Showing 6001 words to 9000 words out of 36237 words
Chapter 3 - ZUCIYA DA KWANJI 1 NA MAIMUNA IDRIS BELI.pdf
bidi'a ne,kuma a matsayin
saki daya yake. Sai kawai ta bayar da kai bori ya
hau,ta kuma iya jure tunkarar kawu da
maganar,Allah ya sa kawu ba mai karamin sani
ba ne, sai ya dubeta da kyau cikin nazarin ta
sosai, sannan ya ce. "To ni ban gamsu ba,ba
kuma na karyata fatawar da ya kawo ba ne. Sam!
Ni hankalina ya fi kwanciya ga wadda ta haramta
aurenku har sai kin auri wani namijin kin tare da
shi. Wadda wannan fatawar jamhurun malamai
suka tafi akai kar ki kara kawo min irin wannan
maganar,ban son rudu. Dole ta karkade zani ta
mike cikin hawaye. Daga nan ne kuma cira kafa
ita da Alh ta bin hanyar duk suka sa zata mayar
musu da juna,kawu na dago logarsu saboda farin
sanin da ya yiwa fatima da irin mijin da ayke
zaton zata zabawa kanta. Sau hudu tana kawo
masa samari zata aura,idan kawu ya saka su a
kwana da tambayoyi sai ya dago su. Don haka
ya tattara dukkan lurarsa akan fatima,ya alkwarta
wa ransa sai iyakar inda karfinsa ya kare..Zuciya D Kwanji
13) Abdullahi ya hadu da Alh ne a
wani tsadadden asibiti lokacin da ya je dubo wani
abokinsa da aka yiwa aikin kaba,shi kuma Alh ya
je bisa larurarsa ta hawan jini,wadda ta matsa
masa yanzu. Tun da Alh ya ga Abdullahi ya dora
dukkan burinsa a kansa,don ya tabbatar in dai
Abdullahi ne kawu ba zai taba dago yawarsu ba
tunda bai rasa komai da ake bukata kafin a ba
wa mutum aure ba. Ya dinga ribatar Abdullahi
har ya samu suka kebe,sannan ya koro masa
bayani. "Dan halak ke nan, shekaran jiyan nan ka
fado min a rai,dama cikin satin nan nake son na
neme ka". Cikin fuskar rashin fahimta Abdullahi
ya ce," Allah sarki,ina fatan kalau?" Fuskar Alh na
bayyana jimami ya rangwada kai ya ce. "To
lafiyar mahaukaci ba,wani aikin lada da ceton rai
nake son baka,don a duniya ba ni da mai yi min
sai kai". Kallonsa kawai Abdullahi yake cikin
rashin fahimta,har sai da ya dure sanan ya kuma
dorawa. "Allah ne mai saka soyayya a zukatan
bayinsa Abdul,ya jarrabe ni da son mace daya a
duniya,wato matata. Wani tsautsayi yasa na yi
mata saki uku. To yanzu duniyar ta yi min
kunci,na gane ba zan iya rayuwa ba tare da ita
ba..... Shi ne nake rokon ka tainaka ka halarta
min ita". Kallon Alh kawai Abdullahi yake yana
sauraron wannan rainin hankali da na wayo. Jima
kafin ya shawo kan fushin zuciyarsa sannan ya yi
magana mai ma'ana. "Me yasa sai ni zan yi
maka wannan aikin?" Yana rufe baki Alh ya
amsa. " Saboda zumuncin da ke tsakaninmu,
nasan ba zaka so akan wannan lafiyata ta
salwanta ba.... Kawunta ne ya matsa matukar bai
ga mutum mai kamata irin ta gidanku ba,ba zai
bayar da aurenta ba, don ya sanya mana ido.....
Ni kuma wallahi ba zan iya hakura da ita ba....
Sai inda karfina ya kare wallahi...." Abdullahi ya
tare shi da cewa. "Ba ka ganin hakan zai zubar
da martabar gidanmu......?" Alh ma ya tare shi
kamar zai yi kuka. "Ka fansar Abdullahi,ka ceci
raina.wallahi na yi maka alkwarin biyanka
makudan kudade...... Zan daga darajarka a garin
nan sai ka shiga sahun attajirai". Abdullahi ya
jima yana tunani,sannan ya dube shi da kyau ya
ce. "Ka fa san halin mahaifa,babu yadda za'a yi
na kawo matar da ta girme min da zummar aure
bai nemi ba'asi ba. Na kuma san duk wahala dole
matarka ta girme ni". Cikin doki Alh ya ce. "Au ba
ka santa ba?" Kallonsa kawai abdullahi ya yi cike
da takaici. To ta wacce hanyar zai san matar
wani? Musamman alh kawai don yana abokin
wansa? Sai ya girgiza kai kawai,Alh ya ce.
"Shekarunta talatin da biyu,kuma da yake tana da
kyan jiki zaka zaci ba ta fi shekaru ashirin da
biyar ba".Zuciya d kwanji
.14) Abdullahi ya kara jan fasali sannan ya ce.
"Da yardarta a ciki?" Alh ya yi saurin gyada kai.
"Eh,idan ma ka amince sai na gabatar maka da
ita kafin ku fara magana". Kai tsaye Abdullahi ya
amsa. "Ti na amince,Allah ya tabbatar maka da
ita kafin ku fara magana". Kai tsaye Abdullahi ya
amsa. "To na amince,Allah ya tabbatar mana da
alhairi". Farin cikin Alh ya tsananta,kawai sai ya
rungume Abdullahi yana godiya. A nan suka
shirya haduwa da yammaci a gidan namun daji,a
haduwar tsu kuma suk jaddada kudirinsu,sannan
suka yi musanyar lambar waya tare da shirya a
washe garin ranar abdullahi zai fara zuwa tadi.
***************** **************** Washe gari da
yamma bayan sallar la'asar,fatima na kwance kan
kujera 3 sitter,a kasalce ta ke kwarai,kasal irin
wadda ke tasowa daga zuciya sakamakon bacin
rai da damuwa. Ta sanar da mutum gidan cewa,
tana da bako kowa murna yake yana dokin ganin
bakon cikin zakuwa,wanda ta tabbatar da biyu
suke yi... Kowa sai hidimar tarensa yake daga
kan masu aiki akan abincinsa,har jama'ar gidan
masu murna da doki. Wannan ya sa fargabarta ta
kara tsananta..... Tasan kawu sarai akwai dora
ido. Dazun da safe Abdullahi ya yi mata waya ya
ce, karfe uku zai zo,amma ga shi hudu da rabi
abu labarinsa,sai bacin ranta ya karu,ta kuma
kara jin tsanar abdullahi cikin ranta.Ta tsani
mutumin da ba ya daukarta da muhimmanci,ko
kuma ba ya girmamata. Ta lura da abdullahi
mugun dan tsaurin ido ne...... Ya iya dizga
mutane. To idan ma halinsa ne dizga mutane ai
tana jin ta fi karfin hakan,don ba ta rasa duk
wani abu da ke janye so da biyayya ba,ko ba
domin Allah ba. Tana da kyau,kuma tana da
kudi,sannan ta iya takunta. Da damuwar ta isheta
sai ta janyo waya ta hau facebuk domin debe
kewa,tsawon mintina goma,sai ga safiya kanwar
momi matar kawuta shigo da karadinta "Anti
wannan yayan namu zai tilasta ni kuma kwannan
gidan don ba zan wuce ba sai na ganshi,don Allah
ki yi masa waya ya karaso mu gaisa. Fatima ta
dago ta dube ta, sai ta rasa ansar da zata
bata,akan me zata yi masa waya,kuma ta ce
masa me? Sai kawai ta yi shagare tana kallonta
cikin zancen zuci,safiyya ta bude baki tana
kallonta ta ce. "Anty..... Wannan mutuwar ido
biyun fa? Duk yayan ne da wannan aikin?" Fatima
ta yi murmushin karfin halin da ya yi kama da na
shauki, sannan ta juya baya ba tare da ta tanka
ba, safiyya ta mike ta ita tana tuntsura mata
dariya. Sai shidda saura abdullahi ya iso,ya yi
kiran wayarta tana ta faman kallon wayar sai da
ta katse ya sake kira, sannan ta daga a kule,kum
ba ta tanka ba. Muryarsa a sake ya ce. "Fatima
na iso". Haushin gatsa sunanta da ya yi kai
tsayeya sa ta taso masa da bala'I. "To me zan yi
maka? Kane nawa karfe nawa ka ce min zaka
zo?" Ya yi sjiru,sannan ya nisa a zafafe ya ce. "Ki
yi hakuri,amma don Allah ki dinga yi min
uzuri,bana son masifa wallahi". Sai ta saki baki
cikin al'ajabi,ta ma rasa abin da zata ce
masa,koda yake ko tana da abin fadar bai ba ta
damar fadar ba, tunda ya kashe wayar.......
Wannan wanne irin dan zafin kai Alh ya hadata
da shi? Duk mazan da ya kawo mata a bayan
masu ladabi ne,amma wannan yana jin kansa shi
wata tsiyar ne.
Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
zuciya d kwanji
15) Ta fi mintina ashirin tana faman sacewa
tare da tunanin turbar da zata bi da wannan dan
hayaniya har ta kai ga zargin kanta.Ta gama
babu wani dalilin da zai sa ta dinga damuwa da
zafin kansa,ya karaci jaridarsa ya gama. Ta sa
baki ta yi kiran safiyya,sai gata a guje,tana zuwa
ta ce. "Ya zo ko Anti?" Ta yi murmushi,tukunana
ta ce. "Ya zo, sai ki shigo da shi,don na ga
alamar kin fi ni dokin ganinsa". Safiyya na
dariya,ta ce. "A'a bazan fi ki ba anti,ke da
zazzabi ya kusa tsegumi kawai ke dawainiya da
ni in ga dai dan talikin nan da ya rikita mana ke".
Fatima ta hadiye takaicinta,ta ce. "Nasan ba zan
ba mara danki kunya ba shigo da shi sai ki kare
masa kallo". Safiyya ta fice fatima na binta da
kallo cikin kunar rai,haka kawai ta ji sam ba ta
kaunar ganinsa. Tana jiyo jama'ar gidan na ta
kara-kaina a kansa.Da akwai alamun sun yaba,
can sai ga safiyya da sauran 'yanmatan gidan
sun shigo,suna mata kaudi. "A'a Anti kin yo
wawan kamun ya ya muka ganki haka? Don Allah
tashi ki canja tsari,don ya gane gidan ya tarar".
Ta yunkura ta tashi zaune ta rafta tagumi hannu
biyu tana sauraron cagwadar da suke mata. "Na
rantse Anti yanzu kika yi mijin da ya dace da ke,
ko babu kudi akwai kyau da iya taku......"
"Sannan ga fara'a da iya shirya zance kalma
bayan kalma...." Irin kalaman yabon Abdullahi da
suke ta jero mata ke nan, wadanda suke faranta
mata,sannan suka bakanta mata,karbuwar da ya
yi a gurinsu ne ya faranta mata.tana kuma jin
haushin yabon da suke masa don bai cancanci
yabon na ko dayua,sai dai babu damar ta
bayyana. Haka suka yi ta ribatarta sai da ta
canja shiga,ta yi kyau tamkar ranar walimar
aurenta. Ta same shi a falon momi durkushe a
gabanta,kamar zai kwanta mata saboda ladabi.
Momi na ganinta ta hau zolayarta. "Kin gaji da
jira kika biyo bayansa ko?" Ta yi murmushi
kasaita,ba ta tanka ba ta nemi kujera ta zauna
tana kallon ikon Allah. Momi ba ta jira cewarsa
ba,ta juya ga Abdullahi ta ce. "Ina fatan ka shirya
da kyau,wannan yarinyar shan kamshinta ya yi
yawa". Ya kara kan - kan da kai,muryarsa a
ladabce, ya ce. "Na sani momi,a taya mu da
addu'a". Cikin fara momi ta ce. "Idan Allah ya
so,kar ka ji na ce haka,fatima na da saukin kai ga
wanda ya iyawa dabi'arta da tarbiyyarta,ina
tsammatar muku zaman lafiya da saukin fahimtar
juna,domin dukkanku kun fito daga gidan tarbiya
da sanin ya kamata. "Mun gode". Kalmar da
Abdullahi yake ta maimaitawa ke nan,ya yin da
fatima ta yi shagare tana kallon momi zuciyarta
cike da tambayoyi.A ina momi tasan
Abdullahi,kuma dan gidan waye? "Don Allah ka
rike amana,ka ga marainiya ce, nasan kawunta
ma nasihar da zai yi maka ke nan. To kafin ka
ganshi ma ni na fara yi maka. Ka rike ta amana
don Allah ku zama masu hakuri hat ku fahimci
juna". Abin da momi ke ta jaddada masa ke nan,
idon fatima a kanta,yayin da kunnuwanta ke
sauraron Abdullahi cikin ladabi yana amsar
amanar yana kuma tabbatar mata da yarda Allah
ba zasu yi nadamar ba shi aurenta ba. Har cikin
ran fatima ta yarda yana kirari yana dabawa
kansa wuka nekawai,don bai kamata ya furta ko
kalma daya a cikin maganar momi ba matukar ba
zai iya toshe kunnensa daga saurare ba.
Tsawomn wasu mintuna,sannan momi ta yi musu
iznin su tashi.Abdullahi ya fara mikewa,sanna
fatima ta bishi a baya har zuwa katafaren falon
da aka sauke shi. Suna shiga falon ya soke
hannu a aljihu ya kuma canja fuska,sannan ya
juya mata baya. A gajiye kuma fuskarta a bace ta
nemi kujera ta zauna tana faman harara a
duhu,tunda bai san tana yi ba. Suka kwashe fiye
da mintina goma a haka,sai da ya jiyo
maganganun su safiyya a kusa da falon sannan
ya juyo ya dube ta,duba irin wanda duk kwakwar
mutum ba zai iya karanta abin da zuciyarsa ta
boye game da ita ba.Zuciya d kwanji
.16) Sai ta kara bata rai,shi kuma bai damu ba,
ya tako har zuwa gabanta ya sunkuya
hannayensa dafe da ahnnun kujerar da ta ke
zaune,yadda ta ke jin hucin numfashin sa
sosai,ya dubi tsakiyar idonta da kyau, sannan ya
fara magana kasa kasa. "Duk wata halitta mai
motsi a cikin gidan nan tana da kirki matuka! Ba
kamar ke ba ba abin ya daure min kai sosai". A
tunzure ta taure shi ta mike,ta dinga nun shi da
yatsa,amma ta kasa cewa komai,bakinta sai
motsin yake,ya rungume hannu kawai yana
kallonta,ko kadan fuskarsa ba ta sauya ba, abin
da ma ya kara kular da ita ke nan. Da kyar ta
hadiye ta sami abin cewa. "Oh,abin da ya kawo
ka ke nan?" Ya yi saurin gyara kai tare da
mokade lebe, ya ce. "Eh,tunda da fuska biyu na
zo,idan muna cikin mutane nake masoyinki,a irin
wannan filin ban gane sunan da zan kira kaina ba,
kuma ban san matsayin da ya kamata na baki
ba. Kuma ban san matsayin da ya kamata na
baki ba. Ga shi kuma bana son barin lokutana su
tafi a banza,shi yasa nan fada miki abin da yake
hakkun.Ba laifi ba ne don ne ce,ba ki da kirki,ko
kina da shi?" Zuciyar fatima ta dinga bugawa
saboda tsabar bakin ciki,ita ce dazu har da girin
gidinshin jin haushin ya gats sunanta,ashe rabin
lamab ne cikin rashin mutumcinsa? Ta fara tafiya
da baya a hankali har ta riski wata kujerar ta
zauna,sannan ta dube shi cikin yanayi barcin
rai,ta ce. "Haka ne, rashin kirkina ya zarce inda
kake tsammatar masa,musamman a muhallin da
na tabbatar yin kirkin da barinsa ba zai amfanar
min komai ba, wato muhalli irin naka,me yasa zan
maka kirki? Fada min dalilin don Allah". Tana
rufe baki ya amsa. "Ni ma dan ba ni da dali...."
Ta yi saurin dakatar da shi da hannu hade da
masifa. "Ka ga bana son rashin arziki don
Allah,kirkin idan a gidanku ake rabawa gobe ka yo
min guzirinsa". Ya jima yana kallonta ba tare da
fuskarsa ta bayyana bacin ran da ta ke ciki ba.
Sannan ya murza hannu yana fuskantarta. "Ki
dinga yiwa harshenki linzami ya zama mai furta
alkhairi kinji? Ko don ki ci gaba da kasancewa
cikin shahararun mata a duniya masu sanyin hali
da sanyi kyau,mace na da kima kwarai bai
kamata ta dinga salwantar da ita wajen yin
hayaniya da ihu kamar na karnuka a gaban namiji
ba, mata masu irin wannan halin ina musu kallon
ballagazaye wallahi....." Wannan karon zuciyarta
ba ta buga ba, mamakinta da tsaurin idon
Abdullahi kuma ya yi. Sauki, sai dai ya fara sa
wa tana raina kanta..... Ashe tana da sauran
gibin da ba ta cike ba? Ta rasa da lafazin da zata
kalubalance shi ko ta tsawatar masa, tunda nasa
harshen ya fi nata kaifi..... Idan ta fadi daya sai
ya fada mata goma,sai ta tsaya kawai tana
kallonsa tana huci,ya bude baki zai yi magana ta
dakatar da shi.A sanyaye ta ce. "Ka ga ya isa kar
ka sa min ciwon kai,ban son dogon surutu". Ya
fara murmushi har kumatunsa suka loba,bai
tanka ba sai ya dauko magazine table ya dire a
gabanta. Sannan ya zauna suna fuskartar juna,
amma idanunwansu na wani muhallin daban, ita
ta kurawa talabijin ido,shi kuma yana kallon tile
din da ke shimfide a falon. Suka kwashe sama da
mintuna goma a haka sai da ta ga ya fara
hararar agogo,sannan ta harari kayan kwalam din
da aka shirya masa a tsakiya dakin. A kuntace ta
ce masa. "Idan fa ka tafi ba ka dan taba wani
abu daga cikin kayan abincin nan da suka jera
maka ba zaka bar zuciyarsu da zargi". Shi ma ya
sha kamshi,sannan ya tanka. "Haka ne,sai ki dan
bani wani abu na ci idan kina gudun zargin".
Haba! A hanzarce ta juyo tana masa wani
wulakanctaccen kallo,aka yi sa'a shi ma yana
dubanta,sai ya yi saurin dafe kai,ya ce. "Ash!"
Sannan ya kuma dubanta yana daga mata
hannu,ya ce. "Yi hakuri na manta sunan boyi
nake amsawa a wajenki,sai dai kar ki manta Alh
ya ce mu yi acting sosai,na tabbatar kuma zamu
fa di assigment idan wani ya shigo ya tarar da ni
ina be bude a kwanuka ke kuma kina kallon
talabinjin"
Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
17) Ba ta kop dube shi ba,ta zabga tsaki,ta je
ta zuba masa gasassun 'yan shila wanda
kamshinsu ya gauraye falon. Ta kwashe
lemunkan da suka zube wanda ya fara hucewa,ta
mayar fridge ta dauko masu sanyi duk ta dire kan
center table.A cunkunshe ta ce. "Ga shi nan". Ya
hadiye dariyar da ke damunsa,ya ce. "Don me ba
zaki kawo min nan ba? Ta zabga masa harara
kamar idonta zai fado,ta ce. "Don ni ba baiwarka
ba ce,idan ma ba zaka ci ba,ka bar shi". Ta dauki
lemon kwakwa ta wuce kujera ta harde ta fara
kurba,shi ma sai ya mike ya je ya dauki lemon
kwakwar.yana tsaye ya dire gwangwanin sannan
ya zauna ya fara cin naman cikin gwaninta da
kwarewa yana amfanin da wuka da fork. Ta saci
kallonsa ta yi tsaki cikin ranta ta ce, duk yadda
aka yi ya lakanci barin matansa da gabza shi ya
zagaya restaurant ya barje. Duk sai haushinsa ya
kara kumeta. Yana gamawa ya koma muhallin da
ya tashi, wato na kusa da ita.Bai dubeta ba,sai
ya dubi a gogonsa ya ce. "To ni zan wuce". Tq yi
tsaki kawai ba ta tanka ba. Ya dube ta da
kyau,fuskarsa na rinewa da bacin rai, kawai shi
ma sai ya zabga tsaki. Ta dago da sauri ta dube
shi. Ya murza hannu rai a bace,idonsa cikin nata
ya ce. "Ji nan malama, neman kudi fa ba bariki
ba ne.mene ne za ki dinga yi min tsaki ke ba
tsaka ba,wai ba ku kuka gayyato ni ba,ni ban
miki ba ku karbi kudinku in san na yi,ina fatan ya
sanar da ke ba daudar talauci ya kankare min ya
dauko ni ba..... Uzurinsa kawai na kalla na karbi
tayin". Maganunsa suka ci gaba da kona mata
zuciya.amma ta rasa kalaman raddi, sallamarsa
zata yi ya yi gaba su koma fafutukar neman wani
tunda shi tsaurin idonsa ya yi yawa,ko kuma
shiru zata yi masa ya ci garin? Dole shirun ta yi
masa tunda shi ma yana da tasa darajar,idan an
rasa shi da wuya asami kamar shi,sai ta ta buge
da kallon talabijin shi kuma ya. Mike cikin
sassauta murya ya ce. "Kamar yadda na fada