Showing 42001 words to 44270 words out of 44270 words
ce"tashi ki tafi ki kwanta dare ya yi sosai" gyaɗa mata kai kawai tayi sannan ta tashi
ta fice daga ɗakin ajiyar zuciya Mommy ta sauke sannan itama ta tashi ta fita.
*MAITAMA DISTRICT*
*MA'EESHA POV*
A hankali take tafiya a cikin gidan ko ina ya yi shiru kowa ya kwanta bacci dan lokacin wajejen
12am ne tura ƙofar tayi a hankali kwance ta samesu suna bacci ƙarasawa tayi ta tsuguna wajen
General ta dakeshi da hannu da sauri ya buɗe idanunsa kallonta ya yi da mamaki sai kuma ya
tashi zaune hasken ɗakin ya kunna yaga ta zuba masa idanu tana kallonsa murmushi ya yi ya
ce"meya faru?" tura baki tayi gaba batace masa komai ba, Mami wacce ta farka sannan ta
kallesu ta ce"lafiya?" ɗaga kafaɗa ya yi ya ce"i don't know kawai ganinta nayi" da hannu Mami
tayi mata alama da tazo tasowa tayi ta zauna gefenta Mami ta kalleta ta ce"mene ne?" girgiza
mata kai Ma'eesha tayi sai kuma ta nuna mata bacci za tayi Mami ta ce"muje na rakaki ɗaki ki
kwanta" tura baki tayi sai ta nuna mata kan gadon General ne ya ce"a nan zaki kwanta" da sauri
ta gyada masa kai ya yi ya ce"common" tashi tayi ta kwanta kan cinyarsa yana shafa kanta not
too long bacci ya ɗauketa tashi Mami tayi ta ce"bari a mayar da ita ɗaki" girgiza kai General ya
yi ya ce"barta ta kwana a nan ɗin tunda haka take da buƙata" shiru Mami tayi sai kuma ta koma
ta kwanta kasancewar gadon babba yasa ya ishesu suka kwanta duk su ukun rabonda su
kwana tare da ita tun kafin ta fara zuwa makaranta sai gashi yau tarihi ya maimaita kansa.
*RIYADH*
*Al takhasosi residence*
A hankali ya kalli mudubin dake maƙale a bangon wani killer smile ya yi sannan ya juya ya fita
yana murɗa handle ɗin ƙofar wayarsa ta fara ƙara ɗan siririn tsaki yaja kafin ya kalli screen ɗin
ganin sunan Taj yasa ya ɗaga ya ce"ya akayi Taj?" daga ɗaya ɓangaren Taj ya ce"sir da alama
yau kana cikin farin ciki dan naji a muryarka" murmushi Dmash ya yi ya ce"tunda kabani farin
ciki ai dole nayi" Taj ya ce"Sir ina gidan yanzu please kazo it's something important nd ka tawo
da Muhaira dan kowane lokaci Zaki na iya kawo maka farmaki ina wajen da aka saba gudanar
da taro kowa ya hallara kai kaɗai ake jira" okay Dmash ya ce sannan ya kashe wayar tura ƙofar
ya yi ya shiga dakin zaune ya sameta inda ya barta gaba ɗaya idanunta sun kumbura saboda
kuka dan murmushi ya yi sannan ya kamo hannunta bin bayansa Muhaira tayi tana Kalle-Kalle
dan ita gaba ɗaya a tsorace take dashi tunda yace zai kasheta burinta bai shige taga Papinta
yazo ya rabata da wannan wajen ba.
Babban ɗakin taro ne mai matuƙar kyau da haɗuwa kana kallon wajen kasan an kashe iyayen
kuɗi wajen haɗashi wasu manyan mutane ne zaune a parlon kowannesu yana sanye da suit ko
ba'a faɗa maka ba kasan ba talakawa bane dan kana ganinsu kaga kuɗi, tashi Taj ya yi yana
murmushi ya ce"welcome Sir" jinjina kai ya yi sannan ya nemi guri ya zauna da kallo Muhaira ta
bi Taj amma sai taga ko kallonta bai yi ba hakan yasa ta sunkuyar da kanta hawaye na zubo
mata, tattauna suka shiga kan abinda ya shafe su Taj ya ce", yanzu ma na tawo muku da wasu
ƙarin matan ai" dafa kafaɗarsa Petor ya yi ya ce"weldone Taj" murmushi kawai ya yi sannan ya
miƙe ya ce"I'm coming" ya juya ya fice daga parlon kallonsu Tyha ya yi ya ce"come out" okay
sukace sannan suka fito daga motar suka bi bayansa miƙewa tsaye sukai duka ɗan daso ya
ce"wowwwww wannan tayi min kyau sosai" ya faɗa yana kallon Zeey, sunkuyar da kansu suka
yi Taj ya ce"Nima nasani sir shiyasa na samo muku latest waɗanda nasan zaku ji daɗinsu fiye
da ƙima" wata dariya suka yi sannan Dmash ya ce"Taj aikinka yana kyau akwai wata kwangila
da nakeson na baka" murmushi ya yi ya ce"okay sir Ina ji" Dmash ya ce"ina son ka kashe Zaki
idan kayi haka nikuma nayi maka alƙawarin baka ragamar daularmu wacce yanzu take hannun
Zaki" miƙewa Muhaira tayi cikin kuka ta ce"a'a wlh bazai karɓa ba hamma Taj nasan ai bazaka
kashe Papi ba ko?" ta faɗa tana riƙe hannun Taj wata kyakkyawar tsawa Taj ya yi mata wacce
ta sanya tayi baya tana fashewa da kuka kallonsa Dmash ya yi ya ce"why zaka mata tsawa sai
ka ce mata Eh" girgiza kai Taj ya yi yana miƙewa tsaye ya ce"i can't Sir coz bana ƙaunar
yarinyar nan na tsaneta kamar yanda na tsani Zaki" tashi Dmash ya yi yana kallonsa ya
ce"wannan ba hujja bace karka sake irin haka" murmushi Taj ya yi ya ce"idan kuma nasake fa?"
da mamaki duk suke kallonsa Petor ya ce"Taj kaji abinda ka faɗa kuwa" kallonsu ya yi sai kuma
ya dafe kansa ya ce"oh I'm sorry sir I thought da Zaki nake magana" okay sukace daidai lokacin
suka fara jiyo ƙarar harbi da mamaki duk suke kallon ƙofa Dmash ya ce"what happened?"
girgiza kai Taj ya yi alamar bai sani ba turo ƙofar da aka yi ne ya sanya suka kallo ƙofar da sauri
sanye yake cikin wasu uniform na sojoji wanda sukayi matuƙar yi masa kyau baki buɗe duk
suke kallonsa da sauri su Tyha suka sara masa irin yanda akewa babba idan anganshi da sauri
Dmash ya kalli su Petor wanda yaga sunyi the Same irin abinda su Tyha sukai ciki harda Taj
takowa ya yi cikin parlon yana taku na isa da taƙama hannayensa zube cikin aljihun kayan
jikinsa baki na rawa Dmash ya ce"hii...hy..you" murmushi Zaki ya yi ya ce"kayi mamakine?, ai
banyin tunanin zakayi mamaki ba Sir Fahad Dmash nayi zaton ai kanada dakakkiyar zuciya"
girgiza kai Dmash ya yi ya ce"ya akayi ban ankara da wuri ba?, meyasa na yarda dakai Zaki?"
ɗaga kafaɗa Zaki ya yi ya ce"call my real name" kallon tag ɗin jikin rigarsa ya yi sai kuma ya
ce"General Aliyu Ahmad Aliyu" "Yes it's my name ka ɗauka duk tsawon lokacin dana bata tare
dakai sbd ina son harƙalla dakai ne?, koda wasa baka taɓa burgeni ba gabaɗaya na tsaneka
ina rayuwa dakai ne kawai sbd hakan ya zame mini dole ka gagari mutane dayawa an turo
sojoji babu adadi amma ƙarshe saidai su rasa rayuwarsu a banza sbd haka nayi alƙawarin na
daina aiken kowa da kaina zanyi maganin abun. A duk sanda muka haɗu dakai ina jin kamar na
fasa kwanyar kanka a wannan lokacin saidai wata zuciyar ta hanani ban shigo rayuwarka ba
saida nagama sanin komai naka a tunaninka kai ne ka jawoni cikin rayuwarka amma kayi
kuskure dan ni ne wanda na jawoka cikin tawa rayuwar kuma yanzu zan miƙa ka ga hukuma"
wata dariya Dmash ya yi sannan ya ce"haba kai ma kayi irin wannan dabarar ballantana ni"
yana faɗin hakan ya ɗora bindiga kan Muhaira yana shaƙeta ya ce"ko ku rabu dani ko kuma na
harbeta" murmushi Zaki ya yi yana tsaye inda yake ya ce"taya zaka yi harbi bayan babu komai
a cikin bindigar?" kallon gun din Dmash ya yi shidai yasan ya zuba bullet a ciki amma ya kasa
yarda da abinda Zakin ke faɗa masa cikin zafin nama Zaki ya ƙarasa gabansa ya finciketa yana
buga masa kan gun aka riƙe kansa ya yi yay baya zai faɗi Taj ya tareshi yana murmushi ya
ce"haba sir naga zaka fadi har kayi give up?" girgiza kai Dmash ya yi daidai lokacin yaransa
suka shigo parlon without second thought kuma suka fara buɗe wuta hannun Taj Zaki ya kama
ya danƙa masa Muhaira ya ce"go" girgiza kai Taj ya yi ya ce"mu bar ka anan sir?" gyaɗa masa
kai ya yi Taj ya ce"no sir I can't" "Taj!! ba shawara nake baka ba" sara masa ya yi sannan yaja
hannun Muhaira suka fita daga parlon. Duk yawancinsu saida Zaki ya harbesu duk ba baya
harbin inda mutum zai mutu dan a raye suke buƙatarsu yana yi Petor na tayashi saida suka
rage sai su biyu sannan suka tsaya taɓa shi Petor ya yi ya joyu ya ce"Sir ka tuna?" girgiza kai
Zaki ya yi ya ce"sanda ka kashe Smallo he's my brother sbd shi na shiga hukumar sojoji kawai
dan na ɗaukar masa fansa" buɗe baki Zaki ya yi zai magana ji kake tassssss ƙarar shigar
bindigar cikin ƙirjinsa da gudu Taj suka ƙaraso da wasu tarin sojojin garin Saudiyya Petor na
ganin haka ya dasa gun din akansa ya kashe kansa zubewa Muhaira tayi awajen tana
zunduma ihu ta shiga jijjiga Zaki wanda yake kwance baya ko numfashi sai jini ne yake zuba a
ƙirjinsa rungumeshi tayi tana kuka kamar ranta zai fita take kiran"Papi!! Papina ka tashi ka tashi
dan Allah kaima tafiya zaka yi ka barni?? kaima su Dada zaka bi?? Papi wake up ka tashiiiii
don't leave me alone please Papinaaaa!" ko alamar motsi Zaki bai yiba har sannan kuma banda
jini babu abinda ke gudu a jikinsa gaba ɗaya ta bata jikinta da jininsa da sauri Taj ya zo ya
janyeta yana girgiza mata kai cikin kuka ta ce"hamma Taj ka cewa Papi ya tashi ya tashi mu
gudu" shiru Taj ya yi mata dan bashida amsar bata koda ace shi ba likita bane zai iya faɗa cewa
kai tsaye Zaki ya tafi domin duba da inda aka yi masa harbin balle kuma shi da yake likita wasu
zafafan hawayene suka shiga sakkowa kan fuskarsa tabbas ya yi rashin aboki domin Zaki
abokinsa ne tun na yarinta. Kallonsa Muhaira tayi daidai lokacin da wasu likitoci suke ɗauke
Zaki daga wajen da idanu Taj ya yi masa magana ya girgiza masa kai alamar he's gone juyowa
ya yi zai yiwa Muhaira magana yaga ta sulale ƙasa nan ta faɗi ƙasa sumammiya.
*Nmandi azikewe Airport*
Furzar da wani irin zazzafan numfashi ya yi yana sake duba rollex ɗin hannunsa misalin ƙarfe
3am ne ɗan siririn tsaki yaja daidai lokacin motar tayi parking da sauri ya fito ya ƙaraso cikin
ladabi ya ce "I'm sorry sir" taɓe baki ya yi bai ce masa komai ba ya yi gaba shi kuma yabi
bayansa Saida ya sanya trolley ɗinsa a bot sannan ya dawo wajen driver seat ya tayar da motar
da wani irin speed suka bar airport ɗin. A firgice ta farka tana Kalle-Kalle kallonsu Mami wanda
suke bacci ganinsu tayi tamkar wasu dodanni hakan yasa ta runtse idonta da gudu kuma ta fice
daga ɗakin kai tsaye stairs tayi tana zuwa ta buɗe ƙofar entrance ɗin gidan ta fita da gudu, buɗe
gate ɗin da tayi shine ya farkar da gatemans ɗin wanda bacci ya ɗaukesu da sauri suka kalli
ƙofar sukayi wajen Kofar da gudu saidai me sam ƙofar taƙi motsi gabaɗaya ta cije tana fitowa ta
yi kan titi tana gudu kamar mahaukaciya wani irin wawan birki drivern yaja, ɗago kansa ya yi ya
kalleshi kafin yayi Magana yaga mace a gabansu tsaki ya yi sannan ya fito daga motar kallonta
ya yi da gudu ta ƙaraso wajensa ta riƙe hannusa tana nuna masa bayanta waro idanuwansa ya
yi da mamaki ya ce "Muhaira?" shigewa jikinsa tayi tana sakin kuka rungumeta ya yi ya shige
motar da sauri drivern yaja suka bar wajen buɗe gate ɗin ya yi daidai da farkawar General
fitowa ya yi saman bene sbd hayaniyar mutanen da yaji hangosu ya yi sunata kokawa da ƙofa
lokacin sojojin suka fito wani soja ne ya ja ƙofar da ƙarfi aikuwa ta buɗe da gudu sukayi waje
suna nemanta sakkowa ya yi da sauri yana zuwa ya kalli sauran waɗanda basu fitan ba ya
ce"what's going on?" cikin inda inda ya ce"sir.. sir...daman Ma'eesha ce ta... fita" "what?" da
sauri General ya buɗe ƙofar ya yi waje shima yabi bayansu. Har akayi sallar asuba suna waje
saidai babu Ma'eesha babu alamarta dawowa gidan suka yi yana shigowa parlon ya tarar dasu
kowa yayi cirko-cirko a tsaye kallonsa Mami tayi ganin yanda idanunsa suka faɗa cikin rawar
murya ta ce"yallaɓai tana....tana ina?" girgiza mata kai General ya yi hawaye na zirarowa kan
fuskarsa duk dauriya irin tasa
"Tassssssssss"
Da sauri suka juya suka kallon Mami wacce ta faɗi ƙasa sumammiya girgiza kai General ya yi
sannan ya yi hanyar upstairs saidai ko stairs biyu bai taka ba ya haɗo shima nan ƙasa a sume.
Wani irin tashin hankali ne ya mamaye a halin da gudu Aleema tayi kan Mami tana fashewa da
kuka ta ce"Mamiiiiiiiiiii!!"
*SHIN WANENE ZAKI?*
*INA MA'EESHA TA TAFI?*
*SHIN DA GASKE ZAKI YA RASU KO A'A?*
*WACE IRIYAR RAYUWA MUHAIRA XATAYI IDAN YA KASANCE ZAKI YA TAFI YA BARTA?*
*SHIN WANE WANDA YA YIWA MA'EESHA KURCIYA?*
*WANE NE WANDA YA KIRAYETA DA SUNAN MUHAIRA?*
*MENE NE HAƊIN MUHAIRA DA MA'EESHA HAR SUKE KAMA ƊAYA?*
*INA MAHAIFIYAR KHALIL TAKE?*
*SHIN MUHAIRA ƳAR WACE KUMA MENE NE DALILIN DAYA SANYA AKA YARDA ITA TUN
TANA JARIRIYA?*
*SHIN MEYASA AKE CEWA BA ITA BA CE! IDAN BA ITA BA CE TO WACECE?*
*DUK WADANNAN TAMBAYOYIN DAMA WASU DA DAMA ZAKU SAMU AMSARSU SU NE
A YAYIN DA KUKA BIYA ONLY 500# FOR NORMAL GROUP 1K FOR VIP VIA 9086030007
HAUWA LAWAN OPAY EVIDENCE OF PAYMENT VIA 08106608363 OR 07041901078 KI BIYA
KI KARANTA CIKIN SAUƘI DA NISHAƊI SISTER*
*FOR MORE INFORMATION A YIMIN MAGANA VIA MY NUMBERS*
_TAKU HAR KULLUM NANAMEERA MU HAƊU A PAID GROUP_.