Showing 18001 words to 21000 words out of 44270 words
duka ta
ce"aikuwa ku zuba idanu kuga in sha Allah sai haƙata ta cimma ruwa sai nayi rayuwa a
apartment ɗin Zaki" mikewa Abra ta yi ta ce"na fuskanci bakuda abunyi shiyasa kunga tafiyata
school" da harara suka bita har ta fice daga parlon sannan Amrish ta ce"wai ke nawa Taj yake
baki ne?" haɗe rai Tyha tayi ta ce"ina ruwanki banson gulma ke" murmushi tayi ta ce"nifa ina
son guy ɗin nan dan shima ya haɗu" wani kallo Tyha tayi mata kafin ta miƙe batace komai ba ta
shige bedroom ɗin. Ganin yanda take binsa da kallo yasa ya haɗe rai yana kallonta ya ce"bar
kallona" murguɗa masa baki ta yi ta ce"to kai ya akayi kasan ina kallonka", baki buɗe Zaki ke
kallonta da alama sai ya koyawa yarinyar nan hankali, ajiye turaren hannunsa ya yi ya ƙaraso
gabanta yana kallonta sai kuma ya nemi waje ya zaune da hannu ya yi mata alama da tazo
aikuwa ta tashi babu musu ta ƙarasa har zata zauna a ƙasa ya riƙe hannunta ya zaunar da ita
kan cinyarsa turo baki ta yi cikin gunguni ta ce"nidai Allah kabari banason iskanci" ware
idanunsa ya yi ya tamke fuska kamar bai taɓa dariya ba, tattausan hannunsa ya sanya kan lips
ɗinta sosai ya yi laushi taɓe baki ya yi sannan ya murza da ƙarfi kuka ta saki tana yarfe
hannunta ƙara murɗewa ya yi da duk ƙarfinsa. Kuka take son yi amma yaƙi bata damar hakan
aƙalla yakai wajen 5mins sannan ya saki bakin yana jingina da jikin kujerar, rushewa tayi da
kuka jin yanda bakinta yake raɗaɗi yayi wani irin jaa lumshe idanunsa ya yi above two minutes
yana jin kukan nata ganin tana son rikita kwakwalwarsa yasa ya jawota ya matseta a faffaɗan
ƙirjinsa luf tayi kamar bai rufe komai ba dan kwata-kwata Muhaira batada ƙiba, a hankali kamar
mai koyan magana ya ce"shii...shiiiiiii ya isa haka" tura baki tayi gaba tana hawaye ɗago
fuskarta ya yi ya ce"what's ur name?" shiru tayi masa ya haɗe ya ce"I'm ur mate?" girgiza kanta
ta yi cikin shashshekar kuka ta ce"Muhaira" harararta ya yi ya ce"Malama ur real name"
zumɓura baki ta yi ta ce"A'ishah" sakinta ya yi ya ce"ɗagani" ƙuri tayi masa da idanu ya ce"ta
Allah ba taki ba kike wani kallona witch kawai" harararsa tayi ta ce"wlh ni ba mayya ba ce"
girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce" rashin kunya kike min ko?, zanyi maganin bakin
rashin kunyar" turo baki gaba tayi ya kai hannu zai riƙe bakin da gudu ta tashi daga jikinsa
takoma can bakin ƙofa ta tsaya.
Murmushin mugunta ya yi ya ce"zan kama kine yarinya sai kin raina kanki" gwalo tayi masa
tana dariya, kallonta ya yi tayi yadda dariyar tayi mata wani masifar kyau taɓe baki ya yi ya
ce"aljana" sannan ya miƙe bai sake bi ta kanta ba ya yi waje.
*9ja*
*Prime University, kuje, FCT Abuja*
*10:40am*
Tafiya suke tana basu labari sai dariya suke banda Ma'eesha wacce ta haɗe ranta kamar bata
taɓa dariya ba, lura da haka yasa Fateema ta ce"takwara what's wrong with you?" numfasawa
Ma'eesha ta yi ta ce"bakomai kawai bana jin daɗi ne, nd inason naje gida" murmushi Fateemah
ta yi ta ce"kedai ki daina zurfin ciki wlh, ko zaki ɓoyewa kowa wani abu ai ni nayi zaton zaki iya
faɗamin dan Allah talk to me dear" kallonta Ma'eesha tayi hawaye kan fuskarta ta ce"Takwara
ina cikin matsala bansan ya zanyi ba kuma bansan wa zan faɗawa ba hankalina a tashe yake"
tsayawa Fateemah tayi tana kallon Ma'eesha ta ce"kin barni cikin duhu Ma'eesha faɗa min
mene ne ya dameki?" share hawayen fuskarta ta yi ta ce"bari muje gida dan Allah" numfasawa
tayi ta ce"to shikenan" suka cigaba da tafiya dan fita daga makarantar. Da sallama ta shigo
parlon babu kowa gidan shiru kamar ruwa ya cinye da alama Mami ma ta fita ne, riƙe hannun
Fateemah tayi suka shige apartment ɗinta, saida ta rage kayan jikinta sannan ta zauna da sauri
Fateema ta ce"yanzu faɗa min" ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce"wlh nakamu da soyayya ne
kuma da ɗan uwanmu gashi bansan taya zan tunkareshi da maganar ba, Fateemah bantaɓa jin
son wani ɗan adam irinsa ba nikaina bansan yaushe nafara sonsa ba tun ina ƴar ƙaramar
yarinya rabonsa da ƙasar nan, kuma har yanzu bai dawo ba amma ana saka ran nan bada
jimawa ba zai dawo yanada mata harda ƴa yanzu ma anyi masa kucciya ne shine yabar ƙasar
gaba ɗaya rannan Mami ta nuna min hotonsa tun daga ranar ban sake bacci mai daɗi ba kullum
shi nake mafarki bansan ya xanyi ba takwara dan Allah ki taimakeni..." Ta ƙarashe maganar
tana sakin wani kuka mai ban tausayi. Riƙe hannunta Fateemah tayi tana goge mata hawayen
fuskarta ta ce" ya isa haka ƙawata, insha Allah za ki zauna dashi matsayin mijin aurenki karki
sanyawa kanki damuwa kinsan yanayin lalurarki, kinada buƙatar kulawa ta musamman
Ma'eesha dan Allah karki sanya komai cikin ranki yanzu yaushe ne ake saka ran zai dawo?"
numfasawa ta yi ta ce"Mami bata faɗa min ba amma ni inason kafin ya dawo naje Masarauta
dan inada buƙatar haɗuwa dashi" murmushi Fateemah tayi ta ce"shikenan karki damu zan
taimaka miki in sha Allah kawai abinda ke zaki yi yanzu shine kiyi ƙoƙari ki gano sanda zai dawo
ƙasarnan daga nan komai zai zo da sauƙi in sha Allah" rungumeta Ma'eesha tayi tana dariya ta
ce"Nagode sosai takwara Allah ya barmu tare" tana murmushi itama ta ce"Ameen takwara,
yanzu dai ba wannan ba kenan bazaki bawa Sir Najeeb dama ba?" harararta ta yi ta ce"nifa
koda wasa bai taɓa burgeni ba wlh kuma har ma Father ya ce zai sameshi ya faɗa masa ya
rabu dani akanme taɓ" dariya Fateema ta yi tana kallon ƙawarta ta ta ce"taɓ lallai ma ke ɗin nan
maganar har wajen Father taje lallai abun naki ya girmama" miƙewa Ma'eesha tayi ta ce"uhnn
naki wasane bari na kawo mana abinci".
*FAROOQ POV*
Murmushin takaici ya yi ya ce"Mommy nifa abun nan ya isheni nagaji kuma haba dan Allah duk
sanda mukayi attempting nayi wani abu sai aikinmu ya ɓaci yanzu dan Allah ya zamuyi Mommy
nifa nagaji da zama ƙasan General sonake duk dukiyar ta dawo ƙarƙashin ikona, sannan ya
zamuyi da Ma'eesha? yarinya nema take tafara bamu ciwon kai bansan wace mai kama da ita
wacce har ni kaina banganesu ba amma dole akwai wani abu a ƙasa saboda haka yakamata
tun wuri musan abunyi idan ba haka ba zamu tashi a tutar babu." shiru Mommy tayi dan itama
abun ya fara fin ƙarfinta tsawon shekaru sun kasa cimma komai kullum sune suke faɗuwa
yaushe zasu yi nasara akan General ne??, ganin taƙi cewa komai yasa ransa ya fara ɓaci ya
ce"Mommy naga baki ɗauki abun nan serious ba to bari ni zan ɗauki matakin daya dace tunda
ke kin gaza" ya juya ya fice yana buga ƙofar, da kallo Mommy ta bisa sai kuma ta girgiza kai
kwata-kwata tarasa me zatayi akan al'amarin duk wata dabararta ta ƙare idan mallaka ce ta
saba da mallake General kuma Allah da ikonsa ya fita shiyasa ma ita tabar layin malamai dan
da ace zasuyi aiki da ba'a kawo wannan lokacin ba da wannan tunanin ta kwanta dan gaba
ɗaya agajiye take.
"Ma'eesha!! Ma'eesha!! Ma'eesha!!"
"na.. na'am Mami"
Kallonta Mami tayi ta harɗe hannayenta a ƙirji sunkuyar da kanta tayi tana wasada fingers ɗinta,
ƙarasowa Mami tayi ta dafata tace"kedawa Ma'eesha?" rungume Mami tayi tana fashewa da
kuka, shiru Mami tayi tana shafa mata bayanta sosai tayi kuka jikin mahaifiyar tata sannan ta
ɗago Mami ta ce"now tell me meyake damunki kwana biyu?" murmushi ta yi tana goge
hawayen nata ta ce"kawai ji nayi inason nayi kuka Mami" wani kallo Mami tayi mata wanda ya
sanya tasha jinin jikinta. Kama hannunta Mami tayi ta jata gefen royal bed ɗin suka zauna cikin
sanyin murya ta ce"Ma'eesha kinsan bakida wacce ta fini duk duniyar nan, ni ce ya kamata
nazama abokiyar hirarki da kuma shawararki saboda haka kar kiji komai ki sanar dani
damuwarki please" riƙe hannun Mami tayi ta ce"Mami kinsan da akwai wani abun zan sanar
daku wlh babu komai kawai nima banajin daɗi ne amma babu abinda aka yimin wanda zai sa ku
shiga damuwa kawai ku tayani da addu'a" numfasawa Mami tayi ta ce"tunda kin ce haka
shikenan Ma'eesha Allah ya yaye miki abinda yake damunki" murmushi tayi ta ce"Ameen
Mamina".
*RIYADH*
*Al-Takhasosi Residence*.
Wani irin haɗaɗɗen parlon ne mai Matuƙar girma komai na cikinsa silver ne sai sheƙi yake
parlon ne mai kamada faɗa kana ganinsa kasan wasu ishasshun mutanene ke rayuwa a ciki
zaune suke sunyi da'ira akan wani katafaren dinning table mai kyau abincine baje a gabansu sai
wanda kaga damar ci, manyan masu kuɗi ne amma ba larabawa ba kana ganinsu kasan
zamane ya kaisu ƙasar, dan larabawan basuda yawa sosai a cikinsu, wani babban mutum ne ya
kalli Zaki wanda ke zaune kujerar dake facing tasa yana sanye cikin wasu suit black colour ya
ɗora Glass akan fuskarsa ya yi wani sihirtaccen kyau cikin isa ya ce"Lion" ɗagowa Zaki ya yi ya
ce"Yes sir" ajiye cokalin hannunsa ya yi ya ce"mata nawa ne yanzu a hannunka?" cikin sanyin
murya ya ce"only 5 remains" murmushi ya yi ya ce"zuwa dare ka bawa Taj ya kawosu" ajiyar
zuciya Zaki ya sauke sannan ya ce"amma Sir da an nemi wasu cox waɗannan sun ɗan daɗe a
ajiye" gyaɗa kansa ya yi ya ce"Eh kuma hakane amma ai naji Taj yana maganar wata yarinya
da ka siya right" da sauri Zaki ya kalleshi kafin ya ce"hakane" murmushi ya yi ya ce"kawai ka
bawa Taj ita ya kawomin da daddare hope virgin ce?" gyaɗa masa kai kawai Zaki ya yi yana
sauke wani numfashi ya miƙe without looking at anybody ya yi waje, da kallo suka bisa sannan
wani daga cikinsu ya ce"wannan yaron ɗan zafin kaine yanada wahalar sha'ani" murmushi ya yi
ya ce"haba Bala ai Zaki ba daga nan ba shiyasa nakeson mu'amala dashi above 5yrs muna
tare dashi anan amma koda wasa bai taɓa yimin abinda ba daidai ba. Yasan aikinsa sosai
shiyasa duk cikin yarana both na nan dana 9ja nafi sonsa kuma bakowa yakewa aiki ba"
murmushi wanda aka kira da Balan ya yi ya ce"ai naga alama gashi yasan takan mata idan ya
kawo maka mace kamar karka rabu da ita shiyasa nake son aikinsa" murmushi ogan ya yi ya
miƙe ya ce"bari naje na shirya yau inada sabon jini" tuntsirewa sukayi da dariya ɗayan ya ce"
kaifa Dmash bakada kyau kuma baka wasa da kaya" sunkuyowa ya yi ya ce"wazai yi wasa da
abinci ai babu" yana faɗin haka ya haye sama suka bisa da dariya.
Shigowa ya yi parlon hannunsa zube cikin aljihu yana tafiya yana furzar da wani irin zazzafan
numfashi, zaune ya samesu ita da Taj yana bata labaru kanta a ƙasa dan bata san shi ba kuma
batada saurin sabo, miƙewa ya yi yana kallon Zaki ya ce"sai yanzu?" gyaɗa masa kai kawai ya
yi sannan ya haye sama, miƙewa Muhaira tayi Taj ya ce"A'a beauty ina za ki kuma?" turo baki
gaba tayi tana wasada fingers ɗinta masu tsayi ta ce"to ba wajensa zan je ba" murmushi ya yi
ya ce"shi wa?" da sauri ta kallesa da idanun ya kashe mata ido ya ce"kinsan shi ne?" kwaɓe
fuska ta yi ta ce"Papina ne ai to" dariya ya yi ya ce" su Zaki Papi are you Fulani?" gyaɗa masa
kai ta yi ya ce"enyeee kuma kin iya fulden?" gyaɗa masa kai nan ma ta yi ya ce"to yimin naji"
buɗe baki ta yi zatayi magana suka ji ƙarar taku da sauri duka suka juya suna kallonsa. Sanye
yake cikin wata armless maroon colour ya sanya Three-quater Maroon colour shima ya sanya
Gucci brand fara akansa gashinsa ya sauka akan bayansa hannunsa riƙe da mug ɗin coffee.
Taɓe baki ya yi bai kulasu ba ya zauna kan wata kujera ya zauna komawa suka yi suka
zauna suma duk sunyi shiru kamar waɗanda akawa dole, a hankali yake sipping coffee ɗin
hannunsa har ya shanye sannan ya ajiye mug ɗin a table ɗin gefensa ya juyo yana kallonsu,
murmushi ya yi yana kallon Taj ya ce"munafiki" dariya Taj ya yi ya ce"naji ɗin, wai Sir Dmash ya
ce nazo na tafi da yarinyar nan" haɗe rai Zaki ya yi bai ce masa komai ba ya kalli Muhaira
wacce take kallon Taj ya ce"kee come here" miƙewa tana tafiya a hankali ta ƙaraso gabansa ta
tsuguna kallon fuskarta ya yi for some minutes sai kuma ya ce"jeki bedroom ɗina ki ɗaukan
wayana" miƙewa tayi ta haye sama, sai a sannan ya kalli Taj ya ce"zan kai masa ita da kaina
kawai kayi tafiyarka" kallonsa Taj ya yi da mamaki ya ce"da kanka kuma amma why?" haɗe rai
ya yi ya tashi ya miƙe tsaye daidai lokacin Muhaira ta sakko hannunta riƙe da wayar tasa,
kallonta ya yi sanye take da wata riga long sleeve amma bata ƙarasa saukar mata ba ta tufke
gashin kanta ya sauka har wajen ƙugunta, miƙa masa wayar ta yi ya karɓa sannan ya yi waje
yana jan hannunta.
Kai tsaye part ɗin ƴan matan gidan yana nufa har sannan kuma yana riƙe da hannunta ita
kuwa sai binsa take kamar wata doluwa suna zuwa ya tura ƙofar bakinsa ɗauke da sallama
wacce ba lallai bane su jita, zaune take a parlon tana karatun littafinta da sauri ta miƙe cikin
rawar murya ta ce"bar...barkaaa da fitowa yallaɓai" kallonta ya yi from head to toe sai kuma ya
ɗauke kansa ya ce"uhnnn ina suke sauran?" cikeda ladabi ta ce"suna bedroom bacci suke" bai
ce komai ba ya juya ya bar wajen Muhaira ta bita da kallo. Cikin wata mota Fererri ash colour ya
sanyanta sannan ya zagaya wajen driver da sauri guards ɗinsa suka tawo ya ɗaga musu hannu
sannan shiga motar ya yi mata key bakinsa ɗauke da addu'a.
A hankali ya sanyo ƙafarsa waje bayan ya kashe motar kusan 2mins yaga bata fito ba hakan
yasa ya koma side ɗinta yana yi mata wani kallo ya ce"jira kike saina fito dake ne?" zumɓura
baki ta yi ta ce"to ni nasan yanda ake buɗewa ne da zaka yimin faɗa" kwafa Zaki ya yi sannan
ya buɗe motar yana harararta ya ce"baƙauyiya kawai" fitowa ta yi sannan itama ta galla masa
harara cikeda tsiwa ta ce"naji ɗin kai kuma mai yiwa mutum iss..." maganar ta maƙale saboda
wani mugun kallo da taga ya watsa mata ta haɗe rai itama tana ɗauke kanta tsaki ya yi sannan
ya ce"Mumu kawai witch" wasu hawayene suka shiga sakko mata na baƙin ciki ita kwata-kwata
batasan mutumin nan saboda ko kaɗan bashida kirki a hankali ta shiga murza idanunta tana
shashshekar kuka dafe kansa ya yi ganin yarinyar na son tara masa mutane ya ce a
fusace"idan baki yimin shiru ba saina kwaɗa miki mari wlh" banza ta yi masa ta nemi waje ta
zaune kasancewar duk ƙasan garin kamar glass yake ko'ina tsaf, kallon agogon rollex ɗin
hannunsa ya yi sai kuma ya kalleta ya ce" shikenan tashi kiyi shiru kinji" turo baki ta yi tana
murza idonta ta ce"to ka maidani gidanmu ni, banason nan ni banasoo!!" ta faɗa tana sake
fashewa da kuka.
Ganin da gaske Muhaira bazata tashi ba yasa ya yi gaba cikin wata iriyar murya mai ban tsoro
ya ce"gasu nan ku kamata" da gudu tabi bayansa tana riƙe masa hannu kyakkyawan murmushi
ya yi ita kuwa ta riƙe shi gam gudun kada ya tafi ya barta. *Olaya Aqua park* shine sunan dake
saman haɗaɗɗen ginin cikin tafiyarsa ta isa ya shiga ciki tana riƙe da hannunsa.
*ZAKI HAKA ZAMU YI DAKAI*
# *LOVE*
# *DESTINY*
# *POWER*
# *TRAFFICKING*
# *SQUAD 2024*
# *NANAMEERA CE!✍️*
[8/7, 1:58 PM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!..*
*Ameenatou I Ibrahim*
*Nanameera*
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
```Page 09```
*Olaya Aqua park*
Kallon wajen kawai Muhaira take kamar idanunta zasu faɗo iyaka haɗuwa wajen ya haɗu park
ne mai ɗauke da swimming pool amma rufaffe akwai wadataccen haske a wajen dan bazaka
taɓa cewa ba rana ba ce ba jan hannunta Zaki ya yi suka shiga wata ƙofa sai a sannan tagane
ashe da ba taga komai ba inda suke tsaye yafi inda suka shiga da farko haɗuwa tsayawa ya yi
gaban swimming pool ɗin wanda yake bada feshin ruwa mai matuƙar sanyi murmushi tayi tana
cire hannunta daga nasa ta ƙarasa wajen tana shirin zura ƙafafunta taji an riƙeta. Kwaɓe fuska
tayi tana kallonsa taga ya haɗe rai sai ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya ta ce"dan Allah
Papi nashiga?" girgiza mata kai ya yi ta langwaɓar da kanta cikin sigar roƙo ta ce"wlh bazan yi
wasa ba" taɓe bakinsa ya yi sannan ya ja hannunta zuwa wasu kujeru wanda suka zagaye
wajen zama ya yi ya zaunar da ita gefensa bai ce mata komai ba, sosai ranta ya ɓaci dan ita a
rayuwarta tana matuƙar son wasan ruwa dukda illar da hakan ke mata wata waiter ce tazo ta
ajiye musu ice-cream a table ɗin gabansu sannan tabar wajen, kallon ice-cream ɗin Muhaira ta
yi amma bata ɗauka ba wayar hannusa ya mayar aljihu sannan ya ɗauki ice-cream ɗin guda
ɗaya ya fara sha sosai yake lumshe idanu saboda daɗin ice-cream ɗin hakan yasa Muhaira ta
sanya hannunta zata ɗauki ɗayan, buge mata hannu ya yi yana harararta har sannan kuma bai
ce mata komai ba. Turo baki ta yi cikin shagwaɓa ta