Showing 9001 words to 12000 words out of 44270 words
tana nemawa ƴar tata addu'ar shiriya wajen ubangiji.
*FAROOQ POV*
"Mommy nace miki ki kwantar da hankalinki na tabbata ba za'a samu wata matsala ba domin
nasan wanda nabawa aikin kawai yanzu zan nemo hanyar da zata fita ne amma ba tare dani ba
yanda babu wani wanda zai yi zargina da zarar nasamu wannan to komai fa zai zo ƙarshe zamu
gama da General cikin sauƙi batareda munsha wata wahala ba" ajiyar zuciya Mommy ta sauke
tana sanye cikin wani less peach colour mai manyan zane ɗinkin Bubu tayi ɗaurin ture kaga
tsiya, ga mata iya mata amma sai mummunar zuciya, cikin sanyin jiki ta ce"to Allah yasa muyi
nasara dan ni wlh abun ya fara damuna koda wasa ban taɓa tunanin haka zata kasance ba, na
ɗauka munyi abinda ya kamata kuma zamu samu sakamako mai kyau amma sai ta sauya zani"
wani killer smile ya yi ya ce"Mommy nace miki ki saka a ranki cewa angama komai domin ni
nasan halin wanda na bawa aikin nan wlh koda da wasa baza'a taɓa samun wani abu wai shi
matsala ba, infact ma Mommy shi baya taɓa kuskure cikin aikinsa bayan haka kuma ya rigada
ya turon kuɗaɗen kinga munci riba biyu kenan" murmushi ta yi daidai lokacin Ma'eesha ta turo
ƙofar bedroom ɗin ta shigo, a ɗan tsorace suka kalleta amma sai sukaga tana murmushi hakan
yasa Mommy ta ce"shalelen Father ce kuma?" murmushi Ma'eesha ta yi tana kallon Farooq ta
ce"yaya guess what?" lumshe ido ya yi ya buɗe ya ce"Father ya siya maki chocolate" girgiza
kanta ta yi tana murmushi ta ce"baka canka baaa" murmushi ya yi ya ce"shikenan naji I'm
looser now tell me" rufe idanunta tayi sai kuma ta buɗe ta ce" ranar Friday zamu tafi excursion"
baki buɗe da matukar murna ya ce"awwwn wane waje?" tana dariya tace "National museum
Damaturu nd kuma Father ya yarda hakama Mami" wani ƙayataccen murmushi ya yi yana kama
hannunta ya ce"wowww amma naji daɗi shalelen Father gaskiya zo mu fita let's celebrate"
murmushi tayi sannan suka fita daga bedroom ɗin tana cigaba da bashi labarin.
*YOBE STATE*
*GASHUA MARKET*
*MUHAIRA POV*
Dakyar take tafiya cikin kasuwar duk jikinta ya yi weak, wajejen ƙarfe 12pm na rana ne duk
mutane sun fito suna hada-hadarsu wata Irin yunwa take ji dan rabonta da abinci tun jiya da
rana gashi ƙirjinta yana mata ciwo jikinta kuwa kamar wacce aka naɗawa duka haka takeji, wani
mutum tagani yana gashin masara hakan yasa ta ƙarasa wajen, tsugunawa tayi cikeda ladabi ta
ce"Baba ina yini" kallonta tsohon mutumin ya yi aikuwa ya saki baki dan shi bai taɓa ganin mai
kyau irin haka ba duk zatonsa ma aljana ce, ganin bai amsa mata ba yasa ta ce"Baba dan Allah
ka taimaka min da masarar nan yunwa nakeji" da sauri ya ɗauki guda uku ya sanya mata cikin
leda ya miƙa mata dan shi ko magana ma ya gagara yi dan tsoro yake kar yaje ba mutun ba ce,
sosai Muhaira tayi murna cikin sanyin murya ta ce"Allah ya biyaka da gidan aljanna Baba
Nagode" kai kawai ya gyaɗa mata dan tsorone ya ƙara kamashi sanda yaji muryarta, miƙewa
tayi ta cigaba da tafiya dan ta samu wani wajen ta zauna ta ci masararta hankali kwance, Wani
tebur ta samu gefen wani mai kayan awo ta zauna a hankali tayi bismillah tafara cin masararta.
Duk wanda ya zo shigewa sai ya kalleta ganin yanda tayi wani irin kyau dukda ita ba'a cikin
nutsuwarta take ba, irinsu Muhaira ne idan suka samu hutu tofa basu ganuwa saboda kyau da
kuma tsarin halitta.
*BANI KURA RESIDENCE*
Tsaye suke cirko-cirko kowa ya yi shiru shi kuwa Bani kura ya zauna kan dakalin ɗakinta ya
zuba uban tagumi yama rasa ta ina zai fara, ko ina Muhaira ta tafi?, yaushe tabar gidan?, Allah
shine masani, taɓe baki Falmata ta yi ta ce"wama ya sani ko yawonta data saba ta tafi daman ai
duk irinsu ƙarshensu yawon banza" a fusace Bani ya ɗauketa da wani lafiyayyen mari yana
kallonta ya ce"dallah rufe mana baki wama ya sani ko kune kuka koreta kamar yanda kuka
shirya, ku sani zan fita neman Aishatu amma duk abinda ya samu rayuwarta Allah bazai barku
ba jahilan banza kawai!" yana gama faɗin haka ya fice daga gidan kamar zai tashi sama, da
harara Ya'acca ta Bisa sannan ta ce"can kaje gayyar tsiya kuma in sha Allahu bazaka taɓa
ganinta ba mun rabu da wahala shegiyar yarinya tana gidan nan ubanma zai zo ya auri
ƴaƴanmu ai gwara data tafi Allah yasa mota tabi ta kanta ta markaɗe" tuntsirewa sukai da dariya
Kulu ta ce"wlh kuwa Umma rannan Salisu cemin yai wai shi wannan ta gidan namu yakeso"
kwafa Falmata ta yi ta ce"yoo daman wannan ai annoba ce shiyasa shima baban naku yace zai
aureta ai wai mu zaiwa duniyanci heheheheeeeeeee!" Tsaki Ya'acca ta yi ta ce"ai wlh da ya
aureta ya jaza mata bala'i dan Allah watarana saina kasheta kowama ya huta, daman ɗiyar
Fulani ai mugunta garesu ni bansan mema ya haɗashi abota da ubanta ba" Allah dai ya kyauta
cewar Falmata sannan ta cigaba da wankin da take.
# *BA ITA BA CE!*
# *Human trafficking*
# *Destiny*
# *Unconditional love*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce!*.
[8/3, 9:23 PM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!..*
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
*@Nanameera08* _wattpad_
*nanameera08* _arewabooks_.
*Nanameera ce!*
# *SQUAD 2024*.
```Page 05```
*MA'EESHA POV*
Sanye take cikin wasu English wears white colour masu ɗan kama jiki sai kuma ta ɗora rap
Abaya black colour akai tayi rolling fuskarta da veil ɗin rigar Masha Allah tayi kyau sosai abinta
hannunta riƙe da mug na tea mai zafi tana sha, takun da taji abayanta yasa ta juya murmushi ta
sakar masa saida ya sake kallonta dan ba ƙaramin kyau tayi masa ba tabbas badan bashida
halin aurenta ba da ya mayar da ita mallakinsa yana matuƙar son kyakkyawar mace gashi kuma
Ma'eesha Allah ya hore mata ga kuma kuɗi wanda shine yasa kyan nata ya sake fitowa fili cikin
sanyin murya ta ce"yayana I'm gonna to miss you wlh" murmushi ya yi yana bata peck a goshi
ya ce"same dear, da ace banida wasu ayyukan ai ni ne zan rakaki" turo baki ta yi tana
langwaɓewa ta ce"toh yaya dan dai three days please mu tafi tare" cikin son kwantar mata da
hankali ya ce"shalelen Father kenan, ai three days dayawa a wajena karki damu idan zaki
Masarauta nida kaina zan rakaki" murmushi ta yi ta ce"yaya da gaske kake?" gyaɗa mata kai ya
yi yana kwaikwayon muryarta ya ce"Eh da gaske nake babyn yaya" tuntsirewa ta yi da dariya ta
ce"kai ko yaya hmmmm!" waro idanunsa ya yi ya ce"ni ko me?" girgiza kanta tayi tana rufe baki
daidai nan suka ƙaraso parlon, General ne sanye cikin wasu kayan sojoji t-shirt da trouser sai
jacket ya ɗora a sama sai Mami tana sanye cikin wani ubansu less blue colour mai ƙananun
zane ɗinkin riga da zani ta ɗora mayafi pink akai idan ka kalli Mami ba zaka taɓa cewa ta haifi
Ma'eesha ba tun daga yanayin fuskarta har zuwa jikinta Allah ya yi mata zubin halitta mai kyau
hakama kuma ƴar tata, murmushi General ya yi idanunsa kan matar tasa sosai ta burgeshi dan
yana matuƙar son ado da kwalliya shiyasa koda yaushe yake jin Mami kamar amarya a wajensa
ko auren Mommy da ya yi saboda mahaifiyarsa ta matsa masa ne sai gashi itama ɗin bata
samu haihuwar ba, fitowa Mommy ta yi cikin wata abaya ash colour tayi rolling veil kana kallon
fuskarta zaka san ta fara manyanta dan Mami ta fita kyan jiki
"Father mu tafi ana jirana please"
Maganar Ma'eesha ce tadawo dashi daga tunanin daya tayi ya kalleta sai kuma ya yi murmushi
ya ce"wato dai na fuskanci kin fison tafiyar nan ko?, mune kaɗai muke jin zamuyi kewarki ai
Shikenan" ɓoye fuskarta tayi a jikinsa tana dariya ta ce"A'a Father nima wlh ina ji ai ba daɗewa
zan yi ba"
"Kina da tabbacin ba zaki daɗe ba?"
Da sauri General ya kalli Mommy sai kuma ya ce"kamarya naga only three days zasu yi"
duru-duru ta fara yi dan batasan sanda maganar ta suɓuce mata ba sai kuma ta ce kamar me
koyan magana"uhmm...in daman nufina bata saniba ko a ƙara musu kwanaki" taɓe baki ya yi
bai ce mata komai ba ya kama hannun Ma'eesha suka yi waje hakan yasa duk suka bi bayansu.
Saida suka ga jirginsu ya tashi sannan suka koma gida sosai Ma'eesha ta yi kuka dan daman
duk sanda zatayi wata tafiya sai tayi kuka kamar bazata dawo ba, wani killer smile Farooq ya yi
sanda yaga jirgin nasu ya fara yawo a sararin samaniya cikin wata murya mai nuna zallar farin
ciki ya ce"good bye lovely sister, I'm gonna to miss you shalelen Father" murmushi Mommy da
take gefensa tayi dan taji abinda ya ce cikin ƙasa da murya ta ce"ka tabbata baza'a samu
matsala ba?" kallonta ya yi sai kuma ya kama hannunta ya matse cikin nasa alamar Eh sannan
ya saketa ya yi gaba, ajiyar zuciya Mommy ta sauke tana murmushi ko babu komai sun kusa
samun abinda suka daɗe suna muradi.
*YOBE STATE*
*GASHUA MARKET*.
Tsugune take ƙofar wani shagon mai saida abinci tana wanke-wanke jikinta sai rawa yake
kasancewar garin damuna kuma jiya da daddare anyi ruwa sosai batada wani zaɓi daya shige
tayi aikatau dan samun abinda zata sanya a bakinta dan kwata-kwata bata iya jure yunwa ba
fitowa matar ta yi tana kallonta ganin har kusa gamawa ta ce"yawwa yarinya kiyi sauri ki gama
kizo ki ci abinci nasan kina jin yunwa" gyaɗa mata kai kawai Muhaira tayi dan magana ma
wahala take mata koda yaushe cikin tunanin mafita take tabbas bazata cigaba da rayuwa cikin
kasuwa ba dolene ta fita daga ciki tsawan waɗannan kwanakin batada aiki sai tunane-tunane
duk ta hargitsa kwakwalwarta ko ya zatayi?????.
*MA'EESHA POV*
Tana fitowa daga wankan sannan ta sanya doguwar riga pink colour sannan ta gyara gashinta
wayarta ta ɗauka sannan ta zauna dan kiransu Father, Da sauri ta faɗo jikinta tana dariya tsaki
Ma'eesha tayi sannan ta tureta ta ce"wai dan Allah Suhaila yaushe zaki yi hankali jifa yanda
kika wani faɗo min a jiki salon ki karyani" miƙewa zauna tayi tana kallonta ta ce"ke banza ce wlh
kinsan me??"girgiza kai Ma'eesha ta yi Suhaila ta ce" gobe zamu koma gida right?" gyaɗa mata
kai Ma'eesha ta yi sannan ta cigaba da faɗin" to kafin mu tafi zamu shiga kasuwa haka sir ya ce
kinga zamuga gari sosai daman duk an riƙemu" ihu Ma'eesha ta saki tana rungumeta ta
ce"wayyoo Allahna daɗi kasheni, zan yi wa su yaya Farooq tsaraba kenan, daman wlh tun jiya
nakeson mu fita, kai Allah ya yiwa Sir Ahmad albarka naji daɗi sosai wlh" tashi Suhaila ta yi ta
ce"lemme take shower then muci abinci" girgiza kai ta yi ta ce"banza Acici kawai" gwalo ta yi
tana shigewa toilet ɗin ta ce"naji ɗin".
*MONDAY*
*4:00pm*
*GASHUA MARKET*.
Wani irin farin ciki ne ya mamaye Ma'eesha da ƙawayenta both maza da matan tana sanye cikin
wata Abaya purple colour sosai suke murna saboda ganin kasuwar gashua ɗin tunda take a
rayuwarta bata taɓa shiga kasuwa ba saidai supermarket dan kome zasu siya anan suke siya
hakama sauran ƙawayen nata kasancewarsu ƴaƴan masu faɗa aji, banda dariya babu abinda
suke yayinda wasu suka shiga tiktok sunata ɗaukan vedio wasu kuma na hoto ko'ina kallonsu
ake domin sun burge kowa duk abinda sukaga ana siyarwa wanda basu san shi ba sai sun
tsaya sun tambaya sannan sunyi hoto da mai siyarda abun, murmushi ta yi tana kallon matar ta
ce"Nagode Adda Allah ya ƙara arziƙi" rungume Muhaira ta yi ta ce"karki damu yarinya kinyi
kyau sosai, yanzu jeki ki yo mana cefane" da sauri ta karbi kuɗin sannan ta fita duk murna ta
isheta barinma idan ta ƙara kallon Abayar dake jikinta dukda ƴar ɗinki ce amma zata iya cewa
bata taɓa saka kaya mai tsadar wannan ba gashi kuma kalar purple ɗin ta karɓi farar fatarta duk
inda tabi sai kallonta ake tayi wani irin kyau Masha Allah. Murmushi ta yi bayan ta ɗaga kiran
tana kallonsa ta ce"yaya ka ganmu nan a kasuwar gashua zan tawo maka da tsaraba"
murmushi ya yi ya ce"Allah ƙanwanta ki ce zan ci abun daɗi" gyada masa kai ta yi sannan ya
ce"okay shalele I'll call you later" gyaɗa masa kai ta yi sannan ta katse kiran suka cigaba da
kallonsu.
*FAROOQ POV*
A hankali yake sintiri a bedroom ɗin nasa kwata-kwata hankalinsa ya gaza kwanciya so yake
kawai su kirashi su faɗa masa magana mai daɗi, ringing ɗin daya ji yasa ya yi saurin kallon
screen ɗin wayar wani killer smile ya yi sannan ya ɗaga wayar
"She's wearing Abaya purple colour"
Sauke wayar ya yi yana sakin wani numfashi.
*POV*.
Kallon mutumin daya tsaya gefenta ta yi, sanye yake cikin wasu English wears ɓaƙaƙe ya rufe
fuskarsa da face mask, kallonta ya yi sai kuma ya kalli wayarsa sannan ya ce" two pack of
tomato" okay ya ce sannan ya juya dan ɗebo tumatur ɗin, matsowa ya yi kusada ita bata yi
auneba taji ya ɗora mata wani hankaci a hanci nan take tayi baya zata waɗi da sauri ya riƙeta
cikin hanzari kuma ya sanyata bayan motar ƙirar Honda Accord sannan ya shiga gidan gaba da
wani irin speed drivern yaja motar suka bar filin kasuwar. Saida suka yi nisa sosai da kasuwar
sannan ya ce"stop the car!" a hankali drivern ya yi parking juyawa ya yi ya ɗagota ya kalli
fuskarta sannan ya kalli pic ɗin da ke kan wayar tasa daidai nan kira ya shigo ɗagawa ya yi
daga ɗaya ɓangaren ya ce"what is going?"
"I got her"
Ajiyar zuciya Farooq ya sauke sannan ya ce "lemme see her" juyoda fuskarta ya yi, bai san
sanda wani murmushi ya ƙwace masa ba ya ce"good job!," kashe wayar ya yi sannan ya koma
inda yake ya zauna ya kalli drivern ya ce"Airport".
*MAI ZAMANI POV*
*6:30pm*
Cikin son kwantar masa da hankali Mami ta ce"wai dan Allah General mene abun tashin hankali
anan?, kasan fa inda Ma'eesha take kuma yau ta ce zasu dawo amma duk kabi ka rikice" wani
banzan kallo ya watsa mata sannan ya juya ya fice daga bedroom ɗin, bayansa tafi har ya
sauka main parlon na gidan dialing numbern Farooq yayi, suna zaune shida Mommy
kowannesu da fara'a a fuskarsa ta ce"shiyasa nake alfahari dakai son nasan duk abinda ka
sanya a gaba sai ka aiwatar yanzu mene ne nagaba?" buɗe baki ya yi zai magana kiran
General ya shigo wayarsa, ɗagawa ya yi cikin ladabi sai kuma ya ce"ok gani nan" tashi ya yi
yana kallon Mommy ya ce"kizo muje kisha labari, yau zanga yanda wasu zasu rikice" tuntsirewa
tayi da dariya sannan ta miƙe tabi bayansa, hatta yanda suke sauke ƙafarsu a ƙasa zaka gane
cewa cikin farin ciki suke, yana ya tsaya yana kallon General ganin yanda duk ya birkice ya
ce"Father lafiya dai?" General ya ce"please gwada kiran Ma'eesha na kira har yanzu switch up
gashi har ana shirin margib bata dawo ba" okay ya ce sannan ya shiga dialing numbern ta, still
dai akashe take cewa, nan take tashin hankali ya bayyana a fuskar General ya ce" bari naje
school ɗinsu na tambaya maybe ko wani abun ne" baki buɗe Mommy take kallonsa sai kuma ta
ce"dan girman Allah ya yallaɓai ka nutsu, haka zakaje makarantar tasu duk ka fita hayyaci?,
Ma'eesha fa da girmanta kuma i think kodai basu tawo bane" da sauri Mami tace"faɗa masa
dai" kallonsu ya yi duk idanunsa sun yi jaa ya ce cikin ɗaga murya" bazan kwantar da hankalin
nawa ba!, nace bazan kwantar ba!, ina naga wani kwanciyar hankali bayan ƴata bata dawo gida
ba?, madadin ku tayani baƙin ciki da nuna tashin hankali shine ma kuke cewa na kwantar da
hankalina you said I should come down saboda ba ƴarku ba ce kema kuma wai har da ke kina
matsayin uwarta nonsense!" ya ƙare maganar yana kallon Mami, numfasawa Mami tayi sannan
ta ce"Allah ya huci zuciyarka yallaɓai amma ni gani nai..."
"Heyyyyyyyy!, Shout up!!"
Shiru Mami tayi tana kallon mijin nata, itama kanta hankalinta a tashe yake amma General ya
damata shiga tashin hankali kuma shi baya iya ɓoye nasa indai akan Ma'eesha ne. Cikin sanyin
murya Farooq ya ce"Father dan Allah came down yanzu zan je school ɗin su na tambaya
tunda..." Maganar ta maƙale a maƙoshinsa saboda sallamar Ma'eesha data daki kunnuwansa
da sauri kuma a matuƙar razane ya juya mai zai gani?, Ma'eesha ce tsaye daga ɗan nesa dasu
tana sanye cikin Abaya black colour hannunta riƙe da ƙaramar trolley ɗinta da gudu ta tawo
tana zuwa ta rungume Father sai kuma ta saki wani irin raunataccen kuka, Farooq bai san
sanda ya zauna kan kujera ba koma faɗawa ya yi bashida masaniya, Mommy kuwa jikinta sai
rawa yake cikin sarƙewar murya ta ce"Ma..Maee.. Ma'eesha ke ce!" Kuka Ma'eesha ta cigaba
tana ƙara shigewa jikin mahaifinta, General hannayensa yasa ya rungumeta ƙam shima a
hankali yake sauke ajiyar zuciya Mami kuwa hamdala tayi a zuciyarta sannan ta nemi waje ta
zauna, sun ɗauki lokaci mai ɗan tsawo a haka har saida Ma'eesha ta yi shiru sai ajiyar zuciya
take saukewa, nauyin da yaji ta sakar masa yasa ya tabbatar bacci tayi hakan yasa ya ɗauketa
kamar Baby ya rungumeta sannan ya haura sama without looking at anybody. Bayansa Mami ta
bi hakan yasa Mommy tayi nata apartment ɗin da sauri tana zuwa ta faɗa kan gadon