Showing 39001 words to 42000 words out of 44270 words
hakan yasa ya juyo yana kallonta ya ce"mene ne?" turo
baki ta yi sannan ta nuna masa can gefe inda akayi wani waje ana siyarda ice-cream kallonta
ya yi sai ya ce"za ki sha?" da sauri ta ɗaga masa kai dungure mata kai ya yi ya ce"kinsan ai
bakida lafiya ko sbd haka bazan siya miki ba" kuka ta sanya masa amma ya yi mata banza dan
daman shi haka halinsa yake inda ya ce bazai abu ba to kome za'a yi bazai yi ɗin ba babu irin
kukan da Ma'eesha batayi amma ya yi funfurus popcorn kawai ya siya musu suka bar wajen
ana kiraye-kirayen sallar magrib ya yi parking fita Aleema ta yi ta shige cikin dan duk a gajiye
take, murɗa handle ɗin ƙofar tayi taji a rufe hakan yasa ta juyo ta kalleshi da idanunta da suka yi
jajur alama tayi masa daya buɗe motar ya girgiza mata kai jawota ya yi yana gyara zamanta a
kan cinyarsa ya ɗago fuskarta hannu tasa ta tureshi tana fashewa da kuka yasan fushi take
dashi murmushi ya yi yana haɗe jikinsa da nata ya rungumeta yana shafa kanta sosai tayi kuka
a ƙirjinsa kafin ya sake ɗago fuskarta ya yi coping da tasa suna sauke numfashi a tare saurin
janye fuskarta tayi saboda wani iri da taji a jikinta murmushi Khalil ya yi ya juyo da fuskarta ya
kama kunnensa alamar ta yafe masa ɗauke kanta tayi hawaye na zirarowa kan kuncinta dafe
kansa ya yi ya ce a hankali"I'm sorry eeshana" kallon bakinsa tayi sai kuma ta nuna masa ƙofa
alamar ya buɗe mata da hannu shima yayi mata alama da ta yafe masa saurin gyaɗa masa kai
tayi dan Allah Allah take tabar motar buɗe mata ya yi yana gani ta sauka da sauri ta shige
parlon daidai nan Farooq ya fito da kallo yabi motar yana gani har securities suka gama kwashe
kayan dake motar suna shiga dashi gidan sannan ya juya ya bar gidan taɓe baki Farooq ya yi
yana kallon uban kayan da suke shigowa dashi ko ba'a faɗa masa ba yasan ba ƙananan kuɗi
aka kashe ba furzar da wani zazzafan numfashi ya yi sannan ya buɗe motarsa ƙirar coralla ya
shiga da wani irin speed ya bar gidan.
"Haba Aleema wannan kayan ai sunyi yawa"
Turo baki ta yi Fulani ta ce"babu wani yawa da sukayi daman haka akewa kowace ƴa idan za'a
aurar da ita" murmushi Mami ta yi tana kallon mahaifiyartata sai kuma ta ce" to shikenan ai"
dariya Aleema ta yi ta ce"Fulani kice ta ɗaga ki" kallonta matar tayi kyakkyawace sosai kuma
sannan kamarsu ɗaya da Mami dan harma tafi Mami kyau kana ganinta kasan ta manyanta
sosai amma kuma kuɗi da mulkin daya zauna musu shine abinda ya ɓoye tsufan nata Fulani
kenan mahaifiya a wajen Mami kuma matar sarkin Katsina marigayi Alhaji Aliyu ɗan sarari ya yi
tashen kuɗi a lokacinsa dan babu wani sarki wanda ya kai shi a arziƙi a lokacin yanzu kuma
ɗansa Alhaji Ahmad Aliyu shine wanda yake karagar mulkin mace ce mai faran faran da jama'a
musamman jikokinta suna matuƙar jin daɗin zama da ita kasancewar sunanta aka sawa
Ma'eesha yasa take matuƙar sonta duk cikin matan sarki na wannan lokacin babu wacce ta
kaita ƙarfin iko dan ita ce wacce mai martaba yafi so kasancewar da ita ya yi aure tun saurayi
da budurwa kuma ita ƴar sarki ce wannan kenan.
Hararar Aleemah ta yi ta ce"ai sai kizo ki sanya ta ɗagani ja'ira kawai" gwalo Aleema ta yi ta
ce"ke kam kin fiye rikicin tsufa wlh ko mema kika zo yi nan ohho!" Cikin kunfar baki Fulani ta
ce"ubanki Mahamuda shi nazo yi nan ja'irar yarinya kawai" buɗe baki ta yi zata sake magana
Mami ta ce"ke shiga hankalinki uwartawa kika mayar abar wasanki" da sauri Fulani ta ce"a'a
kekam Asma'u banson ƙin Allah idan banyi wasa da jikokina ba dawa zanyi wasa kinsan dai su
kaɗai gareni" girgiza kai Mami ta yi dan ta fuskanci rikicinta ne ya tashi hakan yasa ta miƙe ta
ce"to Mama bari na kawo miki abinci" ta ce"ai da nayi zaton babu abinci a gidan ne nasa a
kiramin janar din naji dalilin da zai barki da yunwa" tuntsirewa Aleema ta yi da dariya ta ce"to ke
Fulani idan baya basu abinci ina ruwanki" banza Fulani tayi mata tana shafa kan Ma'eesha
wacce bacci ya ɗauketa.
Daren ranar basu kwanta da wuri ba sbd hirar Fulani hatta Ma'eesha da ba jin abinda take cewa
tayi ba saida ta zauna tana kallonta idan taga tayi wani abun tayi dariya saida Mami ta zo ta
lallaɓa Fulani sannan ta kwanta, da sassafe kuma masu gyara jiki suka dira a gidan part guda
Mami ta ware musu aka basu abinci sannan aka kai Ma'eesha wacce take ta kuka dan harga
Allah baso take ba yinin ranar bata fito ba dan hanata suka yi sai wajen magrib sannan ta sanya
kuka dole suka barta ta tafi tana zuwa ta kwanta jikin Fulani wacce take ta mita ta gyaran jikin
wai an ɗauke mata ita Ita dai Mami batace mata komai ba sai Aleema ce take janta. Haka aka
dinga yi mata gyaran jikin har ya rage sauran kwana uku a ɗaura aure kasancewar ba wani fita
zasu yi ba tunda batada lafiya yasa aka ɗauko mai henna tazo har gida tayi musu ita da Aleema
washegari da azahar tawagar Mami suka iso gidan ciki harda matar sarki Hajiya A'isha mace
mai karamci da Mutane ba bahaushiya bace ta kasance balarabiya dan lokacin da sarki yaje
Makkah gidansu abokinsa ya ganta ya ce yana sonta bai baro ƙasar ba saida aka ɗaura musu
auren da ita. Tuni gidan General Ibrahim Tijjani mai Zamani ya cika maƙil da manyan mutane
kowa sai hada-hadarsa yake a cikin gidan Ma'eesha kuwa tana part ɗin General dan ko kaɗan
batason taron mutane ranar da akayi mata henna da rana aka ɗauko photographers aka dinga
ɗaukanta hotuna tayi kyau cikin lufayar da aka ɗaura mata purple colour gashin nan yasha
gyara ya zubo har gadon bayanta sai sheƙi yake yi ƙunshi mai matuƙar kyau aka yi mata sai
murmushi take musamman sanda taga su Fateemah sun zo hakan ba ƙaramin faranta mata rai
ya yi ba.
*RIYADH*
*AL HAMRA RESIDENCE*
Kallonta ya yi ganin yanda take faman kuka kamar ƙaramar yarinya a kwana biyun nan gaba
ɗaya ta hanashi sukuni gashi yanzu ko kaɗan baya samun lokacin kansa abubuwa duk sun sha
masa kai gajiya ya yi da jin kukan kawai ya kashe light ɗin daƙin duhu ya mamaye ko'ina cikin
wata iriyar murya ya ya ce"ga dodo nan"da gudu Muhaira ta taso tana zuwa ta shige cikin
blanket ɗin ta cukwuikuyeshi tana sakin kuka shafa kanta ya yi a hankali ya ce"ya isa to kiyi
shiru karya kamaki" ajiyar zuciya ta shiga saukewa tana sake shigewa jikinsa dan gaba ɗaya a
tsorace take cikin kuka ta ce" ni ka kaina gida Papi banso nan ka tafi dani Allahhhhh!"
numfasawa ya yi ya ce"bana faɗa miki xan kai ki ba gidan wa zamu ce idan munje garin naku?"
turo baki tayi ta ce"ni banida gida kawai kasuwa Gashua zaka kaini wajen Mama mai abinci
anan nake kwana" da mamaki ya kalleta cikin duhun ya ce"wace haka?" turo baki ta yi ta ce"ni
duhuuu" murmushi ya yi sannan ya kunna dum light hakan yasa ɗakin ya yi wani irin blue ya
kalleta ya ce"now tell me wace ita?" Numfasawa tayi sannan ta fara bashi lbrn rayuwarta tun
daga farko har zuwa sanda Taj ya saceta ba ƙaramin tausayi ta bashi ba dan bai yi zaton hakan
zai iya kasancewa da mutum ba cikin kuka ta ce" dan Allah Papi karka kaini wajen Bani kura
wlh banaso bazan iya aurensa ba dan Allah Papi kasuwa zaka kai ni" rungumeta ya yi ya ce"ya
isa haka stop crying sleep kinji" yana ji tana shashshekar kuka har bacci ya ɗauketa shafa kanta
ya yi sannan ya gyara mata kwanciyarta ya rufeta da duvet ya kashe AC ya fito parlon kai tsaye
kitchen ya shiga ya haɗa coffee sannan ya fito ya shiga wani daƙi gaba ɗaya bangon ɗakin an
rubuceshi wani wajen kuma an maƙala hutuna babu haske a ɗakin hakan yasa ba komai ake
iya gani ba zama ya yi akan wata kujera da table a gabansa ya buɗe system ɗin ya shiga
dannawa a hankali yana sipping coffee ɗinsa sai wajen 3am sannan ya tashi daga wajen ya rufe
system ɗin ya fito kai tsaye kuma toilet ya shiga ya yi wanka ya ɗaura alwala sannan ya shirya
cikin wata embroidery Jallabiya Black colour ya shimfiɗa prayer mat ya shiga sallolinsa na nafila
har lokacin kiran asubahi ya yi saida ya tasheta sannan ya fita dan gabatar da sallar a masjid
bayan ya idar kuma ya zauna karatu bai shigo gidan ba sai wajen 6am kai tsaye kuma kan
kujera Three seater ya kwanta ya lumshe idanunsa nan da nan bacci ya ɗaukeshi.
Ringing ɗin wayarsa ne ya farkar dashi yana ɗagawa ko sallama bai yiba ya ce"ohk I'm
coming" ya ajiye wayar ya shiga bedroom kai tsaye bathroom ya shiga ya yi wanka sannan ya
fito ya shirya a gurguje kallonta ya ya ganin yanda take bacci hankali kwance kasancewar ranar
weekend yasa bai tashe ba ya yi waje.
Murmushi Dmash ya yi bayan yaga shigewar motar Zaki ya yiwa drivern magana suka shiga
gidan kasancewar gidan babu wasu securities sai mai gadi yasa ya ce masa wajensa yazo
sanin yasan yana zuwa wajen nasa yasa bai hanasu shiga ba, shiga cikin gidan ya yi
mutanensa na biye dashi kana ganinsu kaga marasa mutunci da imani kallon parlon ya yi ganin
babu kowa a ciki yasa ya haye upstairs kai tsaye kuma bedroom ɗin ya nufa yana shiga
hangota kwance tana sharar baccinta hankali kwance lumshe idanu ya yi yana cije baki sai
kuma ya yi wani killer smile ya ƙarasa gabanta cikin takunsa na isa yana zuwa ya sanya
hannunsa ya yaye bargon jikinsa runtse idanuwansa ya yi ganin surar jikinta dan ƴar ƙaramar
sleeping dress ce a jikinta wata dariya ya saki sannan ya.
_Free pages sun kusa ƙarewa only two pages remain you can start making ur payment via
9086030007 Hauwa lawan adamu opay 500# for normal group 1k for VIP posting sau biyu a
rana ki biya sister bazakiyi dana sani ba nayi muku alqawarin haka_
_BA ITA BA CE!_
# *SQUAD 2024*
# *Power*
# *Unconditional love*
# *Trafficking*
# *Nanameera ce ✍️!*
[8/13, 11:43 AM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!...*
*Nanameera*
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
```Page 19&20```
*Last free pages*
A firgice Muhaira ta farka tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya sai kuma ta saki wata razananniyar
ƙara hawa kan gadon ya yi ya riƙe hannunta cikin sanyin murya ya ce"hyyy I'm not here to hurt
you kinji" gyaɗa masa kai ta yi da sauri dan gaba ɗaya a tsorace take murmushi Dmash ya yi
sannan ya ce"tawo muje" cikin rawar murya ta ce"in...ina?" bai ce mata komai ba ya kama
hannunta suka sauka daga kan gadon tsorone fal fuskar Muhaira sai dube-dube take ko za taga
Zaki amma bata ganshi ba suna fitowa compound ɗin gidan ta zare hannunta daga nasa tana
kwaɓe fuska kallonta ya yi sai ya yi murmushi cikin sanyin murya ya ce"mene ne?" "ni Papi
zani" numfasawa ya yi Sannan ya ce"to ai nima wajensa zan kai ki" langwaɓar da kai ta yi ta
ce"nidai mu jira shi a nan" dafe kansa ya yi ya ce"to ai shima yana can yana jiranmu Muhaira
kinga let's go" turo baki tayi sannan ta zauna kan wata kujera tana haɗe rai ta ce"ni dai ya ce na
dinga jin magana kuma ai bai cemin na fita ba kaga idan na fita faɗa zai yimin kawai ka kirashi
shi ya zo" shiru Dmash ya yi yana saurarenta ya fuskanci bazata taɓa yarda ya fita da ita ba
dan da alama tanada kafiya da gardama da idanu ya yiwa wani yaronsa magana gyaɗa masa
kai ya yi sannan ya ƙarasa ta bayanta wani gyaɗa ya rufa mata a fuska nan da nan idanunta
suka rufe baya tayi zata faɗi ya yi saurin tare ta tunda mai gadin yaga haka ya yi saurin kiran
wayar Zaki amma baya picking hakan yasa ya rasa yanda zai yi yana kallon sun ɗaukota ya
ƙarasa wajen duk da tsoron da yake ji cikin dakkakiyar murya ya ce"Sir ina zaku tafi da ita"
kallonsa yaran sukai dan tuni Dmash ya shige mota girgiza kai ya yi ya ce"aikuwa babu wanda
ya isa ya fita cikin gidan nan har sai mai gidan ya dawo" taɓe baki Dmash ya yi ya kalli Drivern
ya ce"what are you waiting for?" girgiza kai ya yi a nutse ya ce"shot him" ƙarar bindigar da naji
shine yasa na kalli wajen amma me sai naga gateman ɗin a kwance cikin jini yanata kokawa da
numfashi ko second ɗaya basu ƙara ba a cikin gidan suka fita, Above 10mins kafin Zaki ya
ƙaraso gidan cikin wani irin speed ya ƙarasa wajen mai gadin tsugunawa ya yi ya riƙeshi dan
tun sanda ya tura masa msg hankalinsa yake a tashe dukan kumatunsa ya yi ya ce"si... Sir I'm
sorry nakasa cetonta" girgiza kai Zaki ya yi"don't worry john isn't ur fault" wani irin jan numfashi
ya yi yana rike hannun Zaki ya ce"Sir na sanka karka barshi kar ka rabu dashi kada ka bari
yallaɓai nasan zaka iya kaji..."tari ne ya turnuƙeshi ya yi saurin sakin hannunsa riƙo fuskarsa
Zaki ya yi ya ce"don't worry john yanzu zan kai ka asibiti kaji zaka samu lpy" kallonsa ya yi da
idanuwansa wanda suka sauya kala sun rine sunyi jajur dasu ya girgiza masa kai yana
murmushi a hankali kuma ya sauke wani wahalallen numfashi kansa ya yi baya runtse idanunsa
Zaki ya yi for some seconds kafin ya buɗe su ya kalli fuskar John wacce a yanzu ta zama gawa
daidai nan securities suka shiga shigowa gidan da guards ɗinsa bai ce musu komai ba ya shige
gidan su kuma suka ɗauke John daga wajen.
Kai tsaye bathroom ya shiga yana zuwa ya sakarwa kansa shower ta ruwan sanyi yana jin
yadda ruwan ke ratsa kowace ƙofa ta jikinsa hannayensa ya tura cikin gashin kansa wanda
shima ya gama jiƙewa da ruwan ya jima sosai a haka kafin ya kashe showern ya yi wanka
sannan ya fito sanye da bathrobe Acn ɗakin ya kunna nan da nan wani irin sanyi ya mamaye
ɗakin kai tsaye kan royal bed ɗin ya kwanta yana lumshe idanunsa above 10minutes kafin wani
baccin wahala ya ɗauke shi. A firgice ta farka tana bin inda take kwance da kallo kafin kuma ta
fashe da wani irin kuka mai gunji nan take ta fara birgima a ƙasa tana kiran sunan Papi buɗe
ƙofar a kayi ya shigo hannunsa riƙeda mug da sauri ya ƙaraso gabanta ya ajiye mug ɗin a kan
table sannan ya kamo hannunta turewa tayi cikin kuka ta ce"ka barni ni karka sake riƙeni ni
wajen Papina zani" ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka janyota Dmash ya yi ya shaƙe
wuyanta cikin kakkausar murya ya ce"keee I'm not ur mate duk ranar da kika sake yimin tsawa
saina kasheki" iyaka tsorata Muhaira ta tsorata hakan yasa ta haɗe jikinta waje guda sai rawar
sanyi take tuni fa fara ficewa hayyacinta tsaki ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin kai tsaye
kuma nasa ɗakin ya nufa dan yau babu abinda zai hanashi karɓar budurcinta. Ƙarar Alarm ce ta
farkar dashi a hankali ya buɗe idanunsa ya ɗauki aƙalla awanni 3 yana baccin kuma ba ƙaramin
daɗin hakan yaji ba tashi ya yi bakinsa ɗauke da addu'a ya shige toilet wanka ya sake yi sannan
ya fito ya shirya cikin wasu suit black colour ko tsayawa gyara gashinsa bai yi ba ya juya ya yi
waje, yana zuwa aka buɗe masa mota ya shiga gidan baya kafin drivern ya ja motar da gudu
suka bar wajen tun a mota ya buɗe system ya shiga dannawa a hankali kuma tym to tym yake
magana da mutane a waya a haka har suka ƙaraso gidan nasa yana shiga ya yi apartment ɗin
su Tyha zaune ya samesu suna hirar cikin sanyin murya suka gaishe shi gyaɗa kansa ya yi
sannan ya ce"get ready" ok sukace masa sannan ya juya ya shige apartment ɗinsa zaune ya
samu Taj ya shirya cikin wasu English wears murmushi kawai ya yi masa sannan suka gaisa
babu wanda ya sake cewa komai a Cikinsu shi ya yi sama shi kuma Taj ya yi waje.
*ASOKORO VILLA*
*RAMLAH POV*
Cikin shashshekar kuka ta ce"ni Mommy nagaji da jin wannan maganar da kike faɗa min kina
gani fa gobene ɗaurin auren amma babu wani abu da kika yi wlh Mommy zan iya mutuwa idan
Khalil ya yimin kishiya ni bazan jure ba mutuwa zanyi Mommy" ta ƙarashe maganar tana
rushewa da wani sabon kukan murmushin takaici Mommy tayi ta ce"kenan Ramlah kina ganin
kamar na gaza ne ko?, kina tunanin zan bari Khalil ya yi aure kenan ko?, kenan duk baki yarda
da abubuwan da nake miki ba kenan idan ba daban ni ba babu yanda za'a yi Khalil ya aureki
dan ko mahaifinsa bazai yarda ba amma yanzu akan wannan ɗan ƙaramin abun kike ɓata ranki
nima nawa yana ɓaci bari kiji indai aka ɗaura auren Khalil da Fateemah gobe to na yadda ki
sauyani a matsayin uwa!" da sauri Ramlah ta kalleta ta gyaɗa mata kai rungume mahaifiyartata
tayi tana goge hawayen fuskarta ta ce"thank you Mommy" murmushi tayi sannan ta ɗago
fuskarta ta