Showing 12001 words to 15000 words out of 44270 words

Chapter 5 - BA ITA BA CE! Free Books by Nanameera.pdf

11 May 2025

2492

tana sakin
wani kuka akaro na wajen uku kenan sun sake faɗuwa, anya kuwa zasuyi nasara??, Shigowar
Farooq ya sanya ta miƙe zaune jijiyoyin kansa duk sun tashi idanunsa sunyi wani irin mugun ja
ko ba'a faɗa maka ba kasan yana cikin tashin hankali mara misaltuwa, ko kallonsa Mommy bata
yiba ta cigaba da rera kukanta wayarsa ya ɗauko ya yi dialing wata number wacce ta kasance
international number ce, saida ya yi wajen 5missed call sannan aka ɗaga ana shiddan, cikin
faɗa ya ce

"Heeeee!! Daman haka mukayi daku??, Why zaku yaudareni?" a hankali mutumin yake buɗe
idanunsa cikin wata iriyar murya ya ce"uhnnnnn!, Ahhhhh!!, Beb" cikin ɗaga murya Farooq ya
ce" kaiiii au wani abunma kake daban?, ina yi maka magana kana harkar gabanka?, kace min
kun saceta ashe ƙarya kake!!" da sauri ya ture yarinyar dake kansa ya miƙe zauna yana gyara
zaman wayar a kunnensa ya ce"Hey guy bangane me kake cewa ba, wace yarinya kake
magana akai?, ka siyar mana da yarinya mun biyaka kuɗinka sannan kuma yanzu kana mana
wani maganar nonsense!" gaba ɗaya kan Farooq ya kulle ya kasa fahimtar komai, cikin sanyin
murya ya ce" please Taj ka fahimtar dani wlh Ma'eesha tadawo gida yanzu haka tana wajen
babanta ko kuma sakinta kuka yi bayan nan?" mikewa Taj ya yi yana zura wata bathrobe ya ce
lemme show you" yana faɗin haka ya yi waje, wani bedroom ya buɗe sannan ya sake kiransa
vedio call yana ɗagawa ya ce"look at her"


"What!!!"

Sake waro idanunsa ya yi waje, babu abinda ya rabata da Ma'eesha Allah mai halitta baki buɗe
yake sake kallonta kwance take kan royal bed ɗin har sannan kuma bacci take bata farka ba,
cikin ɗaga murya ya ce

"Wannan ai *BA ITA BA CE!*"

# *Incident*
# *Human trafficking*
# *Destiny*
# *Unconditional love*
# *BA ITA BA CE!*
# *SQUAD 2024*


# *Nanameera ce!*[8/4, 8:13 PM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!..*


*MIKIYA WRITERS ASSO...*


*nanameera08* _arewabooks_


*Nanameera ce!*

# *SQUAD 2024*


```Page 06```.


Cikin ɓacin rai Taj ya ce"kai malam me kake nufi?, wane irin ba ita ba ce to wacece kenan?,
kaine fa ka bamu pic nata nd bayan na ɗaukota na kiraka ka ce Eh ita ce then yanzu kuma ka
zo kana yimin wani nonsense" bakin Farooq na rawa ya ce"ka fahimceni Taj wlh ba Ma'eesha
ba ce coz yanzu ita ta dawo gida ma amma bansan mene ne abinda ke going ba, kawai tunda
an yi haka ka saketa tunda bansan wace ba" wani killer smile Taj ya yi yana kallonsa ya ce"da
alama kanada matsala a ƙwaƙwalwarka ko?, kana tunanin Zaki zai asarar kuɗaɗensa ne?, ko
ita ce koma ba ita ba ce wannan matsalarka ce ba tawa ba kai bari ma na ƙarashe maka
magana zuwa anjima zamu shiga Riyadh sbd haka karka sake kirana akan wannan maganar"
yana faɗin hakan ya katse kiran cikin ɓacin rai ya ce"aikin banza ina cikin jin daɗi na zai takura
min nonsense!" ya faɗa yana kallon kyakkyawar fuskar Muhaira sai a sannan na lura kamarsu
ɗaya da Ma'eesha babu abinda ya raba tamkar twins haka suke lumshe idanunsa ya yi ya
ce"wowww kaga yarinya da halitta ina ma Zaki ya bar min wlh I'll pay for her" murmushi ya yi shi
kaɗai sai kuma ya juya ya fice daga ɗakin har sannan yana kallon fuskar Muhaira. Kallon
screen ɗin wayar ya yi baki buɗe dan yama rasa abinda zai yi tabbas yasan Zaki bazai taɓa
yarda da rainin hankali ba amma shi yanzu matsalarsa ɗaya idan ba Ma'eesha ba ce to kenan
wacece wadda har take kamada ita haka harda shi kansa ya kasa ganesu tabbas akwai wani
abu something fishy, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya cilla wayar tasa kan bed ya shige toilet
dan watsa ruwa.

*MA'EESHA POV*

Kwance take kan ciyar General yana shafa kanta har sannan kuma bata ce musu komai ba sai
ajiyar zuciya take saukewa, cikin sanyin murya Mami ta ce" Ma'eesha tell us mene ya sameki
uhn, meyasa kike kuka keda wa?" miƙewa zaune tayi tana kallon Mami ta ce"koba Sir Najeeb
ne ya ce yana sona ba kuma wai aurena zai yi" tafaɗa tana sakin wani sabon kukan, murmushi
Mami ta yi sai kuma ta ce"wait amma mene ya hanaki dawowa da wuri ɗazu sannan kuma ina
wayarki?" turo baki ta yi ta ce"ai faɗuwa ta yi acikin kasuwa shine ta fashe kuma bamu samu
jirgin da mukayi booking ba saida muka sake jira that's why ban dawo da wuri ba" ajiyar zuciya
General ya sauke sannan ya ce"ok saboda malamin kike kuka?" gyaɗa masa kai ta yi tana turo
baki gaba, murmushi ya yi ya ce"shikenan zan yi masa magana yanzu ki kwanta okay"gyaɗa
masa kai tayi sannan ya a tashi yana kallon Mami ya ce"Fulani muje ko" miƙewa ta yi suka fita
kafin ya rufe ƙofar ta ce"Fatherr" kallonta ya yi ganin yanda ta shagwaɓe fuska ya ce" mene?"
"Father yaya Farooq nakeson gani" numfasawa ya yi ya ce" okay kwanta" ya ƙarasa rufe kofar
sannan ya bar wajen. Lumshe idanunta ta yi tana tunanin jiya ta kasa mance abinda Sir Najeeb
ya ce mata, ganin lokaci na tafiya yasa kawai ta tashi ta shige toilet dan yin wanka babu wanda
takeson gani a wannan lokacin sai yaya Farooq hakan yasa tana fitowa ta zura wata long
sleeve ɗin riga milk colour ta ɗora Baby hijab black akai ta yi waje.

Murɗa handle ɗin ƙofar ta yi bakinta ɗauke da sallama lumshe idonta ta yi saboda wani irin
ƙamshi daya ziyarci hancinta murmushi ta yi har saida dimful ɗinta ya loma ta ce"uhnnnnn yaya
Farooq ɗan ghayu" ƙara sawa ciki tayi baya cikin parlon sai kawai ta shige bedroom ɗin
batareda taji koda ɗar ba, waro idnaunta ta yi ganin nan ma baya nan hakan yasa ta zauna
gefen bed ɗinsa tana jiran ya shigo juyawa zatayi sai ta hangi wayarsa da sauri ta ƙarasa wajen
tana kallon wayar a fili ta ce"laa wayar ma akunne" ɗauka tayi tana kallon hoton dake kan
screen ɗin, da sauri ta miƙe tsaye tana sake waro manyan idanunta sai kuma ta yi dariya ta
ce"Allah sarki yaya Farooq ashe har hoto ya yimin jiya" ta faɗa tana dariya taɓe baki ta yi sai
kuma ta ce"ko yaushe nayi bacci ohho" ajiye wayar tayi sannan ta koma ta zauna tana
Kalle-Kalle cikin bedroom ɗin, murɗa handle ɗin ƙofar akayi ya shigo da mamaki yake kallonta
ita kuwa da gudu tazo ta rungumeshi tana dariya ta ce"yayaaa nayi missing naka sosai" dakyar
ya iya saka hannunsa ya rungumeta shima yana murmushi ya ce"same ƙanwata" ɗagowa tayi
tana jan gemunsa ta ce"yaya na tawo maka da tsaraba"waro idanunsa ya yi ya ce" da gaske?"
gyaɗa masa kai ta yi ya ce"okay ki bani" girgiza kai tayi tana haɗe hannayenta a ƙirji ta ce"inada
condition" murmushi ya yi yana girgiza kansa ya ce"Ma'eesha rigima inaji" dariya ta yi ta
ce"please ka siyomin ice-cream yanzu sai na baka" har ya buɗe baki zai faɗi wata magana sai
kuma ya yi murmushi ya ce"Shikenan kamar angama don't worry" rungumeshi ta yi ta ce"yawwa
yayana amma please kar ka bari Father ya sani"gyaɗa mata ya yi sannan ta juya ta fita daga
ɗakin, tsaki ya yi yana kallon bayanta ya ce"Mumu" sannan ya ƙarasa ya ɗauki wayarsa ya fita
shima.

*WEDNESDAY*
9:00pm.

*Saudi Arabia*
*RIYADH*

*Al-Olaya Residence*

Zaune yake cikin wani katafaren haɗaɗɗen parlon mai tafiya da imanin mutane wani irin parlon
ne wanda kana gani kasan a ƙasar waje kake ƙasar wajen ma kuma inda ake ji da ganiyar kuɗi
wani irin sanyi ne irin mai ratsa jijiyar nan ne ke tashi a parlon zaune yake yana taunar cingam
cikeda isa da jinkai yana sanye cikin wasu English wears t-shirt da trouser Black colour yana
danna wayarsa aƙalla ya ɗauki kusan one hour yana jiransa amma har yanzu bashida alamun
fitowa tsaki ya yi sannan ya tashi tsaye yana bin parlon da kallo sannan ya yi waje, buɗe wata
ƙofa ya yi mai kamada ta zinare ya rabbi nan ma wani irin ƙaton parlon ne dan har ya fi wancen
girma amma bai kai tsaruwar wancen ba wasu mazane majiya ƙarfi suna sanye cikin uniform
black colour kana kallonsu kasan babu wasa a tare dasu ƙara sawa cikin parlon ya yi inda wasu
mata ke zaune su biyar dukkaninsu farare ne kuma kana ganinsu kasan ƴaƴan manyane saidai
suma ƙaddara ta faɗawa rayuwarsu, zaune suke duka sunyi shiru suna kallon Tv inda ake
haska wani show babu alamar wahala atare dasu suna sanye cikin wasu banzar shiga wacce
kwata-kwata batayi kamada shigar musulmai ba wata ƴar ƙaramar rigace irin mara hannun nan
iya gwuiwa sun naɗe kansu da bandana kallonsu Taj ya yi sai kuma ya yi murmushi cikin sanyin
murya ya ce" Tyha" da sauri wacce ya kira sunanta ta juya ta kalleshi sai kuma tayi murmushi
da sauri ta taso tana kwarkwasa tana zuwa ta shige jikinsa rungumeta ya yi yana dariya ya
ce"nayi missing naki sosai" ɗago kanta tayi tana kallonsa ta ce"nima haka kadawo amma?"
gyaɗa mata kai ya yi ya ja hannunta ya ce"muje ki rakani" fitowa sukayi tana yi masa hira ganin
inda ya nufa yasa ta waro idanunta tana kallonsa da kyakkyawar fuskanta ta ce"ina zamuje ne?"
jan kumatunta ya yi ya ce" wajen Zaki" da sauri ta sakeshi ta ce"wait" sannan ta juya da gudu.
Girgiza kai ya yi dan yasan me ta tafi yi ya tsaya yana jiranta not too long ta fito tana sanye da
Abaya black colour tayi rolling veil ɗin murmushi ya yi ya ce"kuna matuƙar tsoran Zaki" dariya ta
yi ta ce"ba dole ba kaima fa kasan halinsa" Taj ya ce"hmmm nima nan wani tym ɗin tsoransan
nakejin mutum sai rashin mutunci" ta ce"kaga nidai babu ruwana wlh" dariya ya yi daidai lokacin
suka zo bakin ƙofar murɗa handle ɗin ƙofar ya yi wani irin ƙamshin turaren Creed Aventus Eau
de perfume spray shine ya daki hancinsu lumshe idanu suka yi a tare sannan ya shiga bakinsa
ɗauke da sallama tsaye yake jikin wani ƙaton Enlargement na hoto ya zuba masa idanu yana
sanye cikin wata armless Fara wacce takama jikinsa sosai sai Chinos Three-quater black colour
gashi ne zube kan gadon bayansa tamkar na mace yasha Saloon duk ya kanannaɗe kamar
macaroni ya sanya Prada brand black colour akansa hannunsa ɗaya cikin aljihun wandon ɗaya
kuma yana riƙeda wani haɗaɗɗen mug, kusan mintuna biyu da shigowarsu amma bai juyo ba
kuma badan bai ji shigowar tasu ba saidan wata irin halitta da ubangiji ya yi masa ta jin kai.
Girgiza kai Taj ya yi sannan ya sake yin gyaran murya ya ce"Zaki" a hankali ya juyo cikin wani
action mai ɗaukar hankali ya ilahy ubangiji ya yi halitta akan fuskar bawansa tamkar ba mutum
ba saboda tsananin kyau tun daga girarsa wacce take cike da gashi baƙiƙƙirin da ita sai dogon

hanci wanda yake har baka ga lips ɗinsa sunyi wani irin pink alamun yana yawan taunesu ganin
yanda suka zuba masa idanu kamar basu taɓa ganinsa ba yasa ya haɗe rai yana waro musu
manyan idanunsa masu matuƙar kwarjini hakan yasa suka sunkuyar da nasu taɓe baki ya yi bai
ce komai ba ya nemi kujera ya zauna ya shiga girgiza ƙafa da kallo Tyha tabi ƙafarsa wata irin
kyakkyawar gargasa ce kwance kan farar fatar tasa batasan sanda ta saki wata ajiyar zuciya ba
tana lumshe idanunta ita inama wata rana Zaki ya nemeta ai da tafi kowa farin ciki saidai sanin
shi ba halinsa kenan ba ya sanya ta kawar da tunanin daga cikin kwakwalwarta, riƙe hannunta
Taj ya yi sannan ya jata suka zauna kan kujera ɗago kansa ya yi yana kallonsu sai kuma ya ce
cikin hucky voice"Keee get out" da wani mugun sauri Tyha tayi waje har tana neman faɗuwa ko
kallonta bai yi ba ya mayar da kansa gun Taj ya ce"where is she?" "Tana mota amma bata
farfaɗo ba that's why na barta, nd then kuma naji Farooq yana mini wata magana wacce ban kai
ga fahimtar ba" yana danna wayarsa ya ce"uhnn ina jinka" gyara zama Taj ya yi ya ce"cewa
yake wai ba ita ba ce yarinyar daya siyar nd lokacin dana ɗaukota saida na kirashi ya tabbatar
min da cewa ita ce amma yanzu ya ce wai ba haka ba" ajiye wayar ƙirar iphone 16 ya yi yana
maida dubansa ga Taj ya ce"then what he mean, Taj kasan halina banason rubbish kuma ni bai
dameni ba na rigada na biyasa dan hakan ko yau na samu wanda zai karɓi yarinyar nan zan
bashi ne without second thought" murmushi Taj ya yi ya ce"to dan Allah na karɓeta hannu
bibbiyu wlh zan biya yanda kayi mata kuɗi please Zaki kayi min wannan taimakon" wani kallo
Zaki ya watsa masa ya ce"ɗan iska kawai kai bakada wani aiki sai na Sex ne kai kenan abu
ɗaya, wait dan Allah mata nawa ka yiwa ciki tell me truth" tuntsirewa ya yi da dariya ya ce"kai
bakada dama wlh ai inada kayan aiki da tsari nakeyin komai, nidai dan Allah kayi min wannan
alfarmar wlh yarinyar ta haɗu" taɓe baki Zaki ya yi ya ce"bring her" okay ya ce sannan ya miƙe
ya fita daga parlon, girgiza kai Zaki ya yi sannan ya cigaba da danna system ɗin dake gefensa,
after some minutes ya dawo yana rungume da ita da kallo Zaki ya bisu har ya kwantar da ita
kan ɗaya daga kujerun parlon zama ya yi yana kallonsa ya ce"gatanan kamar baka ɗauki
Mutum ba ban taɓa ganin yarinya mara nauyi irinta ba kamar bata cin abinci" kallonta Zaki ya yi
wanda hakan yasa ya miƙe tsaye cikin tafiyarsa da cikkaken namiji mai ji da kansa ya ƙarasa
gabanta hannunsa zube cikin aljihu yake kallon kyakkyawar fuskanta taɓe baki ya yi sai kuma
ya koma ya zauna yana kallon Taj ya ce"saboda kyanta kake sonta?" murmushi Taj ya yi ya
ce"to wa yaƙi mace mai kyau?" "Ni" kallonsa ya yi sai kuma ya tuntsire da dariya ya ce"ai kai
Aliyu banda kai a lissafi dan ba kai ɗaya bane, yanzu nidai zaka bani ita ko A'a" buɗe baki ya yi
zai yi magana daidai nan ta buɗe idanunta kallon inda take ta yi sai kuma ta miƙe a birkice tana
kallonsu ba Taj ba hatta Zaki saida ya sake kallonta, murmushi ya yi ya ce"woww what a
prettiest girl" da sauri Muhaira ta miƙe tsaye ta kallesu duka sai kuma tayi waje da gudu bin
bayanta Taj ya yi da gudu yayinda Zaki ya tsaya yana kallon ikon Allah taɓe baki ya yi sai kuma
ya bi bayansu shima.



Tsaye ya samesu a farfajiyar ƙaton gidan sunata kokawa da Taj harda wasu guards ɗinma
nema take tafi ƙarfinsu dan turawa ɗaya take musu ta watsar dasu sannan ta ƙara nufar waje su
bita da gudu su riƙeta, wani kyakkyawan murmushi ya yi wanda ya ƙara fito da zallar kyawunsa
girgiza kansa ya yi yana kallon dramar da akeyi tamkar a cinema, kallonsa Taj ya yi cikin ɗaga

murya ya ce

"Zakiiiii dan Allah help me wlh tafi ƙarfina"


Tsayawa ya yi na wasu seconds sannan ya taka har gabansu kallonsu ya yi duka sannan ya
ƙarasa wajen Taj wanda ya cukwuikuyeta ya riƙe gam yana zuwa ya sanya tattausan hannunsa
ya karɓeta hannun Taj wani wahalallen numfashi Taj ya sauke yana dafe ƙirjinsa zullo ta shiga yi
a hannun Zaki hakan yasa ya yi wani murmushi sannan ya ɗauketa cak a kafaɗa ya shige ciki,
bin bayansa Taj ya yi har sannan bai gama dawowa daidai ba ya shiga parlon bai ga Zaki a
parlon ba hakan yasa ya nemi waje ɗaya ya zauna yana sakin wani Irin numfashi. Ganin da
gaske aljanun kanta suke kuma koda wasa sunƙi magana yasa ya danneta akan gadon yana
kallon fuskarta wacce tayi wani irin jaa girgiza kansa ya yi sannan ya ɗora hannunsa kan
goshinta ya shiga murzawa da sauri ta saki wata irin ƙara cikin sautin kuka kuma ta ce"mu ka
rabu damuuu ina ruwanka ka sakemu" taɓe baki ya yi cikin cool voice ya ce"bazan rabu daku
ɗin ba me kuke a wajenta?" "batada kowa batada gata ta rasa duk wani farin cikinta tun ranar
da tazo duniya babu wanda ya damu da ita rayuwarta cike take da ƙalubale dolene mu kula da
ita mune kaɗai gatan ta ka rabu damu muyi aikin gabanmu kar kace zaka shiga tamm" yanda ta
wani taune lips ɗinta wanda duk suka gama jiƙewa ya yawo sai ta bashi tausayi, ƙara
yunƙurawa ta yi zata miƙe ya sanya hannunsa ya tokareta a hankali take sakin wani numfashi
shiru ya yi na wasu mintuna sai kuma ya ce"uhnnn ku bar jikinta" tsaki ta yi ta ce"kai ne zamu
ce ka rabu da ita amma mu babu wanda ya isa ya rabamu da ita" haɗe ransa ya yi ya ce"ohk
rashin kunya zaku yimin?" girgiza kai tayi tana taɓe baki gyara kwanciyarsa ya yi ya sakar mata
dukkan nauyinsa sannan ya kamo fuskarta a tafin hannunsa, cikin wata kamilalliyar murya ya
shiga rera karatun Alkur'ani inda yake karanta suratul jinn kuka Muhaira ta sanya kuma duk
abinda ake koda wasa bata buɗe idanunta ba cikin wata iriyar murya mai nuna fita hankali ta
ce"kayi haƙuri wayyoooo zamu tafi kabari dan Allah zaka kashemuuuu!" ko saurarenta bai yi ba
ya cigaba da karatunsa saida yakai inda ya yi niyyar sannan ya ɗago yana kallon fuskarta cikin
sanyin murya ya ce"now leave her" cikin ƙaraji ta ce"wlh mun tafi amma zamu dawo kasa
wannan a ranka" taɓe baki ya yi yana dungure mata kai ya ce"karku fasa dawowa nima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login