Showing 15001 words to 18000 words out of 36237 words

Chapter 6 - ZUCIYA DA KWANJI 1 NA MAIMUNA IDRIS BELI.pdf

ka da mutunci wallahi. Na gode". Ya
jima yana kallon wayarsa,kalamanta na yawo a
kwanyarsa. Ya dan kafa ido alamun son raba
hankali fiye da gida biyu,har lokacin da
jarumtarsa ta motsa ta danne komai ta ba shi

damar tabe baki ya ci gana da harkokinsaa
Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
.26) Fatima ta wuni da wannan takaicin da
zarar babu idon mutane sai dai ta yi ta faman
hawaye. Ta rasa inda zata tsoma ranta ta ji
sanyi bare hanyar da zata bi ta fanshe wannan
cin mutumcin da Abdullahi ya yi mata. Wannan
bai hanata da $omi zuwansa ba, aka yi ta
hidimarsa kamar wancan lokacin ko m$a fiye
tunda yanzu ya zma a halin gida. Ita ce dai ba
ta
wani shiri game da zuwan nasa,har sai da
jama'ar gidan suka kwabeta bisa rashin wanka
da canja tsari, sai ita da kanta ta ga beken
kanta.To mutumin da ka yi kwalliya ma ya. Ce ba
ka da kyau ina ga ba kayi ba? Kawai sai ta
biyewa su safiya,ta yi gayu na garari ta saka
kaya wadanda suka lafe a jikinta suka kuma
dace
da fatarta,ta yi fes kamar mai shirin gasar
sauraniyar kyau.A yau babu ma rigakafin wato
laffaya,sai yalolon mayafi ta yafa irin rufin
'yammatan zamani. Karfe biya dai dai ya

rangada
mata waya tana ganin sunansa sai da gabanta
ya
fadi, haka kawai abdullahi ya fara tsoratata,ga
kuma su safiya a wajen bare ta dizga shi. Ta
daga wayan da walwala a fuskarta,amma ta
kasa
tanka shi, shi ma a takaice ya ce. "Na karaso".
Ta dinga zabga murmushin dole,a$$a ta kasa
tankawa, sai mata sauke wayar tana ajiyar
zuciya. Safiya da shukura suka tafa,shukura ta
ce, "Tabdijam, wanna gayen ya tafi da
imaninki."
Duk suka fice suka barta tana binsu da kallo
wasu kwalla suka cika mata ido,in banda dole
mai Sanyawa a kwana a ido,ai babu dalilin da
zai
kai ta inda wancan dan rainin hankalinm zai ga
inuwarta. Har wasu mintuna tana zaune sai da
ya
turo mata khalid da kira sannan ta dauro amsa
kira. Tan shiga falon suka doramata ido su
duka,musammam Abdullahi wanda yake mata
kallo daga sama har kas,idanuwansa na fitar da
wasu sakwani wanda zai sa ka tsammaci

tsantsar soyayyar amaryarsa a cikinsu bai tsaya
ga tura sakon kawai ba sai ga shi tsaye nuna
alamun girmamawa da marhabin. Su salma sun
baz amata ido sai ta rasa irin acting sin da zata
karbe shi,don haka ta ji kafarta na
hardewa,shi
kuma Abdullahi ya sami distination da nasa
acting din, domin har ya isa gabanta bai kuma
bata lokaci ba ya ware hanununta ya rungume
ta.
Dakin ya fara wantsalata,kirjinta yana
harbawa ta
fara kokarin kwacewa lokacin da ta fara jin
shewar su safina yahanata da jarumtarsa ta
namijim da ya lakanci soyayya.ya dago kanta
ya
sumbaci goshinta.sannun a hankali ya bi
kunnenta yana rada mata wasu manyan
kalamomi masu huda zuciyar masoyi,don haka
kwakwalwarta ta kasa fassara mata su. Face
wasu 'yab kwayoyi da zuciyarta ke fada mata
kamar sun shafeta
1 · Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji

27) Wadannan sakanin da za su iya samar da
mintoci sun yi min kama sa mafarki,sun dan
kwatanta min ana samun aljanna a duniya....
Fadima numfashinki na da sanyi da kamshin
shaka kamar yadda jikinki ke tashin kamshi.....
Dole ki yi tasiri mai karfi a rayuwar masoyi ko da
bai shirya hakan ba...." Ta zame tamkar
mutum-
mutumi,tare da shi ya ja ta zuwa kujera ya
zaunar da ita,sannan zauna ya zauna a
hannun
kujerar,ya dafa kafadarta ya kokarin su hada
ido,ya ce. "Ki share su safina,don sun ga kina
jin
kunya suke miki wannan dan bikin". Ya juya
flga
su safina yana dariya. "Ku je abinku na gode
da
karramawa". Ba su bar yi musu shegantaka ba
suka fice, A sakanni goma dakin ya bayar da
dif!
Kafin kowa ya yunkura. Abdullahi ya mike
zumbur
ya bayar da baya cikin kankanin lokaci ya canja
fuska,kamar fuskarsa ta ranar haduwa, wadda

ta
dace da munanan kalamansa a waya. Hakan ne
yab hadar wa fatima takaici da kaicon
mu'amalar
da ya yi mata a yanzu,a matsayinsa na baranta
da matsayinta a gurinsa na wadda ba ta isa
hada
kafada da sauran mata ba, kawai sai ta sami
kanta da kuka kashirban. Ta dinga kuka kamar
ranta zai fita yana tsaye rungume da
hanaye,ya
juya mata baya kamar kukan nata ba ya
damunsa,har dai ya juyo gare ta fuskarsa da
alamu tausayawa irin na tsananin namiji mai
imani da mace mai rauni. Ya durkusa a gabanta
tare da dago fudkarta muryarsa a raunane ya
ce.
"Abin da na yi ya fice yadda yakamata plan
dinmu ya ajiye ko? Ki yi hakuri ban yi don na
bata ranki ba. Ba kuma wani sabon abu ba ne a
cikin dabi'una,dama haka nake don haka ban
ga
wata hanyar da ba ta kai wannan ba wadda zata
nuna farin cikina da kasancewarki amaryata ko
da ta a gaibu ne. Ina jin kin ji ciwon haka ne

domin kiyayyata da ke cikin zuciyarki.... Ama
kuma...." Ta kwace kanta tana share
hawayenta,kuma ta tsayar da kukan sai dai
zuciyarta ta kara rinewa da takaici. A kufulce
ta
ce masa. "Takaici na ya samu ne ta hanyar ba ni
matsayin macen da zata iya shiga gonar
soyayyarka ne, ko da kuwa a plan dinmu ne....
Ko ka manta ne? Yakamata ka bi wata hanya
wadda zata ba ka damar ci gaba da jadadda
abin
da ka fada idan dai ba rikidewa na yi daga
halittar dutse na koma mace a idonka ba......"
Muryarsa a tausashe ya tare ta da cewa."Kin
kuntata fahimtarki ga magana ta fadima, idan
babu soyayyar da zata samar da sha'awa a
tsakaninmu me yasa ba zamu samar da wadda
zata samar da zaman lafiya a tsakani mu ba?
Dube ni a wani dan uwanki,idan ma ba zaki iya
hakan ba, yi min kallon baranki amma ki samar
da kauna ta tsakanin yaro da uwargijiyarsa".
Ta
fara sassarfar numfashi bayan kishiyoyin
abubuwa biyu sun hadar mata lokaci guda
takaicin da maganarsa ta samar mata da tsoron

janyewar biyayyar Abdullahi da ta fara samu
idan
" Na ji,matsa ka ba ni waje". Ya mike yana
dariya,ya ce. "Shi ke nan zo ki ba ni abinci kar
su
ce ban ci ba". Ta dago ta zabga masa harara,ta
ce, "Share guri ka zauna ba zan kara zuba maka
ba,ko kudin ka sanya ka siyo ni?" Ya amsa cikin
dakewa. A'a,ni kika sa kudi kika siyo,kuma
kanki
za ki tsinka,don zasu yi tsammanin mun shagala
da wasu al'amura ne shi yasa ba mu tuna abinci
ba". Da ta dan nutsu sai ta ga kamshin gaskiya
a
maganarsa
1 · Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
I no see 28.... bear wit me....
1 · Like · React · Report · May 14, 2015
Sumaiya Ibrahim Al-hussain
wldn
1 · Like · React · Report · May 14, 2015
Zainab Abdulkadir Sani
Thnx
Like · React · Report · May 14, 2015

Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
29) Tun daga wannan rana Abdullahi
bai kara komawa wajen fatima ba,bai kuma kara
yi mata waya ba, abin mamaki sai hakan ya
dinga yi mata ciwo. Ba don takaicin rashin
ganinsa ko kuma fassarar da jama'ar gidan
zasu
yi mata na rashin kulawarsa a gare ta ba, sai
don
hakan da ya yi shaida ce na bai dauke ta a
bakin
komai ba. Kusan Alh ne ya canje shi,domin da
shi
ta ke raba dare suna hira a waya tunda babu
hali
da rana,sannan ya bude mata bakin aljihunsa
da
kyau, wato ya tura mata makudan kudade
asusunta wanda zata yi hidiman bikin da su.ya
so ma ya tura mata kudin Abdullahi na sallama
ta ki yarda da uzurin cewa, idan kawu ya
ankara
kudaden asusunta sun fice kima zai bincike ta,
tunda bai barta sakaka ba. A ranar asabar

ma'aikata suka je suka kawata mata
dakunanta a
gidan Abdullahi, makeken falo mai dakunan
bacci
biyu kowanne da bandaki,a falon ma akwai.ga
kicin hade da sito da kuma baranda. Abdullahi
mutum ne mai kaunar kawata muhalli don haka
girman gidan sa da kawar da gidan ya kunsa bai
yi kama da nasa ba, musamman idan aka dubi
tilon motar da yake hawa alhalin harabar gidan
zata ci motoci hudu.haka cikin gidan ma yana
da
yalwa bayan a fitar da sashe hudu irin na
fatima
sak! Sadiya,Hindatu,shi kuma yake zaune a
cikin
daya.akwai wasu empty dakunan saboda baki ko
wasu bukata na daban,kai har da karamin wurin
shan iska mai kama da lambu.akwai rumfa gefe
da fararen kujeru, can kuma ga bishiyu har da
fulawoyi. Wannan ta dan kara daga darajar
Abdullahi a idon dangin fatima,duk da cewa sai
a
saka gidan Abdullahi bakwai a cikin na alhaji
wanda fatima ta baro,amma ba za'a ce fatima

ta
kastanta ba.ko kuma tsammanin mamallakin
gidan zaiyi sana uren kisan wuta. To haka ake
kashe dala wajen kawata mata nata dakunan
tamkar ta zo da niyyar zama. Ranar lahadi aka
wuni ana shagalin biki da yammaci aka kai
amarya gidanta bayan an kaita gidan iyayen
Abdullahi har gaban malam ya yi ta sheka mata
albarka,kafin ya koma kwarzanta mata angonta
nata da irin kyawawan halayensa. Bayan sallar
magariba kadan kowa ya watse,aka bar fatima
da
halinta, niyyarta da kuma sake saken wadda
zata
fissheta. Gidan dif! Kamar babu wani mai rai sai
ita sai gaba daya kadaici ya mamaye ta don ta
saba gidansu gidan mutane ya mamaye ta, don
ta saba gidansu gidan mutane ba ma ka jin
kunne. Haka gidan Alh ma babu laifi,amma
wannan kamar kufai! Ba ta jima tana kirga
mintunan da suka samar da awa daya da 'yan
kai
ba ta ji dirin motar Abdullahi wato bayan sallar
isha kadan,kawai sai gabanta ya yi wani
mumunan faduwa. Gaba daya ta rikice,sai barin

jiki ta ke ta tashi ta koma falo,ta kara lullube
jikinta da laffayar da ta ke nade,ta fara
duban
kofa tana tunanin darenta na farko a gidan
alh
wanda idan dai irinsa ake wa kowanne irin
ango,to abdullahi ba shi kadai zai shigo gidansa
ba a yau. Ta dan fara jiyomaganganu sama
sama
wanda ta tsinci muryar Abdullahi sai kuma wasu
muryoyi biyu wanda ba su yi kama da na abokan
Abdullahi ba, domin kamarsu na karbar umarni
daga gare shi ne. Ama abin mamaki abdullahi
bai
nemi dakinta ba har sha dayan dare ta
motsa,wannan ya sa ta dan saki ranta,sai dai
ta
kasa ko motsin,wannan ya sa ta dan saki
ranta,sai dai ta kasa ko motsin kirki, iyakacinta
dai falon kamar wadda ta zo ci rani. Sha daya
da
rabi sai ga alh ya kirata a waya ta daga jikinta
na
bari ko sallamarta alh bai amsa ba.ya ce. Fatima
ya nemi shigowa wajenki?" Da sauri ta girgiza

kai
kamar yana ganinta, tukunna ta ce, "Ko
duriyarsa
ma ban ji ba". Alh ya sauke wata katuwar ajiyar
zuciya
1 · Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
30) , ya ce. "Haba na shiga rudani,tun karfe
takwas nake kiran mutumin nan yana wata
kiran
nawa a kwandon shara,ina shakkar idan bai yi
adding din lambobina to reject list ba, tabbas!"
Cikin fatima ya dauki wani kugi,ta ce. "Ko Alh?
Ni
kuma sai nake shakkar zai hak*,kasan rabon da
shi tun washegarin daurin auren? Kuma bai taba
kiran wayata ba". A matukar gajiya Alh ya ce.
"Toh,Allah ya saya dore,ki sa wa dakinki key
kinji? Kar ki yarda ki dinga barin kofarki
bude".
Ta ce da shi cikin bin umarni. "To bari na je na
rude". Ta kama key zata murza ke nan
Abdullahi
ya murda handle ya turo kofar. Da gabanta ya

yanke ya fadi kawai sai ta yi mutuwar tsaye
wajen. Bai ko dube ta ba ya wuce ta zuwa
tsakiyar falon yana kare masa kallo kamar
wanda
ya zo daga kauye. Ta silalo a mugun kasalce ta
zube kan kujera bakinta fal addu'ar neman
tsari.
Ya juyo ya dube a fuskarsa babu walwala ya ce.
"Ina ta tunanin ki zo da kaza da kayan sayen
baki sai na ji shiru,shi ne na biyo baya"m Ta
tilastawa kanta karfin hali lokacin da ta ke
kallonsa a sakrce,ta ce. "Dama akwai wannan
cikin sharudanmu?" Ya soke hannu a aljihu ya
fara cije lebe, Sannan ya zaro hannu daya
yana
juyawa ya ce. "Ina tsammanin tana daga cikin
sharuda ne masu aiki irin na magani a jikin
cuta,kin san ba ko yaushe aikinsu ke tasowa
ba,ko kin manta? Ba a zube sharadin zan zo
tadi
ki ba ni kudin zance ba kike ba ni. Na rike raina
hakan yana da alfanu kamar dai yau,idan kika
sai
bakina sannan ki ka kawo min kaza kamar ko
wanne mai KWANJI idan ya yi aure". Ta rasa

abin
da zata ce masa saboda fargaba da takaici,sai
kallonsa kawai ta ke. Tana kifta idanuwa,har
sai
da ta sami basirar da zata iya a fada da tasa
basirar. "Idan shi ke nan abin da ya kawo ka sai
ka fice na daina ganin inuwarka,ko kai zaka
biya
ba ni ba. Ba ni da bukatar bakin naka bare ni na
yi asarar kudina... Kaza kuma ka manta illarta
a
tare. Da kai ne da kake nemanta?.... Mts! Mai
tsaurin ido kawai,ka fice ka ba ni guri idan ba
rainin da ka saba ka kawo min ba". Kafin ya
amsa kiran Alh ya shigo wayarta cikin gadara ta
amsa wayar. "Ina fatan kin rufe kofar?" Inji
Alh.
Ta dubi abdullahi wanda ya zuba mata ido a
tsorace,sannan ta dubi kofar bakinta na rawa
ta
ce "Eh, na rufe" "Ya ce mata murya a kwance.
"To sai da safe". Tana sauke wayar Abdullahi ya
dube ta cikin ido ya ce. "Me yasa kika yi masa
karya?" Ta kawar da kai ta ce. "Ai wani lokacin
halal ce...." Ya yi saurin tarar numfashinta, ya

ce.
"Kin ga ni kuwa ban. Karbar halaaccin karya sai
ta yi matukar kure min,ko hakan nema sai na
kan
yi ta a bai bai" Ta kara bata rai,ta ce. "Ka yi
abin
gwaninta,idan ka yi abin da ya kawo ka sai ka
fice zan kwanta". Ya dan ja fasali sannan ya
dora
cikin nata batun. Akwai saura da yawa". Ya yi
fuska sosai ya dubi tsakiyar idonta ya ce.
1 · Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
31) "Kar ki kara yi min tsaki balle ki fadi wata
kalma mai kama da zagi a kunnena,ko ba ki da
tarbiyya ne? Ban girme ki ba? Ya kamata ki ce
min na yi miki tsaurin ido? Ko kuma ki fada min
idan kimar kudi ta zarce ta zarce ta girma da
mutumci....." Ya dan dakata ya shaki iska
kadan
sannan ya dora cikin ci da zuci. " Ba na sarayar
da girmana da mutumcina akan kudi,idan kina
tunanin shi ne tazarar da ke tsaninmu har kika
fi

ni tsawo. To ki ajiye wannan tunanin zai fi miki
kyau". Ya ba ta damar magana,amma ta kasa
ta
rasa ma abin da ya cukwaikwiyo
zuciyarta,mamaki? Takaici? Ko kuma
sallamawa?
Sai fitar da numfashi da kyar take yi. " Sai mu
yi
bakwana". Ya katse lissfina,sai ta saka masa
ido
kawai. Ya yi taku kamar uku da hannu. "Duk
ranar girkinki zan shigo kamar wannan lokacin
in
miki bakwana,ranar da sauran ke da girki zan
shigo miki da maraice,sannan duk safiya zan
shigo mu gaisa,sai maganat abinci kowacce na
girkinta daban ne,idan ina dakinta ta hada da
ni,
ke me kika gani a ranar naki girkin?" Ta
tattare
duk masifat da ke makogoronta akan kalmar da
zata fitar. "Ba na bukatar in dora wata
tukunya a
gidan nan, idan na ci 'yan kwalam ma sun ishe
ni

maneji zuwa sati biyun". Fuskarsa ba ta sauya
ba, ya tambaye ta. " Kin zo da na sati biyun da
zaki yi?" "Ina ruwanka?" Ya kada kai, ya ce. "
Babu,sai dai akwai sharadi...." Ta yi sauri
dakatar da shi da hannu,sannan ita ma ta mike
ya ga tsawonta. "Ba ka da wani sharadi da zaka
kafa min shi a yanzu,wanda ba ka kullo shi tun
ranar da muka shirya ajandarmu ba, saboda
haka
sharadinka ko wanne iri ne ba shi da muhalli a
sha'anina". Ya dinga kare mata kallo sama da
kasa, sannan ya kada kai,karon farko tun
shigowarsa murmushi ya bayyana a kuncinsa,ya
janyo cofee table ya zauan. Ya zamana ita ce a
tsayen,bai dauke ido daga kanta ba ya amsa
mata. " Bayan waccan ajandar ce aka kulla min
damar jagoranci a cikin sha'aninki da son ranki
ko babu.... To wai me kike wa tsoro? Ki jira ki ji
sharadin nawa mana don me za ki hau yi min
wannan masifar?" Tsaki taso ta yi,amma ga
mamakinta sai ta ji zuciyarta na shakkar ta yi
masa tsaki,dole ta buge da kada harshe,sannan
ta dubi wani wajen daban. Ya kara fadada
murmushinsa yana kara nazarinta,ya ce. "
Sharadin nawa ba fa wani mai tsauri ba ne,

dama
fada miki zan yi. Nan gidan babu matar da ta ki
fita sai da izinina,ma'ana idan kina fita a
gidan
Alh ba tare da neman izini ba a nan gidan lallai
ne sai da yardata,don haka kar ki sake in ga
karfarki a waje ba tare da yardata ba" Bai bata
damar magana ba ya kuma dora wani batun
bayan ya mike ya nufi kofa. "A karshe in
shawartarki da karanta waya da Alh, sannan ki
san irin maganganun da zaki yi da shi, saboda
gudun bacin rana wani cikin gidan nan yasan
halin da muke ciki,sannan idan akwai hali ki
dan
boyewa duniya rashin kaunar da kike min,kin
gane ko? Taso ki rufe kofar". Ba tare da ya jira
cewarta v ba ya fice daga falon,tana binsa
galala
da kallo cikin tsabar rudu. Ta rasa makamar da
zata rika don fara nazari akan wannan ba
izgilen
mutumin wanda ko shakka babu ya riga ya gama
damarta,ita ma kuma da alama ta fara sallama
masa tunda ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login