jikinsa bari yakeyi saboda tashin hankali........
More comments😍
More typing 😍
*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[3/14, 9:32 AM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
*WACECE NI?*
*(SANADIN KUKANA!)*
_typing✍🏻_
*Mrs Dr M.A...*
*50-52*
Da gudu ya qarasa gaban mutumin ya sanya hanu ya damqi wuyansa ya miqar dashi ya hada kansa da bishiyar da take gurin ya sake jifa dashi a fusace yace “kasamin shi a waccan dakin horon ka hada masa shocking harsai ya fadi abinda ya kawosa gdana har dakin matata waye ya turoshi.
Juyawa yayi da koma ciki zuciyarsa na wata irin bugawa kamar zata faso qirjinsa ya sake haurawa saman ya taddata kwance inda ya barta wani irin tuquqi zuciyarsa takeyi masa duk yanda yakeso yasa a ransa ba ita ta kawoshi ba ya kasa dubada abinda Ostin ya fada masa cewa “hajiya tayi baqo" inkuwa hakane to tabbas tasan da zuwanshi ga qarin wata hujjar daga kalaman mutumin da yake cewa ta fada masa mijinta baya kusantar ta, idan ba itan ta fada masa ba waye yasan baya kusantarta? Juyawa yayi ya fice zuciyarsa na tafasa ya shiga dakinsa ya zube a tsakar dakin dafe da qirjinsa shi kadai yasan irin zafin da qirjinsa yakeyi masa kwarto a cikin gdansa dakin matarsa da yafiso a duniya diye da kowacce mace hawaye suka zubo masa yana girgiza kansa yanajin wani qunci yana mamaye kowanne kusurwa na jikinsa da gaske ne wannan qazamin mutumin ya kwanta da Zahransa meyesa tayi masa haka meyasa zata ha'inceshi.
Miqewa yayi yana layi kamar zai fadi ya shiga dakin nata baba zulai ya tarar tana shafa mata ruwa a fuskarta tana hawaye saboda wannan sharrin ya girmi tunaninta matuqa tayi mamaki tunda suke da Marwah bata tabayin baqo namiji ba ko a Hira bata taba cewa da ita tanada wani namiji data sani ba bayan Colonel Marwan ba ajiyar zuciya ta sauke me qarfi bakinta yana furta “innanillahi wa innah ilaihirraji'un" hawaye nabin kwarmin idonta, tsallaketa yayi ya shiga cikin dakin ya dauki dansa ya tsaya a kanta yace “kin munafurceni kin ha'inceni bantaba tunanin haka daga gareki ba Zahrah kaico da bamu muka tarbiyyantar dake ba wannan ba tarbiyyarmu bace kina da aurena akanki kike neman wani namijin me kike nema Zahrah meye banayi miki wacce buqata kike da ita da tafi tawa dahar kike neman wani kin cuceni Zahrah Allah ya isa tsakanina dake qato har gidana"
Dakatawa yayi yaja fasali kana ya share hawayen idonsa yace “bazan taba yafe miki ba Zahrah kije gakinan ga duniyar nan bazan iyaci gaba da zama da mazinaciya irinki ba sannan abu na qarshe idan kin haihu ki nemawa danki uba bani bane ubansa Mu'azzam nasan danane amma wannan cikin ba nawa bane" yana fadin haka ya juya zai fita saura kadan suyi gware da Ummuh ya kauce yabata hanya ta qarasa gaban Marwah da takasa furta ko kalma daya sai rawa da jikinta yakeyi kalamansa sunayi mata yawo a kwanya, rirriqeta Ummuh tayi tace “ke ki nutsu shiga nutsuwarki sai me meye dan kin rabu da wannan alaqaqai din dama ai ba ajin aurenki bane qaddara ce ta hadaki dashi kaje Bunayyah kaje Allah ya sakawa wanda aka zalumta ka turamin a waya ka saki matarka qanwarka saki daya ka kyauta amma inaso kasan wani abu ni nasan Allah bazai taba hadamin ku duka iri daya ba sama ace Zahrah tana neman maza to da kake mata wannan babatun laifin waye kuma horon waye komai tayi kaine sila kuma a gurinka ta gani wacce irin macece baka nema ba da aurenka sai ita dan anyi mata sharri?"
Dagowa yayi ya zuba idonsa akan Marwah da sai yanzu ta samu damar sakin wani kuka me ciwo sai yanzu ta tuna ashe zarginta yakeyi da zina a fili tace “ hasbunallahu wa ni'imal wakil wlh Ummuh ban aikatab...." Rufe mata baki Ummuh tayi tace “kin ma aikata Zahrah kin aikata kuma cikin mu munaso tashi kibar masa gdansa" juyawa yayi wasu hawaye sunabin kuncinsa zai fita ta zabura ta miqe da sauri ta janyo loccar ta dauko qur'ani cikakke tace “wlh tallahi billahillazi La'ilaha illah huwa ban aikata abinda mijina kuma yayana yake zargina dashi ba Allah kaine shaidata Kaine zaka wankeni Allah..."
Rufe mata baki Ummuh tayi ta qwace qur'anin tace “bakida hankali wannan dan iskan zakiyiwa rantsuwa dan ya yarda dake kada Allah yasa ya yarda dake koma ya kike ni inasonki Zahrah matsawa tayi tasa hanunta ta sharara masa mari ta fuzge Mu'azzam da yake hannunsa tace “baka isa mubar maka danmu ba kaje ka haifa da matar sonka shima ba naka bane zamu nema masa uba"
Tana fadin haka ta fuzgi hannun Marwah suka fice tana waiwayensa tana hawaye shikam ya tsaya kamar mutum mutumi ya kasa motsa ko yatsansa zubewa yayi a gurin yayi zaman yan bori maganganun Ummuh sunayi masa yawo a kwanyarsa rabawa baba zulai tayi ta gefensa ta wucce ta sauka qasa ta fada saman kujerar ta fashe da kuka tana fadin “Allah ka biwa marainiyarka haqqita wannan zalumcin yayi yawa" ta jima a gurin tana kukan tausayin Marwah kafin taji saukowarsa idanunsa sun kada sunyi jawur ya fice daga gdan ya shiga motarsa ya fice.
Gdan nasu ya nufa shima sanda yaje ya tarar da Ummuh a parlour tayi tagumi rungume da Mu'azzam a jikinta tana kuka, durqushewa yayi a gabanta ya riqo hanunta zaiyi mgn ta katseshi tace “tashi ka bani guri Marwan wlh zan iya illataka na tsani ganinka Marwan ka ficemin daga gdannan" dagowa yayi idanunsa kamar garwashi yace “don girman Allah Ummuh kada kiga laifina adalcin da zan iya yiwa Zahrah kenan..." Miqewa tayi tace “nasani ai banga laifinka ba dama" wuccewa tayi ta shige dakinta ta datso ta qyaleshi miqewa yayi ya nufi dakin Marwah a kwance ya tarar da ita ta qudundune da blanket tanata ajiyar zuciya wani tausayinta yaji ya ratsa zuciyarsa ya matsa a hankali ya zauna a gefen gadon ya dagota tayi saurin janyewa ta miqe a fusace ta nufi bathroom yayi saurin janyota yace “ki tsaya kiji abinda zan fada mik..." Angajeshi tayi ta fice daga dakin da gudu ta shige kitchen ta datse qofar binta yayi da kallo tare da cije lebansa ya juya ya fice daga gdan Saida Ummuh taji tafiyarsa sannan ta fito ta nufi kitchen din ta kamota tace “kinyimin daidai don Allah ki cire damuwa a ranki ba kanki aka fara ba uwar muminai ma Nana Aisha (R.A) anyi mata irin wannan qazafin qarshe munafukai sune sukaji kunya kema insha Allahu duk wanda yakeda hanu a rabaki da mijinki shine zaiji kunya jibi insha Allahu zan kaiki Lebanon kiyi zamanki acan ki huta da wannan banzar rayuwar"
Itadai batace komai ba haka suka yini har zuwa dare da Abuh ya dawo Ummuh ta sanar dashi abinda yake faruwa shima ransa ya baci matuqa musamman da yaji furucin da Marwan yayi wai cikin jikinta ba nashi bane bai iya cewa komai ba saboda baqin ciki kuma bai nemi Marwan din ba.
Washegari da wuri yazo gdan saboda kwana yayi bai rintsaba abubuwa uku suke damunsa takaicin kama matarsa da yayi da wani qato da takaicin sakita da yayi da takaicin qin saurararsa da iyayensa sukayi da kuma takaicin Kiran da Ra'isah tayi masa wai lallai saidai ya cikewa Marwah saki uku kuma yaje a gwada jininsa idan bata liqa masa wani ciwon ba, yana zuwa ya tarar da Abuh a parlourn yana duba jarida ya zauna suka gaisa shiru ta ratsa kafin daga baya ya dago yace “Ummuh fah Abuh?" Kallonsa yayi yayi murmushi yace “tayi tafiya" dagowa yayi da sauri cikin faduwar gaba da baisan dalilinta ba yace “matata da dana fah?" Kallonsa Abuh yayi yace “matarka kafini sanin inda take da kuwa bansan kanada shi ba Mu'azzam da wanda zaa haifa nan gaba duk ba naka bane munyi musu uba"
Kallon Abuh yakeyi amma ya kasa furta komai miqewa Abuh yayi yace “zan hau sama inason hutawa idan zaka fita ka rufe mana qofar" binsa yayi da ido har ya haye saman ya miqe a kasalance ya fice gda ya koma ya shiga dakin dayasa wannan mutumin yana shiga mutumin ya fara kuka yana durqushewa yace “wlh Alh biyana akayi akace nazo na shiga dakin matarka Ostin shine ya nunamin dakinta Hajiya bata taba ganina ba" matsawa yayi gabansa ya damqi wuyansa yace “waye ya turoka kuma nawa aka baka saboda ka tarwatsamin farin cikina?" Shaqa yayi masa bata wasa ba Saida yaga ya galabaita sannan ya sakeshi ya zaro bindiga ya sanya masa a maqogaro mutumin yayi saurin cewa “Haj...Hajiya Ummah ce ta sanyani tace wannan din kishiyar qawarta ce wlh dubu ashirin suka bani".............
More comments😍
More typing😍
*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[3/14, 8:12 PM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
*WACECE NI?*
*(SANADIN KUKANA!)*
_typing✍🏻_
*Mrs Dr M.A...*
*53-55*
Wani mugun mari ya zuba masa jikinsa na rawa ya fice daga dakin da sauri ya koma cikin gdan ya zube akan gado yana dafe da kansa yace “ya Salam wannan wacce irin masifa ce me Ra'isah take nufi da rabashi da matarsa wannan wacce irin qaddara ce" dare yayi sosai saboda haka ya kwanta amma fa bai iya rintsawa ba da asuba ya fice daga gdan ya nufi gdansu wannan ma Abuh ne kadai a gdan suka gaisa yace “don Allah Abuh kayi hqr wlh bacin raine nayi kuskure dana yanke hukunci cikin fushi..."
Daga masa hanu Abuh yayi yace “babu wata damuwa a cikin lamarinka da Zahrah face abinda Allah ya hukunta Allah bai qadarta zama na har abada tsakaninku ba ka godewa Allah ka rabu da mazinaciya wacce tayo ciki a waje ta kawo maka gda" toshe kunnensa yayi saboda kalaman na Abuh sunyi masa nauyi zuciyarsa na tafasa.
Miqewa Abuh yayi ya fice daga parlourn zuwa gurin da yake training duk safiya, haka ya qari zamansa a gurin har ya gaji ya miqe a gajiye ya koma gdansa ya shige dakinsa ya kulle ya kwanta yanata kiran wayar Marwah da Ummuh amma taqi shiga zuciyarsa tana qara daukar zafi ji yake kamar yayi tsuntsu yaje ya ishesu a duk inda yake, yananan kwance kiran Ra'isah ya shigo wayarsa yana gani har tayi ring dinta ta katse bai dagaba duk yanda yake tunanin bacin ransa ya wucce haka zuciyarsa har bugawa takeyi saboda bacin rai, yanajin kiran ya katse wani ya kuma shigowa shima bai dagaba wata masifaffiyar tsanar Ra'isah yakeji a ransa wannan ranar dai duk Kiran da akayi masa qin dagawa yayi daga qarshe ma ya kashe wayar.
*************************
Bayan dogon lkc al'amura gabadaya sun rikicewa Colonel Marwan Jos ba dadi bukur ba dadi azaba sosai gashin