Showing 30001 words to 33000 words out of 44270 words
ya saki kallon fuskarta ya yi sai kuma ya kalli hannunta wanda
yake cikin nasa ya ɗauki ƴan mintuna a wajen kafin ya kwantar da ita ya rufa mata duvet ya fice
daga ɗakin.
Kai tsaye kuma ɗakinsa ya shiga yana zuwa ya ajiye wayarsa sannan ya shige bathroom ya
sakarwa kansa shower saida ruwan ya dakeshi sosai sannan ya dafe kansa wanda ya kejin ya
yi masa nauyi tunani ne kala-kala cikin ransa lokaci ɗaya kuma ya tuna da maganar Dmash
furzar da wani irin numfashi ya yi sai kuma ya yi tsaki kawai ya yi wankansa, fitowa ya yi cikin
wata bathrobe fara dryer kawai ya saka a kansa saboda jiƙewar da ya yi sannan ya kwanta
yana rufe jikinsa nan da nan bacci ya ɗaukeshi. Sai wajen 6:20pm sannan ta farka daga baccin
da sauri ta shiga toilet tayi wanka ta ɗauro alwala sannan ta fito wata jallabiya ta sanya mai
ƙaramin hannu ta gyara gashinta sama-sama dan ita a rayuwarta ta tsani a taɓa mata kanta ko
da itace kuwa parlon ta fito saboda wata irin yunwa da take ji da sauri tayi hanyar kitchen,
dube-dube ta shiga yi dan ganin ko zata samu abinci tura baki tayi ganin babu komai a kitchen
ɗin kuma tsoron kunna gas take gudun kar abinda ya faru da ita ɗazu ya sake faruwa, fitowa
tayi tana jan ƙafa da sauri ta ƙarasa wajen ledojin da tagani tana zuwa ta shiga buɗewa
takeaway ne guda uku a ciki na farkon ta buɗe taga jallof rice ce wadda taji wadatattun kayan
haɗi ƙamshinta ne bai yi mata ba hakan yasa ta buɗe ɗaya takeaway ɗin fried rice tagani a ciki
tayi murmushin jin daɗi sannan ta ɗauko ɗayan ta buɗe taga gasasshiyar kaza da sauri ta
ɗauko sannan ta dawo ƙasan carpet ɗin ta baje ta hau cin abincinta hankali kwance tass ta
cinye shinkafar kazar kawai ta rage amma itama taci tafi rabi sannan ta ɗauka ta mayar ledar ta
buɗe fridge ta ɗauki ruwa tasha sannan ta koma ɗaya parlon tayi zamanta tana kallo.
Fitowa ya yi cikin wata t-shirt da 3quater kai tsaye wajen ledojin ya nufa saboda wata irin yunwa
da yake ji buɗe ledar ya yi yaga empty takeaway a ciki da mamaki ya kalli take away ɗin sannan
ya buɗe ɗayan jallof rice ya gani itama kuma da alama taci dan ba haka ya ajiye ba yana buɗe
ɗayan yaga babu kazar sai ƴar kaɗan a fusace kamar zai yi kuka ya yi ɗaya parlon yana wuci
da sauri ta ɗago kanta jin yanda ya buga ƙofar yana kallonta ransa a haɗe kamar hadari ya ce"
# *Unconditional love*
# *Destiny*
# *SQUAD 2024*
# *BA ITA BA CE!*
# *Ameenatou I Ibrahim*
# *Nanameera ce!✍️*.
[8/10, 11:19 AM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!..*
*Nanameera ce ✍️*
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
```Page 13```
# *DESTINY*
"Keeeee!" a ɗan firgice Muhaira ta kalleshi sai kuma ta turo baki tana cigaba da kallonta kwafa
ya yi sannan ya ce"ubanwa ya ce kije ki cinyen abinci ko ke kika siyamin? nabaki permission
ne?" kallonsa tayi da manyan idanunta sai kuma ta zumɓura baki tana wasada fingers ɗinta a
tsawace ya ce"ba dake nake magana ba!" sosai ta razana sai kuma ta fashe da kuka tana
murza idanunta sakar baki ya yi yana kallon ikon Allah tsakanin shi da ita kowane ya dace ya yi
kuka??, ƙarasowa ya yi cikin takunsa na isa ya zauna kujerar da take fuskarsa babu alamun
rahama ya ce"tell me meyasa kika cinyemin abinci?" cikin shashshekar kuka ta ce"koba yunwa
nake jiba shiyasa naci amma kana yimin faɗa to zan biyaka" wani kallo ya yi mata sai kuma ya
ce"da gaske?" gyaɗa masa kai ta yi tana murza idanunta. Girgiza kansa ya yi yana murmushi
ya ce"shikenan biyani abincina tunda bake kika siyamin ba" kallonsa ta yi da idanunta wanda
ruwa ya kwanta akai ta ce"to zan dafa maka wani" gyaɗa kansa ya yi ya ce"hurry up" sannan ya
tashi ya fita, tura bakinta tayi wanda sukai jajur dasu sannan ta miƙe kamar wacce aka yiwa
dole tayi waje kai tsaye kitchen ta nufa tsayawa tayi tana tunanin abinda zata dama masa sai
kuma ta yanke shawarar tayi masa shinkafa tunda ita ta cinye masa dakyar ta iya kunna gas ɗin
dan gaba ɗaya ta tsorata dashi, cikin sanyin take yin aikin dan lokaci ɗaya jikinta ya fara yi mata
ciwo amma kuma tsoron faɗan da zai yi mata yasa ta daure ta cigaba above 2hrs kafin ta
kammala dafa shinkafar da bata shige 1cup ba ko kaɗan batada saurin aiki kuma hakan ya
samo asali ne dalilin ciwonta zuwa lokacin idanunta sun kumbura sosai gabaɗaya jikinta rawa
yake da sauri ta kwashe a plate sannan ta fito parlon.
Zaune ta sameshi yana danna system ɗinsa yanda ya bada attention ɗinsa zaka gane abu
yake gabatarwa mai muhimmanci a gaban table ɗinsa ta ajiye masa plate cikin sanyin murya ta
ce"gashinan na biyaka" kusan 5mins sannan ya kalleta ya kuma kalli plate ɗin ya ce"ni abokin
wasanki ne?" sunkuyar da kanta tayi ya ce"za ki ɗauke daga gabana ko saina ɓata miki rai
shashasha kawai" da mamaki Muhaira ta kalleshi cikin rawar murya ta ce"amm.. amma kaine
kace na biyaka kuma dakyar nadafa wlh" rufe system ɗin ya yi yana yi mata wani kallo ya
ce"wai ke bakida tunani ne what are u thinking ni ne zanci abinda kika dafa kina ƙazama are
you mad?" tuni hawaye suka fara ambaliya akan fuskar Muhaira cikin kuka ta ce"wl..wlh banyi
ƙazanta ba kaci kaji"
"Tassssssssssss"
A matuƙar razane ta kalli plate ɗin abincin wanda ya fashe duk abincin ya tarwatse a parlon
cikin tsananin ɓacin rai fuskarsa har wani jaa ta yi ya ce"get out of my side!!" da gudu Muhaira
ta shige bedroom ɗinta tana kuka, faɗawa kan gadon tayi ta fashe da wani raunataccen kuka an
daɗe ba'a ɓata mata rai irin na yau ba wani irin kuka ta dinga yi tana jan numfashi a hankali
kuwa jikinta ya fara rawa sai kakkarwa sanyi take wani irin amai taji ya taso mata da gudu ta
tashi ta shiga toilet tana zuwa ta fara yunƙurin amai madadin tayi aman wani abun sai wani
guda gudan jini ya fara fitowa daga bakinta dafe kanta tayi sai kuma ta tafi luuuuu ta faɗi a ƙasa
sumammiya.
Murmushi Taj ya yi ya ce"karka damu Sir nayi maka alƙawarin kawo maka yarinyar nan har gida
kawai kabani 24hrs" numfasawa Dmash ya yi ya ce"nayarda dakai Taj sbd haka go on"
sunkuyar da kansa ya yi alamar girmamawa sannan ya juya ya fita, furzar da numfashi Dmash
ya yi ya ce"Zaki taka ta ƙare". Ƙarfe 8:20am ya fito daga bedroom ɗinsa sanye yake cikin wasu
suit coffee colour ya tufke kansa da ribbon fari kunnensa ɗaya ɗauke da yarin diamond kallon
parlon ya yi wanda yake tsaf dashi kamar ba wanda ya ɓata ba jiya sai wani irin ƙamshi mai
daɗi ne ke tashi a parlon taɓe baki ya yi yana ƙarewa parlon kallo da mamaki ya kalli agogon
hannunsa ganin lokaci yaja har haka gyara zaman Bluetooth ɗin kunnensa ya yi cikin wata
murya ya ce"yarinyar nan ta fita school ne?" "No sir she didn't come out at all" gyaɗa kansa ya
yi sannan ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga ƙarewa parlon ya yi ganin komai tsaf dashi kamar
ba yarinyace a ciki ba taɓe baki ya yi sannan ya ƙarasa bedroom ɗin da mamaki yake kallon
kan bed ɗin ganin babu kowa da alama ma ba'a kwanta akansa ba, kallon kofar toilet ɗin ya yi
sai kuma ya ƙarasa ya yi knocking yana faɗin"keee! keee come out" shirun da yaji ne yasa ya
murɗa handle ɗin without second thought kuma ya tura kansa cikin toilet ɗin. Cikin hanzari ya
ƙarasa inda ya ganta kwance yana zuwa ya ɗagota da mamaki ya kalli wajen ganin gudan jini
wanda ya daskare a wajen sosai hankalinsa ya tashi amma ko kaɗan babu hakan a kan
fuskarsa da sauri ya ɗauketa yana miƙewa tsaye idanunsa ya sauka kan sink ɗin ganin duk
daskararren jini yasa ya yi waje da sauri ya yi waje tun kafin ya ƙarasa driver ya buɗe masa
motar yana shiga shima ya shiga kai tsaye kuma asibiti suka nufa, rungumeta ya yi sosai a
jikinsa jin yanda jikinta ya yi sanyi klao da alama ta daɗe da sumewa dan duk jikin nata ya saki
sosai kiran Taj ne ya shigo wayarsa gyara Bluetooth ɗin ya yi daga ɗaya ɓangaren Taj ya
ce"Zaki kana gida?" girgiza kai ya yi ya ce"no" Taj ya ce"daman..." "Please Taj I'll call you back"
da mamaki Taj ya kalli screen ɗin wayar sai kuma ya taɓe baki ya shige toilet, har suka ƙarasa
asibitin bai ɗauke idanunsa daga kanta ba.
*Asokoro Villa*.
Murmushi Dad ya yi yana kallon Khalil ya ce"General ya amince da aurenka da Ma'eesha sbd
haka yanada kyau ka fara shiri dan ba wani lokaci za'a ɗauka ba" murmushi ya yi ya ce"wowww
Dad thank you I really appreciate naji daɗi sosai" girgiza kansa ya yi dan ba tun yau ba yasan
irin son da Khalil yakewa Ma'eesha ko sanda zai bar ƙasar saida ya zubar da hawaye sbd zai
rabu da ita gashi cikin ikon Allah kuma zai aureta bayan wasu shekaru, da sauri Mommy tabar
wajen ta shige bedroom ɗinta zaune ta samu Ramlah tana kallo a TV tsaki ta yi sannan ta
ce"keee maza-maza tashi zamuje wani waje" da mamaki Ramlah ta ce"Mommy ina zamu je da
yammacin nan?" tsaki Mommy tayi tana yafa veil ɗinta ta ce"idan bazaki tawo ba ki zauna kina
tambayata shashasha kawai" tana faɗin hakan tayi waje, buga ƙafarta tayi aƙasa sannan ta
miƙe tabi bayan Mommy tana sauke veil ɗin dake kanta kasancewar Abaya ce ajikinta. Convey
ɗin da sukaji yasa Dad ya ce"ina kuma ta sake fita da yammacin nan?" taɓe baki Khalil ya yi ya
ce"Maybe ko wani abunne ya taso mata urgent, nima zuwa anjima nakeson mu tafi gida" girgiza
kai Dad ya yi ya ce"but kafara tsayawa ta ƙara samun sauƙi sbd kaga can idan ka koma babu
mai kulawa da ita" gyaɗa masa kai ya yi sannan ya miƙe tsaye ya ce"zan je asibiti" ohk Dad ya
ce sannan ya juya ya fita.
Shiru General ya yi yana saurarenta har ta kammala maganar sannan ya ce"then me kikeso
nayi akai?" murmushi Mommy tayi ta ce"A'a kawai daman naga ya kamata ace na sanar maka
ne shiyasa" bai ce mata komai ba ya cigaba da sipping coffee ɗinsa, sakkowa tayi daga saman
tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya murmushi Mommy tayi ta ce"Shalele an tashi" shiru Ma'eesha
tayi mata tana zuwa ta zauna gefen General ta ɗora kanta a cinyarsa shafa kanta ya yi sannan
ya ce"Shalelena meya faru?" shiru tayi masa hakan yasa ya leƙa fuskarta ƙuri tayi masa da
idanu ya sake cewa"ƴar gidan Father tell me kedawa?" ganin tayi banza yasa Mami ta kalleta
cikin ɓacin rai ta ce"ke bakijin ana yi miki magana ne kikayi shiru Ma'eesha ki kiyayeni fa!" ko
kallonta Ma'eesha bata yi ba hakan yasa General ya sake kallonta idanunta a buɗe suke balle
ace bacci take ɗago kanta ya yi ya ce"ƴar Baba meyasa kika yi shiru" a hankali ta ɗora
hannayenta bisa fuskarsa ta shiga shafawa sai kuma tayi murmushi da tsananin mamaki duk
suke kallonta General ya ce"faɗa min mene ke yi miki ciwo?" bakinsa tabi da kallo sai kuma ta
girgiza masa kai miƙewa tsaye ya yi yana riƙe da hannunta ya ce"Ma'eesha bazaki magana
ba?, ni abokin wasanki ne? Ma'eesha I'm ur mate da nake miki magana nd u remain silence?"
da kallo kawai Ma'eesha ta bishi sai kuma ta faɗa jikinsa tana sakin wani kuka mai sauti" da
sauri General ya kalleta sai kuma ya durƙusa yana kallon kyakkyawar fuskanta ya ce"Ma'eesha
baki jin abinda nake faɗa miki ne ko kunnenki na yi miki ciwo ne?" bakinsa ta ƙalla sai kuma ta
girgiza masa kanta da hannu ta nuna masa bakinta sai kuma ta nuna masa kunnenta da sauri
Mami tace"Ma'eesha baki jin abinda muke faɗa, tell us Ma'eesha" ta faɗa tana jijjigata fashe tayi
da kuka tana rungume Mami, cikin tashin hankali Mami ta ɗago fuskarta ta ce"Ma'eesha kinji
abinda na faɗa?" kallon bakinta tayi sai kuma ta girgiza mata kai tana goge mata hawayen dake
zuba a fuskarta. Cikin kuka Mami ta ce"inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun Ma'eesha wane yayi
miki haka?, Wa ya kurumtaki?, me kika yiwa wani? Inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun mun shiga
uku" da sauri Mommy ta rufe mata baki tana kuka itama ta girgiza mata kai ta ce"ki daina cewa
an shiga uku zaki ƙara wata masifar kawai muyi mata addu'a koma wane ya yi mata wannan
abun Allah ya saka mata kuma ya bi mata haƙƙinta" fashewa Mami ta yi da kuka tana dafe
kanta ta ce" me tayiwa wani?, yarinyar da bata shiga harkar kowa babu ruwanta da mutane
wane mara imanin ne ya cuci rayuwarmu" ta ƙarashe maganar tana sakin wani kuka mai gunji.
Miƙewa General ya yi wanda idanunta suka kaɗa sukayi wani irin jaaa waje ya yi ko gabansa
baya gani sake tashi Mami tayi ta koma inda Ma'eesha take zaune tana kuka ta kama hannunta
ta ce"Ma'eesha kinyi faɗa da wani ne ko akwai wanda ya ce zai yi miki wani abu?" girgiza mata
kai Ma'eesha ta yi takama hannun Mami tana ɗorawa akan bakinta ta girgiza mata kai
rungumeta Mami tayi tana sake fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya ita kaɗai ce ƴar
data mallaka kuma take burin taga tayi aure kodan su samu ƙarin zuri'a tunda su basuda yawa
sai gashi an samu wani mara imanin ya kurmantata dan babu shakka wannan abun ture akai
mata ko jifa. Shigowa Farooq ya yi da mamaki yake kallonsu duka dan shi tunda sassafe ya fita
ƙarasawa ya yi ganin yanda suke kuka kamar waɗanda aka yi mutuwa ya kalli Mommy ya
ce"Mommy what happened?" kasa bashi amsa Mommy tayi saboda kuka da yaci ƙarfinta hakan
ya sa ya ce"Mami dan Allah ku sanar dani abinda yake faruwa" kallonsa Mami tayi da idanunta
wanda suka yi wani irin jaa ta ce cikin kuka"Farooq sun kurmantata sun cucemu Ma'eesha bata
jin abinda muke cewa kuma bata magana" cikin tsananin tashin hankali ya ce"what!!!?"
ƙarasowa gaban Ma'eesha ya yi ya kama hannunta ya riƙe cikin nasa cikin wata iriyar murya
mai nuna zallar tashin hankali ya ce"Shalelen Father ki cemin ba haka bane abinda Mami
tafaɗa ki yimin magana dan Allah Ma'eesha kice wani abu ko naji sanyi a raina nasan halinki da
wasa dan Allah Ma'eesha stop joking tell me the truth kar zuciyata ta buga kiyimin magana naji
muryarki kinji shalelen ƙanwata" da idanu kawai Ma'eesha ke binsa da kallo dan yawan
maganar da ya yi mata yasa ta gaza fahimtar koda magana ɗaya abu ɗaya kawai tasani shine
yana magana ne akan abinda ya sameta hakan yasa ta nuna masa bakinta da kunnenta
sannan ta girgiza masa kai. Durƙushewa Farooq ya yi kamar ƙaramin yaro ya shiga rera kuka
wanda ya daɗe bai yi irinsa cikin rayuwarsa ba kuka ne wanda yake fitowa tundaga zuciyarsa
yana matuƙar son Ma'eesha bashida burin daya shige ganin farin cikinta koda yakeson ya
rabata da iyayenta yana yine sbd hakan ya kasance ƙudirinsa amma bazai taɓa mance
Alkhairin Ma'eesha a gareshi ba bazai manta irin so da ƙaunar da take nuna masa ba tabbas
duk wanda ya yi mata wannan aika-aikar to ɓa ƙaramin maƙiyinta bane. General ne ya shigo
cikin sauri gabaɗaya ya fice hayyacinsa wasu doctors ne guda biyar suka shigo sai Farooq da
His Excellency Muhammad Tanka da sauri Khalil ya ƙarasawa wajenta ya kama hannayenta
cikin sanyin murya mai nuna rauni ya ce"
_Ƙaddara a bace wacce bawa baya iya tsallaketa kowa da kalar tasa ƙaddarar kuma kowa da
akwai silar tasa ƙaddarar ba'a iya guje mata domin ita ta kasance rubutacciyar aba ce tamkar
zanen dutse haka take duk yanda zakayi bazaka iya gogeta ba no matter who are you or what
you have nobody can change his/her destiny either good or bad ya rabbi ka bamu ikon cinye
duk wata jarrabawar da zaka yi mana_.
# *Love*
# *Destiny*
# *Manifestation*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce ✍️*.https://chat.whatsapp.com/BghAYLLnNSvK6y3XpGoE9I
*BA ITA BA CE!..*
*Nanameera ce ✍️*
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
```Page 14```
"Eeshana da gaske baki jin abinda nake faɗa? eeshana ki ce ba gaskiya bane abinda ake faɗa
min talk to me please" ya faɗa yana jijjigata, fashewa tayi da kuka ta rungumeshi tana girgiza
masa kai Dr Sabo ne ya ƙaraso wajen yana kallonsu ya ce"aje da ita asibiti maybe agano
abinda ke damun nata" okay kawai Khalil ya ce sannan ya miƙe tsaye yana riƙe da hannunta
sukayi waje ajiyar zuciya Mami ta shiga saukewa tana binsu da kallo har suka fice sannan ta
tashi da sauri ta haye sama da kallo Mommy ta bita sannan ta tashi itama ta shige nata
apartment ɗin, cikin tashin hankali take cewa"wlh Fulani bazan iya jurewa ba zuciyata bazata
iya ɗauka ba tashin hankalin ya yimin yawa Ma'eesha fa dan Allah" daga ɗaya ɓangaren ta
ce"haba Asma'u mene haka?, ki yarda da ƙaddara mana babu wanda ya isa ya sauyata koma
wane ya yiwa Ma'eesha mugunta ai Allah yana ganinsa kuma zai yi maganinsa saboda haka
karki sake cewa zaki damu kanki ku tayata da addu'a Allah ya bayyana asirin koma wane idan
kuma Allah ne ya ɗora mata to shi zai yaye mata zuwa gobe ko su Jakadiyane zasu zo sai su
tawo da Aleema" gyaɗa mata kai Mami tayi saboda kuka da