Showing 3001 words to 6000 words out of 44270 words

Chapter 2 - BA ITA BA CE! Free Books by Nanameera.pdf

11 May 2025

2485

amma ba bacci take ba ajiye kofin hannunta
ta yi sannan ta shiga kamata tana faɗin" Dada tashi, tashi kinji na dama miki kokon tashi kisha
sai kisha magani" dakyar Dada ta buɗe idanunta ta kama hannun Muhaira ta miƙe daga
kwancen ɗora kan Dadar tayi akan ƙirjinta dukda nauyin da tayi mata amma ko kaɗan hakan bai
dameta haka ta ɗauki kofin kunun ta kai mata bakinta, girgiza kai Dada ta yi tana riƙe hannunta
ta ce"A'a Muhaira bazan iya sha ba akwai abinda nakeson na faɗa miki tabbas wannan cutar
tawa bata tashi ba ce saida... wani irin jan numfashi ta yi tana saukeshi a hankali runtse
idanunta tayi hawaye suka shiga rige-rigen sakkowa kan kuncinta alama ta yi mata data bata
kunnenta a hankali Muhaira ta kara kunnen nata kusada fuskar mahaifiyartata dan taji me zata
faɗa mata. Above 5mins tana yi mata magana zuwa lokacin kuma banda hawaye babu abinda
Muhaira ke yi gaba ɗaya tunaninta ya tsaya cak batada wata sauran dabara zuwa sannan kuma
bata iya fahimtar abinda mahaifiyar tata ke faɗa mata. Shirun da taji Dada tayi yasa ta kalleta
wata irin razananniyar ƙara ta fasa wacce ta yi daidai da shigowar Falmata cikin bukkar da sauri

ta ƙaraso tana kallonsu duka ganin yanda Muhaira ta ƙamƙame Dadan har sannan kuma kuka
take yi kallo ɗaya Falmata ta yi mata tasan cewa Ubangiji ya karɓi abarsa, ikon Allah kenan
babu yanda mutum ya iya kamar yanda Papi ya mutu haka yanzu itama Dada tabi bayansa

"Dadata! dan Allah dan Annabi ki tashi karki mutu ki barni banida kowa Dadaaaa...ki taimaka ki
tashi Dada ko kinfi son nayi kuka har ƙarshen rayuwata?, banida kowa Dada kema kuma bakida
kowa Papina ya tafi har yau bai dawo ba kema shine zaki bisa??? kenan duk baku sona?
meyasa Dada?, me nayi muku?, ina zani yanzu? wane zai kula dani Dadaaaaa..." maganar ta
tsaye a maƙoshinta sakamakon wani irin nauyi da zuciyarta tayi da gudu ta miƙe ta fita daga
bukkar saboda wani irin amai daya tawo mata saidai me???? madadin amai na abinci ko kuma
na ruwa wani irin guda-gudan jini ne ya shiga fitowa daga bakinta sai kuma ta faɗi nan ƙasa
sumammiya.

Allah sarki rayuwa tabbas babu abinda ke ɗorewa sai ikon Allah cikin ɗan lokaci ƙalilan
Muhaira tarasa iyayenta guda biyu wanda hakan shine mafarin ƙaddararta, tabbas labarin
rayuwarta akwai taɓa zuciya, musamman daya kasance tanada ƙarancin shekaru Hakazalika
kuma babu wani wanda zata kama ta ce wannan danginta ne kasancewar iyayen nata Fulanin
tashi ne, tarasa gatanta tun tana jaririya sannan kuma ta sake rasa waɗanda suka maye mata
gurbin wannan gatan data rasa ya zatayi??dawa zata rayu?? wace irin ƙaddara ce ke bibiyar
rayuwarta??...

*17 years*.


*Maitama district, Abuja*
*No:113*.

*Mai Zamani pov.*

Wani zazzafan numfashi ya sauke bayan ya saki curtain ɗin, a hankali cikin tafiyarsa mai nuni
da isa ya ƙaraso gefen kujerar dake gaban gadon ya zauna sanye yake da wata Polo T-shirt
white colour sai kuma wani Cargon Three-quater black colour a jikinsa ba wani fari bane can
haka zalika kuma ba baƙi bane yana dai da haskensa dai-dai misali, ɗan ƙaramin tsaki yaja
sannan ya buɗe system ɗin gabansa ya shiga dubawa. Duba da irin yanda yake kallon system
ɗin zaka fahimci tabbas wani abu mai matuƙar muhimmanci yake gabatarwa, turo ƙofar ɗakin
tayi bakinta ɗauke da sallama a ciki ya amsata sannan ta ƙaraso gabansa zama tayi gefensa
tana sanye cikin wani material black colour mai adon flower pink ɗinkin doguwar riga A-shape
mug ɗin gabanta ta ajiye masa gefen table ɗin gabansa ta cigaba da kallon abinda yake, above
tens minutes sannan ya kammala ya rufe system ɗin sai a sannan ya ɗago yana kallonta fara
ce tass kuma asalin kyakkyawa dan ko ba'a faɗa maka ba kasan ita ɗin ba ta kasance cikin
ƙabilar Hausawa ba ganin irin kallon da yake mata ya sanya ta sunkuyar da idanunta ƙasa tana
wasa da fingers ɗinta masu ɗauke da zanen flower wacce tayi matuƙar amsar farar fatarta taɓe
baki ya yi sannan ya ɗauki mug ɗin data ajiye a hankali kuma yakai tea ɗin bakinsa wani runtse

ido ya yi saboda wani irin zaƙi da yaji har cikin kansa da sauri ya ajiye mug ɗin yana mata wani
hargitsatsen kallo ya ce "Ma'eesha I'm play with you?" kallonsa ta yi fuska a kwaɓe ta ce" A'a
yaya I'm sorry wlh banson sugar ya yi yawa ba I'm so sorry" kallonta ya yi from head to toe
sannan ya yi tsaki ya tashi bai tsaya cigaba da jin abinda take faɗi ba ya ɗauki wayarsa ƙirar
iphone 14pro max ya yi waje. Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe ƙirjinta sanin halin yayan nata sai
kuma ta miƙe itama tabi bayansa.


A nutse take taka stairs ɗin benen har ta sakko gaba ɗaya, ya rabbi wani irin haɗaɗɗen
parlon ne irin mai tafiya da imanin mutum ɗin nan komai na cikinsa golden colour ne tun daga
kan kujeru, curtains, carpet, center table even bulb da suke parlon golden colour suke bayarwa
banda sanyin A.C babu abinda ka keji a parlon sai kuma wani irin daddaɗan ƙamshin da yake
fita daga kowace kusurwa ta parlon ko ba'a faɗa maka ba kasan wannan parlon bai yi kamada
na ƙananan mutane ba ko kuma basu ji da ƙaramin arziƙi parlon ne irin wanda koda a cikin Villa
yake sai ance ya haɗu iya haɗuwa, parlon ne na irin manyan nan wanda suka jiƙu da manyan
kuɗaɗe, a hankali ta ƙaraso cikin parlon inda ta hangin iyayen nata. Zaune yake kan kujera
Three seater yana sanye da wata dakakkiyar shadda Madam gezner blue black ɗinkin jamfa da
babbar riga idanunsa maƙale da wani farin tabarau yayinda yake kallon jaridar dake hannunsa
da alama kuma karantawa yake duba da yanda ya bada full attention ɗinsa a wajen magidancin
mutum ne dan aƙalla zai kai irin 60yrs ɗin nan amma idan har kayi duba da yanayi na siffarsa
zaka iya cewa bai fi 46yrs saboda kwarjini da kuma hutu wanda ya zauna masa. Major General
Ibrahim Tijjani mai Zamani kenan wanda ke riƙeda muƙamin shugabannin sojoji na ƙasa kuma
sanannen ɗan kasuwa mai tashen arziƙi mamallakin Companyn mai Zamani corture indai
magana kake ta kuɗi to tabbas M.G Ibrahim ƙarshene sannan kuma uwa uba ya kasance
mutum mai taimakon na ƙasa dashi wannan shine dalilin daya sanya yake da mabiya daga
kowacce fuska. Da sauri ta zauna gefensa tana shagwaɓe fuska ta ce" Father narhhhh!!"
murmushi ɗauke a fuskarsa yake kallon tilon ƴar tasa kallo mai nuna zallar so da ƙaunar da
yake mata shafa kanta ya yi cikin kamilalliyar muryarsa ya ce" Shalelen Father what's wrong
uhn" turo baki gaba tayi ta ce" Father ko ba yaya Farooq bane" da sauri Farooq wanda yake
zaune kujerar dake opposite tasu ya ɗago yana kallonta amma bai ce komai ba, murmushi
Father ya yi sanin halin rigimarta ya ce"keda yayan naki ne kuma yanzu?, To kiyi haƙuri bazai
sake ba ya tuba" taɓe baki ta yi sannan ta ce"Father kace masa ya kaini saloon ɗin" dafe kansa
ya yi yana zare glasses ɗin idanunsa ya ce" ohho!! Shalelen Father rigima ko?, Ki tambayeshi
da kansa idan yaga zai rakaki fine idan kuma yanada wasu uzurin sai ki tafi da guards zasu
jiraki" girgiza kai tayi ta ce"nooo! nasan ma zai rakani" kallon Farooq ta yi wanda yake kallonsu
tun ɗazu ta ce"yaya zaka rakani ko?" da sauri ya gyaɗa mata kai ko babu komai ya samu damar
da zai gasa mata aya a hannu, murmushi ɗauke a fuskarta ta kalli Father ta ce"yawwa Father
kaji ko ya ce zai rakani" numfasawa Father ya yi ya jinjina mata kai sannan ya miƙe yana riƙe da
hannunta ya ce"na tayaki murna amma karku daɗe zan fita byee" gyaɗa masa kai ta yi tana
murmushinta mai kyau ta ce"ok Allah ya tsare hanya Father narh" kissing goshinta ya yi sannan
ya yi waje.

# *BA ITA BA CE*
# *Human trafficking*
# *Destiny*
# *love*.
# *SQUAD 2024*

# *Nanameera ce!*.
[8/1, 7:28 PM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!..*


*MIKIYA WRITERS ASSO...*




*nanameera08* _arewabooks_.

*@Nanameera08* _wattpad_.


*Nanameera*.


# *SQUAD 2024*


```Page 03```



Kallon Farooq ta yi ganin ya miƙe tsaye sai kuma ta ce" yaya bari na sauya kaya" taɓe baki ya
yi bai ce mata komai ba ta juya tabar parlon, kwafa ya yi sannan ya yi waje. Haɗaɗɗen bedroom
ne kana ganinsa kasan an kashe kuɗaɗe wajen haɗashi komai a bedroom ɗin purple colour ne
coz ita ce favee colour ta Ma'eesha, kallon gefen bed ɗin ta yi sa kuma ta saki murmushi a
hankali ta ƙarasa wajen ɗaukan Teddy bear ɗin ta yi wanda ita ce ta kasance purple colour ce
sannan tayi waje.


*Haj.Salma pov*

Zaune take kan royal cusion ɗin dake zagaye da parlon idanunta bisa TV tana kallon show ɗin
da ake haskawa a MBC Max turo ƙofar tayi hakan yasa ta ɗago dara-daran idanuwanta tana
kallonta sai a sannan na ƙare mata kallo fara ce tass kuma asalin kyakkyawa kallon Ma'eesha

nayi sannan na kalli Haj.Salma ko ba'a faɗa maka ba kasan Ita ɗin mahaifiyarta ce domin babu
inda suka sha banban ta kammani zama tayi gefenta tana ɗora kanta a cinyarta ta ce"Mami
zamu tafi"shafa kanta Mami tayi sannan ta ce"to Shikenan sai kun dawo Allah ya tsare hanya"
Ameen Ma'eesha ta ce sannan ta miƙe dan fita daga parlon
"Ma'eesha!"

"Na'am Mami"

Kallon fuskarta ta yi sai kuma ta ce"where is your mask?" langwaɓar da kai tayi sai kuma ta
ce"Mami yana cikin jakana" harararta Mami ta yi ta ce"oh daman amfaninsa kenan?, Bring it out
my friend!" turo baki gaba ta yi sannan ta buɗe ƴar ƙaramar jakar hannunta ta zaro mask ɗin

"saka shi"

Kallon Mami tayi taga ta haɗe fuska babu alamar wasa sai kawai ta maƙala face mask ɗin
sannan ta fice daga parlon tana buga ƙofar, girgiza kai Mami ta yi sannan ta ce"Allah ya shirya
ki Ma'eesha". Zaune ta sameshi a motar yana danna wayarsa murmushi ta yi ta ce"sorry yaya I
kept yhu waiting" ɗan siririn tsaki ya yi sannan ya ajiye wayar ya juya yana kallonta, sanye take
da wata turkish Abaya black colour tayi rolling veil ɗin a kanta sosai tayi kyau tamkar balarabiya.
Zazzafan numfashi ya furzar kafin ya kama hannunta ya riƙe cikin nasa cikin cool voice ɗinsa ya
ce"uhnn kinsan ai ina jiranki kika barni" langwaɓar da kanta tayi tana kallonsa idanunta rau-rau
ta ce"I'm sorry yayana" girgiza kansa ya yi sannan ya saki hannunta ya kunna motar, akwai ƴar
tafiya daga parking lot ɗin gidan zuwa gate dan kwalta ce aka shimfiɗa tamkar titi, tsaki tayi tana
kallon sojojin da suke bakin street ɗin gidansu har zuwa cikin gidan, ita kam har ga Allah
batasan irin wannan tsaron da ake musu. Kallonsa tayi ganin inda ya yi parking motar sai kuma
ta ce"yaya naga ka tsaya anan?" banza ya yi mata ya ciro wayarsa ya shiga dannawa abinsa
haɗe rai Ma'eesha ta yi ta kuma cewa"yaya Farooq kaga da wajen saloon ɗin can kuma kai kayi
parking anan muƙarasa please kaga Father ya ce..."


"Heyyyyyyyy! yimin shiru aku kawai bazan ƙarasa ba anan zan tsaya sauka kije ayi miki idan kin
gama kizo mu tafi or else..." kallonsa tayi tuni hawaye ya fara sintiri akan kuncinta cikin kuka ta
ce"dan Allah yaya kayi haƙuri kaga idan naje ƙafana ciwo zai yimin dan Allah ka ƙarasa dani" ba
zaka taɓa cewa da Farooq take magana ba dan ko inda take bai kalla ba danna wayarsa kawai
yake, sanin halinsa na kaifi ɗaya ya sanya Ma'eesha ta sauka daga motar tana tafe tana kuka
har ta tsallaka ɗaya side ɗin, tafiyar wajen 5mins ce ta kawota bakin shagon a hankali ta tsaye
ta goge idanunta sannan ta shiga ciki. Above 1hour kafin a gama gyara mata kan, kasancewar
ba kuɗi take biya ba already an biya ya sanya ta fito dan su tafi gida saidai me??? tana zuwa
inda tabar Farooq ɗazu taga babu shi babu alamarsa kuma babu motar ga wani irin ciwon ƙafa
da take yi zama tayi gefen titin ta rushe da kuka tamkar jaririya tana yi tana jan numfashinta
saboda asthmarta dake shirin tashi, ta ɗauki aƙalla awanni biyu zaune a wajen kafin ya dawo da
sauri ya ƙaraso gabanta yana kallon yanda ta dunƙule waje ɗaya ya dafata, da sauri ta ɗago

kanta ta kallesa sai kuma ta sake rushewa da wani kukan, kyakkyawan murmushi ya yi sannan
ya kama hannunta cikin sigar rarrashi ya ce"ya isa tawo ƴar Babyn Father daina kuka kinji"
ganin taƙi miƙewa yasa ya sanya hannayensa duk biyun ya ɗauketa kamar Baby ya sanyata a
motar. Zama ya yi sannan ya ɗorata akan ƙirjinsa ya rungumeta tamkar wacce ake turata haka
ta sake fashe da wani kukan, shafa kanta ya shiga yi cikin cool voice ya ce"I'm sorry naje
unguwa ne amma bazan ƙara ba kidaina kuka kefa jaruma ce" ɗago fuskarta ya yi to see her
reaction yaga sake haɗe ranta tana murza idanunta. Murmushi ya yi ya ce"shikenan muje na
siya maki chocolate sai mu koma gida" da sauri ta ɗago ta kalleshi ya ɗaga mata gira ya
ce"then you love it?" tura baki tayi sai kuma ta girgiza masa kai tana sake komawa kan ƙirjinsa,
dariya ya yi ya ce"gulma ko?" murmushi tayi tana ɓoye kanta ta ce cikin wata murya irinta
shagwaɓaɓɓun ƴaƴa "yaya ƙafana zai cire wayyo zafi yake minnnn!" a ɗan rikice ya kalli ƙafar
tata sai kuma ya ce"I'm sorry bari muje gida sai a samiki magani sannu kinji" gyaɗa masa kai
tayi tana matse hawaye shikuma ya yi motar key suka bar wajen.



*MALAM DUDU POV*


Cikin wata iriyar murya mai tsananin amo yake cewa"daman ai mun sanar dake lokacin zai
ƙarato to yanzu gashi nan yazooo Hhhhhh!, Keee Hajiya yanzu lokacin daya dace ya auri
wannan yarinya komai na ƙarƙashin kulawar mu karku wani damu ku bil'adama Hhhhhhhh!"
cikin rawar murya matar gabansa ta ce"tooo yanzu zan yi masa maganar idan naje gidan amma
ya za'a yi shi Alhajin ya yarda da auren nasu ba tareda ya yi tunanin wani abu ba??" haɗe rai
bokan ya yi sai kuma ya ce" mantamu kika yi dolensa ya yarda da haɗin auren kuma shine
wanda zai fi kowa farin ciki akan hakan Hhhhhhhh!, Ni Dudu nayi miki wannan alƙawarin" shiru
tayi sai kuma ta ce"to me zan baka?" Wani mirmushin mugunta ya yi sai kuma ya ce"aikema kin
sani" murmushin itama tayi sannan ta tashi ta shige bedroom ɗin dake kusada zauren, mikewa
ya yi shima yabi bayanta, sai bayan 50mins sannan ta fito daga ɗakin tana gyara ɗaurin zaninta
sannan tayi waje.



*MAI ZAMANI POV*


Kallon doctor yake har ya kammala dubata sannan ya ce"doctor what's going up?" numfasawa
ya yi sannan ya ce"sir ba wani abu bane kawai tayi stressing kanta ne nd kuma kasan yanayin
lalurarta but nayi mata injection zata samu sauƙi in sha Allah" numfasawa ya yi ya ce"okay you
can go we should talk later" okay doctor ya ce sannan ya ɗauki first eid box ɗin nasa ya yi waje
daidai nan ta shigo tana kallonsu duka ta ce"yallaɓai ya jikin nata?" batareda ya juya ba ya ce"
Alhamdulillah call Farooq" taɓe baki tayi sannan ta juya ta fita, zaune ta sameshi yana shan
coffee ɗin nasa na ƙa'ida kallonsa tayi ganin kamar wani abun yake tunani ta ce"Farooq me

kake tunani haka" furzar da wani zazzafan numfashi ya yi ya ce"Mommy wlh I'm tired!, nagaji!! I
can't endure it anymore haba!" zama tayi gefensa da mamaki a fuskarta ta ce"then what
happened?" a ɗan fusace ya kalleta sai kuma ya ɗauke kansa yana kwafa ya ce"Mommy Are
you questioned me?, bama kisan meke damuna ba?, haba Mommy!!" Kama hannunsa ta yi
cikin nata cikin son kwantar masa da hankali ta ce" Farooq kanada saurin ɗaukan zafi uhn,
ƙoƙari fa nake ganin abubuwa sun tafi yanda mukeso meyasa kake damuwa?" zare hannunsa
ya yi daga cikin nata ya miƙe tsaye yana zagaye parlon tamkar wanda ya yi wa Sarki ƙarya
miƙewa itama ta yi ta ce"dan Allah ka kwantar da hankalinka kasan farin cikinka shine nawa,
amma dole na iya takuna saboda kafini sanin halin General bashida kirki idan yaso" harɗe
hannayensa ya yi a ƙirjinsa still looking at her ya ce"then mene ne abunyi Mommy?, Shekaru fa
tafiya suke, mistakely idan General ya mutu yanzu zan fa tashi banida komai kema kuma haka
amma kin ɗauki abun not serious" murmushin takaici tayi tana kallon ɗan nata ta ce" yanzu me
kake so?" ajiyar zuciya ya yi sannan ya kama hannunta ya ce"good!, Mommy kije wajen
General da buƙatar mu, tun kafin yarinyar nan wani a waje ganta labari ya sauya she's 17yrs fa
yanzu kuma University take zuwa anytime zata iya cewa tana son wani kuma kinsan general
bazai mata auren dole ba!" murmushi ta yi ta ce"Farooq ka kwantar da hankalinka indai wannan
ne angama aurenka da Ma'eesha ka ɗauka anyisa, Ma'eesha takace kaima kuma kasan da
wannan" sai a sannan ya saki fuskarsa ya yi murmushi ya ce"Mommy banson aurena da
Ma'eesha ya wuce 2months kiyi iya bakin ƙoƙarinki please" shiru ta yi kamar me nazari sai
kuma ta ce"in sha Allah za'a yi amma kafin nan akwai buƙatar na koma wajen Malam dan muji
ta bakinsa" miƙewa ya yi ya ce"hakanma yanada kyau ko zuwa dare saina kaiki dan nima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login