Showing 3001 words to 6000 words out of 36237 words
Chapter 2 - ZUCIYA DA KWANJI 1 NA MAIMUNA IDRIS BELI.pdf
inda ya fahimci
fushi nasa ba shi da ma'ana,sannan ba ya dariya
a inda ba a san darajarta ba.8) Don haka kankantarsa ta tsaya a jikinsa ne
kawai,amma zuciyarsa dattijiya ce.azancinsa
kuma tsoho ne mai rankarfe. Matarsa ta fari
sadiya,wadda ya aura shekarar da ya kammala
karatu ko fara aiki bai yi ba,makociyarsu ce
wadda soyayya mai zafi ta shiga tsakaninsu kafin
auren,wadda kuma ita ta taimaka wajen
amincewar mahaifinsa akan auren sadiyar da
shi,kasancewar sadiya ba ta fito gidan tarbiyar
da ta gamsar da malam ba,sai dai dole kunyar
idon mahaifinta tasa ya amince wanda takanas
ya ishe malam din ya ce ya bai wa Abdullahi
auren sadiya. Sai dai kash! Sadiya ba ta wa
masa dan malam kunya ba,sai au enta da
Abdullahi ya dinga haifar da matsaloli,matsakaita
da kanana,wasu kishiyoyin juna,sadiya
mafadaiciyar mace mai yawan kuncin zuciya da
tsarguwa.Ga kuma Abdullahi miskilin mutum
kuma mara daukar raini,sannan mara daukar
korafi da muhimmanci, wadannan dalilin suka sa
zuciyoyinsu suka canja daga masoya juna zuwa
wani abu daban. Kullum su ke nan cikin
hayaniya,sadiya ta dauki kafa ta yi yaji,shi kuma
ya yi zuciya ya share ta har sai manya sun shigo.
Da abin ya ishi malam sai kawai ya nemar wa
Abdullahi wani auren. Hindatu ke nan matar
abdullahi ta biyu, wadda ya aura ba bisa doron
so ba,sai dai ta sami filin karamci a zuciyarsa
saboda hakurinta da saukakawa kai buri.tana
nuna masa wadatarta akan iyakar soyayyarsa da
adalcin da ya yi mata duk da kuwa ba ya iya
boye bambancin da zuciyarsa ta ke nunawa
tsakaninta da sadiya wadda za a iya kira
mowarsa duk kuwa da tambelenta. Shekarun
hudu ke nan da auren fari,kuma shekarun biyu da
auren Hindatu,amma cikinsu babu wadda tataba
ko batan wata, wannan ma sai ya bi layi cikin
matsalolin da suka dami duniyar Abdullahi.
****************************************** Alh
sulaiman abokin ne na kud-da -kud ga yayan
Abdullahi,mai suna Abdulawahab.sun yi karatun
sakandire tare,kuma daga nan abotarsu ta samo
asali. Ba za a ce abdullahi ya yi masa farin sani
ba, kasancewar lokacin da ya yi wayo
sosai,sabgogin sun yiwa Alh sulaiman
yawa,ma'ana ya yi wuyar gani,amma ya waye da
Alh ya kawo wa yayan abdullahi lokacin da ya yi
aure na biyu. Abdullahi na tare da yayan nasa
yana sauraron hirarasu. Abdulwahab yana zolayar
Alh da cewa. "Sulaiman burinka fa kamar ya wuce
mallakar makudan kudin,gidaje da motocin hawa
kafin ka ajiye iyali,me kake yiwa kanka kawa ne?"
Alhaji na dariya ya ce. "Wallahi har yau na kasa
samun matar da zata da ce dagida na,watanin
baya na so auren wata balarabiya wani abokina
ya dinga kwabata,wai tatike maza suke su
tsere,dole na hakura tunda an ce mutum ba ya
kin ta mutane". Abdul wahab ya ce. "Haka ne,
amma ya kamata ka yi taka tsantsan a cikin
sha'anin mata,sun fi kowacce kawa
hatsari,musamman kyawawa don yawancin su
nagartasu ba ta kai masu karamincin kyau ba,sai
ka zauna da matarka mai karancin kyau ka dinga
sarafa abarka son ranka,amma awajen
kyakkwayawr mace ka yi kadan,komai kudinka da
mulkinka,wuyarta ta kalli kanta a madubi sai ta ji
ta girme idonka,kuma ko yau kuka rabu zata sami
wanda ya fi ka,don haka ba ka isa ka sa ba,balle
ka hana". Kamar a sanyaye Alh sulaiman ya ce.
"To,Allah ya zaba manaZUCIYA D KWANJI
9) Alh sulaiman
ya hadu da fatima ne ranar bikin kammala
karatunta,gaba daya ya sakwarkwarce,don
fatimata kusan zarce tanadin da yake wa kansa
game da mace. Sunanta ya nuna masa daga inda
ta fito,sai ta kwanar masa gidansauki,domin
kawu malaminsa ne tun a sakandire,sannan ya
koyar da shi a digiri dinsa na farko.sun shaku
matuka suna ganin mutumcin juna kasancewar
kawu mai son jarumin namiji mai hazaka da
juriyar cimma burin abin da ya sa a gaba.To
Allah ya horewa sulaiman wannan,mutum ne mai
kaifin kwakwalwa,wanda duk abin da aka zuba
mata sai ta kwashe,shi yasa yake ji da shi tun a
sakandire. Kwana uku da ganinta ya wanke kafa
ya tafi gidan prof.bayan ya nemi izininsa a waya.
Pro ya karbe shi cikin mutumci kafin ya shiga
rudanin abin da ya zo masa da shi,wato neman
auren fatima. "Ko akwai matsala ne?" Alh ya
tambaya saboda ganin yadda kawu ya shiga
damuwa. Prof ya sauke numfashi ya ce.
"Sulaiman fatima ta dade tana dauko min magana
wallahi,manyan mutanen da nake jin kunya ba
zan iya kirga maka wadanda suka zo da kokon
bararsu gare ni na son auren fatima ba.Amma sai
ta watsa mana kasa a ido ni da su,na rasa inda
yarinyar nan tasa gaba,kowa ya zo ba ta so.A
bayanta fa kanwarta ta biyu ake shirin
aurarwa,amma ita ko a jikinta....maraicinya ke sa
ni tausayamata,amma tabbas da ni na haife
fatima da na tilasta mata aurenka". Wannan to
gaciyar ba ta sa sulaiman ya dauke kafa ba,sai
ya ci gaba da kawo gaisuwa da rokon iri har aka
kai matakin da kawu ya ba shi damar bayyana
kansa ga fatima.Amma kash! Sai aka yi rashi
sa'a cikin masu son ta ba ta taba tsanar wani
sama da Alh sulaiman ba, ba ta kaunarsa ko
kadan kuma ba ta iya boyewa kowa ma ya sani.
Shekarunsu biyu a haka, fatima ta kammala
service,ta kuma nemi izinin kawu na neman aiki.A
nan ne kawu ya yi ta maza ya ce sam bai san
wannan zance ba, ya ma ba ta wata guda na ta
fito da miji, idan ba haka ba sai dai ta ji taron
dauran aure. Fatima ta dauke maganar kawu
wasa,har ta bare watan ya share a wasa,sai rana
tsaka ta ga taron jama'a a gidansu,labarin ya zo
mata an daura aurenta da Alh sualiman. Tarihun
auren ke nan,wanda labarin zamansa sam babu
dadi,Alh sulaiman ya cimma burinsa na mallakar
"KYALLI HUDU". Sai dai kash! Kyalli daya ya hana
shi natsuwa,wato fatima,ta hana shi kwanciyar
hankali sam. Ta kwakware dukkan farin cikin da
sauran kyallin suka samar masa.Ga shi Allah ya
jarrabe shi da masifar kaunarta,shi yasa ta ke
dama garinta a sha yadda ta ke so ko da babu
gasara balle sukari. Duk abin da fataima ta
shimfida kpo ba ya so sai ta aiwatar,ga jarabar
kasaita kamar 'yar sarkin santanbil,sai ya yi
magana hamsin fatima ba ta tsinka daya ba,idan
ma ba ta so ba, sai su kwashi kwanki ba su ga
juna ba,don babu ruwanta da duk wani abu da ya
shafe shi, cinsa ko shansa da kula da
dawainiyarsa duk ta sallamawamasu yi masa
hidima. Kamar yadda bai isa sanin wani abu
game da shige da ficenta ba bu ruwanta da
daukar damarsa,ko yana cikin gidan sai dai ya
hangi ficewarta da mota,ko kuma duk sanda ya
shigo gida ya binciki masu gadi,"hajiya na ciki,ko
ta fita?" Kai kansu ma'aikatan gidan hakan na
bala'in bakanta masu rai,ballantana danginsa
wadanda fatima ba ta dauke su a bakin komai
ba,ko gidan suka zo kashi ma ya fi su daraja a
idonta.Gaisuwa kadai ke hada su, babu duka
babu zagi,amma babu ruwanta da mutum har ya
karaci kwanakinsa ko wuninsa ya bar gidan.
Mahaifiyarsa ce kawai ta ke samun arzikin kallon
kirki,shi ma a wani yanayi na kamar dole don ita
kanta mahaifiyar tasa tasan fatima ta tsane
ta,kamar yadda ta tsane dantaZUCIYA D KWANJI
.10) Duk wadannan munannan dabi'u na fatima
ba su taba rage matsayinta a zuciyar Alh ba, da
zata yi mugun bata masa rai,idan ya hangi
murmushinta ko tsakainta da wani ne sai ya ji ta
wanke masa zuciya.Don haka duk yadda
mahaifinyarsa da sauran danginsa ke nuna masa
illar fatima ba ya gani,idan ma ba a yi wasa ba
sai reshe ya juye da mujiya,ma'ana ya tsani me
kawo sukar,har dai kowa ya fahimci shi aka daina
kawo masa sukar,illa addu'ar ganewa. Duk wata
biyayya da mace ya kamata ta yiwa mijinta
fatima ba ta santa ba a tsakaninta da Alh kuma
ta kan yi komai domin ta bata masa, wanda tana
yin hakan ne domin ya ji zafi ya saki aurenta
kamar yadda ta ke iya keta idonsa ta fada masa.
"Ba a nemi amincewa ta ba kafin a hada mu
rayuwa tare, saboda haka har abada kada ka
saka ran zaka mallaki karamar kofa ko kamar ta
allura daga kofofin zuciyata.Raina ba ya sonka,
kuma ni mutum ce da ban iya boye kiyayya ba"m
Bai taba daukar wani mataki akan fatima ba ko
da na zare ido ne, sai rarrashi da lallabawa tare
da yi mata manya manyan kyauta masu motsa
zuciya.gwala gwale,kadarori, manya kudade ita
da duk wanda ya rabeta,amma fatima kamar
dutse,zata karba ta kalmashe,idan ta ga dama ko
godiya ba zata yi masa ba. A haka suka yi
rayuwar,sai su kwashi watanni ba su hada
shimfida ba, wanda a nan ma tana kara tafiya da
imaninsa ya ci gaba da kwadayin zaman har
abada tare da ita,saboda baiwar da ta ke da ita
na kasancewa daga cikin matan da ake kira
sa'ida. Shekarun uku tare sannan ta sami ciki
wanda ya bare a lokacin da yake shiga watanin
hudu,cikin shekarun ukun da suka kuma biyu
bayan shidda ke nan da aurensu,ta jera bari sau
hudu,har waje ya fita da ita,amma lamarin ya ci
tura.wannan ya sa ta kara tsanarsa,musamman
idan yana lallabata da cewa rabo ne ya kaddara
aurensu,takan ce "Rabon wahala ba, tunda akalla
ko dan tsako na kasa haifa". Bayan wannan aikin
da aka yi mata kawai sai ta dinga munafintarsa
tana karbar allurar hana daukar ciki,saboda yadda
ta tsani mutuwarta haka ta tsani haihuwa da shi,
saboda ta rayawa ranta haihuwarta zata tilasta
mata zaman gidansa Shakaru da suka yi goma
tare,bai zama wani sabon abu da zai hana a
yanzka kaza ba, don babu abin da ya
canja,fatima ba ta fasa nuna masa iyakarsa
ba,shi kuma ko kwayar zarra bai rage sonta ba,
duk da ta dalilinta ya sami hawan jini. Kai ko a
murnar cikar su shekara goma da aure wani
katoton gidan gonarsa ya mallaka mata wanda
kudinsa ya kai miliyo ashirin. Kuma wannan ne
ya tashi mahaifiyarsa a tsaye wajen farraka su,
don ta hakikance Alh zai iya mallakawa fatima
dukkan dukiyarta da ya mallaka,ko da kuwa yin
hakan ba zai amfane shi da komai ba. Ta dinga
ziyartar bokaye da malaman surkulle amma shiru
babu labari,dole ta koma wa gaskiya,ta sa aka
dinga yi mata rokon Allah ana neman idan akwai
alkhairi ya shirya fatima idan babu ya farraka
auren. Sai da kura ta yi kamar ta lafa,ku san Alh
bai taba mallakar fatima irin yadda ya mallake ta
a wannan shekarar,kai kamar ma ita ce shekarar
zumarsu,wadda bai dandana a farkon aurensu ba.
Fatima kan yi hira da shi ba tare da bakar
magana ba,sannan takan yi masa rakiya idan
tafiya ta same shi, sannan uwa - uba ta daina
gudunsa a shimfida duk lokacin da ya bukace ta.
Allah mai yadda ya so, ranar wata alhamis da
sasanyar la'asar ta shirya ta fice bikin kanwar
wata kawarta. A lokacin ne wasu miyagun
ma'aikatan gidan suka sami damar shiga dakin
Alh ta hanyar amfani da (master key) suka
kwashe wasu makudan kuadaden waje da ya
shigo da su safiyar ranar. Ya dawo karfe biyar zai
fita da kudin,amma sama ko kasa ya nemi kudin
ya rasa,ya shafa a gidan babu fatima.Haba! Sai
hankalinsa ya yi mugun tashi,ya tabbatar kudin
nan daukarsu aka yi,ya hada dukkan ma'akatan
gidan ya fara surfar su da masifa. A karshe ya
tabbatar musu in dai ba su fito masa da kudinsa.
Ba sai ya salwantar da rayuwarsu. Ya sallame su
kaca kaca bayan ya sanya masu gadi sun
garkame kofar gidan tunda sun tabbatar masa
babu wanda ya fita bayan Hajiya,wadda ta tuka
mota da kanta. Bai ko iya halarta sallar magariba
da isha'I ba,yana ta faman safa da marwa cikin
yanayn tashin h [truncated by WhatsApp]11) Alh sannu da gida". Ya juyo ya dube ta
cikin matsanancin bacin rai,cikin tsawa ya ce.
"Fatima daga ina kike?" Ta yi saurin juyowa ta
dube shi cikin dukan zuciyar mamaki,bacin ran da
ke fuskarsa ya sa ya kara baki a idonta. Ta ga
kamar babu mutumin da ya kai shi muni a
duniya,sai ta ga ma babu hujjar da zai mata
wannan tsawar ko wannan gizagon,kawai sai ita
ma ta taso masa cikin bala'I. "Ban sani ba,idan
ka halicce ni ne sai ka dauki mataki a kaina".
Haba! Ta kara hada masa bacin rai, Hankalinsa
ba ya tare da shi ya ce. "Au haka kika ce? To
zaman uban wa kike yi a cikin gidan tunda ban
isa na yi iko da ke ba?" Ita ma cikin tsawa ta ce
masa. "Kai ne ka fi kowa sani,zaman kaddara
nake ba zaman uban wani ba..... Ko ka manta ne
ba so da kauna ya kawo ni gidan nan ba.balle
ban wani ya dinga yi min wannan ihun". Jikin Alh
ya dinga bari kamar mazari, gaba daya fatima ta
sauya a idonsa da zuciyarsa,ya ga ma gaba daya
ba ta da wani amfani a wajensa ya fara mata
bala'I. "Ke bana son isakance da rashin tarbiyyar
da kika saba kin ji! Matukar ba zaki zauna a
gidan nan kamar ko wace matar ba, to tun wuri
ki san inda dare ya yi miki,don ba ki da wani
amfani a wajena,kullum ki dinga ficewa kina bar
wa ma'aikata gida kina janyo min asara.....ke dai
ba ki da wani amfani wallahi". Ta tare shi cikin
hawaye saboda tana da saukin kuka,ba domin
nadama ba. "Ai ni ban taba daukar aurenka wani
abin a zo a gani ba,balle na yi abin da matan
aure suke..... Sai ka daina yaudarar kanka da zan
yi wani abu da zai yiwa ranka dadi......." Kai
tsaye ya amsa ta. "To shi ke nan,tafi gidanku na
sake ki saki UKU, don kin san ni ma na mayar da
soyayyarkitarihi don iyayenki bace min da gani!"
Shi ke nan, da shigowar fatima da saki nata ba a
fi mintina biyar ba,Alh ya haye sama ya barta nan
tana kuka matsannanci, sakin ya girgizata
matuka! Alh ya saketa a lokacin da ta daina
sha'awar barin gidansa,ma'ana ta yarda karasa
rayuwa da shi duk da ba ta jin kaunar sa cikin
ranta. Ita ma ba ta jima a wajen ba ta fice,tunda
dama ko mayafi ba ta sauke ba, makullin motar
ma yana hannunta,sai gida wai an daki kare a ka
kawu ya sami bakin labari, amma bai gaskata
fatima ba,sai ya kira Alh a waya,wanda har
wannan lokacin yana kulle a dakinsa cikin mugun
bacin rai. ". Da gaske ne ka yiwa matarka saki
uku sulaiman? "Inji kawu. Ba tare da lissafin abin
da zai tafi ya dawo ba,Alh ya ce. "Kwarai da
gaske,ku zo ku kwashe kayanta,ba na kaunar duk
wani abu da zai tuna min na rayu da ita,mts!" Ya
kife wayar cikin bacin rai. Wannan ne ya kashe
bakin tsanyar kawu dangane da fadan da ya
tanadarwa fatima. Ba sai ya bincika ba yasan Alh
ya gama ganin damarsa bai kuma dauke shi a
bakin kamai ba tunda ya iya keta idonsa ya yi
masa wannan cin fuskar. Kawu ya sauke ido akan
fatima,idonsa cike da kwallah ya ce. "Tashi ki
shiga gida fatima,Allah ya sa hakan ne alhairi
gare ku gaba daya". Washegari ranar Alh ya fito
tafiya sallar asuba ya tarar da jakar kudinsa a
korido,ya dauka ya shigar falo sannan ya fice
masallaci. Har aka idar da sallah cikin hawaye
yake, sai da ya dawo gida ya dinga mai dalilin
kuka kamar wanda aka yiwa albishir din ranar
mutuwa.zuciya da kwanji
12) Ya tabbatar Allah ne ya jarrabe shi akan
fatima,daukar kudin nan ba ya nufin komai sai
rabuwarsa da fatima,wadda a zahiri da badini ta
fi karfin wadannan kudin a wajensa. Lamarin
kamar alamara kamar mafarki,ya rabu da
fatima,rabuwa mai kama da alamara da ya ya zai
karbi wannan kaddarar?. Kawu mutum ne mai
zuciya kwarai,da sanyin safiya ya turo a tattare
masa kayan fatima,Alh ya yi tsalle ya ce bai san
wannan zancen ba,har sai da ta kai sun kira
kawu a waya sun sanar da shi. A fusace ya kira
wayar Alh ya ce masa. "Ban gane abin da kake
nufi ba?" Kawai sai Alh ya sa kuka yana cewa
"Kawu ayi min rai,a binciki malamai ko akwai
gyara cikin lamarinmu, wallahi kawu cikin mayen
bacin rai na yi sakin nan, sam hankalina ba ya
tare da ni......" A kufule kawu ya amsa. "Shi ke
nan,yanzu ka bar su su debi kayan in yaso idan
malam sun budo maka kofar halaccin ci gaba da
zamanku tare sai mu dawo da kayan". Bai jira
cewar Alh ba ya kashe wayar dole Alh ya barsu
suka kwashe kayan fatima tas, yayin da kamar
sun bude kofar kukansa da bakin cikin sa.
Rayuwa ta yi kunci gare shi matuka. A wajen
fatima ma haka lamarin yake,ranar da aka yi
sakin ba ta iya runtsa bacci ba. A zatonta zafinb
kalmar da ya hada mata da sakin ce ta ke
damunta wato. "Don ki san nima naE mayar da
soyayyarki mafarki..... Don iyayenki bace min da
gani". A hankali sai ta gane ba kalamar ce ta ke
son ta tashi hankalita ba,akwai batutuwa da
dama, kuma na shekaru da yawa.yadda ta jima
tana taka rawar da ta ke so a gida da rayuwar
Alh shi kuma yana saka mata da tarin kauna da
farantawa.....me yasa ya dawo daga rakiyarta
yanzu? Kuma zata kuma samun namiji mai nuna
mata kauna kamar Alh kuwa? Wadannan lissafe
lisafe ba su barta haka ba sai da suka yi tasiri
manna mata kaunar Alh,ta dinga yarda wakanta
lallai ta tafka asarar masoyi. Ta rasa sukuni
kwata kwata,hakki ne kawai yake dawainiya da
fatima,hakki irin na mai laifi cikin ma'auratan da
suka sami kansu tsakiyar kaifin almakashin saki
uku! Duk da haka ba za a ce fatima ta kai Alh
damuwa ba, tunda ba ta yi wani yunkurin ba,
bayan na fatan ina ma jiya ta dawo yau, ta mayar
wa da alh raddin soyayyarsa? Ba ta yarda ta yi
zurfi cikin kaunar Alh ba sai da ya nemeta da
tayin yadda za su mayar da aurensu tare da
bayyana mata fatawar da ta bayyana cewa,saki
uku lokaci daya sakin