Showing 18001 words to 21000 words out of 36237 words
Chapter 7 - ZUCIYA DA KWANJI 1 NA MAIMUNA IDRIS BELI.pdf
ke jin shakkarsa,koda yake
dama
can ita ba masifaffiya ba ce, Allah ne kawai
yake
dorata akan mutane suke shakkarat. To da
alama
bai dorata akan Abdullahi ba, wanda yake nufin
wasu abubuwa masu tsauri a kanta,irin wanda
numfashinta zai jure da ma wanda ba zai jure
ba.
"Kar ki sake in ga kafarki a waje..." Maganarsa
ke
nan da ta bude mata kofar hasashen me
Abdullahi yake nufi a kanta? Yana son nuna
mata
iyakartaZuciya d kwanji
.32) Yana son nuna mata iyakarta ne ta hanye
mulkarta don tana cikingidansa ko kuma kawai
yana nufin kuntata mata ne don ya sami
wannan
damar? To idan ba ta fita ba me zata ci? Kuma
idan ta fita ba da izinin nasa ba me ya tanadar
mata? Ba ta iya amsa dukkan tambayoyin da ta
yiwa kanta ba, kuma hakan ne ya taimaka
wajen
raunana zuciyarta ta barke da kuka. Ta je ta
rufe
kofar sannan ta dawo ta zauna ta ci gaba da
kukanta tana tuno tasirin Alh a
rayuwarta,wanda
ba ya iya ja da duk wani zabinta ko da kuwa bai
wa ransa dadi ba, a hakan kuma kullum yake
kirarin sauran mata rakota duniya kawai suka
yi,
amma yau ga ta a gidan da ake aikata mata ita
ta rako matan duniya,har da bita da kullin
takura
da wulakanci. Kusan a nan zaune ta kwana a
nan
falo,sai da aka fara kiraye kirayen sallar asuba
sannan wani malalacin bacci ya fara fizgarta.ta
daure ta jira sallar asuba ta gabatar da ita
sannan ta kum kwanciyar anan falo bacci mai
nauyi ya dauke ta A hannu daya sadiya ta fita
daga nata kuncin tun shigowar Abdullahi a
daren
jiya wanda ko kallon kofar dakin amarya bai yi
ba,ya share guri ya zauna kallon wasan kwallon
Kafa,har wannan daren ya yi musu asuba ta
gari
sannan ya waiwaye amaryar shi ma kamar akan
kaya,sadiya na duban agogo mintuna ashirin da
takwas ya yi ya fito ya shige nasa dakin har
wayewar garin nan. Sadiya ta gama yardar wa
ranta wannan amaryar har ta fi Hindatu
kaskanci
a idon Abu Turab,lallai babu wata mace da zata
sami rabin matsayin da ta ke da shi a zuciyarsa,
wannan ya sa kashi 70% na kishin amaryar ya
fice daga zuciyarta,hanka linta kwance ta shari
bacci har da saleba. Wajen karfe goma Abdullahi
ya kwankwasa kofar sadiya cikin shirin fita,ba
shi
da yakinin zata saurare shi,domin jiya.da safe
kaca kaca suka rabu. Amma ga mamakinsa ko
minti daya bai hada ba ta zo ta bude kofar,ba
tare da ta dube shi ba ta wuce kai tsaye , ya bi
bayanta ya zauna hannun kujera yana mai
fuskantarta,fuskarsa kunshe da walwala,ya ce.
"Kin tashi lafiya?" Ta kawar da kai tana shan
kamshi,ta ce. "Kalau". Ya dan zuba mata ido
ya
ce. "Ina fatan kin ci abinci kafin ki kwanta
wannan baccin naki,bana son zamanki da
yunwa". Ta muskuta ta kara gyarawa,wanda
hakan na bayyana hasken da zuciyarta ke yi,sai
dai ba ta son bayar da kai bori ya hau. Ga
jarabar dokin da ya ishi zuciyarta na son ganin
wannan amarya wadda ta buzuz ta fi ta kima. A
yangance ta dubi kwayar idonsa ta ce. "Wai fita
zaka yi ne?" Yana yi mata wani tsadadden kallo
ya ce. "Eh,uwargida ran gid,ko in zauna akwai
abin da za ki ba ni?" Ta yi saurin girgiza kai. "
A'a sauka lafiya,wai ba zaka gabatar da mu ga
juna ba ne a wajen amayar taka?" Ba tare da
ya
ba wa maganarta muhimmanci ba, ya ce. "Har
sai na gabatar da ku ga juna sadiya,sai ka ce
wasu yara? Ku gabatar da kanku ga juna
mana,ta zo wajenku ko ku uje inda ta ke". Ta
dube shi da gefn ido,ta ce. " Kawai kuma a
matsayina na babba sai na zubar da girmanan
na
shiga wajenta ko? Ya tuntsure da dariya ya ce.
"Sadiya ke nan uwar son girma. To wallahi ta
girme ki, ko wannan kika duba kya ba ta girma".
Fuskarta ta cika da walwala ta ce. "Oh tsohuwa
ka kwaso mana ke nan?
1 · Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
.33) Ya gyada kai ya kuma girgiza, ya ce. "
Idan kin ganta idonki ya kwashe miki". Ya
mikamata hannu alamar ta zo gare shi,yana
cewa. "Wai ba zamu gaisa ba ne?" Ma'ana ya
basar da wancan zancen. Ta kawar da kai ranta
na kara haske,tana kada idanuwa ta ce. "Ai na
sallamawa amarya,idan kwana ukunta sun cika
ka kara mata wata daya a nawa". Ya iso gare ta
yana girgiza kai. "Ba zan iya maraicin rashinki
ba". Ya jima suna faranta ran juna,sannan ya
yi
mata sallama ya nufi dakin hindatu. Yana shiga
kicin dinta ya wuce ya barta a falo ya kinkimo
fulas da kofi ya zo ya zauna tana faman binsa
da
kallo,ya ce. "To tashi da sauri mana ki kawo min
mahadi,kina ganin zan makara". Murmushi
kawai
ta yi,ta mike zuwa kicin ta zubo masa wainar
shinkafar da ta yi da kyakkyawar miyar
albasa,sannan ta kawo masa kayan shayi, sai da
ta hada masa komai sannan ta koma gefe tana
cewa. "Abu Turab ai ban yi tsammanin zaka fita
aiki yau ba. Haba zaka ragewa amaryarka
daraja,
a kawo ta jiya kuma yau ka barta ka fita aiki".
Ya
fara taimakon cikinsa yana cewa. "Aljihuna ne
babu ko karfanfana dole sai na fita,ko
akwai'yan
kudi a wajenki ki sam min aro?" Ta yi saurin
girgiza kai,ta ce. "Ba ka dai kyauta ba. Ai ya
kamata ka yi tanadi tun jiya". Bai dube ta
ba,ya
amsa. "Za a kori gaba". Takawar da kanta daga
gare shi,ta ce. "Me ye sunanta?" Takawar da
kanta daga gare shi,ta ce. "Me ye sunanta?" Ya
dan zuba mata ido,sannan ya amsa "Sunanta
fadimatu,don Allah anjima ki yi kokarin lekawa
dakinta ku gaisa,kar ki duba komai,ki duba ni
da
na ce ki je din kin ji". Ita ma ta dan kafa masa
ido sannan ta kawar gami da ajiyar zuciya,ta
ce.
"Anya ba ka dora min babban aiki ba kuwa Abu
Turab? Me yasa ita ba ka yi mata izinin ta biyo
mu dakunanmu mu gaisa ba?" Ya girgiza kai, ya
ce. "Na fa ce kar ki duba komai". Sai kawai ta
tsaya tana kallonsa yana ta faman cin
abincinsa,dama shi mutum ne mara wasa da
cikinsa. Can ta nisa ta ce masa. "Wai amaryar
ba
ta yi girki ba ne,to ita me zata ci?" Ba tare da
ya
dube ta ba, ya ce. "Yanzu zan fita na nemo
mata". Sai ta ji maganar na yi mata yawo a rai.
A gidan Abdullahi za a ki dora tukunya,kuma a
fita waje a siyo,kuma wai shi ne ma da
kansa,anya? Ta dai share har ya gama ya yi
mata sallama ya fice,can ta ji tashib motarsa
bai
fi mintuna ashirin ba ya dawo. Da sauri suka hau
lekensa daga ita har sadiya wadda ta ke son
sanin abin da ya dawo da shi,yayin da Hindatu
ke
dokin ta ga kalar abincin da za a tarbi amarya
da
shi. Mai masa share sharen harabar gida ya biyo
shi da manyan kwalayen sunfi a kirga sun fi
kala
goma dangin kayan sha,tsotse tsotse da tande
tande,shi kuma abdullahi na rike da ledoji biyu
na
take away mai tambarin wani shahararren
restaurant. Sai da Ayuba ya gama shigowa da
kayan kofar dakin amarya ya fita,sa nan
Abdullahi ya fara kwankwasa mata kofa. Wani
tokareren bakin abu ya tokarewa safiya a kahon
zuci,kamar ta hadiyi zuciya ta mutu,Hindatu
da
sauri ta saki labile zuciyarta na wani irin
bugawa.tunda ta ke ba ta taba jin zafin kishin
Abu Turab irin na ranar yau ba,duk da kuwa Abu
turab tuni ya bayyanar mata sadiya ce mai
kyallin goshi. Cikin magagin bacci fatima ta ji
bugun kofarsa,da sauri ta bude idonta ta dubi
agogo,sai ta tarar sha daya har ta gota, nan
take
kalamansa suka fado mata. "........ Da safe
kuma
ko ba ranar girkin ba ne zan dinga shigowa mu
gaisa......" Ta ture bargo ta dau hijabinta ta
zira
kirjinta sai harbawa ya ke, saboda fargabae irin
cin kashin da ya kunso mata mata a wannan
shigowar, tunda shi dai ya zama annoba, duk
haduwa sa ya gadar mata bakin ciki
3 · Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
34) Sai da ta yi ta gwada irin yadda zata
daure fuska da kuma kalaman da zata iya
fansar
kanta idan ya nemi raina mata hankali,sannan
ta
bude masa kofar,ta koma makwancinta ta
zauna
tana cin magani bayan ta lullube kafarta da
bargo. Sai da ya gama shiga da kayan nan a
kicin dinta tsab, sannan ya kitsa da ledar take
away din, ya ajiye bisa coffe table fuskarsa a
daure ya fara nazarin falom da shiwadda ko
kayanta na jiya ba ta cire ba ga kuma shaidar a
falon ta kwana. Sai daya gama nazarinta tsab
cikin sassaucin murya ya ce. "Kin tashi lafiya?"
Ta kada kwadar ido da kawar da kalba tare da
ta
tanka ba. Ya ci gaba da kallonta wasu irin
abubuwa na huda zuciyarsa juriyarsa na shanye
su. Ya bata murya ya ce. "Ga kayan kwalam din
da kika ce min sun ishe ki sati biyun da kike
zatarwa kanki a gidan nan,idan akwai wani abu
da kike muradi sai ki sanar da ni,wannan kuma
karin kumallo ne na yanzu (yana nuna mata
take
away din) bai kamata na je gidanku na ci abinci
mai kyau ke a nawa ya gagara ba". Ta daga a
wulakance ta dube shi ta ce, "Nawa ka kashe na
biya ka? Ai ba mu shiryo ta zaka yi wata wahala
da ni ba". Tana rufe baki ya amsa mata. "Ni ne
kawai na shiryowa kaina a wani gefen kuma don
na nuna miki kudin kawai kika fi ni,amma na ki
da
shugabanci daga indallah". Takre ya bayana a
fuskarta. "Wa kake shugabanta.....?" Ya tare
ta
da gadara. "Ke!!!!" Ta kada kai tana cije
lebe,ta
ce. "Ai na fi karfinka abdul ya ya zaka yi da
ni?"
Nan ma bai yi kasa a gwiwa ba ya amsa. "Yadda
namiji yake da ko wacce mace musamman
jarumi
irina me jarumtar kashi da ta zuciya..... Ni sam
ban taba yarda wata mace ta fi karfin namiji ba
duk irin kasaitarta...." Ta motsa baki kamar
zata
yi tsaki,sai ta hadiye shi,Nan take kanta ya
fara
ciwo saboda tsabar takaici,ta dafe goshi kawai.
Zai kuma dorawa ta dago ta kalle shi rai a
bace,ta ce. "Abdul wannan hayagagar taka ta
ishe ni, idan ka gama abin da ya kawoka ka fice
min,kuma daga yau bana bukatar gaisuwarka da
bankwananka.Na yarda ba zan fita ba sai da
izininka, sai dai ba zan taba neman izinin naka
ba
ma'ana ba zan fitan ba har wa'adin mu ya cika
mu rabu kowa ya huta,isa kuma na yarda ka isa
ai ga alama nan tsurut da kai ka ajiye mata
biyu
kana shirin ta uku ko wannan aka suba sai a
sara
maka....." Kuncinsa kunshe da murmushi ya
tare
ta. "Kin zare kanki daga ciki ne?" "Kin zare
kanki
daga cikih ne?" Ta yi fuska,ta ce. "Ai dama ba
a
ciki nake ba". Ya yi mata wani kallon mai tarin
fassarori wanda ita kanta duk hikimarta ta kasa
ba shi ma'ana.ya jima yana jan fasali sannan
ya
kada kai,ya ce. "Akwai amanarki a tare da
ni,wanda shugabancinki a yanzu ya jaza
min,saboda haka dole na shigo na miki
bankwana
kuma na ga yadda kika kwana...." Sai ta yi masa
shiru ranta na kara daci,ya jima tsaye yana
kallonta ta rasa yadda zata yi da shi,ta san
neman abin da zai bakanta mata kawai ya
ke,kuma ba zai samu ba don ba zata dinga biye
masa yana sa mata ciwon kai ba. Hai kuwa
bayan ya gama kare mata kallon sai ya bita da
kulli. "Wai a nan kika kwana ne? Duk me ya yi
zafi?" Ko motsi ba ta yi ba bare alamar zata
tanka,sai ya kada kai ya juya. "Sai ki tashi
haka,ki yi wanka ki dan gyara gurin kara a yi
baki
su yi miki kallon kazama ki daga bakin kura".
Haba wasu hawaye masu radadi suka tunludo
mata,ba ta iya hadiyewa sai da ta ce. "Abdul
aniyarka ta bi ka". Ko a jikinsa don yana
dariya
ya fice,ta dafe kai a wajen tana maimaita.
"Innalillahi wa inna illahi raji'un" Ta yi
kukanta ya
ishe ta, sannan ta bai wa kanta hakuri ta tashi
ta
gyara falon,sannan ta fada wanka a gurguje
don
ta dan fara jin hayaniya a cikin gidan. Ta
shirya
da shigar turawa,ruwan kasar wando wanda ya
fito da kirarta da farar vest saboda zafin da ke
gari duk da na'urar sanyaya daki ta wadata a
gidan,amma ji ta ke komai ya yi mata nauyi da
zafi,kamar yadda zuciyarta ta ke.. Ta saki
ranta
ta kwashi abinci don ta tabbatar babu ruwan
abdullahi da abin da yunwa gauraye da bacin rai
za su haifar mata,ita kadai wannan asarar
data
shafa. Cikin kayan da ya zube mata a kicin ta
tarar da abin da ta fiye so,wato yellow peach. Ta
balle gwangwani biyu a faranti ta koma falo
zamanta ke da wuya aka kwankwasa mata kofar
falo,haba gabanta ya yi mummunan faduwa
don
ta yi tsammanin dan hayaniyarta ne, tunda
tasan'yan gidansu babu mai zuwa mata a
wannan ranar. Sai da ta leke ta tagar kicin ta
ga
wasu bakin mata biyu sannan hankalinta ya dan
kwanta,sai da ta koma mazauninta ta zauna ta
dauki farantin peach dinta ta tsiro da cokali ta
kai baki sannan ta yi izinin a shigo. Sadiya da
Hibdatu ne, an kullo tsegumi an taho,amma
daga
tsomo kafarsu numfashinsu ya so ya dauke
saboda haduwar falon,sai wani kamshi da sanyi
mai rahama ke dukan mutum. A kasaice kamar
yadda ya zame mata dabi'a ta ce. "Ku shigo".
Sadiya dai don da kunya ne ace ta koma amma
tana dora ido akan fatima sai ta ji gaba daya
falon ya fara zagaywa da ita.amarya Abu Turab
ke nan? Sadiya da gama tsinkewa don tasan
mijinta dama can ba sauki,bare ya sami wannan
'yar mai kama da gwal. Ko hindatu ta ji babu
dadi game da amaryar Abu turab ba zai wuce na
kasaita da rashin kulawarta ba, sai kuma
ledojin
abincin da ke gabanta wanda a arharsa da
matsayin resturant din da aka siyo shi ya haura
duba uku.kudin cefane su na kwana biyu a karin
kumallon mace daya! Turkashi! Da gaske
matsayin mace biyu ta ke amsawa... Ko ma ta
haura. Su suka yiwa kansu wajen zama suna mai
fuskartarta,sannan ta sami damar matsawa a
yangance ta ce. "Ina kwananku?" Hindatu ce
ta yi
kokarin amsawa da murya a bude,amma sadiya
kusan a ciki ta amsa ta kuma kasa sake daga ido
ta dubi fatima. Sai da fatima ta ci peach yanka
biyu sannan ta dire faranti ta mike cikin yauki
tana cewa "Bari na kawo muku ruwa". Da sauri
hindatu ta ce. "A'a mu fa yan gida ne ba sai
kin
ba mu komai ba". Ba tare da fatima ta dakata
ba,
ta ce
1 · Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
35) "To'yan gida ba za a karrama ku ba, ina
zuwa". Ta zuba lemon mangwaro biyu a dogon
farnti,yellow peach biyu da sosa ruwa faro da
tambulan biyu da kuma choculate cake guda
biyu. Ta kawo musu ta ja wa kowace coffee table
a ganata,ta bude musu lemo,sannan ta zazzage
musu peach ta yi musu bismillah,sannan ta koma
nata muhallin. Ko kallon kayan sadiya ba ta yi
ba, sai Hindatu ce ta dauki lemon ta kurba
sannan ta dube ta ta ce. "Abu Turab ne ya
zubar
da ladansa bai gabatar da mu ga juna ba, shi ne
muka yi karambanin zuwa inda kike tunda ke ba
ki nemo mu ba. Ga yaya babba ( ta nuna sadiya)
ita uwargidanki,sai ni Hindatu na bi bayanta. A
kasaice fatima ta juyo ta dube su, da dokin ta
ga
matan da suka fita.ta yi tsaki a zuci kawai ta
kawar da kai,haushinsu kuma ya kara turnuke
mata zuciya,daman tunda ya ce matansa sun fi
ta taji gaba daya ta tasne su, ashe ma burgar
banza ce ko kama kafarta ba su yi ba, duk da shi
ya ce ba a nan ta ke ba. To amma abu a duhu
wa zai dorar? Da kyar ta hadiye tsanar da ta yi
musu ta amsa batun da suka zo mata da shi a
hagunce. "Wane ne kuma kuma abu turab
Kamar
a kufule sadiya ta ce. "Angonki!" Fatima ta
kawar
da kai tana kara hadiye takaicinta, kamar dole
ta
ce. "Au,ban sanshi da wannan sunan ba".
"Amma
ba ku dade tare ba?" Tamabayar da sadiya ta yi
mata ke nan,ita kuma sai ta juyo kawai tana
kallonta tana ta faman kuma sai ta juyo
kokawa
da zuciyarta wadda ke karanta,don ta buge da
kai
peach a baki ta taune ta hadiye,sannan ta dubi
talabijin ta ce. "Ba ki da labari ke nan?" A dan
zafafe sadiya ta ce. "Kusan haka ne, don an yi
abin ne cikin gaggawa kinga zan iya tsammanin
akwai wani 'yar burum burum". Duk da fatima
ba
ta iya bakar magana ba,sai ta ji yau kamar an
kimsa mata,don sadiya na rufe baki ta amsa.
"To
ko ma dai odiyo diyo ne ya fice wai tunda ya
zama dahir,ko a mafarki dai muka hadu
haduwar
ta yi amfani tunda mun auri juna,auren da na
tabbar a yanzu ya fice gaibu. Sadiya ta fara
murmushin da ya fitar da sauti,ta ce. "Dama ga
abu turab da aure aure,shi har kwallon kafa
aura
yake jiya raba dare ya yi yana kallon kwallo,na
yi
mamakin yadda kika saki wannan damar".
Maganar ta daki zuciyar fatima,amana nan da
nan sai ta fanshe. "Babu wani abin mamaki
akan
aurensa don in dai namiji bai yi sa'ar auren
farko
ba to ya gama garari,ba kwallon kafa ba har
kwallon ciki ma wataran sai ki ga ya aura,abin
da
kuma zai fi saukin yi min ciwo ke nan,wato akan
gazarwa