Showing 33001 words to 36000 words out of 36237 words
Chapter 12 - ZUCIYA DA KWANJI 1 NA MAIMUNA IDRIS BELI.pdf
ke, sai ta gaza barshi ya dauki mataki,ta
yi tarangahumar tsoma baki. "Toh! Au kare ne
shi
da yake miki iju? Kin ga kuwa ko ni da nake da
kason abinci kawain.uke kafada da kwallon
kafa.... Ba zan ce ....." Da sauri Abdullahi yasa
hannu ya rufe bakinta,sannan ya dora yatsansa
akan labbansa ya amabata "hush!" Nan take ta
karbi umarnin sa cike da shakkarsa har ya
fahinci
hakan,don haka ya dora don ta rage mata
tsoron
cikin zuciyarta. "Kar ki kuma yarda wannan
maganar ta hada ki da wani a cikin gidan nan,ki
barsu kawai su shafta iyakar fahimtarsu su
fassara.... Ba na son ki kara musawa kowa kinji?
Da abinci kawai kika tsira ranar girkinki duk da
haka muna zaune lafiya babu wanda yasan
cikinmu,kin gane?" Ta kada kai,kawai,sannan
ya
juya ga sadiya,ya ce. "Kina da lokacin da zan ci
gaba da yi miki ihun ko na yi gaba. A tunzure ta
ce masa. "Ba bi da shi" Kai tsaye ya yafici
fatima
suka fice, sadiya kuma na yi musu Allaj ya isan
kebewar da suke a kwananta. Suna fita fatima
ta
turje ta rungume hannu, ta ce, "Abdul,idan
waccan ma kansa ba ka isa da ita ba kar ka fara
kai ni wajenta wulakanta ni,don wannan
masifar
tasu tana daya daga cikin abin da yasa na kagu
na bar gidan nan
Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
53) Dama hindatu mace ce mai kara da boye
bacin rai, don haka da ladabinta sosai ta gaishe
da su kawu,yayin da abdullahi ya bayar da
uzurin
sadiya na wanka. Kawu ya hadu ya dinga yi
musu nasiha. "Don Allah ku rike amanar
junanku,babu wata rayuwa me dorewa bare
wayonka ya fissheka,an san dai zama ko da da
iyye ne ana sabawa,amma fahimtar juna ke
hana
kullaci. To ku janye kullaci a cikin zamanku na
tabbatar zaku ci ribar hakan a gaba ko bayan
kasa ta rufe idanunwanku,sab oda kun bar
iyalanku masu mutunci da zumunci". Hakika
hindatu ta ji dadi maganganun prof wanda ta
tabbatar abin da fatima ta ke kawai albasa ce ba
ta yi halin ruwa ba,kuma gatan da sadiya ta
rasa
ke nan,don kulliyar danginta tayata kishi
suke,sau
nawauwarta ke zuwa hindatu na gaishe ta tana
sharewa? Da hindatu ta ke sallama da su,sai
prof
ya mika mata dubu biyar ya ce ta raba da
yar'uwarta. Ta yi godiya sosai,da suka tashi
tafiya sai ga ta da turaren wutanta katuwar
kwalba ta kawowa momi dama sana'arta ke nan.
Fatima da Abdullahi suka yi musu rakiya har
wajen mota kafin su shiga motar ne Abdullahi
ya
dinga nuna son su kebe da kawu,kawu na
fahimtar hakan ya cewa momi. "Wai kuwa kin
leka dakin nata? Kar ta ce mun yi mata "yan
goranci,ku je momi suka tafi. Cikin tsananin
ladabi Abdullahi ya ce. "Kawu don Allah kar a ba
wa fatima waya, babu abin da ya sami wayoyinta
ni na kwashe su, ko cikin dabara ne a sanar da
'yan uwanta kar su zo ta sanya su su siyo mata
waya,ko ta karbi tasu ta yi amafani da ita. A
taimaka min da wannan kawu". Prof ya yi
kasake
cikin bugun zuciya,ya ce. "Wani abin ta yi ko?"
Da sauri Abdullahi ya girgiza kai, amma bai ce
komai ba. Kawu ya kara shiru sannan ya kada
kai. "Nasan ba za a rasa dalili ba, sai dai ba zan
matsa maka inji ba, hasalima zan yaba maka a
matsayinka na namiji mai boye sirrin iyali,kuma
ina tabbatar maka zan ba ka goyon baya don in
zaton alkhairi tare da kai. Ban taba ganin
mutumin da fatima ta ke shakka bayan ni
kamar
kai ba, saboda haka zaka iya tarbiyyarta don ba
ta lankwasuwa ga mutumin da ta rainawa
wayo.zan karantawa 'yan uwanta zuwa gidan
nan,kai ma ka sanya ido ga kawayenta ka bi
shawarar momi,duk wadda tarbiyyarta ba ta yi
maka ba runtse ido ka hanata zuwar maka
gida,ka fahimci ni? Cike da farin ciki Abdullahi
ya
dinga yiwa kawu godiya har momi ta fito suka
kara sallama da su suka tafi. Fatima ta yi saurin
shigewa cikin gida ba tare da ta jira shi sun jeru
kamar yadda suka fito ba. Shi ma hakan sai ya
yi
masa dadi don yana fargabar kebewar su ta hau
yi masa maganar tafiya. Yana shiga ya zira
takalminsa ya fice, bai kara waiwayar gidan ba
sai da sha biyun dare ta gota kowa ya kai
bacci,kai daya idan ka dauke fatima da
duniyar ta
yi mata kunci,tana jinsa ya shige dakinsa ya
garkame kofa. Sai bayan sallar asuba ya nemi
dakin hindatu domin ya wanke mata zuciya
tunda
ita ke da girki. Hindatu ta yi hakuri ne kawai
don
ta gane lallai akwai tarin abubuwa da ke damun
zuciyarsa a cikin lamarin fatima,sannan ta
tabbatar borenta ba zai amfane ta da komai
ba,kamar yadda bai amfanin sadiya ba, wadda
yake ganin KWALLIN goshinta a da,eh a da
mana
don a yanzu yankewa abdullahi hukuncin inda
zuciyarsa ta karkata abu ne mai wahala.idan an
zuciyarsa ta karkata abu ne mai wahala.idan an
hutar da tunani ne ma za a ce akan fatima
karka
ta fada,wadda a yanzu karkarin dai ace ba ya
kwana a dakinta,ko kuma ita ba ta kwanan nasa
dakin,amma duk wata dawainiya da shakka
wadda ke tasowa karkashin soyayyarsa ita ta
mallake su. Sai ta nuna masa ba ta damu ba,
suka yi harkokin arzikinsu tare har ya shirya
fita,kafin ya sanya kayansa ya dubeta a
nuste,ya
ce. "Don Allah hindau ki yi min afuwa na je na
nemarwa yarinyar can abinci". Ta jima tana
dubansa,
Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
"54)Abu Turab don Allah wannan wanne irin
zama ne? Shin kasaitarta ce tasa ba zata shiga
kicin ta yi girki ba,ko kuma don ba ta iya ba,
saboda ta fito gidan hutu ko kuma tsabar
soyayyarta ce ta saya ba ka so ta wahala?" Kai
tsaye ya amsa mata. "Duk cikin abin da kika
fada
babu dalilin Hindatu,ki yarda dai a ranki akwai
dalilin sai dai kar ki kwadaitar da zuciyarki
sani,domin sirrinmu ne ni da ita,fahimtar
junan da
ke tsakanina da ke ya sa na nemi ki goyi
bayana.bana son kananan magangnun da suke
tasowa a tsakaninmu dalilin zuwan fatima,kin
sani hindatu ba a sanyawa namij karfi wajen
mallakar soyayyarsa,amma ana iya mallaka ta
hanyar kyautatawa da biyayya,shaidar da na yi
miki ke nan, don Allah Hindatu kar ki canja,ki
tayani neman abin da nake so sai ki ga Allah ya
dora ki a kaina na yi miki adalci ko raina bai so
ba. Ki daina bin yamma kina shan kida tunda ba
ki san abin da ke fake ba, wai har ku dinga fitar
da sirrina hindatu.ina amfanin kawayenki su zo
ki
fada musu zaman da nake da matata, wace
ribar
kika samu a hakan? Babu ma wanda ya fi
bakanta min irin sanar da muftahu da kuka yi,
raina ya yi mugun baci wallahi don dai kawai na
shanye ne. Ke kanki kuma kin san wannan ba
dabi'ar mace ta gari ba ce, ni ina saka ku kuna
warwara,idan kuka korar min ita da wanne idon
za ku dube ni? Ba zan munafubce ki ba
Hindatu,fatima tana da muhimmanci a
rayuwata".
Hindatu ta ji ciwon maganarsa ta karshe,sai dai
laifinta da ya fara gabatarwa ya danne shi,don
haka fuskarta ta nuna nadama.A sanyaye ta
ce.
"Ka yi hakuri da yarda Allah ba za a kuma ba".
Suka yi shiru na wani lokaci,sannan ta kuma
dagowa ta dube shi. "To ka je mana,sai ka yi
gaggawa kar ka makara,ga shi yau monday". Ya
yi firgigit ya tashi yana cewa. "Haka ne,na gode
da fahimtar da kika yi min". Ya fice.ta bishi da
kallo tana maimaita wasu kalamansa a fili.
.......Ki tayini neman abin da nake so.... Idan
kika
korar min ita da wanne ido zaku dube ni.........?
Fatima na da mahimmanci a rayuwata'.
Wadannan kalaman sun isa awon iyakar zurfin
da
abu turab ya yi a kaunar fatima,don duk
kaunarsa
ga sadiya bai taba fitowa a gabanta ya fada
mata
ba..... To yanzu ina mafita? Tambayar da ta
yiwa
kanta ke nan. Wanda ba ta yi dogon nazari ba ta
shawarci kanta rungumar hakuri da juriya.
Abdullahi ya jima a kofar fatima yana addu'a
kafin ya fara kwankwasawa.ba a jima ba ta zo
ta
bude,gabansa ya kara faduwa da ya ganta kace
kace da hawaye. A dan tsorace ya kawar da kai
kamar bai gani ba ya ce. "Kin tashi lafiya?" Ta
yi
gum da bakinta, sai ya canja fuska ya ce.
"Lafiyaki kuwa?" A tunzure ta ce masa. "Ni ban
sani ba. Ya sassauta murya ya ce. "Allah ya ba ki
hakuri,ban hanya na wuce . Me kike so na girka
miki?" Ta ki ba shi hanyar,sannan ta kara bata
rai,(a ce. "Ba na bukatar komai,kasan
matsalata,
saboda haka ita ya kamata ka magance min ba
wai ka yi ta faman tura min abin ci ba. Ya dube
ta da kyau,ya ce. "Na zaci mun rufe wannan
maganara,bana ce ki tsumaye ni zuwa gobe
ba....? Ta tari numfashinsa da masifa. "Na ce
maka ban amince ba..." Shi ma ya tareta da
kayshin murya. "Idan kina da abin yi sai ki yi....
Abu daya zan cire miki a ciki shi ne, sanya kafa
ki
ce za ki fita daga gidan nan,yaji ko wata
sabgar,kina faukan wannan matakin ni ma zan
dauki nawa wanda na tabbatar ba zai miki dadi
ba, wato zantar da kawu.... Na ce ki ba ni gobe
kin ishe ni da masifa haba!" Kamar turata ya yi
ta
kara ruwan masifar "Ka tafi inda ranka da
taskar
labarai ka fada Abdul..... Bisa wacce hujjar
zaka
ishe ni da naka iya yin..... Dama mun yi da kai
zaka dinga kafe ni da wa"azi?. Ya amsa mata
kai
tsaye cikin daure fuska "Aure ne hujjar!
Wanda na
tabbata ko giya kika kurba kin san ba a kullo shi
da wasa kamar yadda lissafinku ya wallafa ke
da
wancan mutumin.... Ki ni ni a hankali fatima
kin
ganni nan? Ba ni da dadi ni ma". Bai jira
cewarta
ba ya ja kofar da karfi ya barta tsaye a gurin
dakin na juya mata,so ta ke ta yarda abin da
ke
faruwa a mafarki ne, amma ta gane yaudarar
kai
ne.... Wannan kalmar ta yi dai dai a wanne
nau'in
cikin masifa?. To amma ba ta son tabbatar da
ita
da nata saurin yanke kaunar bari ta yi
tsumayinsa zuwa goben tunda ya zama
kadangaren bakin tulu...... Hindatu ta gansshi
ya
dawo akan kari,kuma a birkice. Da kirkinta tare
shi, tana dannar kirjinsa ta ce. "Anya ba zaka
bi
manganar muftahuba ku kai matsalarku gu
manya?" Ya yi murmushin karfin hali, ya ce.
"Babu inda zamu Hindu,wannan yakina ne ni
kadai, don ni kadai na zunguro sama da kara,
yakamata na ji a jikina ni kadai,ke dai kawai ki
tayani da addu'a". "Kana son fatima da
yawa".
Ta fada don zolaya da bugun ciki,amma bai
tanka
ba sai ya yi mata murmushi kawai. Ta kuma
kallonsa da wutsiyar ido,ta ce. "Wannan karon
malam ya yi abin a zo a gani a zabin da yake
maka". A nan ta samu ya amsa. "Dama can
malam ba ya zabin banza". Ta ce,"haka ne, sai
dai a samu akasi shi ya yi zabi kalmar nan ta
babu ruwan so da wayo ta yi aikinta". Ya bude
ido sosai ya dubeta,ya ce. "Ke duk fa lauyarki
ba
zaki sa ni fadar abin da zan daure kaina da
kaina
ba". Kawai sai ta tuntsure da dariya,shi ma ya
tayata,sai ya ji zuciyursa tana sanyi,wato ya
rage
'yan adawa a cikin gida,Hindatu ta bi ko ba ta
taimaka da fatar baki da KWANJINTA ba, zata
taimaka ta fannin kin tuzura masa fatima.
Amma
da ya tuno kasha di da jaye jayen bala'in da
Alh
ya yi masa a waya bayan ya kira shi da bakuwar
lamba. Ya kadu da kashedin da tsoratarwar
Alh.watsar da tsaoro bayan kaunar fatima ta
yunkura ta nuna nata fin karfin. "Hum, Allah
ka
zamo gatana". Ya furta a fili,yayin da cikin
sauri
Hindatu ta dago ta sanya masa ido,shi ma sai
ya
yi tsuru yana kallonta,alamar hankalinsa ba ya
tare da ita, ko kuma fargabar Allah ya sa bai
furta abin da zuciyarsa ke karantawa ba.
Washegari ranar bai shigo gida da wuri ba, sai
daba da magarinba. A gurguje ya yi wanka ya
fice masallaci
2 · Like · React · Report · May 14, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
55) .bayan sallar isha sai ya kasa barin
masallacin,ya yi ta kaiwa Allah bukatunsa har
da
hawaye,tsawon lokacin sannan ya hakura ya bar
masallacin,ya siyo musu kaya motsa baki,sannan
ya nufi gida A sanyaye yake komai,yamikawa
sadiya da Hindatu nasu,sannan ya koma
dakinsa
ya shiryo kayan baccinsa set uku cikin jaka,da
kayan sawa set biyar,kannan kaya uku,manya
biyu,da duk wani abu da yasan zai bukata cikin
kwanaki biyun da zai yi a dakin fatima,ya hada
da
wasu makudan kudi da cek. Ya rufo dakinsa ya
ja
jakar zuwa nata dakin bai samu kofar a rufe
ba,
don haka ba ya bukatar kwakwasawa,sai kawai
ya shiga ya yi addu'a,sannan ya murza key.
Tun
daga nan gaban fatima da ke zaune tana
kallonsa
ya fadi. Amma fuskarta ba ta nuna razana ba,
kawai sai ta kawar da kai ta zubawa talabijin
ido.
Shi ma bai dube ta ba,ya wuce kai tsaye dakin
baccin da ya fahimci ta fi mu'amala da shi. Ya
jima a tsakiyar dakin numfashisa na neman
shidewa saboda kayatuwar dakin da ni'imar da
ya
hada da kamshi mai dadi da sanyi mai tarar da
zuciya,amma ga ma'abociyarsa cikin kunci da
jazawa kai tashin hankali. Ya jima zaune gefen
gado ba tare da ya yanke shawarar ta inda ma
zai fara abin da ya kwaso ba, a karshe ya
hakura
ya dora jakarsa kan chest of drawer ya kashe
wayoyinsa ya zira su a jakar sannan ya fito. Nan
ma bai dubeta ba ya wuce kicin sai ita ke binsa
da satar kallo kawai. Ya zubo gasassun 'yan
shilan da ya shigo da shi a faranti,ya kawo
fresh
milk,lemo da ruwa yana komai cikin gumin
fargabar tashin hankali duk kuwa da sanyin da
ke
ratsa dakin.Don haka ya zabi kum yin wani
wankan,wanda ba ya nufin komai a wajen
fatima
sai jan lokaci. Ya koma dakinta ya canja wasu
kayan,ya yi amfani da turarenta,sannan ya
fito
falon dauke da envelop Ganinsa da wannan
envelop din wani matsanancin farin ciki ya daki
zuciyarta har sai da fuskarta ta nuna,sai nasa
kishin ya motsa, sai dai babu yadda zai yi, dole
ya hadiye shi ya share. Ya ajiye envelop din kan
kujera ya zauna gaban abincin anan ya dubeta
kai tsaye. "Zo mu ci abinci". Ta kawar da kai
tana yamustsa fuska. "Ni fa tuni na fada
maka,ba
abinci ne a gabana ba". Tana rufe baki ya amsa
cikin dakewa. "Ashe ke nan zamu daga
tattaunawanmu zuwa wani lokaci,domin abin da
na zo da shi yana bukatar nutsuwarki da
koshinki... Ko zamu daga zuwa gobe? Ni dai
nasan akwai yunwa a tare da ke, har ma kin
dan
rame fa! Bana bukatar mutanen gidanku su
ganki
darama". Ya zuba mata ido kawai sai ta
yunkura
ta tashi zaune tana gyara riga.ta yi fuska ta ce.
"Sai ka zubo min nawa,don babu dalilin da zai
sa
ka ce sai na ci abinci da kai". Ya ce,"na
sani,amma tunda babu dalilin da zai hana mu ci
tare,ina laifi don mun ci? Ranar yau ta zame
mana ranar tarihi mana fadima? Zo mu ci don
Allah ki yi hakuri da laifin da kike jin na yi
miki,in
Allah ya so zai takaita shi". Sai ta kasa
tankwabe
magiyar tasa, musamman da yake yayi mata
magana cikin taushin harshe.Amma tana ji a
ranta shakkarsa ce kawai ke dawainiya da
ita,kamar ba ta son bacin ransa. Ta tashi ta
shiga bandaki ta wanko hannu da baki,sannan
ta
zo ta zauna gabansa ta tankwashe kafafunta
suka fara ci. Kamar dama don ita ya tashi cin
abincin,ita ya dinga yiwa hidimar zarewa kashi
yana tura mata tsokar gabanta abin da ya kara
faranta ransa ba ta takwabe kokarinsa har sai
da
ta gamsu sannan ya zuba mata madara ya mika
mata, ajiye kofin ta dauki ayaba guda ta koma
gefe tana cinyewa ta tashi zuwa kicin ta koma
gefe tana cinyewa ta tashi zuwa kicin ta wanko
baki da hannu,sannan ta dawo ta zauna tana
tsumayinsa,wanda sai sannan ya mayar da
hankalin yana cin nasa. Ya dinga yanga kamar
ba
ya so har dai ya kai ga kammalawa ya kwashe
kwanukan ya wanke nasa bakin,sannan ya cin
mata, inda kai tsaye ya zarce ya dauki envelop
din ya mika mata,bai jira ta ce wani abu ba ya
wuce daki ya dauko kudin da ya zubo a jaka.
Kafin ya fito ta farke envelop din ta zaro
takardar
da maimakon takardae saki uku sai ta tarar da
taller da copy na cek din kudin na 700,000.
Wanda cikin sakanni ta gane dangantakar cek
din
da Alh. Taller ma ta shigar da wannan kudin
wani
asusun ne. Fiye da wasu sakanni masu dama
zuciyarya ta tsaya da aiki cak! (0) ke nan,ta ki
gana (+) ta ki baya(-),don haka ta kasa dorar
da
komai bare ta yi tunanin baya.tana tsaye da
takardu a hannu kamar mutum mutumi idonta
akan kofar dakin da Abdullahi ya shiga,har
Abdullahi ya fito,sannan zuciyar tata ta fara
harbawa harta aikawa kwanyarta sakon neman
dalili ita kuma ta yiwa harshenta umarnin
furtawa. "Ina bukatar karin bayani Abdul". Ya
yi
fuska ya ajiye kudin kusa da kujerar da ta ke
zaune a hannunta,sannan ya dauki remote ya
nemi guri ya zauna,ba tare da ya dubeta ba ya
ce. "Kudin da Alh ya ba ni ne nake nufin dawo
muku da shi don in son na mallaki 'yancina da
kudin ya sarayar, hakan zai ba ni damar ci gaba
da yiwa Allah biyayyar da kuke son gotar da
ni,ya
kuma ba ni damar zama da abin da raina ke so
ba tare da an