Showing 33001 words to 36000 words out of 44270 words

Chapter 12 - BA ITA BA CE! Free Books by Nanameera.pdf

11 May 2025

2493

yaci ƙarfinta girgiza kanta tayi tana
ajiye wayar ta ce"Allah dan girmanka da buwayarka Allah dan zatinka ka bayyana koma wane
ya aikatawa Ma'eesha haka Allah ka bata lafiya ka yaye mata ka kuma bamu ikon cinye
jarrabawar" ta ƙarashe maganar tana kuka kamar ranta zai fita gabaɗaya duniyar tayi mata zafi
rabonda ta shiga tashin hankali irin wannan tun ranar da Mai martaba ya rasu girgiza kanta ta yi
tana jinjina mugunta irinta ɗan Adam ko me Ma'eesha ta aikata?????.



Sai wajen 5pm suka dawo gida lokacin tayi bacci Khalil ya ɗaukota duk irin wasu gwaje-gwaje
da aka yiwa Ma'eesha ba'a ga wata alamar ciwo wanda zai hana majiyanta aiki ba manyan
likitoci na gidan president ne suka dubata amma basuga komai ba haka suka dawo babu wani
result mai kyau har bedroom ɗinta Khalil ya shiga ya kwantar da ita sannan ya fito babu wanda
ya yiwa sallama ya yi waje dan gaba ɗaya baya cikin nutsuwarsa. Allah sarki General gaba
ɗayansa ya fita hayyacinsa kana ganinsa kasan Akwai tashin hankali mara misaltuwa a tare
dashi idanunsa duk sun zurma dan rabonsa da abinci tun daren jiya tunda ya shiga bedroom
ɗinsa bai fito ba har akayi sallar isha'i dan ko masjid bai jeba, wajejen 9pm Mami ta tura ƙofar ta
shiga zaune ta sameta kan gadon tana sanye da baby hijab da alama sallah tayi zama Mami
tayi a gefenta da sauri ta dora kanta akan cinyar Mami ɗumin hawayenta Mami taji shafa kanta

tayi kawai dan itama ɓoye nata hawayen take numfasawa tayi sannan ta ɗogata tana mata nuni
da abinci, girgiza kai Ma'eesha tayi Mami ta ce"A'a Ma'eesha tun jiya babu abinda kikaci kar
kuma wani ciwon na daban ya sameki" tana faɗin haka ta buɗe plate ɗin gefenta wainar
shinkafa ce a ciki sai zuba ƙamshi take miyar taushe aka yi mata wadda taji wadatattun kayan
haɗi da nama a hankali ta gutsuro ta kai mata bakinta a hankali ta buɗe bakinta ta karɓi abincin
haka Mami ta yita feeding ɗinta saida ta tabbatar da cewa ta ƙoshi sannan ta rabu da ita ruwa ta
bata tasha sannan ta ce taje tayi wanka, Mami na zaune a ɗakin har saida tagama wankan ta
shirya cikin wata sleeping dress fara ta kwanta saida Mami ta tabbatar bacci ya ɗauketa sannan
ta gyara mata kwanciyar ta rufeta da duvet tabar ɗakin. Da sallama tashiga ɗakin zaune ta
sameshi kan kujerar dake gefen gadon ya zuba uban tagumi gefensa al-qur'ani ne da alama
karatu ya gama a sanyaye Mami ta ƙarasa ciki ta zauna gefensa shiru bedroom ɗin ya ɗauka na
wasu mintuna sannan Mami tayi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin"yallaɓai bakaci abinci ba
tun jiya kar ciwonka ya tashi" ɗago idanuwansa ya yi wanda sukayi wani irin jaaa ya kalleta
sannan ya ce" Asma'u ko kaɗan banajin yunwa yama za'a yi naji yunwa Asma'u? kin manta
halin da ƴata ke ciki? Ma'eesha fa dan Allah karki karyamin zuciya ki barni kawai" girgiza kai
Mami ta yi ta ce"bawai zan karya maka zuciya bane a'a zan ƙarfafa maka ita ne ka tuna cewa
Allah shine wanda ya azurtamu da Ma'eesha bayan tsawon lokaci bayan mun yanke tsammanin
zamu samu haihuwa sannan kuma muka kusa rasata a yayin haifarta nanma Allah ya sake
bamu dama kada ka manta kowane bawa akwai irin tasa jarrabawar mu wannan ita ce tamu
dukda zuciyata a karye take amma naji zan dogara da Allah kuma zan cigaba da roƙonsa har
sanda zai bawa Ma'eesha lafiya kaima dan Allah dan Annabi karka saka wannan abun a ranka
ka cire komai mu fawwalawa Allah haƙiƙa shi ɗin mai jin kukan bayinsa ne idan kana shiga
damuwa Ma'eesha bazata samu salama ba kullum zata kasance cikin tashin hankali dan Allah
General kayi mani wannan alfarma" numfasawa ya yi sannan ya kalleta ganin tana hawaye.
Hannunsa yasa ya goge mata sannan ya ce"shikenan Asma'u Allah ya bamu ikon juriya da
haƙuri da ƙaddara amma tabbas kowane ya yi wannan abun bazan taɓa yafe masa ba da
sannu kuma Allah zai bayyana mana shi" gyaɗa masa kai Mami ta yi ta ce"dan Allah ka daure
kaci abinci ko yaya yake kar ulcer ya tayar maka" bayason ya sake nuna mata damuwarsa
hakan yasa ya gyaɗa mata kai kawai da sauri ta tashi ta fita dan kawo masa abincin yanda ta
sanya Ma'eesha a gaba haka shima ta sanya shi a gaba saida ta tabbatar ya ƙoshi sannan ta
rabu dashi tashi tayi zata fita ya ce"Asma'u" da sauri ta juyo sai kuma ta dawo ta zauna wainar
shinkafar ya gutsuro ya kai mata baki batayi musu ba ta karɓa kawai dan itama rabonta da
abincin tun jiya.




Khalil na zaune ya yi shiru hannayensa bisa kumatunsa ya tafi can duniyar tunani his
Excellency ne ya shigo ya zauna gefensa dafashi ya yi wanda hakan ya dawo dashi daga
duniyar tunanin da ya tafi gyara zamansa ya yi ya ce"na'am Dad" numfasawa ya yi ya ce"Khalil
tunanin me kake?" jiki a sanyaye ya ce"Dad Ina tunanin Ma'eesha ne ina tunanin halin da take
dan Allah Dad kayi magana da Father a sakko da maganar aurenmu ya dawo nan kusa
zuciyata zata iya bugawa idan na cigaba da ganinta cikin wannan halin dan Allah Dad" kallonsa

ya yi sai kuma ya dafashi ya ce" ka yarda zaka zauna da ita a haka?" "Dad koda makancewa
Ma'eesha zatayi zan zauna da ita domin ni ita nakeso kamar yanda nasan da ace ni ne na shiga
wani hali to babu abinda zai rabani da ita" murmushi Dad ya yi ya ce"kayi abinda ya dace Khalil
I'm so proud of you nagode sosai" girgiza kansa ya yi ya ce"karka godemin Dad wannan yiwa
kai ne" dafa kafaɗarsa Dad ya yi alamar jinjina sannan ya tashi ya shige ciki, da sauri ta koma
bedroom ɗin tana zuwa ta faɗa jikin Mommy tana sakin wani irin kuka hankali tashe Mommy ta
ce"ke Ramlah ke dawa?? meya sameki?" cikin kuka ta ce"Mommy kina ji ya ce zai aureta a
haka Mommy Doctor ya ce zai zauna da ita koda ta kurumce dan Allah Mommy help me wlh ina
cikin tashin hankali ki taimaka mini banason na rasa mijina kuma na tabbata ya aureta shikenan
bashida lokacina" ajiyar zuciya Mommy ta sauke sannan ta ce" Ramlah karki wani damu kanki
nasan abinda zanyi yanda na faɗa miki Khalil bai isa ya yi miki kishiya ba indai ni ce na haifeki
saboda haka ki daina kukan nan" goge hawayenta tayi dan tasan tunda Mommy ta faɗa to ya
zauna tashi ta yi ta ce"bari naje wajensa" okay Mommy ta ce har takai baƙin kofa ta ce"karki
kuskura ki nuna masa kinji abinda suka tattauna ko kuma ranki ya ɓaci" gyaɗa mata kai Ramlah
ta yi sannan ta fita.


Tsaye yake jikin ƙaton Enlargement ɗin hoton ya zuba masa idanu wasu hawayene suka shiga
zirarowa kan kuncinsa cikin sanyi murya ya ce"Mom why?why? meyasa kika barsu Mom? kin
barni Mom banajin daɗi Mom yaushe zaki dawo ne? I really need you" ya ƙarashe maganar
yana goge hawayen fuskarsa komawa ya yi ya zauna gefen bed ɗinsa a hankali ya fara
recalling abinda suka shige some years back tabbas Mommynsa tabar baya da ƙura babu Irin
neman da ba'a yi mata ba amma har i Wannan lokacin basu sake jin lbrnt ba dukda an tabbatar
da asiri akayi mata na kucciya baisa sun hakura da nemanta ba aƙalla ankai wajen shekaru 30
da ɓacewarta ganin lokaci na tafiya yasa ya miƙe ya shige bathroom gudun kada ya makara.



*Riyadh*
*Al hammadi international hospital*

Zaune yake kan kujerar dake facing gadon idanunsa a lumshe suke ya yi matuƙar gajiya har
zuwa sannan kuma Muhaira bata farfaɗo ba duk da sunyi mata allurar bacci

"Papi"


Da sauri ya buɗe idanuwansa yana kallon inda yaji an kirashi idanunta a rufe suke ƙarasawa ya
yi ya zauna gefen gadon ya riƙo hannunta cikin sanyin murya ya ce"yarinyar Papi kin tashi?"
gyaɗa masa kai kawai tayi har sannan kuma idanunta a rufe suke ta ce"ka mayar dani gida
please ni bazan sake kwana anan ba wajen Papina zani ka mayar dani garinmu dan Allah"
hawayen da yaga suna zuba daga idanunta yasa yaji jikinsa ya yi sanyi yasan shine wanda ya
jawo komai ko kaɗan bai ji daɗin abinda ya yi mata ba hannunsa yasa ya goge mata hawayen

sannan ya ce"kidaina kuka kinji ki bari ayi discharging naki" girgiza masa kai tayi cikin kuka ta
ce"ka mayar dani gida ni banason nan banson zama dakai ni na tsanek..." da sauri ya rufe mata
baki yana girgiza mata kai buɗe idanunta tayi wanda suka sauya kala wani irin ruwa ya kwanta
a cikinsu batace masa komai ba ta fashe da kuka tana ɗauke kanta daga kallonsa dafe kansa
ya yi ya ce"ki yiwa Allah ki daina kukan nan haira naji zan mayar dake gida" da sauri ta kalleshi
sai kuma ta ce" da gaske?" gyaɗa mata kai ya yi kawai daidai nan Taj ya shigo ɗakin yana
kallonsu ya ce"




# *BA ITA BA CE!*
# *Haira*
# *Zaki*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce ✍️*.[8/11, 7:55 PM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!..*


*Nanameera ce ✍️*


*MIKIYA WRITERS ASSO...*


```Page 15&16```


"Ya jikin nata?" numfasawa Zaki ya yi ya ce"da sauƙi Alhamdulillah" zama ya yi kan kujera yana
kallonta ya ce"Muhaira" buɗe idanunta ta yi ta kalleshi amma bata ce komai ba, murmushi ya
sakar mata itama ta mayar masa tsayawa Zaki ya yi yana kallonsu sai kuma ya ɗauke kai daidai
nan Dr ya shigo ɗakin sake duba jikin nata ya yi sannan ya yi discharging nasu kallonsa tayi
ganin yanda ya juya baya tura baki tayi gaba ya yi murmushi ya ce"hau na goyaki mana" ɗauke
kanta tayi sai kuma ta hau bayan nasa tana riƙeshi sosai dariya ya yi mara sauti ya ce"tunani
kike zan ya dake?" batace masa komai ba ya girgiza kansa sannan ya fice daga asibitin zaune
suka sami Taj a mota yana jiransu sauketa ya yi ta shiga back seat sannan shima ya buɗe gaba
ya shiga. Sunyi nisa sosai Taj ya ce"Dmash fa yana gidanka nd kuma yana jiran ka dawo ya
karɓi Muhaira ne kuma ba shi kaɗai bane sunada yawa gabaɗaya ma dai abun nasu da akwai
alamar rashin gaskiya saboda haka kar kaje gidan yana tunanin ya haɗa baki dani ne domin na
ce masa zan kawo masa Muhaira without ur permission" kallonsa Zaki ya yi sai kuma ya yi
murmushi ya ce"daman nasan dole haka zata iya kasancewa kada ka damu ka kasance a tare
dashi komai ya kusa zuwa ƙarshe in sha Allah anjima zan yi magana da Sir" gyaɗa masa kai Taj
ya yi sannan ya kalli Muhaira wacce tayi tsuru da idanu tana kallonsu murmushi ya yi ta
mudubin ya ce"Baby lafiya?" turo baki tayi tana fashewa da kuka harararsa Zaki ya yi ya

ce"wannan ma ai rashin mutunci ne kasan da anyi mata magana kuka take amma zaka kulata
ni wlh nagaji da jin kukan nan" dariya ya yi ya ce"to na tuba please ki daina kuka kinji" cikin
shashshekar kuka ta ce"ni gida zani" Taj ya ce"to kiyi shiru za'a mayar dake kinji" girgiza kai
Zaki ya yi bai sake cewa komai ba har suka ƙarasa gidansa dake Al Hamra.


Haɗaɗden gidana amma bai kai wancen girma ba kallon gidan kawai Muhaira tayi ganin ba
gidan da ta saba zama ba jan hannunta Zaki ya yi ya haura da ita upstairs wani parlon ya buɗe
mata ta shiga sannan ya ce"oya kiyi sallah zan kawo miki abinci sai kisha drugs ɗinki" gyaɗa
masa kai tayi sannan ya juya ya fita ita kuma ta shige bedroom, zaune ya tararda Taj yana
danna wayarsa yana ganin ya fito ya miƙe ya ce" ya kamata na tafi yanzu" numfasawa Zaki ya
yi ya ce"inason na tambayeka wani abu daman" Taj ya ce"ina jinka" "a ina ka samo yarinyar nan
ne?, sannan wane ya siyar da ita kaine ka sanshi ni bansan wane ne ba please ka nemo min
information nasa" gyaɗa masa kai Taj ya yi sannan suka jera suka fita.



Kwance ya sameta amma ba bacci take ba tana ganinsa ta miƙe zaune har sannan kuma
fuskarta a kumbure take zama ya yi a kan carpet ɗin parlon da hannu ya yi mata alama da tazo
ta taso a hankali ta zauna gefensa kamo hannunta ya yi ya zaunar da ita kan cinyarsa ya ɗora
kansa bisa wuyanta cikin sanyin murya ya ce"ke dawa? wane ya sakaki kuka?" riƙe hannusa
tayi sai kuma ta sake fashewa da wani sabon kuka dafe kansa ya yi ya rungumeta ya ce"ya isa
kidaina kukan okay" sosai tayi kuka a jikinsa sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya shafa
bayanta ya yi ya ce"now tell me mene yasa kike kuka?" cikin shashshekar kuka ta ce"ni gida
zani banason nan ka mayar dani gida" murmushi ya yi ya ce"shine kike rigima?" da sauri ta
kalleshi sai kuma ta ɗauke kanta tana turo baki gaba tattausan hannunsa ya sanya ya juyo da
fuskarta kallonsa tayi sai kuma tayi saurin rufe fuskarta da hannunta tana faɗawa jikinsa cikin
shagwaɓa ta ce"Allah ni bansoo!" murmushi ya yi ya ce"to naji bakiso me kike so?" "Ni kawai ka
mayar dani gidanmu Allah" shafa kanta ya yi ya ce"i promise you zaki gida sooner or later" "to ni
yanzu yanzu nakeso naje ai" tafaɗa tana ɗago kanta daga jikinsa jan kumatunta ya yi ya ce"to
yanzu so kike nazama fly na kaiki gida?" murmushi tayi tana jan cute beard ɗinsa ta ce"to nan a
ina muke?" waro idanuwansa ya yi tayi saurin kautar da fusakarsa cikin shagwaɓa ta ce"ni
kadaina kallona da wannan idanun naka abun tsoro" dariya sosai Zaki ya yi rabonda ya yi
dariya mai yawan haka har ya manta Muhaira kuwa zuba masa idanu tayi kamar ta samu Tv
bata taɓa ganin mutum mai kyau da cikar zati irinta Zaki ba yanada wani irin halitta mai matuƙar
ɗaukan hankali yanayin jikinsa zaka irin zaton balarabe ne dan ko kaɗan baya kamada
hausawa dukda ya iya hausan sosai. Ganin yanda take kallonsa kamar ta samu Tv yasa yakai
hannunsa wajen idanunta da sauri ta ture hannunsa ta ce"A'aaaaa kabarni ni" murmushi ya yi
ya ce"idanun nawa ne suke baki tsoro?, da idanuna da naki wannan ya kamata ace anji tsoro
ke baki kalli naki idanun bane kamar wata mage?" wani kyakkyawan murmushi tayi tana riƙe da
gemunsa ta ce"ai kai naka manyane kamar na dodo" "dodo kuma mene ne haka?" ta ce"abun
tsoro mana wanda Dadata take bani lbr a tatsuniya" murmushi ya yi yana kama hannayenta ya

ƙura musu idanu kamar wanda yake kallon wani abu kallon hannun nata tayi itama sai kuma ta
janye su daga hannunsa ajiyar zuciya ya sauke ya ce"in tambayeki?" gyaɗa masa kai tayi ya
ce"bani labarin inda kike sannan a ina Taj ya ɗaukoki ina iyayenki?" turo baki ta yi lokaci ɗaya
jikinta ya yi sanyi ta ce"Papina ya tafi ya barni Dada tayi ta cemin zai dawo amma bai dawo ba
sai kuma Dadata ta mutu tabarni duk sun tafi sun barni banida kowa sai Bani kura shine kawai
ya ɗaukeni sannan..." katseta ya yi ya ce"eat ur food first sai ki bani lbrn" gyaɗa masa kai tayi
sannan ya miƙa mata plate ɗin abincin kwaɓe fuska tayi bata karɓa ba girgiza kansa ya yi kawai
sannan ya ɗauki spoon ɗin ya fara bata abincin a baki lumshe idanunta tayi saboda daɗin da
abinci ya yi mata gyaɗa kanta tayi ta ce"unnnn daɗi" murmushi kawai ya yi bai ce mata komai
ba dan shi a ƙa'idarsa idan yana cin abinci baya magana sbd haka ne itama ya yi mata shiru.
Sosai ta ci abincin ta ƙoshi sannan ya bata drugs ɗinta dakyar tasha hardasu kuka tana gama
sha kuma bacci ya ɗauketa a wajen wani zazzafan numfashi ya sauke sannan ya tashi ya fice
daga parlon.


Kai tsaye ɗakinsa ya shiga yana zuwa ya faɗa bathroom ya yi wanka sannan ya fito shiryawa
ya yi cikin wata jallabiya ash colour ya tufke kansa da ribbon ash colour sannan ya ɗauki
turaren Creed Aventus ya fesa ƙarar da yaji wayarsa nayi ne yasa ya kalli inda take a hankali ya
ƙarasa wajen ya ɗauka shiru ya yi yana kallon sunan dake kan screen ɗin wayar har sannan
kuma bai ɗaga kiran ba yana ji har ya katse mamaki ne sosai kan fuskarsa duk da yasan zai iya
kiransa amma ko kaɗan bai kawo yanzu ba ƙarar kiran ya sake ji a karo na biyu dafe kansa ya
yi kamar wanda aka yiwa dole ya ɗaga shiru ya yi yana sauke wani numfashi daga ɗaya
ɓangaren ma haka cikin sanyin murya ya ce"good afternoon sir" cikin kamilalliyar murya mai
nuni da kamewa aka ce"Aliyu duk inda kake ka dawo gida" buɗe bakinsa ya yi zai magana yaji
wayar ta katse kallon screen ɗin wayar ya yi sai kuma ya ajiyeta yana dafe kansa abubuwa
nasan kwaɓe masa dole ne yayi azama ya yi abinda ya kawo shi ƙarar kiran wayar ne ya dawo
dashi daga tunanin daya tafi kallon wayar ya yi sai kuma ya ɗaga cikin girmamawa aka ce"sir
gamu nan kai muke jira" okay kawai ya ce sannan ya kashe kiran ya tashi ya fice kallon ƙofar
apartment ɗinta ya yi sai kuma ya fice daga gidan.


Bata farka ba sai wajen ƙarfe 5pm a hankali ta buɗe idanunta tana ambarta sunan Allah tashi
tayi daga kan bed ɗin ta shige toilet tayi wanka tayo alwala shiryawa tayi cikin wata abaya data
gani black colour ta ɗaura veil ɗinta tayi sallah shiru tayi tana tunani sai kuma ta tashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login