Showing 36001 words to 36237 words out of 36237 words
Chapter 13 - ZUCIYA DA KWANJI 1 NA MAIMUNA IDRIS BELI.pdf
yi min kallonm mai ci da karfin
ba".
Ta mike cikin tangadin tashin hankali, sannan
ta
dake ta tsaya da kafafunta tana
fuskantarsa,ta
ce. "Gajarta min abin da kake nufi a kalmomi
goma zuwa ashirin idan zai samu" Tana rufe
baki
ya amsa mata " Na karbi tayin auren kisan
wutar
da Alh ya yi min da zummar in kubuta da ku
zaman haramcin da kuke yiwa kanku tanadi tun
kafin a sanyaki a idona. Na dauki hakan
jahadi,sai
aka dace ina dora idanuna a kanki na kamu da
matsananciyar kaunarki.daga lokacin na fara
nawa acting din wanda ya sha bam ban da
naku...." Ta dakatar da shi cikin haki da neman
sarkewar numfashi,cikin kakkausar murya ta ce.
"Ya ishe ka! Zan duddura maka zagi wallahi!
Bai
damu da masifarta ba,ya tari numfashinta. "Ki
zage ni mana fatima,sai me? Kin san dai zagi
ba
hanya ce ta samun solution ba, kuma bai cika
zubar da kimar wanda ya yi, musamman idan
wanda ya isa ya zagi wanda bai isa ba".
Hankalinta kamar ba ya jikinta ta watsar da
takardar ta nufe shi gadan gadan kamar tana
zuwa hadiye shi zata yi. A nan zan dakata,sai a
nemi littafi na biyu don dorawa. Taku
MAIMUNATU IDRIS SANI BELI
3 · Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
SAI KUYI MUN UZIRI.... PART2 SAI ANJIMA KO GOBE... ASHA KARATU LAFIA
Compelled by hauwee jidderh abdulkadir AKA mssjidderh