Showing 51001 words to 54000 words out of 70663 words
Chapter 18 - WACECE NI BOOK COMPLETE BY UMMUH HAIRAN.txt
kalaman da ya fadawa matar tasa wasu hawaye masu zafi suka zubo masa yarasa meyasa yakejin tsanar yarinyar a kowacce gaba ta jikinsa tare da jin haushin hada zuri'a da ita da yayi.
Hawayene sukebin idonsa ya miqe ya dauro alwala yayi sallah yana roqon Allah ya yaye masa abinda ke damunsa game da Marwah ya rasa laifin da tayi masa da yake nisanta kansa da ita ko waya idan ya daga zai kirata sai yaji ya kasa dole ya ajiye.
Ita kuwa yana katse wayar jikinta ya dauki wata rawa zuciyarta na bugawa da qarfi fat² tayi saurin dafewa tare da furta “Allahummah la sahla wama maja'altahu sahla wa'anta taj'alul hazna iza shi'itah sahla Innanillahi wa Innah ilaihirraji'un Allahummah ajjirni fi musibati wa'akalifni khairin minha...." Wani kuka me ciwo ya qwace mata jikinta yana rawa ta zame daga kan gadon tana jin numfashinta yana qoqarin daukewa tace “Na dade Ina tunano zuwan wannan ranar gata tazo shiyasa naqi sakin jiki dakai tun farko saboda tsoron fadawa wannan tarkon meyasa zaka gujeni a lkcn da nafi kowa buqatarka meyasa zaka karyamin alqawarin da kayimin Colonel me nayi maka haka daka tsaneni meyasa ka tsaneni ka fadamin laifina wlh zan gyara banida kowa saikai bansan kowa ba saikai Allah na roqeka kada ka rabani da mijina Allah kasani inason mijina...."
Kukan da takeyi ne yasa mata wani azabbaben ciwon kai tana zaune a gurin ta kasa tashi tama rasa meye ya kamata tayi hakanan ta miqe daqyar ta shiga bathroom ta wanke fuskarta ta dauro alwala ta dauki hisnul muslum ta fara karanta wasu addu'o'i da tasan zasu sama mata sauqi a zuciyarta ta danji sauqin radadin da zuciyarta takeyi mata amma ta kasa tsayar da hawayen idonta a wannan rana daga ita harshi babu wanda yayi bacci kwana yayi yana tunanin halin da zata shiga sanadin kalaman daya fada mata har kuka yayi sosai shima bude system dinsa yayi ya zubawa hotonta da Mu'azzam da sukayi ranar suna Ummuh ce duk ta turo mishi donshi ko gurin sunan bai iya zuwa ba, kyawun yarinyar na musamman ne yanajin qaunarta a can qasan zuciyarsa saman ta kuwa qiyayyarta yakeji har wani bangare na zuciyar nasa yana fada masa idan yaci gaba da zama da ita zai cutu.
Wata sama da daya har an tafi uku rayuwar daga ita harshi babu wanda takewa dadi kullum zai kira Ummuh su gaisa ya tambayeta lfyr dansa amma baitaba tambayarta lfyr uwar dan ba ta lura da barakar dake tsakaninsu amma kullum ta tambayi marwa cewa takeyi da ita babu komai tsakaninsu suna waya dashi.
Babu yanda zatayi da ita hakanan ta qyaleta kullum sai rama Marwah takeyi Ummuh ta rasa dalilin ramar tata har Helin Ummuh ta kira waiko Marwah ta fada mata abinda yake sata rama haka itama amsa dayace ta tambayeta tace mata babu komai.
Wata ranar laraba suna zaune a parlourn Ummuh ta dauko wani tsohon hoto tace da Marwah “kinga hotonnan qanwa tace mahaifiyar Baby Zahrah mu biyu tak Grandma ta haifa wannan yarinyar kuma me shekara biyu da rabi itace baby Zahrah sunyi hoton nan ne a ranar da zasu baro Lebanon zuwa 9ja, idan mutum ya mutu zuciyar makusantansa takan samu sukuni Marwah amma mu tamu ta kasa hutawa bamusan dalili ba"
Karbar hoton Marwah tayi ta zuba masa ido jikinta ya dauki rawa ta zubawa fuskar yarinyar ido qirjinta ya buga da sauri fuskar hoton da yake gurinta wanda ta dauko a gidan marayu tana yi mata yawo akan wannan hoton katin da sauri ta qara bude idonta tare da qanqame hoton ta miqe da sauri ta nufi dakinta da mugun gudu Ummuh ta miqe ta bita daidai lkcn da Colonel Marwan ya shigo parlourn shima ya rufawa Ummuh baya hoton katin da akace an tsinta a aljihun wandon jikinta lkcn da aka tsinceta wanda suke tare da wani saurayin balarabe da take hasashen babanta ne shi ta dauko da kuma wanda akayi mata ranar da aka kaita gdan marayun ta zube akan gadon tana dubawa tana kuka me tsuma zuciya da sauri dukkansu suka matso dan ganin abinda take kallon ta hada hotunan uku tasa wanda Ummuh ta bata a tsakiya, da sauri Marwan ya matsa ya fara kallon hotunan bakinsa na rawa ya dauki wanda take tare da wannan saurayin yace.
“Mar...Marwah ina kika samu hoton nan waye ya bakishi Ummuh duba ki gani hotonane da Baby Zahrah ranar daurin aurena da ita wlh shine Ummuh kigani kingani lkcn tanayi min dariya tana wasa da gashin kaina rugota yayi jikinsa sosai yace “sai... Wlh saikin fadamin ina kika samu hotonnan waye ya baki?" Ummuh ce ta matso ta dauki dayan wanda akayi mata ranar da aka kaita gdan marayu kayan dake jikinta ranar da zasu baro Lebanon sune a jikinta saidai baqi da sukayi suka kukkuje jikinta duk ya kukkuje.
Wata muguwar rungume Ummuh tayi mata tace “kadiran ala mayyasha'u wlh tun ranar dana fara ganinki kike rikidemin kamar mahaifiyarki Ukteeh ashe kece Zahrah ashe kece a tare damu tabbas kece wlh kece da gaske kece Zahrah kece da gaske kece Bintun kece Bintu Ukteeh na...."
Kuma rushewa tayi da kuka me tsuma zuciya tace “Allah kaine kake zartar da komai kaine kake qaddara komai Allah na gde maka daka qaddaramin ganin yata a cikin gdana matsayin matar dana Allah na gde maka Allah Bunayyah naji dadi yau Ina cikin farin ciki wanda bantaba yiba a rayuwata"
Shikam Marwan ya zama kamar mutum mutumi ya kasa motsa komai sai bakinsa da hannunsa da suketa rawa yana nuna Marwah daqyar ya iya cewa “Ba...Baby Zahra...." Baya yayi luuuuuu ya fadi kamar matacce da mugun gudu tayo kansa ta haye jikinsa tana kuka tana girgizashi tana cewa “kada ka mutu Abuh Mu'azzam bani bace banice Baby Zahranka ba nima bansan ya akayi na samu hotunan nan ba ni banida kowa bansan kowa ba ba kowace ni ba face qasqantacciya wadda qaddara ta saka hada jiki da ita har kayi mata ciki ta haifa maka dan da kakejin dama kasani ka zubar dashi kafin yazo duniya, don Allah ka tashi ka cikamin alqawarin da kayimin na zaka nemomin dangina"
Shigowar Abuh ne yasa Ummuh dagowa rungume da Mu'azzam tace “dama ka fadamin Abuh nabi a sannu akwai wani boyayyen abu tsakanin yarinyar nan da Bunayyah yaudai gaskiya ta bayyana Marwah itace Fatima Zahrah itace Baby Zahransa ashe bata mutu ba Abuh duba ka gani duba hotunan nan ka gani wlh bana ko tantama Zahranmu ce wannan tabonta yananan wanda Bunayyah ya qonata da ruwan tea yananan a cinyarta lkcn data haihu inayi mata wanka naganshi har saida na tsorata matsawa tayi jikin Marwah ta janye gashinta daya zubo ya rufe qirjinta ta dora hanunta a saitin nononta tace kalli Abuh wannan digon baqin duk wata ya mace da aka haifa a family dinmu tanada shi shima yasamin kokwanto da wasu wasi akan yarinyar nan abinda yasa nayi shiru saboda nasan mahaliccin dayane komai zai iya faruwa Abuh ashe har gori Bunayyah yakeyi mata Innanillahi wa Innah ilaihirraji'un"
Numfashi Abuh yaja me qarfi yace “Alhmdllh Sukhaina bai kuka ya kamata kiyi ba kina ganin halin da yake ciki shima fah" jan hanun Marwah tayi tana masifa tace “yaje daganan ma ya mutu na samu yata ta dawo zai gane wlh sai yasan yayi mata gorin nasaba bandama qaddara da rashin gata me zatayi dashi mazinaci dan giya...." Saurin rufe mata baki Marwah tayi ta fuzge hanunta tace “ki daina banaso Ummuh koma ya yake inasonsa don Allah ki daina bayin kansa bane uban danane kuma yayimin alqawarin zai tayani neman dangina niba nice Zahranku ba bani bace ni yar 9ja ce ni baqace ni kukuwa farare ne ku larabawa ne ku"
Mamaki ne ya cika Ummuh ta saki hanunta a sanyaye ta koma ta tsuguna gaban mijinta tana kuka tanayi masa magiyar ya tashi ya fada mata yanasonta bai tsaneta ba ya tashi yayi Mata alqawarin ba zai qara yi mata gori ba, cikin hawaye Abuh ya bude fregde ya dauko ruwa me sanyi ya sunkuya yarinqa zuba masa a kansa cikin gashinsa zuwa fuskarsa zuwa qirjinsa, ajiyar zuciya ya fara saukewa a hankali ya bude bakinsa yace “kece Zahrah da gaske kece Marwanatu kece Zahrah ta".............
More comments😍
More typing😍
*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[3/10, 3:10 PM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
*WACECE NI?*
*(SANADIN KUKANA!)*
_typing✍🏻_
*Mrs Dr M.A...*
*38-39*
Kukane ya qara cin zuciyarta ta miqe a sanyaye zatabar gurin ya cafko hanunta ta fado jikinsa ya matseta tare da dora kansa saman sumarta yana jero ajiyar zuciya yace “ko lkcn da bansan matsayinki a gurina ba nasoki kamar rayuwata balle yanzu da nasan wacece ke a gurina Ina sonki everlasting tunaninki da damuwar rashinki shine yasani tahowa nazo naji dumin jikinki ko na samu sauqin abinda yake damuna"
Dago kanta tayi da sauri ta kalleshi kawai sai taji digar hawayensa cikin qwayar idonta ta lumshe idonta tare da sake kwanciya a jikinsa tanajan zuciya tanajin ninki qaunarsa a zuciyarta.
Janyeta Ummuh tayi daga jikinsa ta jata suka fice daga dakin yana me binsu da kallo tare da tsananin jin kunyar Marwatuh a zuciyarsa, ya jima a zaune kafin ya iya miqewa ya matsa inda Mu'azzam yake kwance yaron ya girma sosai kamarsa da mahaifiyarsa ta qara fitowa hasken fatarsa ne kawai na ubansa sai hatsunsa, ajiyar zuciya yayi yasa hanunsa ya dauko yaron ya zuba masa ido yana murmushi hawaye na zubo masa yana tuna rabonsa da dannasa tun ranar sunansa gashi har ya shiga wata na hudu dakansa yake tambayar kansa ya akayi hakan ta faru?
Miqewa yayi dauke da yaron yanajan karan hancin ubannasa ya fita dashi ya dauki key din motar Ummuh ya fice, kai tsaye gdan daya gina saboda Marwah ya nufa an zuba komai na amfanin mace a gdan yayi kyau sosai har saman saida ya haura dakuna biyu ne sai wani dan qarami na Mu'azzam wanda aka sanya masa dan qaramin gado na yara, qasanma da daki biyu da alama na baqi ne dana yar aiki iyakar haduwa gdan yayi, yayi murmushi ya juya suka fita gdan Ra'isah ya nufa dansa yana jikinsa da yar tazara tsakanin Nassarawa Layout da Badawa Layout.
Tunda suka taho gabansa yake faduwa hakanan yakejin bayason zuwa gdan yadai rinqa danne zuciyarsa ya isa gdan da Baba Zulai ya fara haduwa takuwa yi tsalle ta miqe tana murna tace “ga jikana yazo gaisheni ga jikana oyoyo" murmushi yayi shima Mu'azzam dake yasanta ya rinqa bangale baki yana miqa mata hanu ta sanya hanu zata daukeshi dadai lkcn da Ra'isah take saukowa daga saman cikin shirinta na fita ta daka mata tsawa tace “idan kika taba shegen dannan a bakin aikinki wlh shashasha kawai da batasan ciwon me kyautata mata ba wannan dan zinar har abin dauka ne"
Tsayawa sukayi sororo suna kallonta harta qaraso qasan da isarta da gadararta ta qaraso gabansa ta nunashi da yatsa tace “Marwan idan ka qara kawomin dannan me kama da yartsana wlh saina dura masa poison ya mutu ka huta nima na huta...."
Bata rufe bakinta ba taji saukar hannunsa a kuncinta tayi baya ta fada kujera ya bita ta dora qafarsa a qirjinta ya nunata da yatsansa yace “ki shigo hankalinki akan matata da dana idan ba hakaba zakiyiwa kanki asarar aurenki kada ki qara sheganta min dana dan sunnah ne me asalin da baki dashi"
A matuqar tsorace take shiyasa bata iya ce masa qala ba har ya gama sababinsa ya dauki dansa ya nufi saman ya bude dakinsa ya shiga yaja ya tsaya turus saboda tsananin mamaki tunda ya sanya qafa yabar qasar baa gyara dakin ba, qwafa yayi ya bude bathroom din ya dawo yana bude wadroop ya dauki kayansa kala biyu ya juya ya fice daga gdan tana kallonsa ya watsa mata wata uwar harara ya fice a fusace har yaje jikin motarsa ya juya ya koma yace da Baba Zulai tazo su tafi, da murnarta ta dauko kayanta suka rankaya harda juyawarta tace “to Hajiya saduwar alkhairi"........
More comments😍
More typing😍
*Mrs Dr M.A...✍🏻*
[3/11, 9:35 AM] MRS M.K.D: https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/
*FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )
*( F.W.A)🖌*
*WACECE NI?*
*(SANADIN KUKANA!)*
_typing✍🏻_
*Mrs Dr M.A...*
*40-41*
Suna fita kai tsaye gdan da Marwah zata zauna nan suka nufa yayi parking ya fita ya bude mata yace “ki shiga ki gyara komai na gdan anjima zata dawo" gdy tayi ya juya ya fice bai bata lkc ba ya dawo da kayan abinci aka jibge a store ya kuma fita yanayima dansa wasa suka sake komawa gdansu Ummuh.
A parlour ya tarar dasu dukkansu har Abuh Marwah tayi matashin kai da cinyar Ummuh dawowarsu kenan daga gdan marayun sunje an basu bayanin zuwan Marwah gdan, sunata hirarsu gwanin dadi Marwah tanajin wani sanyi a ranta lkc zuwa lkc tana share hawayen gdy ga Allah daya nuna mata danginta yau har taji muryar mahaifinta a waya duk da bayajin Hausa saida turanci suka gaisa yana kuka yana godewa Allah daya kawoshi wannan lkcn yana cewa dama yanaji a jikinsa Zahransa bata mutu ba.
Ummuh ce tayi masa alqawarin bazata koma gdanta ba harsai tazo taga danginta nan ya qara cika da mamaki Abuh ne yake fada masa ai matar MARWAN ce wadda ta haihu kwanaki ya qara jinjina lamarin ubangiji wani abun saidai ubangijin badai mutum ba, shigowarsa ce tasasu dagowa idanunsa ya sarqe cikin ns Marwah yanajin wani irin bugun zuciya gabadaya kunyarta yakeji da haushin kansa akan abubuwa da yawa da suka faru a baya amma maimakon yaga ta nuna masa alamar bacin rai sai yaga tayi murmushi ta miqe ta nufosa ya zubawa qirjinta ido yana hadiyar yawu.
Miqa hannunta tayi ta dauki Mu'azzam yanata Bangale mata baki tace “ina kakaimin shi tun rana gashi yanzu har dare yayi" murmushi yayi ya janyota jikinsa da sauri ya rungumeta ita da dansu yace “inasonki everlasting don Allah kiyimin adalci kada ki hukuntani akan abinda ya faru a baya kinji?" Zuciya taja tare da janyewa ta zauna a kujera shima ya zauna Ummuh ta tashi zatabar gurin yayi saurin cewa “Ummuh yau Zahrah zata koma dakinta an gama aikin harma na zuba komai yanzu haka na baro Baba Zulai tana gyara mana gdan"
Wani banzan kallo ta watsa masa tace “ai Kaine kake da kanka bamu muke dakai ba amma ka manta cewa munada haqqi akan ita Zahrah saboda haka ban shirya mayar da ita gdanka yanzu ba..." dagowa sukayi daga ita harshi gabanta yayi muguwar faduwa tayi saurin kawar da kanta saboda Allah ya sani ta tayi missing din mijinta mugun buqatarsa takeyi.
Dakewa taketa qoqarin yi kuma sai taji Abuh yana cewa “Bunayyah dadai kayi hqr ankaita Lebanon taga danginta Abuha yace jibi zaizo ka bari yazo idan yazo sai su tafi Qatar din tare yaje ya nunata a dangi daganan kuma sai Ummuh ta wucce da ita Lebanon taga danginta mahaifiyarta" wani yawu ya hadiye yace “nidai na roqeku kada kuyimin haka Abuh wlh akwai matsala don Allah kuyi hqr kubani matata duk inda kukeson taje ni zan kaita da kaina..." dakatar dashi Ummuh tayi da cewa “ai munsan dakai din bamuce ka kaita ba so bamu buqatarka ne a cikin lamarinta ka tsaya kawai matsayinka na miji" idanunsa ne ya ciko da qwallah zuciyarsa na raya masa kodai wani abu Marwah tace yanayi mata? Amma a fili sai yace “ok amma ai zaku bani ita naje na gyara bangarena na gdannan mu kwana acan ko?"
Murmushi Abuh yayi yace “aa dauki matarka ku tafi kada kayi mana kuka a gaban danka" shafa kansa yayi yana dariya yace “na gde Abuh Ummuh ta daina sona yanzu so take na mutu ta huta" ba Abuh ba ita kanta Ummuh yanda yayi mgnr saida ya bata dariya, yayi murmushi ya kalli Marwah yace “tashi mu tafi dare ya farayi" ajiyar numfashi tayi ya miqe ya shiga dakin nata ya dauko mata mayafinta sanda ya fito Ummuh tajata daki tabata ruwan rubutun da tasa akayi musu na tsari ita da Mu'azzam tasha sannan ta bata wani tace ta dafawa Marwan din tea dashi ya shanye ta sake bata wasu qwayoyin magani tace ta hadiye zasu dade a jikinta, hakanan ta hadiya tayi mata gdy ta bata turaruka da kayan bacci tsadaddu kuma fitinannu harda zaba mata wadda zatasa a daren yau itadai kunya ta cikata suka fito Abuh dake yiwa Marwan nasiha ya hada harda ita ya sake yi musu sanna suka rakasu har gurin motar suka fita daga gdan dayake babu nisa tsakaninsu sosai saida suka biya ta wani gurin saida kayan ciye² ya siya musu ya dawo ya zauna tare da kissing din kuncinta yace “na matsu najini a samanki Baby Zahrah na yau zanyi kwanan farin ciki da bantaba yiba a rayuwata"
Qasa tayi da kanta a kunyace yau tasan ta kade har ganyenta dama ya take qwatar kanta a gurinsa bare an dade baa haduba, batasan sun isa gdan ba saida taji yayi horn ta dago tana qarewa gaban gdan kallo har zuwa lkcn da aka bude da gani basai ka tambaya ba an shirya rayuwa a gdan ta sauke numfashi tare da kallonsa suka hada ido ya daganta gira tare da daukar Mu'azzam da yayi bacci ya fita ya bude mata qofar ta fito ya zagaya baya ya dauki kayan daya siyo miqa hanu tayi zata karba ya janye yace “saurin me kikeyi aikinki da ciki"
Sunkuyar da kanta tayi ya wucce yana cewa “ita munafukar kunyar data dawo a daidai wannan lkcn zanyi kaca² da ita a daren nan" suna shiga sukayi karo da Baba Zulai a parlourn takuwa rangada guda tace “ina bayanki uwar gijiyata Allah yaja kwana ya qarawa rayuwa albarka" murmushi Marwah tayi tace “Baba kwana biyu kin daina ziyararmu Junior har yayi fushi" da sauri tace “tuba nake ranki shi dade abubuwa sukayi yawa