Showing 24001 words to 27000 words out of 36237 words
Chapter 9 - ZUCIYA DA KWANJI 1 NA MAIMUNA IDRIS BELI.pdf
rana mahaifiyata ne sa na ki kai ki ki ga
yan'uwa". Har yau ta kasa dauke ido a
kansa,fuskarta ba ta bayyana rashin kunya ba,
illa ta bayyana damuwa kamar a raunane ta ce.
"Wacce irin rigima ce wannan abdul,bisa wacce
fuskar zaka kwaso min fita da kai?" Ya kawar da
kai,ya marariraice mata. "Ki yi hakuri,kin san
sha'anin iyaye,sai ka kansace mai taka tsan tsan
a cikin lamarinsu don ka samu ku rabu kalau....
Kuma ya kamata mu yiwa malam uzuri tunda bai
san me ye akwai a tsakaninmu ba... To banda
abinki ma waye zazai yarda mun fita taren? Idan
Alh ne sai kar ki sanar da shi a waya alal akalla
dai ai ba ki taimaka na ma mahaifina ba don ban
taba yi miki irin abin da ya yi min wannan
sakayyar ba" Ta dan yi rau rau da ido,amma sai
ta hada ta motsa,ta ce. " Ban hanya na wuce".
Ya ba ta hanyar na wuce". Ya ba ta hanyar, sai
da ta jima a falo sanyaye ya bita jiki a
sanyaye.ya same ta sanye da hijabi ta rafka
tagumi. Ya kara kan kan da murya,ya ce. "Ki
daure muje fadimatu". Ta janye tagumin,ta ce.
"Zan je,amma kai ma ka yi kokari salin'alin jibi
ka sallme ni na bar gidannan nan". A takaice ya
ce. "Toh". Sannan ya dubi agogo ya dube ta.
"Tea za ki sha? Bari na hada miki ki sha sai in yi
wanka ki shirya da kyau,don Allah ki binne
matsalarmu a zuci kar ki bari ko kadan a san
babu jituwa a tsakaninmu kin ji? In kin yi hakan
ma kin gama biyana". Cikin mintuna kadan ya
hada mata tea din tun a kicin ya hada komai.ya
zo mata falon da shi a kofi da choculate guda
biyu,ya ajiye a coffe table ya janyo mata har
gabanta ya yi mata kyautar murmushi,sannan ya
juya yana cewa. "Idan na dawo sallar isha sai mu
tafi". Kai tsaye masallaci ya wuce,har bayan isha.
Yana dawowa ya fece ado kamar mai zuwa zance
ya baza turare,sannan ya rufo kofarsa ko su
sadiya bai yiwa sallama ba ya nufi dakin fatima.
Ta gaji da nata kyan cikin riga da style din zanin
atamfa super milk kala mai ratsin purple da
ruwan zuma.ta gama hadawa idon Abdullahi sai
dai iyakarsa ke nan ganin da zatawa kai haduwar
tata,ko yabo ba shi da ikon ya yi balle abin da ya
fi shi. Tana ganinsa ta yi saurin shigewa daki ta
dauko mayafin da takalmi da jaka purse,ya yi
saurin shanye kallon da yake mata lokacin da ta
karso kusa da shi,muryarsa a dask [truncated by WhatsApp]
Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
.40) Ko gezau ba ta yi ba, sai dai ta saci kallon
kofar dakin,sannan ta mayar da hankali ga
nazartar gidan. Ya kayatu kwarai,ya sha adon
furanni ko'ina,ga shi makeken gaske saboda
yanayi shirunsa kamar babu kowa a cikinsa,sai
karar A.C ko'ina. Sai da suka bi wani korida
sannan suka fita harabar gidan,tana binsa a
baya
har wajen motarsa ya bude mata kofa ta
shiga,sannan ya zagaya ya shiga ya tashi motar
suka fice waje, sannan ya tsaya ya fito ya rufe
garkamemiyar kofar gidan da key. A sannu
yake
tafiya da motar bayan gilasai da ya rufe
kirif,ya
kunna A.C, ga kamshin airfreshner da ke motar
ya gauraye da kamshin turarukan jikinsu ya
hadu
ya ya zama samfurin wani kamshin daban.
Motar
ta yi dif! Kowa zuciyarsa na na zarin,hakurin
Abdullahi dai ya fara zarce awon da ya mallaka,
kusancinsa da fatima ya dinga buga masa zuciya
yana kuma kore masa duk wani tashin hankali
da
zai iya samun kansa a ciki. Ya dinga satar
kallonta yana kallon titi.A karshe sai ya mika
hannu ya latsa sautin D.bany a wakarsa ta Fall
in
love. Fatima ta kara yin dif! Ko motsin kirki ba
ta
son yi.zuciyarsa ta kasa nutsuwa don ta
tabbatar
Abdullahi na nufin wasu abubuwa masu tsauri a
kanta,abin da yake ba za ataba kiransa plan
ba,na gaske ne kuma ba yau ya soma ba tunda
ya tsiro da aure.to amma da wanne KWANJIN
zata kalubalance shi,mutun mai fuska biyu
irinsa?
Sai kawai ta zabi yin bakam ta manne jikin
kofar
motar,tare da alkawarin anyi na farko anyi na
karshe. Har suka je salon wakokin da yake sa wa
ke nan,daga fall in love ya fada,no one like u,
ya
zarce I'm in love, duk ta shanye ta yi banza da
shi. Da ya tsayar da motar kofar gidan ma sai
ya
ki bude mata kofar ta ja mabudin ta saki ta
dube
shi,lokacin da ya kife kai a sitiyarin,a kufule ta
ce. "To ka bude ni mana!" "Ya dago a gajiye ya
dube ta,ya ce. "Oh ba zaki barni na nutsu ba ke
nan?" Sai ta kasa magana,tsawon fiye da
mintuna goma sannan ya gaji ya dago ya dube
ta. "Ki yi kokari don Allah ki toshe duk wata
barakar da zata nuna ba kya sona fatima,ina so
su ganki a mace mai ilmi da tasan abin da ta ke,
ki daure ki ba ni wannan alfarmar domin
ubangijin
da ya halicceki". Kai tsaye ta amsa mas. "Na
ji,amma sauti,idan ba haka ba wallahi babu
wata
alfarmar da zaka kuma neman a wajena na yi
maka,ko da kuwa zata shafe ni" Ya hadiye
dariyarsa ya ce. "Don dai in tsargu ne,amma ni
ba
ke na sa wa ba, bari na bude miki kofar". Ya
balle kofar sannan ya fito ya bude mata, ta
fito
ya rufe kofar sannan ya yafuceta suka zagaya
ta
wata hanyar daban saboda cikar da kofar gidan
nasu ya yi da masu daukar karatu
1 · Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
41) Iyakar karamcin yau fatima ta je gidansa
babba da yaro kowa na farin ciki da zuwanta.
Waje waje Abdullahi ya dinga kai ta yana
gabatar
mata da masu wajen,matan malam
uku,haj.zainab,haj Anisa da haj umma,ko
wacce
ta karrama su kwarai,turamen atamfa da
turaruka. Haka ya kai ta wajen matan
yayyensa
wadanda ke nasa bangare su ma suka dinga
karram ta. A nan ne ya shiga kiran kannensa
yana gabatar mata su ita kuma tana yabawa da
matukar karamci babu ta inda ta bude kofar sai
suka dinga yi mata kallon mace mai kirk matuka
da son mutane. Kai har dakin da ya yi
samartakarsa sai da ya nuna mata,sannan ya
nuna mata dakin mahaifiyarsa wanda yanzu
kannensa mata suka gaje ya ce. "Kin ga dakin.
Innata,shekararta biyu da rasuwa". Har cikin
zuciyarta ta tausaya masa yayin da kalamanta
suka cika da alhini. "Allah sarki,Allah ya ji
kanta,ya sada ta da annabin rahma". Idonsa
kwal
kwal ya amsa mata,"Amin har karfe goma suna
gidan,sam Abdullahi ya tsani a tafi saboda ya
sami damar mu'amala da fatima da kare mata
kallo,bai kum ataba sanin tana da fara'a
kamar
haka ba. Muryarta sassanya mai dadin
sauraro,kalamanta a takaice masu azanci da
sanyaya rai,ga ta da karrama mutum ta hanyar
ambaton sunansa a duk maganar da zata fada
masa,shi kansa ba ta sanya shi akwandon shara
ba, idan magana ta biyo ta kansa ta kan ce,
"Abdull kaza. Karfe goma da kwata suna dakin
kannensa. Mata ana hira ta dube shi ta ce.
"Abdul mu tafi dare ya yi". Ba shi da wani zabi
duk da ransa bai so hakan ba, suka yi sallama da
kowa wani jikan gidan Adamu ya rako su da
kayan fatima har mota. Sun fara tafiya kun
kun
kun kamar dazu sai dai yanzu babu D.banj
tunda
ta yi hani da wannan. Da kanta ta kawar da
shirun da ke tsakaninsu ta hanyar wani raddi
da
ta ke fatan ranar samuwarsa. "Abdul kulliyar
jama'ar gidanku suna da kirki da son
farantawa
dan Adam ba kamar kai ba". Ya dauke wuta
kamar bai ji ba,sai can ya muskuta ba tare da
ya
dubeta ba,ya ce. "Yarinyar ni na rufe shafin
rigima da ke" Kamar ba zata tanka ba,sai kuma
ta tanka din. "Haka ne,gara mu yi rabuwar
arziki,mu sami kafar zumunci ko?" Tana
kallonsa
kai tsaye shi kuma nasa kallon a titi,bai tanka
ba
amma kuncinsa cike da murmushi. Ya dinga
tukin
cikin matukar kasala kamar masu tafiya a
keken
da babu birki,can ya kira sunanta a kasalce.ta yi
dif, takaici na isarta. "Fadima wallahi ba ni da
lafiya". Ya fito fili ya fada mata.ta kuma
share
shi, sai ya kuma shagwabewa. "Da gaske nake
fadimatu,kirjina bugawa yake, taba ki ji".
Cikin
tsuke ido ta fuskance shi.42) Abdul ka mayar da ahankalinka,babu irin
wannan a tsakaninmu sai ka bari mu isa gida
akwai wadanda zasu iya daukar alhakinsa. Bai
sami damar bata amsa ba wayarta ta shiga ruri
sai ya bata damar ta amsa alhalin dukkan
hankalinsa na kanta don yana tsammanin kiran
alhaji ne. Ilai kuwa ita ma ta amsa ba tare da
wata shakka ba,sukayi gaisuwa irinta
masoya,sannan yace mata ina kika shigane ina
ta
faman kiran wayarki baki daga ba,ta danja
fasali
sannan ta amsa ina falo ne wayar na cikin daki
yace mata.wlh har nashiga damuwa fati,nayi
tsammanin ko kun hada kai da abdul. Kinsan
kuwa dazu gani ga abdullahi agidan mai
yashareni?sai yayi kamar bai ganni ba alhalin
mun hada ido.fatima ko kin bashi dama ne ya
shigo dakinki har yasan wacece ke?Da sauri ta
dubi abdul, wanda take da yakinin zai iy jin
abin
da alhajin ke fada,ta daura maballin rage sauti
sannan ta canja wayar zuwa kunneta na dama
murya na rawa tace..kai haba kila dai bai ganka
bane kawai amma har yau bai saba dangantakar
da ke tsakannmu ba,nakanyi kwana biyu ma ban
sa shi a ido ba.alhajin ya saki ajiyar zuciya yace
to allah yasa ya dore nidai na karaya ko jiya
doctor ya tabbatar min B.P dina ya kai 160,cikin
tausayawa matuka tace Ayya alhaji ka kwantar
da
hankalinka, inshaa allah nan da kwana biyu
mun
fara lissafin rayuwa tare,ya kyalkyale da
dariya
yace inshaa allah,bari ba barki ki huta sai da
safe, Ta sauke waya anutse kuma tayi
fuska,harsukaje gida babu wanda ya tanka
wani,fuskar abdul.ta murde kamr wanda aka
aikowa sakon mutuwa ,sai huci kawai
yake,hakan
bai hanashi rakata dakinta da kyaututtukan da
ta
samo ba,sai dai baice mata kala ba yafice inda
tabi shi da kallo tana mamakin wannan
sauyawar
tasa. Dasafe ma karfe takwas haka ya shigo
mata babu walwala da ledarsa mai hawaye zaki
ahannu,ta bude masa kofa bai ko dubi inda
take
ba ya wuce ya jona ruwa akettle ya fasa kwai
guda uku yasoya ya rufe afaranti.yajuye ruwan
zafi afulas ya jero mata adogon faranti cup da
sauran kayantea,ya dora bread sannan ya ajye
kan center table.muryarsa a cushe
yace,breakfast
is ready, baijira cewarta ba ya kada kai ya
fice,tabi shi da kallo cikin tunanuwa iri iri,gaba
daya zuciyarta ta jagule,me yayi zafi haka?
Haka
ta wuni zuciyar babu dadi gashi ranar ko kare
bai
shigo mata ba bare ya dauke mata kewa,wannan
damuwar ta sabbaba mata dokin ganin jibi
domin
ta sami barin wannan gidan da maabotansa suke
ajuye,daga masiffafu sarakan gori sai
shugabansu
tufkar hagu .
Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
zuciya d kwanji
43) Sai dai duk da haka aranta bata so suyi
rabuwar tsiya da abdul ba.ta fara sabo da
shi,kuma ta yarda da batun mahaifinsa yana
da
kirki da tausayi ga diya mace da son ya
kyuatata
mata.To ita ma zata dorar da wannan duk da
rashin matsayinta agurinsa bai kware mata baya
ba.tana mamakin yadda damuwar yau ta ke
saurin sanyata kuka,Dazarar ta zurfafa
atunani
kawai sai taji hawaye. Da laasar sakaliya tana
kwance dakin baccinta tana kanana hawaye,ta
jiyo abin da aka saba,wato hindatu da
bakuwarta
suna gulmarta.tunda tazo gidan hindatu bata
taba
tararta gaba da gaba da wata magana mai daci
ba amma sau uku kenan tana zuwa mata jikin
windo da baki suna gulmarta,yau ma ga
gulmar.bakuwar tace kwatakwata wannan
amaryar taki ba a ganinta ne?hindatu ta mele
baki tace.ina zaki ganta?bata fitowa sai ta rako
baki jiya dai ya kwasheta sunje gadon kaya,ina
jin iyayenta suka kai ma malam kara,akayi
kiransu akayi musu fada,ko kaca kaca malam
yayi masa oho!Don yau a wani hagunce ya tashi
daga magana ya hau surfa min balai wai na
barshi yaji da abin dake gabansa,cike da son jin
tsegumin bakuwar tace.Oh me yayi zafi haka?
hindatu na daria ta amsa.hum in kika ji labarin
sai mamaki ya dameki,kinga matar ne?
Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
44) "Hum in kika ji labarin sai mamaki ya
dame k-n kinga matar ne? Wanke hannu ka
taba
wallahi kyakkywar mace iyakar saninki. Amma
Abu Turab shakulatin bangaro yake da ita,kallo
ba ta ishe shi ba, ko girki fa ba ta yi kullum
safiya ranar girkin ta.wajena yake cin
abinci,da
dare kuma shi yasan inda yake ci. Ita kuma ya
fita waje ya siyo mata saboda tsabar daurewa
karya gindi...." Bakuwar ta ce. "Allah mai
iko,yaya ran sadiya?" 'E kinga yadda ta
yakune?
Nasan kuma lamarin matar nan ke ramar da
ita.ga kudin ga kyau,ga kuma tsabar mulki. Ga
sadiya da bakin kishi,yau da safe ai a kanta ya
sauke fushin bayan ni na kama kaina. Tana fa
ganinsa a birkicen nan wai ta hau
tuhumarsa,wai
jiya ya fita da amarayarsa bai fada mana ba.
Kin
san Abu Turab da bakar magana,kawai sai ya
nemi guri ya zauna rai a bace ya yanko mai zafi
ya ce. "To kinga sadiya tun da ke kika auro ni
kike kuma daukar nauyina zo ki kafa min
padlock
kar na dinga fita da ita,sai na nemi izininki,ai
duk
ke kike ciyar da mu...." Kin santa ita ma da
dacin
rai,sai kawai ta ara ta yafa ta ce. 'Kamar
gaske,idan kana sonta me yasa ka mayar da ita
'yar gadin dakinka tana fada kuka wuni da
kwana....' Babu shiri fatima ta fice daga dakin
baccinta zuwa falo don ta gaji da wadannan
bakaken maganganun kar ta ji abin da zai balla
mata zucita,ashe kallon da suke mata
wulakancinsa har ya kai haka? Cikin wannan
radadin zuciyar ta yi wanka ta kasance cikin
pink
din kananan kaya,siket din iyakar gwiwa da riga
matsattsiya ko cibiya ba ta rufe mata ba. Ta
kishingida a kujeru tana kallo duk da
hankalinta
ba ya tare da abin da ta ke kallo. Biyar da kwata
ta ji dirin motar Abdullahi,ta dubi agogo
gabanta
na faduwa saboda tunanin yadda suka kwashe
yau da safe. Sam ba ta yi tsammanin shigowarsa
a wannan lokacin ba, don haka ba ta damu da
kayan da ke jikinta ba, amma kwatsam sai ga
shi
kuma ya sami majigin kallo duk da fuskarsa
babu
walwala. Ta kawar da kai tana faman jan siket
sannan ta ja riga,a karshe ta dube shi a
turbune
ta ce. "Haba malam,mene ne haka babu daukar
dama?" Ya dage gira ya ce. "A'a,kaddara ma
barance na zo". Sai ya share wannan batun,ya
nemi guri ya zauna karo na farko ke nan da ya
zauna a dakin tunda ta zo gidan,komai ya kawo
shi iyakarsa tsaiwa. Muryar a saukake ya ce. "Ba
ni da kudi sosai ne zan shiga kicin,me kike so na
girki miki?" Har zata gwale shi,sai ta tuno dan
bikin da Hindatu ta gama yi mata dazu,kawai
sai
ta kawar dakai,ta ce. "Ni 'yar cirani ko me ka ba
ni ai godiya zan yi in karba,yau da gobe ne
kawai,
jibi ya zama tarihi". Ya hadiye duk takaicin da
maganarta ta sabbaba masa,ya ce. "To za ki ci
dan wake? Sai ki hada da fruit salad". Duk da
ba
ta san ya ya dan waken yake ba sai ta kada kai
ta ce. "Zan ci" Ya ce,"to bari na dan huta". Ya
kara share guri ya zauan,idonsa akan talabijin
amma a saukake ita yake more kallo.ta gama
sakwarkwata zuciyarsa da yi masa fami a
soyayyarsa wadda yake ji a ransa ba ta shafi
kyau ko iya wankanta ba. Cikin dabara ta silale
daki,sai ga ta ta fito sanye da after dress suka
dubi idanunwan juna kai tsaye ya tura mata
wani
sako,ta karba amma sai ta zubar har da tare
gira,sai ya fito kai tsaye ya fada mata. "Da
dazun
da yanzu ba ki canja a idona ba". Ta kara bata
rai,ta ce. "Wasa ka ke,amma ni dai nasan na
canja tunda ga shi har bakinka ya bude...."
Tana
rufe baki,ya magantu. "Zan yi tambaya. Ganin
da
na yi miki babu wannan after dress da matsala
ko
babu? Wai idan muka kalli hakan ta fuskar
addini
da kuma al'adar bahaushe". Ta jima tana jan
fasali sannan ta ce. "Ni ba diyar malamai ba
ce,kuma ban karanta Hausa da al'adu ba" Ya
kada kai,ya ce. "Ni na ji a raina a duk
bangarorin
biyu,wato addinin da al'adarta babu matsala.
Abin da kuma azancina ya kasa fassarawa shi
ne,ban ji kin canja idona da zuciyata ba, a
ganin
da na yi miki dazu da na yanzu da ma duk
wanda
na sha yi miki a baya tun kafin aurenmu,ko ke
za
ki iya fassarawa?" Kai tsaye ta amsa masa
Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji .45) "Manta matsayin da ka ba
ni kawai ka yi,
wanda shi ne dalilin da ya sa ba na canjawa a
idonka,ko ka manta ne?" Ya yi saurin taren
numfashinta. "Ban manta ba... Amma ina
cigiyar
wanda ya taba ba wa wani ko wata irin matsayin
da na ba ki don ya wayar min da kai akan abin
da irin wannan matsayin ke nufi" Ta yi
sugudi,sannan ta ce. "Yanzu ka koma
zaurance,idan zaka iya fassara min sai lurarmu
ta dore,idan ba zaka iya ba mu diga aya ka
shiga
kicin dinka". Ya yi murmushi har kumatunsa
suka
lotsa,ya ce. "Na fada miki duk abin da kika ki a
bakina da fassararsu suka fito,amma wannan
bari
in gwada ko zan iya fahimtar da ke. Da ace
maganar soyayya zata iya giftawa tsakaninmu,
ina karrama matsayinki da karramawar da ta
zarce wadda masoya kan ba wa juna. Ga shi
kuma ban tava wani amini ba bare na hasaso
matsayin da