Showing 12001 words to 15000 words out of 36237 words
Chapter 5 - ZUCIYA DA KWANJI 1 NA MAIMUNA IDRIS BELI.pdf
bararmu tare da hikimar kawu ba zai yarda zaki
yi auren kisa wuta da shi ba.... Wai me ya faru?
Ta tsayar da kukanta tana goge hawaye, ta ce.
"To Allah ya takaita". Ya ji kamar ta doki kolin
kansa da tabarya, ya ce. "Ki fada min abin da
ya
yi miki". Ta fari numfashinsa da cewa. " Babu
abun da ya yi min. An daura auren ne yau da
magariba". Shi ma ya ji labarin a wani
hagunce,bakinsa na rawa ya ce. "Ban gane ba?
Sam bai sanar da ni ba,alhalin dazu ma mun yi
waya da shi". Fatima ta hadiye wani kututun
takaici ta ce, "To waya sani ko shi bai sani
ba,don ni ma ba ni da labarin sai bayan daurin
auren,shi yasa na fara tsoron lamarin. Alh ka yi
ganganci da ka dauko dan malamai ka hada ni
da
shi, ina shakkar idan Abdullahi bai zame min
matsala a numfashi na ba". Nan take shi ma
tsoron ya cika shi,ya ce. "Me yasa kika yi
hasashen haka?" Cikin karaji ta ce. "Haba!
Kana
ganin yadda aka yi min aure shigen na lokacin
sahabbai, ranar da kawu ya fara ganinsa. Fa,
washegari da safe. Ya yi kirana ya ce min. " Na
ga Abdullahi jiya, har na ma ba shi aurenki,
saboda. Haka sai ki kiyaye, a yanzu dai dai kike
da. Matar aure,sadaki kawai kike. Jira. Da
shaidu". Yau kuwa suka kawo sadaki aka kulla
auren su I su, sai dazun aka sanar da ni".
"Dakata! Ka daina maganar adalcin nan don
Allah,ka san duk adalci da zai maka bai kai
wanda zai yiwa kansa ba, da me ka shirya
kalubalantar adalcinsa idan ya ki sakina?"
"Kinga
zan kira shi a waya yanzu...." Ya tari
numfashinta ba cikin hayyacin sa ba,ita ma ta
tare shi cikin sheshekar kuka.
Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
.22) "Kar ka kira shi,kasan yana da iyali, zasu
iya. Sauraron abin da za ku tattauna..... Kawai
mu zubawa sarautar Allah idon,ni dai rayuwata
tana cikin wani hali......" Duk suka rude,ita
kuka
Alh kuka,soyayya ke nan ruwan zuma.
*************** ************** Abdullahi
ba shi da
labarin auren, sai washegari ranar da ya doka
sammakon amsa kiran mahaifinsa,wanda ya ce
masa ya biyo kafin ya wuce wajen aiki. Tunda ya
shiga gidan gabansa ke faduwa saboda yadda ya
ga jama'ar gidan na masa wani irin kallo,har
aka
yi masa iso ya isa falon mahaifinsa. Bayan 'yan
gaishe gaishe malam ya ba shi albishir.
Numfashin Alh ya kai gwauro ya kai mari,amma
sai ya hadiye ya ce. "Har yau ban gano inda aka
haifi matsalar da kike mana hasashe ba". Kai
tsaye ta amsa masa. "Ka rayawa ranka hujjar
da
Abdullahi zai gabatarwa mahaifinsa kafin ya
saki
aurena a cikin sati biyu? Labarin da na samu
wajen momi duk 'ya'yan gidan su Abdullahi na
yin abu ne bisa jagorancin mahaufinsu. Sannan
idan ma zai sake ni na tabbatar a matsayinsa
na
dan malamai zai yi min saki ne na sunnah,wato
saki daya wanda yana iya sakina a yau,gobe
mahaifinsa ya sa shi lallai ya mayar da ni, na
mayu fa Alh? Idan ma ba a yi haka ba,ni kuma
in
zo gida na riski tashin hankalin kawa,kila silar
da
zai haramta mana komawa aurenmu ke nan, dul
ba ka yi wannan tunanin ba Alh? Me yasa ba ka
hada ni da wanda ba shi da wata kyakkyawar
nasabar da za a duba ba?". Sai numfashin alh
ya
shiga sassarfa,ya ce. "Duk ban taba wannan
hasashen ba, na fi la'akari da adalcinsa...."
Yana
rufe baki ta amsa. "Dama na kiraka ne don na
sanar da kai jiya ni da iyayenka muka je gidan
prof cikin lamarinsu,ka sanar musu da taushin
harshe, ka yi kokari ka fita hakkinsu ka ji? Ni
kaina na yaba da gidan da ka nemo aurenka irin
su prof a wannan zamanin sun yi karanci".
Abdullahi ya yi shiru kawai,shi kadai yasan abin
da ransa ke zakka a wannan iyali. "Ka je ka
fara
shiri daha yanzu,ni ma bana son a dauki lokaci
ba
ta tare ba,don kar mu zama kananan mutane".
Abdullahi ya jima cikin shiru,sannan a kunyace
ya
ce. "Nan da sati daya ya yi malam?" Malama ya
dan murmusa,ya ce. "Allah ya nuna mana".
Abdullahi ya wuni ne cikin nazarin yadda
rayuwar
aurensa na sati biyu kasance,wai ya ya zai
tunkuri wannan rayuwar ne? Da me zai yi
tunkahon da zuciyarsa ke raya masa a auren
fadimatu? Da wacce hikimar zai tari kalubalen
da
zai dinga shigo masa dalilin auren a cikin gidan
da waje?.
Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
.23) Wannan lissafin ne ya hana shi sukuni a
wunin wannan ranar,har bayan sallar isha'I
inda
ya hallara a gidansa. Girki uwargida sadiya
ne,ita
ke ta dawainiya da shi a katafaren falon inda
ya
langwabe yana bayyana gajiya,yana kishingide
a
kujera idonsa lumshe,kana kallonsa zaka gane
ba
a fata gajiyarsa ta tsaya ba har ma da zuciya.
Sadiya ta dinga nazarinsa,sai ranta ya raya
mata
kawai miskilancin nasa ne ya motsa,domin tun
shigowarsa bai mata maganar da ida an jera
zata
cika layi hudu ba. Duk da haka ba ta yi zuciya ta
bar masa dakinsa ba,sai ta kame ta ci gaba da
kallon talabijin. Dai dai wannan lopkacin kiran
Alh
ya shigo wayarsa,ya daga wayar sannan ya
gyara
kishingida,a kasaice ya yi sallama. Kawai sai Alh
ya fara da tuhumarsa. "Sashe har an daura
auren
tun jiya,amma jiya da na kiraka ba ka sanar da
ni
ba?" Kai tsaye Abdullahi ya amsa masa "Haka
ne,
an daura tun jiya,sai dai ni ma ba ni da labarin
sai yau da safe malam ya yi kirana ya ce da ni
an daura min aure". Hantar sadiya ta yi
masifar
kadawa,ta dora masa ido babu ko kakkautawa
tana kallonsa yana yamutsa fuska,yana
sauraron
kashedin da alh ke masa. "To sai ka yi kokarin
cika alkwari,kuma in son ka ci gaba da dauke
kafa a wajenta tunda an yi mai wuyar,kar ka
sake
ka taba min mata ka ji ko?" A takaice
Abdullahi
ya amsa,"To". Alh ya ce masa. "Yaushe ne
tariyar?" Abdullahi ya mayar masa da amsa.
"Na
sanar da malam nan da sati daya nake son ta
tare,ya kuma amince min, don haka zan yi
kokarin
ganinta a gobe..... Ka dai tsumaye ni nan da
sati
uku". Jikin Alh a sanyaye ya yi masa sallama ya
ajiye wayar,shi ma ya fara shan jinin jikinsa
cikin
lamari,ya fara jiyo kashin gaskiya a cikin
hasshen
fatima,me yasa komai sai da malam za a yi?
Abdullahi na ajiye waya sai ya lumshe ido don
haka sadiya ta yi mugun kuluwa,a kuntace ta
ce.
"Abu Turab wa aka daurawa aure?" Ya yi
firgigit
ya tashi zaune kamar wanda ya ko daga bacci ya
ce. "Oh yi hakuri,dazu na yi ta kiran wayarki na
ji
ta a kashe,zan sanar da ke an ba ni aure har an
daura shi a jiya,yau malam ke sanar da ni".
Maganar da a zane ba ta fi sadara uku ba,
amma
girmanta ya zarce na gwaron dutse a
kwakwalwar
sadiya,sai ta rasa abin da zata ce, kallonsa
kawai
ta ke kirjinta na bugawa,dakin na zagayawa da
ita. Ba tare da ya direta ba ta tilastawa kanta
yin
magana bayan da numfashin ta ma ya karbi
nasa
aikin na tafiya cikin sassarfa. "Na yi nadamar
aurenka Abu Turab,babu wani alkhairi a ciki
aurenka wallahi...." Ya tashi zaune a
hanzarce,ya
kuma ware ido yana kallonta sosai. Ba ya
mamakin fitowa wadannan kalaman daga
bakinta,don ya yarda rashin arzikin sadiya ya
wuce nan, sai dai ya kasa sabawa,sam ya tsani
rainin hankali.sai dai a yaunasihar malam ta yi
masa birki,kawai sai ya sanya ido yana kallonta
har ta sami damar dorawa. "Ai ko na mamajo
ne
kai iyaka ke nan. Cikin shekaru hudu aure
uku,ba
za a hada biyar ba sai ka rufe kofa,haka kawai
da
kuruciyata ka tara min kishiyoyi? Ni ban haifa
na
kana auro 'ya'yan wasu suna neman jaza min
ciwon zuciya,ayi magana ka ce malam ya yi
maka aure kamar wani dan akuya,idan haka ne
gaba daya ma auren malantar ba shi da wani
amfani". Har yanzu ya kasa tanka mata,idonsa
dai na kallonta kai tsaye,fuskarsa kuma ta ki
byar
da wani karatu da zai sa a fahimci matakin da
zuciyarsa ta dauka,watakila hakan ne ya sanya
sadiya mikewa ta ci gaba da zazzaga masifa. "Ni
wallahi idan babu hali sai dai ka bani tikiti na
daware.Ba zan yi ta zaman hakuri da kai babu
tsatso ba, amma kai kullum idonka akan mata,
ka
tara mu ridi ridi babu wani abun arziki ko kai
har
yau ba ka yarda kai ne ba ka haihuwa ba, ka ke
lilon tara mata?" A wannan karon sai ya
tanka,kuma cikin murmushi wanda ke bayyana
walwalar zuci. "Ya ya za a yi na ki yarda alhalin
na riga na gada? Kin san 'ya'ya talatin din. Da
ke
cikin gidanmu a ruwa iyayenmu mata suka
sha?"
Sai ta kara butsarewa cikin tsabar fitsara,ta ce.
"To idan ma ba ka gada ba Abu Turab,babu
shakka an fitar da zakka,kuma babu ta inda ido
ya mutu kwalli ya tono shi". Shi ma tana rufe
baki ya amsa cikin halin ko'in kula da son tura
haushi. "Haihuwar kawai na rasa,amma Allah
bai
hana ni komai ba bayan ta,ciki har da ba ni
damar na auro na kuma aurowa,ko zan dace da
mai tsarkin zuciyar da zata karbe ni
abakararena,ba tare da ta tsangwame ni ko ta
tsangwami kanta ba. Kinga sai kiji mu luf in
yaso
dangi sa haifar mana'ya 'yan da zasu ji
kanmu.
Maganar ta yi masifar bakantawa sadiya rai,
musamman da ta tuno lokacib da zai auro
hindatu irin wannan tabarar ta dinga bare
masa,
amma bai taba damuwa ba,sai ya dinga nuna
mata shi kansa ba da son ransa zai yi auren ba,
don da ba zai iya yiwa malam musu ba ne kawai.
To wannan ta kayatar da zuciyarsa ke nan da
yake neman cin fuskata akan aurenta? Amsar
wannan tambayar ta fara kada hantarta tun
ma
kafin ta santa,ya ya amsar zata samu? Abu
Turab ba shi da kirki idan bai ga dama
ba,soyayya ba ta hana shi rashin mutuncinsa
idan ya motso. To da wanne KWANJIN zata
kubuta daga fifita amaryarsa da zai iya yi idan
ya
fi kaunar amaryar a kanta?24) Gaba daya tashin hankali da rashin hakuri
suka bayyana a fuskarta,sai huci take kamar in
ta
bude baki za aga hayaki,idonta a kansa,wannan
yasa ya yi saurin yin fuska bayan ya dube ta
sakarce,idonsa cikin nata,ya ce. "Kuma ya ishe
ki
haka! Kishi ba hauka ba ne,kar ki nemi ki zage
ni"
Bai ba ta damar magana ba,ya daga wayarsa ya
kira Hindatu,yana ajiye wa sadiya ta sauke
fushinta cikin debe kauna. "Wai Abu Turab idan
na zage ka me zaka yi? Ya hadiye dariyar da ta
cika masa ciki. "Kin fi ni sani. Billahillazi idan
amaryar ta zo sai in nuna miki iyakarki,in dinga
hada mata kwananta da naki in ga abin da zaki
yi, za ki ce in fita in bar miki gidanki ne tunda
ke
kike aure na? Ba ta sami bakin magana ba,sai
ga
Hindatu ta yi sallama ta shigo. Ta same su a
hargitse, sadiya a tsaye tana cika da batsewa,
Abu Turab a kwance ya hada girar sama da ta
kasa. Tana neman gurin zama ya tare ta. "A'a
kar ki zauna! Mike ke ma idan kina da wandon
taki rashin kunyar ki juye min.Aure aka daura
min
jiya,ma'ana kishiya na yi muku". Duk da
maganar
ta caki zuciyar Hindatu matuka,amma sai ta
hadiye kasancewarta mai dabarar boye fushi da
bacin rai,muryarta a sake ta ce. "Da gaske?" Ya
saci kallon sadiya,ya kara murde fuska ya ce.
"Akan me zan muku karya? Wallahi da gaske
ne,
kuma cikin satin nan zata tare". Hindatu jima
tana dubansa,tana kuma satar kallon sadiya,ko
zata ji zafin aurensa tana sa ran sanyinsa
saboda
sadiya,domin mace ce mara kaunar zaman
lafiya,Allah kuma ya ara mata dama tauraron
sadiyar ya fi nata haske a idon Abu Turab,duk
da
munanan halayenta,ke nan Hindatu zata yi
farin
ciki da auren Abu Turab musamman idan
amaryar
zata danne tasirin sadiya. Da murmushin da ya
ratsa har zuci,hindatu ta dube shi ta ce. "To
don
me zan juye maka kwandom rashin
kunya,alhalin
dama nasan kana da sauran kofofin? Ka auro
biyu ma ni yanzu na shirya,abin da ba a kaina a
su zauna ba?" Haba! Sai sadiya ta kara tunzura
ta ga yarfe kawai Hindatu ta yi mata. Ta yo
kanm Hindatu da bala'I. "Abin da ya fi haka
ma
kina da lokacin ki fada tunda a dure kika
ganshi,dama kin san da wata a ciki kika shigo
saboda haka dole wasu su biyo bayanki. Ni ce
nasan darajarsa a sabonsa ko mijin mace dubu
ne ba hudu ba,auren soyayya ai ba karya ba
ne".
Sai da ta jima da sauke numfashi sannan
Hindatu
ta mike tana amsa mata.. "Allah ya yi mana
tsari
da soyayyar fatar baki,salon soyayyar ke nan
kike
juye masa kwandon rashin kunya? Ni da ba na
sonsa yake tsammanin mun shula irinta a
gidanmu? To Abu Turab ba mu da gonarta, aure
kuma Allah ya sanya alheri,Allah ya sa badi war
haka ka cike gurbi" Babu alamun wasa da shakka
a fuskarsa da muryarsa,ya amsa. Ba amin ba,ai
wannan matsayin mace biyu zata shigo,ina
fatan
daga kanta in kulle kofa,babu shiga babu shiga
babu fita Babu alamun wasa da shakka a
fuskarsa da muryarsa,ya amsa. Ba amin ba,ai
wannan matsayin mace biyu zata shigo,ina
fatan
daga kanta in kulle kofa,babu shiga babu fita.
Hindatu kanta ta ji ciwon maganarsa,amma
nan
da nan ta watsa ta kan sadiya. "A'a wannan
sai
dai ka fadawa mai auren saoyayya,ni me amsa
sunan abin da ahnnunka na dama ya rika me
zan
dorar? Duk da ka watsa mata kasa a ido ba ka
ce ita ke amsa matsayin mace biyu ba". Ba ta
jira cewarsa ba bare ta saurari hayaniyar sadiya
ta fice daga falon,shi ma ya mike ya kule a
bedroom har da murza key yana sauraron gorin
da sadiya ke lika masa iri iri har da na sharri
sannan ta koma kan hindatu.
Hafsat
Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
25) Washe garin
ranar sai a office ya karya,don sadiya ta dauki
zafi sosai da shi,har ya bar gidan bai ga keyarta
ba,bayan ya gaji da bugun kofarta ki budewa.
Sai
wajen sha daya ya daure ya kira wayar
fatima,sau biyu tana katsewa yana sake
kira,sai
ana ukun ta daga bayan ta kusa yankewa. Ba ta
ce masa kala ba,shi ma sai ya shiga numfashin
jin isa,sannan murya a bace ya ce. "Zan shigo
anjim,ko kina ganin na zamana kawai?" Ta sha
kamshi da kyau,kafin a kasaice ta ce. "Don me
zaka yi zaman naka?" Tana rufe baki ya amsa
mata. "Don kar na zo mu aikatawa juna ba dai
dai ba,kina satar hararata,ni ma haka. Idan ta
kure ki yi min tsaki....mts! Idan zuwan nawa ba
shi da. Wani muhimmanci na share kawai...."
Ranta ya yi masifar baci,ita kanta kuma ta rasa
abin da ya bata maya ran.tsakin da ya yi mata,
ko ma'anar korafinsa,ko kuma rashin ba ta
girmanda kima? Ya kamata duk ukun,su bata
mata rai, amma ta fi jin ciwon rashin ba ta
kimar,tasan ko makiynta na sonm kallon
kyakkyawar fuskarta ko da tana kunshe da abin
da ya fi harara,amma me yasa kyawunta ba ya
dada Abdullahi a kasa? Dole ta tare wadannan
kalubale ga zuciya ta hadiye,murya a bace
kamar
dole ta ce. "Na fika kin zuwan naka, don akwai
ciwo cikin kaskantar da kai na saurare ka.... Sai
dai kama iya zuwa domin zuwan naka yana
daga
cikin biyan hakkin da muka dauke ka akai". Ya
dan yi jim, tunkunna ya amsata. "To idan haka
ne
zan dauki hutu akan zuwan,zan komo bakin aiki
ranar da akika tare...." Ta yi saurin tare shi a
tunzure kamar tana a gabansa. "Za ka samar
da
gibi ke nan... A halin yanzi jama'ar gidan nan
sun
damu da rashin zuwanka.... Za ka zo ne domin
su ba don ni ba, don ni babu abin da zai amfane
ni a zuwanka.... Kashedi na karshe,idan ka zo
bama son takura,kar ka yi min irin zaman
kunatar
da ka yi min zuwanka na farko...." Shi ma ya
tare
ta kamar sike. "Shi yasa ai na ce na yi zamana
kar na zo,ki ga bakar fuskata". Daga nan ne ta
gane zafinta ba zai ba ta ladabinsa ba, sai ta
dan
sassauta murya ta ce. "Idan ba zaka yi min
zaman kunatar ba ke nan?" Ya dan ja fasali
lafin
ya tanka ba tare da shakka ba. "Kwarai da
agske,ai ban ga dalilin da zai sa ki dinga daga
min hankali ba.ban taba yi miki kallon wata
mace
da don va rabe ta zan ji abin da kike kokarin yi
min katanga da shi ba,watakila da na yi miki
kallon cikkakiyar mace ba zan karbi wannan
kwangilar ba, don na na munafunci...." Tun da
fatima ta ke ba a taba fada mata magana mai
munin wannan ba, abdullahi ya ci fuskarta
matuka! Ya kuma kara sanyawa zuciyarta
kullaci
game da shi.To me ta rasa? Tambayar da
yakanmata ta yi masa ke nan, amma shakkar
amsar da zai iya ba ta ta yi mata birki. Ta
hadiye
yawun takaici, a kausashe ta ce, "Ido kayan
wari
ko? Inji makaho, Na tabbatar idan na rantse ba
zan yi kaffara ba,ba ka ajiye kyakkyawar mace
kamar ni a gidanka ba...." ya tari numfashin ta
a
dake. "Ai ba a nan ta keba, wai an danne
bodari a
ka". Ta yi dif wasu kwalla masu zafi suka fara
cika mata ido,ta rasa ma tunanin da zata yi
akan
wannan mutum wanda wulakanci ya zagayewa
numfashin Dukkan KWANJINTA ba shi da tsiri a
muhallansa.kyauta, kudinta da iya jan zaren
mulkinta ya wasa kefa allamar su duka sai ya
hada da ta mutuncinta da fuskarta. Kuka ya
dan
fara fixgarta,ta kashe wayar bayan ta ce masa.
"Abdul ba