Showing 15001 words to 18000 words out of 44270 words
bazan
fasa ƙonaku ba" turo masa baki gaba tayi sannan ta ce"mun tafi muu" harararta ya yi ya
ce"Allah ya raka taki gona" wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ta sake rufe
idanunta a hankali shima yake sauke numfashi dan ya daɗe rabonda ya yi magana mai tsawon
wannan tashi ya yi daga jikinta wanda ba daban aljanu ba da tuni ya illata ta bai sake
saurarenta ba ya juya ya shige toilet dan watsa ruwa harga Allah ƙamshin turaren yarinyar bai
masa ba duk da yasan ba wani ne ya sanya mata ba sai Taj.
Fitowa ya yi daga wanka yana sanye cikin wata bathrobe ƙirjinsa a buɗe wani lafiyayyen
gashi ne kwance a kansa tudun nononsa Kamar na mace saboda cika nipples ɗin kuma jajaye
dasu, six pack ɗinsa ya fito raɗau ko ba'a faɗa maka ba kasance ba ƙaramin gym yake ba dan
ko ɗan wristling albarka, bedroom slippers kawai ya saka ya juya ya fita gashin kansa na ɗigar
ruwa kamar na Mace, cikin isa yake taka stairs ɗin benen wanda hakan ya sanya Taj juyowa
kallonsa ya yi sai kuma ya ɗauke kai a hankali Zaki ya ƙarasa sakkowa sannan ya zauna
kujerar dake facing tasa taɓe baki ya yi ganin yanda ya ajiye uban Cake a gabansa yana faman
ci girgiza kai ya yi sai kuma ya ce"kwaɗayayye kawai" dariya Taj ya yi yana kai wani slice na
chocolate cake bakinsa ya ce"naji ɗin" saida ya cinye tass sannan ya ɗauki water bottle ya sha
ruwan ya ajiye yana gyatsa ya ce"Alhamdulillah" sai a sannan ya kalli Zaki ya ce"wlh yarinyar
nan aljanu take" "wace yarinya??" harga Allah Zaki ya tambaya dan kwata-kwata ya manta da
wata yarinya, harararsa Taj ya yi ya ce"banson rainin hankali ya kuka ƙare da aljanun" sai a
sannan ya tuna ya taɓe baki yana faɗin"inada abinda yafi wannan yanzu ya kunyi magana da
manager?" gyaɗa masa kai ya yi ya ce"Eh munyi an kammala komai, sannan akwai wasu yara
guda biyu da Abrar ya yimin maganarsu zuwa anjima zanje naga idan zasu yi daman akwai
wani wanda ya ce min yana son guda biyu idan naga sunyi sai kawai na miƙa masa" jinjina kai
Zaki ya yi sannan ya ce"then we should talk later I'm so excited" miƙewa ya yi yana murmushi
ya ce" a wuta lpy" sannan ya yi waje, da kallo Zaki ya bisa sannan ya tashi ya haye sama da
ɗan sauri.
Kai tsaye Taj ɓangaren su Tyha ya nufa yana zuwa ya samesu suna cin abinci da hannu ya yi
mata alama da tazo ta tashi tana ɗaukan veil ɗinta sannan tabi bayansa kai tsaye kuma
motarsa kirar Bugatti suka shiga ya bar gidan.
Bayin Allah nagaji .
# *BA ITA BA CE*
# *ZAKI*
# *MUHAIRA*
# *TAJ*
# *TYHA*
# *RIYADH*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce!*
[8/5, 8:58 PM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!..*
*Ameenatou I Ibrahim*
*Nanameera*.
*nanameera08@arewabooks*
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
```Page 07```
Sheshsheƙar kukanta yaji sanda ya shiga cikin bedroom ɗin, zaune take ta haɗe jikinta waje
guda ta tura kanta cikin cinyoyinta gashin kanta duk ya wargaje taɓe baki ya yi sannan ya
ƙarasa gaban bed ɗin alamun shigowar mutum da taji ya sanya ta ɗago dara-daran idanuwanta
wanda suka jiƙe da hawaye ta kalleshi, shima ita yake kallo kwarjinin nasa idanun ya sanya ta
sunkuyar da nata sai kuma ta cigaba da rera kukanta Zaki bai sake saurarenta ba ya taɓe baki
sannan ya juya ya fice daga ɗakin zaunawa ya yi nan parlon shi kaɗai yake yin tsaki da dukkan
alamu Taj ya haɗashi da wahala, mikewa ya yi ya buɗe wani haɗaɗɗiyar Freezer ya ɗauko
Apple guda biyu da dabinon ajuwa ya dawo ya zauna lumshe idanunsa ya yi saboda wani zaƙin
zuma dana dabinon da suka dakeshi yana matuƙar son abu mai zaƙi a rayuwarsa that's why
koda yaushe baya rasa cake, dabino da chocolate a fridge saida ya ci kusan guda goma
sannan ya rufe robar water bottle ya ɗauka ya ɓalle murfin ya farasha sanyin ruwan ne ya
sanya ya yi saurin ajiyewa dan lokaci ɗaya ƙirjinsa ya riƙe bandama rashin jin magana irinta
Zaki da bazai sha ruwan sanyi ba, idanun da yaji yana yawo akansa yasa ya juya two eyes
sukayi dashi ta ɗauke kanta tana turo baki ɗauke kansa ya yi shima ya cigaba da cin Cake ɗin
gabansa wani takaici ne ya turnuƙe Muhaira kasancewar har sannan aljanun basu gama
sakinta ba. Saida ya gama cin abubuwan daya ɗebo sannan ya miƙe ko kallonta bai yiba ya
shige bedroom ɗin ya rufe ƙofar da kallo kawai Muhaira ta bisa haka kawai taji batasan ganinsa
ko meyasa ohho??, tafiya tayi ta zauna ƙasan carpet ɗin parlon mai wani irin laushi kamar
mage hannayenta ta ɗora kan carpet ɗin tana taɓawa dan ita bata taɓa jin abu mai laushin
wannan ba abu kamar buredi. Gajiya tayi da zaman wajen hakan yasa ta kwanta nan ƙasa not
too long kuma bacci ya ɗauketa dan a matuƙar gajiye take.
A hankali ya buɗe idanunsa, da sauri ya tashi zaune yana kallon agogon dake gefensa babu
kaya jikinsa daga shi sai wando Three-quater milk colour da alama tunda ya yi wanka bai saka
kayan ba, ɗan siririn tsaki yaja sannan ya miƙe ya shige toilet ruwa kawai ya watsa ya fito yana
ɗiga dryer ya ɗauka ya tsane kansa sannan ya sanya wani ribbon baƙi ya ɗauresa har kan
gadon bayansa ya sauka dan gashinsa ko wata macen albarka wata V-neck t-shirt ya sanya
coffee colour sai wandonta wanda ya kasance gajere shima coffee yarin diamond ya sanya a
kunnensa ɗaya sannan ya fito, ƙamshin turaren Aventus Eau de perfume spray ne ya daki
hancinta tana zaune gefen kujera sai baza idanu take idanunta sun faɗa sosai ko ba'a faɗa
maka ba kasan yunwa takeji tsayawa ya yi a parlon yana gyara zaman farin Bluetooth ɗin
kunnensa da kallo Muhaira ta bishi tunda take a rayuwarta bata taɓa ganin mutum mai kyawun
Zaki ba ga iya kwalliya kamar ɗawisu
"Keeee!"
A ɗan firgice ta kalleshi sai taga ba ita yake kallo ba wayarsa yake dannawa kiran wayar ya
shiga yi bayan an ɗaga ya ce"uhnnn sai ka zo" abinda kawai ya ce sannan ya kashe wayar
wata kujera dake facing ɗinta ya zauna yana karkaɗa ƙafa wanda ke nuni da isa da taƙama
kallonta ya yi from head to toe sai kuma ya taɓe baki cikin wata iriyar hucky voice ya ce"hyy
come here" kasancewar tana zuwa makaranta dukda ba kullum hakan yasa ta gane abinda
yake nufi, jikinta babu ƙwari ta ƙaraso wajen tana jan ƙafa zama tayi a gefen ƙafarsa ta
sunkuyar da kanta cikin raunin murya ta ce"gagg...gani" idanunsa a rufe suke ya kifa kansa a
jikin kujerar yana jinta saida ta faɗa sau uku sannan ya ɗago yana kallonta da mamaki take
kallonsa ganin yanda idanunsa suka sauya kala zuwa jaa jijiyoyin kansa duk sun tashi ya haɗa
zufa dukda AC dake kowace kusurwa ta parlon, sosai Muhaira ta tsorata hakan yasa ta fashe
da kuka tana toshe bakinta, ya ilahy tamkar ɗigar dalma haka ya dinga jin kukanta akansa a
hankali hannunsa ya fara kakkarwa ƙoƙarin yake ya yi mata magana amma bakinsa ya gagara
furta komai gashin bashida wata mafita yasa ya kamo hannunta da sauri da miƙe tsaye dukda
yanda takejin jiri harga Allah ita tsoro ya bata hakan yasa ta sake rushewa da wani irin kuka
cikin zafin nama ya janyota ta faɗo kan ƙirjinsa sannan ya riƙe fuskarta gam a hannunsa iyaka
rikicewa Muhaira tayi hakan yasa itama nata jikin ya shiga rawa batasan meke damunsa ba
amma tasan duk abinda zai sa mutum ya dinga ha tofa ba mai daɗi bane ganin taƙi tayi masa
shiru ya sanya ya janyota sosai jikinta har suna jin numfashin juna a hankali ya ɗora fuskarta
akan tasa har sannan kuma ya gagara cewa komai sai zufa wacce ke sakko masa, ita kuwa
Muhaira tsorone ya hanata yin komai sai kawai ta cigaba da rera kukanta ganin taƙi yi masa
shiru ya sanya ya fashe da kuka shima kamar ƙaramin yaro tsabar mamaki batasan sanda ita
tayi shiru ba ta zuba masa idanu tana kallon ikon Allah kamar wannan mutumin yana kuka taɓ
ta faɗa a ranta.
Saida ya yi mai isarsa sannan ya yi shuru yana sauke ajiyar zuciya kusan 5mins kafin ya
janyeta a jikinsa ya tashi batareda ya kalleta ba ya shige bedroom ɗinsa, "taɓ babba da
shagwaɓa taɓɗijan" Muhaira ta faɗa tana kallon ƙofar ɗakin nasa, wani irin murɗawa cikinta ya
yi ta sanya hannayenta ta dafeshi tana sakin kuka yunwa take ji kamar ta mutu rabonta da
abinci har ta manta dan batasan yau yaushe ba balle ta tuna ranar ita burinta ma bai shige ta
tafi daga nan ba ko wama ya kawota?????.
Ganin har kusan ƙarfe 12pm bai sake fitowa yasa ta share hawayenta ta kifa kanta gefen
kujera haka wani baccin rashin abinyi ya sake ɗauketa.
*2:30am*
Wani irin sanyin ne ke ratsa ƙashinta wanda hakan ya nemi ɗaukewar numfashinta batasan
sanda ta miƙe zaune ba tana fashewa da wani kuka gwanin ban tausayi yunwa takeji, ga wani
zazzaɓi daya kawo mata farmaki duk jikinta ciwo yake mata sake kallon ƙofar bedroom ɗin tayi
sai kuma ta tashi da sauri ta koma ta zauna saboda kanta da ya yi wata irin sarawa ganin
batada zarafin tafiya ya sanya sakko daga kan kujerar ta shiga tafiya da rarrafe kamar ƙaramar
yarinya saida taje bakin ƙofar sannan ta miƙe tsaye dakyar tana lumshe idanu, murɗa handle
ɗin ƙofar ta yi ta tura kanta ciki saurin jingina tayi da jikin ƙofar tana toshe bakinta saboda wani
irin ƙamshi da sanyi da suka cure waje guda, sanyin ya yiwa fatarta yawa wasu hawayene suka
shiga zarya akan fuskarta kamar ta juya ta fita amma kuma yunwar da takeji bazata barta tayi
haka ba. Tafiya tafara kamar wacce babu laka a jikinta har ta ƙaraso gabansa kwance yake kan
gadon ya rufe duk jikinsa da duvet. Shashshekar kukanta ce ta sanya ya farka dan kwata-kwata
baya iya bacci waje da hayaniya a hankali ya yaye bargon dake jikinsa kamar ɗazu yanzuma
babu kaya jikinsa da alama haka ya saba baya kwanciya da kaya, kallonta ya yi sai kuma yaja
siririn tsaki ya ce"kee I'm ur mate da har zaki shigo min ɗaki?" girgiza masa kai tayi sai kuma ta
sake fashewa da kuka tana kifa kanta gefen gadon, da mamaki Zaki ya kalleta dan bai saba
ganin mace mai yawan kuka irin haka ba, tsaki ya ya sannan ya sanya hannunsa zai tureta
wani zafi yaji a hannunsa hakan yasa ya ƙara taɓa wuyanta cikin sanyin murya ya ce"are you
sick?" gyaɗa masa kai ta yi ya haɗe rai ya ce"bakida baki?" tashi zaune tayi tana murza
idanunta cikin kuka ta ce"zazzaɓi nakeyi kuma yunwa nakeji" harararta ya yi ya ce"to tunda
yunwa kikeji cinyeni" sunkuyar da kanta tayi tana safe Fashewa da wani sabon kukan, baki
buɗe Zaki yake kallonta dan shi a zatonsa ma ko aljanun ne suka dawo banda haka yarinya ta
dinga kuka babu dalili, haɗe ransa ya yi ya ce"kee wato ke shagwaɓaɓiya ce ko?" Ita dai
kukanta take bata kallesa ba ya ce"rufemin baki ko na kwaɗa miki mari" haɗiye kukan nata tayi
tana jan numfashi. Tsaki Aliyu ya yi sannan ya janye duvet ɗin jikinsa ya miƙe tsaye bai sake bi
ta kanta ba ya fice daga parlon, turo bakinta ta yi tana binsa da kallo sai kuma ta jingina da
prame ɗin gadon mai taushi kamar kujera, lumshe idanunta ta yi tana sauke ajiyar zuciya,
shigowa ya yi hannunsa riƙeda robar dabino sai wani pack na biscuits ajiyewa ya yi gefen
gadon sannan ya juya wajen Freezer ya ɗauko mata fresh milk ajiye mata ya yi ya ce"to
mayunwaciya eat" kallonsa Muhaira tayi ya watsa mata wata harara sai ta sunkuyar da kanta
tsaki ya yi sannan ya buɗe wata ƙofa ya shige ciki, da sauri ta shiga ƙoƙarin buɗe bottle ɗin
robar saidai kwata-kwata batada kwari hakan yasa ta sake rushewa da kuka turo ƙofar ya yi
yana kallonta ya ce"kee mene kuma?" nuna masa robar tayi fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye
ta ce"nakasa buɗewa" wani takaicine ya turniƙeshi ya girgiza kansa ya ƙaraso wajen fizgar
robar ya yi ya buɗe sannan ya miƙa mata ya juya yabar wajen, dolema gobe ya rabu da
yarinyar nan idan ba haka ba sai ta saka masa ciwon zuciya.
Cikin sauri ta shiga cin biscuit ɗin tana korawa da madarar har ta cinye tass dukda babba ne
sannan ta buɗe robar dabinon wani irin lumshe idanu tayi tana taunawa saida ta cinye na
bakinta sannan ta buɗe idanunta tana kallon robar wani kyakkyawan murmushi tayi barinma da
taga zuma kwance akansa a hankali ta sake ɗaukan wani ta ci tana murmushi haka har ta cinye
na robar tass sannan ta ajiye robar sauke robar da ledar biscuit ɗin tayi a gefenta ta gyara
zamanta kan gadon ta kwanta bargon taja ta lulluɓa ta saki wani kyakkyawan murmushi har
saida beauty point dinta suka loma ta ce"ƙamshi" ta faɗa tana rufe idanunta nan da nan wani
bacci mai matuƙar daɗi ya ɗauketa.
Kiraye-kirayen sallar asuba da aka fara ya sanya ya fito da mamaki ya ƙaraso yana kallon
yanda ta ƙugundune cikin lafiyayyen bargonsa tana bacci ɗora hannunsa ya yi a ƙugu tana
kallon zallar rainin hankali irin na yarinyar tsaki ya yi har zai tasheta sai kuma ya rabu da ita da
mamaki ya kalli robar dabinon sai kuma ya tuntsire da dariya mara sauti ganin da ya yi tass ta
cinye komai babu abinda ta rage kallonta ya yi ya ce"witch" sannan ya shige toilet dan ɗauro
alwala.
*Nigeria*
*MAITAMA DISTRICT*
*MA'EESHA POV*
Lumshe idanunta ta yi tana kai chocolate ice-cream ɗin bakinta cikin jin daɗi ta ce"yaya may
god bless yhu" murmushi ya yi ya ce"Ameen Shalele, yanzu dai ina tsarabata zan tafi kinga
dare nayi" murmushi ta yi ta ce"yaya kenan wait for me nagama shan ice-cream zan ɗauko
maka" buɗe baki ya yi zai yi magana wayarsa ta shiga ƙara kallon sunan dake kan screen ɗin
ya yi sai ya ce"kinga idan kin gama kin kawomin ɗaki bye" mikewa ya yi ya fice ta bishi da kallo
sannan ta cigaba da shan ice-cream ɗinta hankali kwance, saida ta shanye tass sannan ta tura
robar ƙasan bed gudun kada Mami ta shigo ta tashi ta zuge trolley ɗinta sannan ta ɗauki wata
leda wacce ta zubo masa kayan ta fice da sauri. Tana ƙoƙarin buɗe handle ɗin ƙofar taji Mami ta
ce"Ma'eesha!" a ɗan firgice ta juyo sai kuma ta saki ajiyar zuciya tana tace a shagwaɓe"Mami
yhu scared me" Mami ta ce"ina zaki je a wannan daren?" turo baki ta yi ta ce"yaya Farooq zan
kaiwa tsarabarsa" wani kallo Mami ta yi mata Wanda yasa ta sunkuyar da kanta ta ce cikin
kakkausar murya"koma ɗaki" sanin halin Mami wani lokacin yasa ta bi gefenta ta shige
apartment ɗinta da gudu tana sakin kuka, girgiza kai Mami ta yi sannan ta shige daman General
ta fito ɗaukarwa wani File.
Yana duba file ɗin gabansa ya ce"kenan me kike nufi?" numfasawa Mami ta yi ta ce"zuwa
yanzu ya kamata ace Ma'eesha ta daina shigewa Farooq coz kasan alaƙar dake tsakaninsu
bayan nan kuma duk sun fara girma akan me zata dinga zuwa apartment ɗinsa da daddare
wannan bai dace ba yallaɓai" zare glasses ɗin fuskarsa ya yi yana kallonta ya ce"
# *BA ITA BA CE*
# *MA'EESHA*
# *FAROOQ*
# *General*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce!*.
[8/6, 5:50 PM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!..*
*Ameenatou I Ibrahim*
*Nanameera*
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
_Hauwa'u Omar writer of A WANI COMPANY Allah ya baki lafiya Masoyiya , pray for my
twinkle wish yhu speedy recovery, Allah ya baki lafiya mai ɗorewa ._
```Page 08```
*RIYADH*
*Al-Olaya Residence*
*8:30am*
Taɓe baki Tyha tayi tana kallon Abra ta ce"wai dan Allah me kike nufi ne?, nifa inason Taj kuma
zanyi duk abinda ya umarceni then what's ur problem?" girgiza kai Abra ta yi ta ce"ke ai saboda
bakida hankali yasa kk gama yarda dashi kwata-kwata bakisan kanki ba bakiga gatan da Zaki
ya yi mana ba, yaƙi siyar damu kamar yanda ya saba siyarda mata ya killacemu cikin gidansa
sannan ya sakamu a makaranta dan mu samu kyakkyawar rayuwa amma ko kaɗan bakiga
wannan ba kin gwammace ki cigaba da iskanci nidai wlh yanda Allah ya rufa mini asiri ya rabani
da wannan rayuwar na barta har abada zan cigaba da karatuna dan nasan watarana zai
amfaneni" tsaki Amrish ta yi ta ce"ai sai kiyi ta yin karatun mukam saidai idan bamu samu masu
tayawa ba amma muddin muka samu wlh sai munji daɗin rayuwarmu" murmushi Tyha ta yi tana
kallon Amrish ta ce"faɗa mata dai ni kunsan wane a target ɗina?" girgiza kai suka yi ta yi
wannan murmushi tana cije baki ta ce"Zaki!" da sauri duk suka kalleta sai kin suka tuntsire da
dariya haɗe rai ta yi Khady ta ce"lallai bakida hankali taɓ ke a ganinki Zaki zai kulaki?, to ni
tunda nake a tarihi ban taɓa jin ya kula wata mace bama iya kaci shidai akawo masa ya siyar ko
ya bada haya amma bansani ba ko sai dare ya yi tashi take zuwa" dariya suka yi