Showing 21001 words to 24000 words out of 36237 words

Chapter 8 - ZUCIYA DA KWANJI 1 NA MAIMUNA IDRIS BELI.pdf

da zan janyo a cika min gida da
kishiyoyi". Sadiya ta yi masifar kuluwa tamkar
ba
ita ta fara zunguro fitinar ba,bacin ranta ya
kasa
boyuwa tana numfarshi ta ce. "Wata kishiyar ai
suna ta tara,kishiyar da zata yi asarar daren
farko ai maraba da ita. Wallahi ni a kawo min
dozen ma" Numfashin fatima ya yi kamar ya
dauke saboda takaici,ta rasa amsar da zata ba
wa sadiya ta fashe,sai gaba daya ta tsani kanta
ta kara tsanar Abdullahi,wannan babu tantama
shi ya janyo mata wannan koma bayan da ya ce
sai ta tare a gidansa
2 · Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
36) Ta dinga gyada kai tsawon
lokaci,sannan ta ajiye numfashi ta dubi

Hindatu,ta ce. "Ita ta gabatar min da kanta,ke
kin
yi shiru ko rakiya kika yi mata?" Hindatu ta
bude
ido ta ce. "A kan me? Igiyarta daban tawa
daban,
don duk abin da ta fada ita kadai ta
sanshi,don ni
ban san shi ba.... Ni umarni na bi,don maigidan
ya ce na zo mu gaisa,na kuma sauke nauyi......"
Fatima ta cije lebe cikin girgiza kai ta tare ta.
"Kwarai kin sauke nauyi,ina kuma godiya ba
tare
da na hakkake taki gabatarwar ba tunda tare
na
ganku.... Ni ban shigo gidan nan don wata ta
dinga zuwa tana min haushi ba saboda duk
fadin
dangima babu karnuka......" "To mun gode".
Abin
da hindatu ta ce ke nan, kuma salin'anlin ta
shi
da lemonta a hannu ta fice,sai sadiya ma ta ke
mata baya bayan ta saki katon tsaki tana
habaice

habaice. Fatima ta bi su da kallo kanta na wani
irin ciwo saboda bacin rai,yau fa ake yinta,rana
zafi inuwa kuna,auren sati biyu mijin babu dadi
matansa babu dadi,ita zara'u ina ta tsoma
ranta?
*********** *********** ********* Karfe
biyar
abdullahi ya dawo gidansa ya zauna a falonsa
da
gajiya yana kallon wasan kwallo cikin rabe
hankali,fiye ma da uku. Amarya fatima ta debi
kason mutum biyu,kwallaon kafa daya,ga kuma
iyayen gida wadanda mintuna talatin ke nan
da
shigowarsa babu wadda ta shigo masa ko sannu
bare ta taushe shi game da radadin gajiyar
zuciya
da ta jikin da ya kwaso. Ya gaji ya fara kiran
wayar sadiya amma har sau uku tana kin
dagawa,sai ya haura ya kira hindau,ita kuma
tana
dagawa don rainin hankali sai cewa ta yi. "
Lafiya?" Takaici ya rufe shi,a zafafe ya ce.
"Wacce banzar tambaya ce wannan hindatu?
Kuna jina na dawo amma don raini a rasa me

bullowa ta gaishe ni?" Kawai sai ta kashe wayar
tana tsaki. Ashe ya ji ta, ya sauke wayar cike da
mamakin mata, mata fa shaidanu ne, kalau fa
ya
bar su,amma yanzu ya je ya dawo duk sun wani
birkice masa,wai ma har hindatu da yake da
garantin ba ta salwantar da mutuncinsa da
kimarsa. Sai ya ji gaba daya ransa ya kara
mugun baci,kawai sai ya tashi ya sa wa kofarsa
makulli don ma kar wata ta yi gigin kwaso kafa
ta zo masa ya sauke mata nasa rashin
mutumcin,don gaba daya haushinsu yake ji. Ya
tara lemuka masu sanyi a gabansa,idan ya dure
wannan gwangwani ya dauki wannan yana
kallon
wasan kwallo wai duk don zuciyarsa ta sami
sanyi,amma kamar turi don ba abin da ta ke
muradi ke nan ba. Fatima ta ke son gani,amma
babu wani dalili na ganinta a yanzu,idan ba
yana
son karyawa kansa tsari wanda Zai iya rushe
masa wata katanga a cikin ginin da ya yi nisa a
cikinsa ba. Haka ya dinga daurewa har daba da
magriba ya yi wanka ya shirya cikin kananan
kaya wadanda suka fito da kuruciyarsa

fili,tana
kuma matukar yi masda kyau,ya fes turaren
five
eleven sannan ya kullo kofa ya fice masallaci.
Sai
da ya sallaci isha'I sannan ya nemi gida dauke
da take away din amarya,zuxiyarsa cike da
sakar
yadda za su bullowa juna yau. Yana shiga ya yi
karo da sadiya a tsakar gidan wanda babu
dalilin
ganinta a tsakar gidan a wannan lokaci,yasan
kwannan zancen,ta fito ne kawai don ta sanya
masa ido kawai ta sami abin yi masa korafi su
hau rigima. Ya share kamar bai san Allah ya
tsire
ba,idanunta kan ledar hannunsa ya shiga
kwankwasa kofar fatima. Ya shafe fiye da
mintina
goma yana bugun kofar ba tare da jin a ransa
zai
gajiya ba idan ya shafe sama da awa daya yana
yi. Can sai gata ta zo ta bude tana sanye da
after
dress,fuskarta na bayyana shirin ko ta

kwana,ta
koma baya zuwa tsakiyar dakin tana sauraron
karasowarsa. Ta gama zuwa wuya ba zata yarda
Abdullahi ya jona mata ciwon zuciya babu dalili
ba. Ya karaso ya ajiye ledar kan table sannan
ya
zuba mata ido,tun ma kafin ya yi magana ta
riga
shi. "Ka ga malam! Matukar rashin arziki ka
kwaso ka shigo min ka juya da takunka,don ni
ma na shaki kamarsa ina ji kum a raina ba zata
yi mana kyau ba....." Ya dan yi galala yana
kallonta cikin murmushi,sannan ya taussa
harshe
ya ce. "A'a,arzikin na kwaso,ba ni hanya na
wuce,amma ke ma ki shaki irinsa". Ta yarfe
hannu ta wuce kujera ta zauna tana tsaki,ya
kara
rage nisan da ke tsakaninsu idanunsa a
kanta,sai
huci ta ke kamar wadda ya kashewa dan fari. Ya
dora kafa kan table yana ci gaba da kare mata
kallo,sannan cikin muryar zolaya ya ce. " Sannu
2 · Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man

Zuciya d kwanji
.37) Ta kada ido ta kawar da kai, ya kuma
zungurota da sassaukar murya. "Ki daina fushi
fatima,sam ba ya yi miki kyau wallahi..... Ina
ganin kamar ba ki saba ba......" Nan da nan ta
kara cika,ta ce. "Ai na ga wadanda fushin ke
yiwa
kyau wadanda babu tantama ka dace da su sun
dace da kai.idan kana na ka muzguna min,idan
ba ka nan ka turo min wakilai,sai dai na yi
mamaki da ba ka hada wannan kwangilar da su
ba,ko kuwa kyashin ba su ba nasu kason kake?
Na ga suna yi min gorin asarar daren farko
alhalin dama can na gaibu ne...... Ya ji kamar
ta
dabawa zuciyarsa adda,wato rashin mutumci su
sadiya suka zo suka yi mata? Ya ji ciwon abin
fiye da duk wani bacin rai da ya riske shi a 'yan
watannin da suka shude,sai dai juriyarsa ta
hanawa fuskarsa bayyanawa,amma muryarsa a
sanyaye ya amsa. "Ni ban turo kowa ba,duk
kuma abin da wani ya yi ra'ayin kansa ne ba
nawa ba......in kuma kishi ne ya sa ki fadar
hakan,to ki tuna.babu wani dalili da zai sa ki yi
kishin matana". Sanyin muryarsa ya sa ta dan

dube shi a tsanake,sannan ta kawar da kai ba
tare da ta tsira da wani abu a cikin kallon nasa
ba. "Ba na bukatar ka yarda da ni,don haka ba
zan yi kokari goge duk wani fenti da zuciyarka
ta
kagi goga min ba. Amma kishin matanka Allah ya
tsare ni,sai dai abin da nake musu ya fi kishi,
domin kuwa ba na kaunarsu,na kuma raina
musu
wayo fiye da yadda kuka raina nawa kai da su.
Ya kara tausasa murya ya ce. "Yanzu don Allah
me ya kawo wannan maganar? Ko don kawai na
yi raddi ki ce na miki rashin arziki?" A kufule
ta
amsa. "Idan ma zaka yi rashin arzikin ai na
shirya masa.... Kai ban ki ba fa a ce a yau na
bar
gidan nan ba, domin DUHUNSA ya fara munan a
idona". Ba tare da wata shakka ba, ya ce. "Ga
shi
kuma kin yi masa shiga sojan badakkare". Ta
yunkuro a birkice ta ce. "Me kake nufi?" Da
karfin
gwiwa ya share tambayar tata, cikin kara
kyautata murya ya ce. "Ya ya kadaici? Na damu

da yawa da kadaicin da nake hasashen kin wuni
cikinsa,sai komai ya gundure ni a office na
matsu
na zama abokin dauke kewa gare ki ko da hakan
na nufin ba zan miki abin burgewa ba". Ta yi
sukuti kirjinta na bugawa tun kafin ta shirya,ta
kalubalance shi. "Wannan dogon zancen naka
yana bukatar tambihi a nawa lissafin,in hali
fito
fili ka wanye min domin in dorar da na fahimce
ka". Ya girgiza kai cikin dariya. "Duk abin da
zan
furta a matsayin tambihi ba zai canza da wanda
kika bukaci na fassara miki ba don ni ne din dai
ba canja ni aka yi ba". Da ta rasa abin ce masa
kawai sai ta nuna masa kofa,ta ce. "Idan ka
gama abin da ya kawo ka, ka fita Allah ya tsahe
mu kalau". Ya dan jima yana nazari,sannan ya
murza yatsu ya juya ya fice yana cewa. "Ga
abincinki nan. ******************
***************
Dare da wuni suka dinga dauki dai dai har suka
samar da lissafin da za a kira kwanaki bakwai
na
kwanan fatima a gidan Abdullahi. Sai dai yadda

al'amura ke faruwa a gidan sun zarce akiyasta
su,musamman a ma'auni irin na
ZUCIYA,zuciyar
ma irin ta fatima da Abdullahi wadanda
dukkansu
abubuwa masu girma ke yiwa kudirinsu.baraz
ana.
Fatima dai tana yiwa nata kallon sauki, domin
gab ta ke da cimma buri idan mai duka ya
rayata
sati daya a gaba,kawu dai ba zai dafata ba
kuma
ba zai la'ance ta ba idan mai afkuwa ta riga ta
afku.,matsalar ta daya shi ne, banjin da aka
samu
tare da Abdullahi,daga wani kungurmin makiyi
zuwa wani mai sadaukar da komai a kanta ko da
kuwa bakin tsanyarsa bai mutu ba. Abdullahi ba
ya yiwa nasa kudirin kallon matsala wadda zata
dada jarumi da kasa,amma a zahirance
jarumtar
tasa ce kawai ta kaga hakan domin shi kadai ne
tilonsa ba shi da mai goyon baya,kuma yana
yunkurin ne a inda ba a san yana yi ba,
hasalima

ba a damu da yunkurin nasa ba, sannan a gefe
ga
ma sa ido da sana'ar korafi da hakkinsu ko
babu.
Cikin sati dayan nan da za a kira abdaullahi
gwauro to zai iya amsawa,domin ko wacce ta
zare wukarta akansa. Don me? Kwanakin fatima
uku wanda shari'a ta ba ta a matsayinrta na
bazawara ba su sauya da kwana dayan da ya
karantu ba. Ba ta cas ba ta as,sai dai Abdullahi
ya shigo mata da abinci daga waje ba na kudi
kadan ba, banda kyayyakin kwadayi iri iri hatta
ruwan sha ba ya ma dosarta da pure water sai
dai na roba, kuma ko baki tayi abin da zasu ci ke
nan. Ranar da sadiya ta karbi girki,washegari
da
safe ta jangwalo masa fitina yana shirin fita
aiki,
ya fita siyowa fatima karin kumallo bayan ya
hantse ke nan da girki sadiya,ya dawo da
abincin
ya kai wa fatima dakinta suka yi dan fadan
nasu
da ya zame masu jiki ya nufi dakinsa ya kara
kintsawa sai jin hayaniyar sadiya ya yi kuma a

bangaren fatima. Haba da sauri ya fito sai yaga
fatima tsaye a barandar kofar dakinta sanye
da
hijab ga kuma sadiya rike da zandameniyar
tsintsiya tana hayaniya. Ya tsaya daga tasa
barandar yana rike da jakar lap top dinsa
fuskarsa
babu yabo babu fallasa ya ce. "Me ya faru?"
Zuciya a kule sadiya ta hau koro masa jawabi.
"Wai ita wannan ba aure ta zo gidan nan ba ne
1 · Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
.38) Ni ban ga wani abu daya da ta ke ko ake
mata wanda zai sanya a kirata matar aure ba".
Bai ko motsa ba ya tari numfashin ta a dake " Oh
wannan tambayar kika kira ta ki yi mata ke
nana?" Cikin nufin tura haushi sadiya ta ce. Allah
ya tsare,kai ma da kake kwanan kallon kwallon
kafa a honey days dinta ba ka ga asarar bata
bakinka ka yi mata wannan tambayar ba bare
ni.... Maganar sharar tsakar gidan na nake
mata,kasan nura ya je auye,kwana dai dai muke
ni da hindatu..... Ita kuma na ga kamar cin abinci
kawai ta zo yi,to mu ba bayin ta ba ne, sai ta

shigo a yi da ita. Ya dinga nazarin
sadiya,idanunsa da fuskarsa na bayyan tarin
bacin rai da suka riska,ya yi gyaran murya ya ce.
"Yau ne za ta fara sharar?" Cikin gadara ta gyada
kai,shi kuma ya ajiye jakarsa ya nufo ta yana
mika hannu. "Ba ni tsintsinyar duk ranar tata
sharar a dinga tuna min ina sharewa. Ta kankame
tsintsiyar tana kallonsa da yanayin takaici,ta ce,
"Abin da ya kamata ka ce mi ke nan?" Ya tsuke
ido ya ce mata. "Dama mun yi ajandar fadin
kamata tsakanina da ke?" Ta yi saroro kunnya
ma rufe ta saboda ta san halin Abdullahi,babu
ruwansa sai ya tsinkata gaban fatima da ta
rungume hannu ta zuba musu ido Sadiya ta yi
dira dira ta ce. "Ka ga ni bana son bakar
magana". Nan ma ya tsare ta da ido,ya ce.
"Amma kika nema?" Kamar zata saki kuka,ta ce,
"To bayanta zaka bi ke nan?" Ya kada kafada
alamar ko in kula,ya ce. "Ke ce za ki fada,tunda
watakila kin yi zaton naki bayan zan bi, sai kuma
aka sami akasin haka..... Ba ni tsintsiyar na ce".
Ta mika masa tana shirin barin wajen,ta ce.
"Lallai aikin shara ya dawo hannunla don kuwa ni
ma bazan kara saka tsintsiya a tsakar gidan nan
ba, kullum sai ka dinga sharewa. Tana direwa ya

amsa. "Ashe? Ga shi kuma ke ba cin abinci kawai
kika zo yi gidan ba,wanne za ki zaba ke nan?
Idan kin zaba sai ki fada min Allah basshi yau na
yi kwannan kallon kwallo da safe na share miki
gida". Takaici ya lullube sadiya ta ma rasa da
kalamar da zata amsa,kawai sai ta wuce ta
barshi tana jinsa ya saukaka murya ya cewa
fatima. "Yi hakuri don Allah,shiga ciki. Ya nade
riga ya share gidan tas inda ya tsallake barandar
sadiya da Hindatu,ya share ta fatima sannan ya
wanke hannu ya fice abinsa. Kwana biyu da suka
biyo baya bai share gida ba,amma yana ware
barandar fatima ya share, ba tare da ya damu da
manya da kanana kalubalen da yake fuskanta
daga sadiya ba kai har ma da Hindatu da a
yanzu ta fara ganin kamar makancewarsa ta yi
yawa duk kuwa da iyakarsa ke nan da dare raba
makwanci suke. Kai sai abin ma ya bar tsakar
gida, kwananta biyar ya lura komai ya yi kura a
falon fatima,sam bai zarge ta da kazanta ba don
yasan ba ta saba ba.Abin da ta sani kawai ta
wanke goma ta tsoma biyar,don haka ranar
lahadi da safe da ya je gaishe ta sai da ya
tabbatar ya goge komai tsab sannan ya yi mata
kyakkyawar shara tana zaune tana

kallonsa,sannan ya fice. Wannan dabi'ar tasa ta
son bauta mata ba tare da neman raddi ba, wani
lokacin ma yana yi suna fada,ta taimaka kwarai
wajen zaba tare fiye da rabin tsatsarsa a zuciyar
fatima. Ta fara bude ido ta kalli kalarsa,kyakkya
wan matashi mai akida,wanda ba ya taba sakaci
ko sarayar da hakki ko damar sa ko a wajen da
yake da kason kaskantar da kai. Sai fadan da
suke yawan yi ya fara birgeta. Ta kuma fara
nazartarsa a matsayin na sabo kawai ba wanda
ake yi a doron kiyayyar da ta ratsa zuciya ba, shi
yasa hankalinta ya kwanta kamar tsumma a
randa,ko yaushe suka yi waya da Alh ta kan
tabbatar masa ai Abdullahi na aiki mai kyau,ya
dauke ta kamar 'yar uwarsa. Matsalarta daya su
sadiya,wanda motsi kadan sai ta kwashi damin
habaici da dalili ko babu,wannan ya kara mata
tsanar su musamman sadiya,wadda ta lura
kamar numfashinta ma neman masifa da gori ne.
Dadinta daya idan Abdullahi na kusa wanda kan
ari rigimar ya yafa ko da kuwa gorin zai fada
kansa. Ranar lahadi girki ya zagayo kanta,a ranar
ne kuma sam ba ta ji duriyar Abdullahi ba tunda
ya yi mata gyaran falo ya fice bai shigo mata
bankwana ba dare duk da ta ji shigowarsa gidan

1 · Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
.39) Ga mamakin sai ta ji ciwon hakan ko
saboda gorin sadiya.to mai gorin rashin
kwanansu a dakin juna ina kuma ya dauke mata
kafa kwata kwata? Da safe da ya shigo kawo
mata karin kumallo bai gabatar mata uzuri ba, ita
ma ba ta nema ba,duk da ba ta so hakan ba
saboda neman tsira da mutumci a idon sadiya a
ragowar kwanakinta a gidan. Daga wannan rana
kuma sai hakan ya zame masa dabi'a,illa da
yamma idan ya dawo ya kan shigo ya kawo mata
abinci kusan kamar akan kaya sai ya fita,ko
fadan ma ba ya saurararta su yi. Kwana sha biyu
girki ya kuma waiwayarta,tana ta dokin. Dawowar
Abdullahi saboda wunin da ta yi da yunwa
saboda ta yi bakin kawayenta. A ranar kuma ba
ta da sha'awar wani abu da ya danganci
gwangwani. Karfe biyar ta ji shigowar abdullahi
gidan,ammahar shidda bai waiwayeta ba, cikin
kuncin kanta da jona ruwa a kettle don ta sha
tea. Tana tsaye tana jirab tafasar ruwan ne
Abdullahi ya cimmata a kicin din cikin kannana
kaya da kamshin turare. Tana ganinsa ta baka

fuska,ko sallamarsa a kicin ta amsa bai damu ba
ya dora. Me kike yi?" Ta share shi, cikin zolaya
ya ce. "Yauwa abinci za ki mana?" Kawai sai ta
kashe butar ta zare cable ta nemi ficewa daga
kicin din,shi kuma ya babbake kofar yana kokarin
su hada ido. "To me ye na fushin don Allah? Ni
ban ga laifin da na yi ba". Ya fada da murya mai
karancin sauti,wadda kuma ana yinta ne masoyin
da aka kadaice. "Wata alfarma na zo nema". Ya
kuma fada yana kara kaskantar da murya. Ta yi
baya rungume da hannu tana kallonsa duk ta
takura,kasancewar ba ta sanye da hijabi, don tun
shigowarta gidan bai taba katarin ganinta haka
ba, hasalima kanta ko kallabi babu sai
kwantaccen bakin gashinta da ta makale da
ribon. Shirunta ya ba shi damar karanto alfarmar.
"Don girman Allah ki zo mu je gadon kaya ki
gaida su hajiya,ba ki ji fadan da malam ya yi min
ba yau akan hakan,har yana ganin ko don babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login