Showing 24001 words to 27000 words out of 44270 words
yiwa Ma'eesha magana saida ko
inuwarta babu tun sanda ya bar gabanta ta fice daga parlon, dafe kansa ya yi sannan yabi
bayanta.
Tsaye ya sameta jikin corridor tana goge hawayen fuskarsa gudun kada General ya gani,
rungumeta ya yi ta baya hakan yasa ta sake fashewa da wani sabon kukan na takaici jan
hannunta ya yi bai ce mata komai ba ya buɗe wata ƙofa suka shiga kai tsaye kuma waje suka
fito motarsa ya buɗe ya zurata ciki sannan shima ya shiga ya yi mata key suka bar gidan, kwafa
Mommy tayi tana sakin curtains ɗin ta ce"dani kake zancen wlh" ta shige bedroom ta ɗauki
wayarta ringing ɗaya matar ta ɗauka Mommy ta ce"kina ina Hajiya?" daga ɗaya ɓangaren ta
ce"kin ganni nan ina gida lafiya?" girgiza kai Mommy ta yi ta ce"gobe ki zo zaki rakani unguwa"
okay kawai ta ce sannan ta kashe wayar ta shiga safa da marwa cikin ɗakin sai kuma ta fita.
Tura ƙofar tayi ta shiga wani haɗaɗɗen bedroom ɗin ya yi kyau sosai zaune ta hangeta tana
danna wayarta hankali kwance tsaki Mommy ta yi sannan ta ƙara sa gabanta tana fincike wayar
ɗago kanta tayi tana turo baki sai a sannan na kalleta fara ce tasa amma ba wata kyakkyawa ba
kana ganinta kasan idanunta a buɗe suke tasan duniya zama Mommy tayi gefenta ta
ce"shashasha kina nan kina danna waya bakisan halin da ake ciki ba" turo baki tayi ta ce"to dan
Allah Mommy me zanyi ai bansan meya faru ba kuma kinzo kina min faɗa" girgiza kai Mommy
tayi ta ce"to idanma zaki daina wannan shashancin ki daina idan kuma ba haka ba nan da ƴan
kwanaki kiji ance mijinki ya ƙara aure" da sauri ta miƙe zaune tana kallon Mommy da manyan
idanunta ta ce"Mommy kamarya mijina?, mene ya samu mijin nawa aure kamarya?" ajiyar
zuciya Mommy ta sauke ta ce"kamar yanda kika ji na faɗa miki dan Khalil na gab da ƙara aure"
miƙewa tayi tsaye tuni attachment ɗin kanta ya wargaje ciki tashin hankali take cewa"dan Allah
Mommy ki daina yimin irin wannan wasan haba, ina Khalil ɗin yake?" kama hannunta Mommy
ta yi ta zaunar sannan ta ce"bari kiji na faɗa miki kinsan yarinyar da yake so da can baya har na
sanya yabar ƙasar saboda kada ya aureta to yanzu daya dawo tazo gidan nan ɗazu da babanta
kuma Khalil ya nuna har yanzu yana sonta kuma yanda ya nuna ma nan gaba kaɗan zai aureta"
ɗora hannunta tayi a ka cikin tashin hankali take cewa"nashiga uku Mommy wayyo Allahna dan
Allah ki hanashi wlh bazan iya zama da kishiya ba" tsaki Mommy tayi ta ce"ke amma anyi
shashashar yarinya Macen kikewa kuka?, kishiyar da ba'a yi miki ba?, to ni bazan lamunci kiyi
kishi da wata ba bare kuma Ma'eesha dana tsaneta tun tana ƙarama kibar komai a hannuna
daga wajenki kawai inason ki tubure ki nuna ke ciwonki ya tashi karki kuskura ki bari ya gane ba
ciwon gaske bane ya tashi nikuma duk sauran zanyi" jikinta na rawa ta miƙe tsaye zata yi waje
Mommy ta ce"gidan ubanwa zaki?" "Mommy zanje na kwanta ne kafin ya dawo" murmushi
Mommy tayi sannan itama ta miƙe ta fice.
*Riyadh*
*Al Olaya residence*
Yana gama breakfast ɗin ya fito cikin cikin wata jallabiya ash colour gashinsa ya sakeshi ya
kwanta kan bayansa kallonta ya yi ganin yanda take hawaye har sannan, girgiza kai Zaki ya yi
sannan ya ƙaraso gabanta yana kallonta ya ce"tashi tsaye" girgiza masa kai ta yi tana yarfe
hannu ya ce"bazaki tashi ba?" kamar zatayi kuka ta ce"ni to bazan iya tashin ba ƙafana yana
zafi sosai" dan ƙaramin tsaki ya yi sannan ya sanya hannunsa ya ɗauketa ya fice daga parlon.
Kallonsa Muhaira tayi sai kuma ta kalli doctorn kawai ta fashe da kuka haɗe ransa ya yi ya
ce"zakiyi min shiru ko saina bige bakin?" ko saurarensa bata yiba ta cigaba da kukanta tana
ganin likitan ya gama haɗa allurar ta miƙe da gudu tana rungume Zaki tana sakin wani irin kuka
gaba ɗaya sun rigada sun gama gano abinda ya sanyata kukan hakan yasa Zaki ya ce"kidaina
wannan abun ki fito ko ranki ya ɓaci" sake zagaye hannayenta tayi a jikinsa ta ce"dan Allah kar
ayimin allura wlh naji sauƙi babu zafi yanzu" cikin son shawo kan rigimarta ya ce"babu zafi?"
gyaɗa masa kai tayi ya ce"to zo naga" da sauri ta dawo gabanshi ya sanya hannunsa ya jawota
jikinsa ya rungume ya ce"to faɗamin mene yake damunki da?" cikin sanyin murya ta ce"ƙafata
ce tana ciwo sai kuma kaina, gashi ƙirjina yana min zafi sosai kuma..."maganar ta tsaya
sakamakon allurar da taji an tsaka mata da sauri ta sake shigewa jikinsa tana sakar masa cizo
murmushi kawai ya yi sannan ya ajiye sringe ɗin yana shafa bayanta ya ce"shhhh ki daina
kukan ya isa haka" kamar yana sake tura ta haka ta cigaba da yi masa kuka ya ce"Shikenan kiyi
shiru zan siya maki chocolate da ice-cream" cikin shashshekar kuka ta ce"ni a'a banso ka
maidani gurin Baba banason nan Papi" shafa kanta ya yi bai ce komai ba yana ji har ta fara
sauke numfashi a jikinsa alamar bacci ya ɗauketa. Cikin nutsuwa likitan yake masa bayani ya
ce"Sir yarinyar nan tana ɗauke da cutar Asthma sannan kuma reason ɗin dake sawa ta dinga
ciwon ƙafa jininta AS ne babbar matsalar kuma ita ce tanada ciwon zuciya wanda yake gab da
kaiwa matakin ƙarshe" da sauri Zaki ya kalleshi sai kuma ya kalli Muhaira wacce take rungume
ƙirjinsa Allah mai iko wannan ƴar ƙaramar yarinyar da ciwon zuciya abun akwai tausayi sai a
sannan maganganun aljanun jikinta suka dawo kansa kenan idan da gaske suke ita ɗin batada
kowa kenan?, amma kuma ai a wajen ɗan uwanta ya siyeta something fishy!.
Maganar likitan ce ta dawo dashi daga tunanin daya tafi ya ce"Sir akwai buƙatar a dinga
kulawa da ita da abinda zata ci da wanda zata sha sannan kuma kada a dinga yawan ɓata mata
rai dan hakan zai iya haifar da matsala" duk wannan maganar da ya faɗeta ne da harshen
labarci, gyaɗa kai Zaki ya yi sannan sukayi sallama ya fito daga asibitin kai tsaye kuma gida ya
nufa da ita.
*FCT, ABUJA*
Hannunsa riƙe cikin na Ma'eesha ya ce"idan Allah ya kaimu gobe zan zo dan Allah eesha ki cire
komai daga ranki karki bari wani abun ya samu lafiyarki" gyaɗa masa kai kawai tayi sannan ta
sauka daga motar ta shige gida, saida ya daina hangota sannan ya juya ya bar gidan zuciyarsa
har sannan cike take da ɓacin rai koda wasa bai taɓa zaton abun zai zama haka ba da bazai
taɓa barin Ma'eesha ba a wancen lokacin. Kallonta Farooq ya yi har ta ƙaraso gabansa tana
shirin shige shi ya ce"Ma'eesha!" yanda ya faɗi sunan nata ne tagane something not good
hakan yasa ta dawo ta tsaya amma bata ce komai ba, miƙewa tsaye ya yi yana kallonta ya
ce"uban wane ya kawoki gida?" shiru Ma'eesha tayi masa dan idan ranta yana ɓace to bata iya
magana, sosai shirun nata ya tunzura Farooq hakan yasa cikin ɓacin rai ya ce"kee dan ubanki
ni nake miki magana kina jina?" wani kallo tayi masa sai kuma ta haye sama da sauri batareda
ta bashi amsa ba, kwafa Farooq ya yi ya tsaya for some minutes sai kuma ya bi bayanta.
Kwance ya tarar da ita sai rusa kuka take kamar wacce aka cewa Mami ko General ya mutu,
cikin ɓacin rai Farooq ya ce" bari na sanar dake wani abu duk ranar dana sake ganinki da
wannan guy ɗin wlh sai na lahira ya fiki jin daɗi sai na ɓata miki rai fiyeda tunaninki ki dinga kula
ɗan iska yaro saboda kinason jawo mana abun magana" a fusace ta mike tana kallonsa cikeda
tsiwa take cewa" wlh saina kulashi babu ruwanka da wanda zan kula da kuma wanda bazan
kula ba abinda nakeso shine wanda zan yi ba wanda kai ka zaɓamin ba tunda kai ba ubana
bane nayi maka biyayya a baya wacce hakan ta jefani cikin wani hali har yanzu kuma ban fita
daga cikinsa ba saboda haka wannan karon bazan ji maganarka ba indai akan Khalil ne" ta
shige toilet tana buga ƙofar da ƙarfi. Kwafa ya yi sannan ya juya shima ya fita daga dakin yana
buga ƙofar, jingina tayi da kofar banɗakin ta fashe da wani sabon kukan inama bata bi Father
ba, inama tayi zamanta a gida wataƙila bataga abinda zai tayar mata da hankali ba inama ace
mafarki take wanda zata farka yanzu nan, ganin lokaci na tafiya yasa ta ɗauro alwala ta fito tayi
sallah sannan ta kwanta kan gado ko zata samu sauƙin abinda takejin yana yi mata yawo cikin
ranta.
*Al Olaya residence*
Da mamaki Zaki yake kallon tarin motocin da suka yi parking harabar gidan taɓe bakinsa ya yi
sai kuma ya ɗauko Muhaira wacce har sannan take bacci ya shiga takawa da ita cikeda isa.
Turus ya yi sanda ya shiga parlon saboda idanu biyu da sukayi da Dmash wanda yake zaune
kan kujera shida tawagarsa a gefe, yana ganin ya shigo ya miƙe tsaye kana ganin fuskarsa
kasan ransa a ɓace yake yana zuwa bai yi wata wata ba ya sauke masa lafiyayyen mari a fuska
ji kake tassssss, runtse idanuwansa ya yi lokaci ɗaya jijiyoyin kansa suka tashi above 2mins
kafin ya buɗe idanunsa yana kallon Dmash wanda yake tsaye gabansa da sauri Muhaira wacce
ƙarar marin ya tasa ta fashe da kuka tana rungumeshi ta ce"Papinaaaa" gam Zaki ya riƙeta a
jikinsa yana kallon Dmash ya ce".
*Dommmmmmmmmmm*.
# *Unconditional love*
# *Trafficking*
# *Incident*
# *Destiny*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce!✍️*.[8/8, 8:11 PM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!..*
*Nanameera*.
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
```Page 11```
# *The incident*
Da sauri Taj ya girgiza masa kai yana yi masa nuni da kar ya ce komai, furzar da wani zazzafan
numfashi ya yi kana ya ɗauke kansa, ganin kamar bashi a mara ba yasa Dmash ya ce"kai har
kanajin ka isa da kake aikata abinda kayi niyya?, wane kai ɗin?, har ni zaka dinga rainawa
hankali ina yi maka magana ka kawo min yarinya amma ka mayar dani ɗan iska yaro wato
kawota ne bazaka yiba ko me?" da sauri Muhaira ta sake shigewa jikin Zaki tana rufe fuskarta a
ƙirjinsa dan ba ƙaramin tsorata tayi da Dmash ba. Ganin har sannan bai ce komai ba kuma
bashida niyyar yin magana yasa Dmash ya sanya hannunsa yana ƙoƙarin fizge Muhaira daga
hannunsa, girgiza kai Zaki ya yi sannan ya janye yarinya yana mayar da ita bayansa cikin wata
iriyar murya ya ce"Sir ya kamata ka tsaya iya matsayarka kasan irin abinda zaka dinga yimin or
else..." ya ƙarashe maganar yana taune lips ɗinsa baki buɗe Dmash ke kallonsa dan koda wasa
bai taɓa jin Zaki ya yi masa makaman iyar wannan maganar ba yana bin duk maganar daya
faɗa masa da muhimmanci amma yau daga ganin yanda yake ɗaga muryarsa zaka gane ba
lafiya yake ba, Taj ne ya ƙaraso yana kallon Dmash ya ce"Sir please sorry maybe akwai abinda
ke damunsa dan Allah ka koma zan tawo maka da yarinyar"
"Stop joking Taj billahil Azeem bazan bada yarinyar nan ba sbd haka ma kasan abinda zaka yi
masa alƙawari amma banda ita mark my words" juyawa ya yi ya haye sama cikin zafin nama
Muhaira na biye dashi. Kwafa Dmash ya yi sannan ya ce"ka gargaɗi abokinka idan ba haka ba
zan yi masa abinda bai taɓa tsammani ba, ba'a faɗa dani a samu nasara" ya juya ya fice daga
parlon sauran suka mara masa baya, girgiza kai Taj ya yi sannan ya haye saman yana kiran
sunan Zakin.
Zaune ya sameshi kan kujera ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sai huci yake kamar wani
mayunwacin Zakin, zama Taj ya yi jikin hannun kujera yana dafashi ya ce"please Zaki kayi
haƙuri da abinda ya yi maka sannan kuma ka ɗauki yarinyar nan ka bashi kodan lafiyarka kada
wannan mutumin wanda ka tabbatar da babu Allah a ransa ya cutar dakai dan Allah" cikin ɓacin
rai ya janye hannunsa daga kafaɗarsa ya ce"dalla can cikani wlh kome zai yi saidai y yi amma
bai isa na bashi yarinyar ba zan ɗauki kowace kasada akan rayuwarta saboda haka leave me
alone" da mamaki Taj yake kallonsa dan yasan halin Zaki da kafiya amma bai ɗauka zai kafe
akan yarinyar ba ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce"to faɗa min meyasa bazaka bada ita ba?"
miƙewa tsaye ya yi yana kallonsa ya ce"saboda haka nayi niyya" ya juya ya bar wajen
"Kana sonta ne?" Taj ya faɗa yana kallonsa, tsayawa ya yi cak ya saki handle ɗin ƙofar sannan
ya dawo yana kallonsa ya ce"wa ni?, God forbid! bazan bada ita bane saboda yarinyar ta bani
tausayi tabbas akwai wani abu cikin rayuwarta wanda ba daidai ba tanada buƙatar mentor
wanda zai dinga kulawa da ita sbd haka nayi alƙawarin kulawa da rayuwarta muddun ina
numfashi kamar yanda ta iya kirana da sunan mahaifinta zan tabbatar mata da wannan muradin
nata bayan wannan babu wata alaƙa dake tsakanina da ita sbd haka kasan me zaka dinga
cemin" yana gama faɗin haka ya juya ya shige bedroom ɗin yana buga ƙofar da ƙarfi. Miƙewa
Taj ya ya sai kuma ya girgiza kansa ya ce"jarababbe kawai".
*Next day*
Da sassafe ta tashi bayan tayi sallar asuba ta zauna tana karatun Alkur'ani mai girma wajejen
6:30am ya shigo gidan daga masjid haka kawai yaji yana son ya ganta, shiga ɗakin ya yi
bakinsa ɗauke da sallama ga mamakinsa sai yaga wayam babu kowa waro idanunsa ya yi yana
sake kallon ɗakin ko ina ta shiga?, fitowa ya yi yana ƙoƙarin shiga bedroom ɗinsa ya juyo
ƙamshi na tashi hakan yasa ya tafi zuwa direction ɗin da yake jiyo ƙamshin, turus ya tsaya ƙofar
kitchen ɗin yana mamakin wanda yake girki a ciki bai sake mamaki ba saida ya shiga ciki ya
ganta ta taƙarƙare tana ta faman aiki ƙarasawa ya yi inda take tsaye ya zuba mata idanu yana
kallonta, cikeda ladabi ta sunkuya ta ce"ina kwana Papi?" bai amsa mata ba kawai ya gyaɗa
mata kai sanye yake cikin wata embroidery Jallabiya Black colour ya ɗora hula akansa
hannunsa riƙe da cazbaha yana ja. Yana kallonta ta ɗauki kwai tafasa sannan ta sanya masa
species ɗin data gani a wajen takunna wuta tana shirin kunna gas ya kalleta ya ce"be careful"
da sauri ta juyo tana kallonsa sai kuma ta ce"please Papi ka kunna min zafi inaji" ɗauke kansa
ya yi sai kuma ya ƙaraso wajen, dakyar ta daidaita numfashinta saboda wani irin ƙamshi daya
taki hancinta a hankali ta lumshe idanunta. Tsayawa ya yi a bayanta ya zuro hannayensa ta
tsakanin hammatarta sannan ya karɓi letar ya kunna mata sannan ya ɗora pan ɗin akai ya
matsa yana kallonta tagama komai kuma yaƙi fitane saboda kada wani abun ya sameta saida ta
zuba a plate sannan ya fice daga kitchen ɗin ya shige ɗakinsa.
Bai fito ba sai wajen ƙarfe 11am yana sanye cikin wasu English wears wata deep V-neck
t-shirt sai kuma Cargon Three-quater gashin nan nasa yasha gyara gwanin sha'awa kwance ya
ganta kan kujera one seater ta dunƙule jikinta waje ɗaya girgiza kansa ya yi sannan ya ƙarasa
inda take yana zuwa ya ja ƙafarta a razane ta buɗe idanunta tana kallonsa sai kuma ta tura baki
tana cewa"to ba na ajiye maka naka ba ai ban cinye ba kuma" taɓe baki ya yi dan baima fahimci
akan abinda take maganar ba ya juya yabar wajen kai tsaye fridge ya nufa yana zuwa ya ɗauko
dabino pack ɗaya sai yogurt roba ɗaya ya dawo ya zauna. Da kallo ta bisa sai kuma ta haɗe rai
ta miƙe tana tafiya a nutse ta koma kitchen ɗin, kallon plate ɗin data ajiye masa ya yi sai kuma
ya kalleta ta ce"ai na ajiye maka naka" abincin ya nuna sai kuma ya nuna kansa ta gyaɗa masa
kai ya galla mata harara ya ce"ni ne zanci abincin ki ƙazama dake" turo baki tayi gaba tuna
kwalla ta taru a idanunta ta ce"to meyasa bazaka ciba?, Bani kura yana cin abincina idan na
dafa" taɓe baki ya yi yana kai dabinonsa baki lumshe idanunsa ya yi saboda zaƙin zumar daya
dakeshi saida ya cinye sannan ya kalleta ya ce"saboda ke ƙazama ce Mumu witch that's why
bazan ci abin hannunki ba" fashewa tayi da kuka ta kwanta tana birgima akan lallausan carpet
ɗin wajen girgiza kansa ya yi yana murmushi ya cigaba da cin abincinsa saida ya gama sannan
ya goge bakinsa da tissue. Taj ne ya yi sallama ya shigo ya amsa masa can ciki, zama ya yi
yana kallonta ya ce"subhanallahi ke dawa beauty?" cikin shashasha kuka ta faɗa masa abinda
ya faru, murmushi ya yi ya ce"sorry dear taso kiga abinda na kawo miki" tashi tayi tana goge
hawayen fuskarta ta zauna a ƙasan ƙafarsa ya miƙa mata wata takarda.
Karɓa tayi ta kalla sai kuma ta miƙa masa yana murmushi ya ce"kinsan ta mene?" girgiza
kanta tayi ya ce"admission later ɗinki ce gobe zaki fara zuwa makaranta" miƙewa tayi tsaye
cikeda murna tahau tsalle a parlon kamar wata ƙaramar yarinya saida tayi mai isarta sannan ta
juyo tana kallonsu hararar da taga Zaki ya watsa mata ya sanya ta shiga taita yinta ta sunkuyar
da kanta tana murmushi. Dawowa tayi ta zauna cikin sanyin murya ta ce"Nagode sosai"
murmushi ya yi ya ce"bani zaki godewa ba Zaki ne yasa a