Showing 27001 words to 30000 words out of 44270 words
kaiki" da sauri ta kalleshi taga ba ita
yake kallo ba hakan yasa ta miƙe ta ƙarasa inda yake a tsugune ta zauna a cinyarsa ware
idanunsa ya yi yana kallonta da alama tafara sabawa da zama a cikinsa cikin sanyin murya ta
ce"Allah ya ƙara maka arziƙi ya baka abinda kake nema Nagode sosai" wani kyakkyawan
murmushi ne ya suɓuce masa ya shafa kanta yana gyaɗa mata kai cikeda da murna ta shige
bedroom ɗinta tana rawa kamar wata Baby. Murmushi Taj ya yi yana kallonta ya ce" gaskiya
yarinyar nan zero tension ce ji yadda take murna dan zata fara zuwa makaranta" girgiza kai
Zaki ya yi bai ce komai ba ya miƙe yana karɓar takardar ya shige bedroom ɗinsa.
*FCT, ABUJA*
"Ma'eesha!! Ma'eesha!! Ma'eesha!"
a firgice ta buɗe idanunta tana kallon Mami sai kuma ta tashi zaune kallonta Mami tayi ta
ce"mene y sanya ki bacci haka? har wajen 9am bakiyi sallar asuba ba?" hamma tayi ta ce"wlh
Mami kaina ne yake ciwo tun jiya to banyi bacci da wuri ba shiyasa na makara sorry" girgiza kai
Mami tayi ta ce"gashinan idanunki sun kumbura hala kuka kika yiwa ciwon kan?" turo baki tayi
Mami ta girgiza kai ta ce"Allah ya shiryeki, maza kiyi sallah ki fito ki ci abinci sai a kira doctor
yazo ya dubaki" gyaɗa mata kai tayi sannan ta tashi ta shige toilet ita kuma Mami ta yi waje.
Kasancewar ranar Saturday ya sanya babu makaranta tana zaune wajejen 2:30pm Mommy ta
fito, kallonta ta yi sai kuma ta ce"Mommy har za ki tafi?" gyaɗa mata kai Mommy tayi tana
murmushi ta ce"General ya hana da mun tafi tare" Ma'eesha ta kwaɓe fuska ta ce"ai yau babu
school kuma ba kwana zaki yiba ko?" gyaɗa mata kai ta yi ta ce"please zan biki" girgiza kai
Mommy tayi ta ce"A'a tunda ya hana ki haƙura kinsan halin babanki ki bari next idan zani sai mu
tafi tare" buɗe baki tayi zatayi magana Farooq ya fito yana sanye cikin wata dakakkiyar shadda
black colour ya sanya hula zanna akansa sai zuba ƙamshi yake, shiru tayi da bakinta sai kuma
ta miƙe ta ratsa ta jikin Mommy ta haye sama. Da mamaki Mommy take kallonta har ta haye
sama sai kuma ta kalli Farooq wanda shima ya bi Ma'eeshan da kallo, taɓe baki ya yi sannan ya
ce"Mommy muje" "lafiya dai meya haɗaka da ita?" bai cewa Mommy komai ba ya yi waje hakan
yasa dole itama tabi bayansa.
Da mamaki yake kallon wanda yake tsaye jikin motar ya harɗe hannayensa a ƙirji sanya yake
cikin wata dakakkiyar shadda Madam gezner ash colour ya ɗora zanna ash akai hannunsa
maƙale da rollex ya sanya Glass baƙi a fuskarsa hannayensa zube cikin aljihu da alama akwai
wadda yake jira, tsayawa ya yi a wajen kamar statue can kuma yaji an buɗe ƙofsr entrance ɗin
gidan Ma'eesha ce ta fito cikin wata Eigypt Abaya purple colour mai manyan flower a jiki white
colour ta yi rolling fuskarta da veil ɗin Abayar hannunta riƙe da wayarta iphone 13pro max. Ta
gabansu ta shige ta ƙarasa inda yake tsabar baƙin ciki yasa Farooq ya shiga binsu da kallo
kamar wani dolu can kuma ya ƙarasa wajen yana tafiya kamar wani damisa. Tsaye ya gansu
yana mata magana cikin ɓacin rai ya ce"kee dan ubanki zo ki shige gida" wani kallon sheƙeƙe
tayi masa sai kuma ta ce" bazan shiga ba wlh kuma karka sake zagin ubana" sakar baki ya yi
yana kallonta sai kuma ya kalli Khalil wanda ya nuna baima san dashi a wajen ba ya ce"kai
kuma idan kanaji da tashen iskancinka kasan inda zaka dinga zuwa kana yi saboda akwai inda
idan kayi ranka zai ɓaci, ka fita a harkar yarinyar nan idan ba haka ba wlh sai na saka kayi dana
sani mara amfani babu ruwanka da ita kaji na faɗa maka idan kuma kaƙi jin abinda na faɗa
maka ta lallami to ka sani zanyi maka Yaren dana tabbatar zaka fahimta kuma..."
"Haba yaya Farooq maganganunka sun fara tsauri kasan irin abinda zaka dinga furtawa idan ba
haka ba kuma wlh nima zan yi maka abinda bakayi zato ba ni ba baiwar ka bace inada ƴancin
nayi abinda nakeso ko mahaifina bai takura min ba balle kuma kai ka fita a harkata"
Girgiza kai Farooq ya yi ya ce"ke ai banida lokacinki yanzu amma ki bari anjima na dawo saina
baki mamaki" yana faɗin hakan yabar wajen kamar zai tashi sama. Da harara ta bisa sannan
tayi kwafa kallonta kawai Khalil ya yi sai kuma ya furzar da nunfashi ya ce"eesha wannan bai
dace dake ba, da hankalinki ki dinga ihuu kowa yana jinki" wani kallo tayi masa tana kwace
hannunta daga nasa ta ce"ni cikani!" yanda tayi maganar cikeda tsiwa ya sanya ya yi murmushi
ya ce" to laifin kaina ya dawo?" harararsa ta yi ta ce a zafafe"karka sake zuwa gidanmu dan ni
bazan auri ragowar wata ba kaje ka kula da matarka wlh" baisan sanda ya tuntsire da dariya ba
yana girgiza kai ya ce"
# *Ameenatou ce✍️*
# *BA ITA BA CE!*.
[8/9, 12:19 PM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!..*
*Nanameera*.
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
```Page 12```
# *Love*
"Narasa yaushe kika koyi tsiwa eesha da dai ba halinki bane" turo baki ta yi ta ce"sanda ka
yaudareni sannan nikuma na koya" girgiza kansa ya yi dan yasan rigima take nema, kusan two
minutes sannan ya ce"munyi magana da Dad jiya kuma ya ce zai yiwa Father magana" zaro
idanu ta yi tana dafe ƙirjinta ta ce"nashiga uku wace magana kenan?, ban fahimta ba?"
murmushi ya yi ya ce"maganar aurenmu mana koda kinyi zaton wasa nake?" haɗe rai ta yi ta
ce"yaya Khalil ka daina yimin irin wannan wasan wollah banaso" cikin tafiyarsa ta isa ya ƙaraso
gabanta ya kama hannunta yana murzawa ya ce"eesha stop joking kinji kinsan Ina sonki nd
kuma ni ne wanda Father ya yiwa alƙawari sbd haka dan Allah ki furamin asiri kar kice a'a"
girgiza kanta ta yi tana zare hannayenta ta ce"A'a ya Khalil yanzu kai ba tsarana bane kada ka
manta a wancen lokacin ba kayi aure ba sannan baka kai matsayin daka taka yanzu ba jiya ban
samu nayi bacci ba saboda tunane-tunane dan Allah karka sake karyamin zuciya ka barni da
abinda yake damuna yaya Khalil" ta ƙarashe maganar tana haɗe hannayenta alamar roƙo.
Hankalin Khalil ya tashi dan abinda take faɗa daga zuciyarta yake fitowa tuni jijiyoyin kansa
suka tashi cikin rawar murya ya ce"ees... eeshana dan Allah karki barni karki jiyamin baya ki
taimaka ki kasance dani a karo na biyu ki bani dama nayi miki alƙawarin bazan yaudare kiba
dan Allah ki taimaka" kallonsa tayi sai kuma ta girgiza kanta tana dariya mai haɗe da hawaye ta
ce" wlh bazan iya ba yaya Khalil kamar yanda na faɗa maka yanzu zuciyata akwai wanda take
muradi saboda haka leave me mu cigaba da kasancewa matsayin ƴan'uwa wannan ya wadatar
please" tana gama faɗar haka ta juya ta koma gida da gudu sbd kukan da yaci ƙarfinta. Dafe
kansa ya yi cikin tsananin tashin ya ce"inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun Allah ka taimakeni ka
sassauta zafin zuciyar Ma'eesha ko na samu salama" ganin yana ɓata lokaci kuma tayi tafiyarta
yasa ya shiga motarsa ƙirar Honda Accord ya bar gidan. Girgiza kai Mami tayi cikin son
rarrashinta ta dafata ta ce"mene ne nayin kuka Ma'eesha?, tunda har Khalil ya baki haƙuri ya
kamata ace kin haƙura kinsan halinsa bashida wani mummunan hali to me kike nema wajen
namiji?" ɗagowa tayi daga cinyar Mami cikin kuka ta ce"Mami bazaki gane irin zafin da zuciyata
ke yimin ba, Mami inaji kamar zan mutu yaya Khalil ya auri wata bani ba bazan taɓa samun
kwanciyar hankali ba idan na aureshi saboda bazan iya jurar ganinsa da wata Macen ba"
murmushi Mami tayi tana goge mata hawayen fuskarta ta ce"Ma'eesha kenan karki kuskura ki
saka a ranki cewa ke mijinki naki ne ke ɗaya yanada damar aurar wacce yakeso matuƙar
yanada halin riƙeta kuma daga gidanku kake fara koyar abu ni kaɗai ce a gidan nan?" girgiza
mata kai ta yi, Mami ta ci-gaba da faɗin"saboda haka kima daina kawo wannan tunanin a ranki
ki maida komai ba komai kinsan babu abinda zai hana babanki ya bawa Khalil aurenki sai ikon
Allah sbd haka ki daina wannan damuwar matuƙar kin riƙe mijinki yanda ya kamata to bazai
taɓa kufce miki ba koda ace ku huɗu ne a wajensa" shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya Mami ta
miƙe ta fita a ranta tana jinjina yarinta irinta Ma'eesha.
Da mamaki ya ƙara sa gaban gadon yana kallon yanda duk ta naɗe cikin bargo ya
ce"Ramlah!! Ramlah!! Ramlahhh" da sauri ta miƙe daga kwancen tana murza idanunta sai
kuma ta langwaɓar da kai ta ce"wlh doctor banajin daɗi zuciyata zafi take yimin" zama ya yi
gefen gadon sai kuma ya ɗora hannunsa kan ƙirjinta dan jin yanda zuciyarta ta ke bugawa,
janye hannunsa ya yi yana miƙewa tsaye ya ce"bari na kawo miki drugs ɗinki da ruwa sai kisha"
gyaɗa masa kai tayi sannan ya juya ya fita murmushi ta yi sannan takoma ta kwanta. Zaune ya
samu Mommy tana kallon wani series da ake haskawa bai ce mata komai ba ya shige parlonsa
ko minti biyu ba ayi ba ya fito hannunsa riƙe da ledar drugs kallonsa Mommy ta yi sai kuma ta
ce"subhanallahi wace babu lafiya?" yana duba ledar drugs ɗin ya ce"wai Ramlah ce bata jin
dadi shine zan bata magani" okay Mommy ta ce sannan ya juya ya koma bedroom ɗin, kwafa
Mommy ta yi tana cewa"yaro baisan wuta ba sai ya taka jira zakaga abinda na aikata" sai kuma
tayi wani kyakkyawan murmushi ta cigaba da kallonta cikeda nishaɗi. Sai bayan sallar isha'i
sannan suka shigo gidan babu kowa a parlon daman kuma haka suka so kawai kowa ya yi part
ɗinsa, taɓe baki Ma'eesha tayi dan tana kallo suka shigo suna sanɗa kamar wasu munafukai
haka kawai taji yanzu bata sonsu musamman ma Farooq wanda take jin da tanada dama da
tuni ta koreshi daga gidan murmushi tayi tana sipping coffee ɗinta Saboda tunawa da yaya
Khalil da tayi idan ta ce bata sonsa to kowa zai gane ƙarya take dan ita kanta tasan tana
mutuwar son Khalil kawai tana jin haushin auren da ya yi ya barta ne. Saida ta shanye tass
sannan ta fito daga kitchen ɗin a hankali ta shiga tafiya saboda duhun daya mamaye parlon
haka kawai taji tsoro ya rufeta.
Numfasawa ne ya kusa ɗaukewa saboda jin abu da tayi agabanta cikin tsananin tashin
hankali ta buɗe baki zaka kwalla ƙara, da sauri ya toshe mata baki yana yi mata alama da tayi
shiru, kusan five minutes kafin ya ɗago ya kalleta da idanuwansa da suka sauya kala cikin wata
iriyar murya ya ce" Ma'eesha! da sauri ta kalleshi dukda ba ganin fusakarsa take yi ba ya ce"naji
I'm sorry amma bazan sake ba bazan sake yi miki abinda nayi yanzu ba dan Allah forgive me
my lil sis" da sauri ta faɗa jikinsa tana kuka mara sauti, murmushi Farooq ya yi sannan ya dafa
kanta ya ce"Nagode sosai ƴar albarka dare ya yi shige ki kwanta" gyaɗa masa kai ta yi sannan
ta juya ta haye sama ta barshi nan tsaye yana saƙa da warwara.
*RIYADH*
*Al Yesmin international school*
Fitowa tayi daga cikin makaranta tana kallon yanda ake ta zuwa ɗaukan yara gaba ɗaya a
gajiye take ga wani irin ciwo da ƙirjinta ke mata tura baki tayi ganin har sannan ita babu wanda
ya zo ɗaukanta waje ta nema ta zauna ta miƙe ƙafarta saboda wani irin ciwo da take mata tun
daga nesa yake kallonta ganin yanda duk ta kwaɓe fuska kaɗan ya rage bata fashe da kuka ba,
fitowa ya yi daga motar yana sanye cikin Jallabiya Black colour idanunsa maƙale cikin sun
glasses kasancewar akwai rana a garin kwata-kwata Muhaira bata lura dashi ba har ya ƙaraso
gabanta girgiza kansa ya yi sannan ya ja kunnenta da sauri ta ɗago tana kallonsa sai kuma ta
fashe da kuka bai ce mata komai ba ya kama hannunta suka bar wajen saida ya sanyata a
motar sannan ya kalleta ganin yanda take kuka kamar wacce aka yiwa wani abu ya ce"za ki
yimin shiru ko sai ranki ya ɓaci?, sbd ke kike da bakin kuka duk abinda aka yi miki sai ki fashe
da kuka?" tura masa baki ta yi tana shashshekar kuka. Siririn tsaki yaja sannan ya ja motar
suka bar wajen, a bakin ƙaton gate ɗin gidan ya yi parking ba tareda ya kalleta ba ya ce"sauka"
kallonsa ta yi sai kuma ta buɗe motar ta fita shi kuma ya bar wajen kallonta suke har ta shigo
gidan suna zaune kan wata kujera suna hira shigewa ta zo yi Tyha ta ce"keee zo nan" juyowa
Muhaira ta yi ta kalleta sai kuma ta tura ƙofar ta shige batareda ta amsa kiran da tayi mata ba
baki buɗe Tyha ta bita da kallo sai kuma ta yi kwafa ta ce"wai wannan wace ce?" ɗaga kafaɗa
Amrish ta yi ta ce"nima nasani maybe dai itama siyanta akai ko kuma aka satota" Zeey ce ta
ce"kenan ita ba a cikinmu take ba naga tana kwana part ɗin Zaki?" Tyha ta ce"tunda kikaga
haka ko Zaki ɗin ne ya riƙeta maybe dan ya ganta da kyau ne kuma daga gani yarinyace sosai"
murmushi Amrish ta yi ta ce"aikuwa amma duk da haka yarinyar batada kunya" numfasawa
Tyha ta yi ta ce"aikuwa zan yi maganinta saidai idan ba zata fito ba" tsaki Zeey ta yi ta ce"ke
daɗina dake rashin tunani to da gani kike tana fitowar?, yau ɗin ma bakiga school taje ba" wani
kallo Tyha ta yi mata ta ce"dalla Malama karki sake cemin mara tunani zan miki rashin mutunci
wlh" ganin abin nasu na neman zama faɗa yasa Amrish ta ce"dan Allah ku saurarawa mutane
wannan ai ba daidai bane ku dinga abu kamar wasu yara" buɗe baki tayi zata yi magana
sukaga Zaki ya shigo gidan da motarsa sunkuyar da kansu sukai har ya fito daga motar
hannunsa riƙe da ledoji. Wani guard ya miƙawa ledojin sannan ya yi gaba, yana zuwa suka
sunkuya cikeda girmamawa suka ce"sannu da zuwa yallaɓai" bai basu amsa ba ya yi gaba, har
ya riƙe handle ɗin ƙofar sai kuma ya juyo yana tafiya hannunsa zube cikin aljihu ya ce" ina
sauran?" Tyha ce ta ce"sunje school" "then ku mene ya hanaku zuwa?" kasa bashi amsa suka
yi ya ce"idan ba zakuyi karatu ba kunfi son ɗaya rayuwar fine zanyi maganinku" yana faɗin haka
ya juya ya shige parlon.
Dafe ƙirji Amrish ta yi ta ce"mun shiga uku wlh tun wuri musan abunyi nidai zan koma school
gobe" Zeey ta ce"nima haka wlh dan nasan idan ya waiwayemu abun bazai yi da kyau ba"
kallonsu Tyha ta yi sannan ta ce"sai abinda Taj ya ce min" tsaki Amrish tayi ta ce"banza kawai"
tashi suka yi suka barta a wajen saida taga sunyi nisa sannan itama tabi bayansu. Da sauri ya
ƙarasa inda take kwance ɗin idanunta har sun fara ƙaƙƙafewa ɗagota ya yi jikinsa yana kallon
fuskarta ya jijjigata ya ce"keeee! keee!" ganin tana neman rasa rayuwarta gashi babu inhaler a
gidan yasa ya zauna yana gyara zamanta akan cinyarta a hankali yayi coping face ɗinsu ya
ɗora bakinsa daidai nata cikin nutsuwa ya zura bakinsa cikin nata sannan ya saki wani zazzafan
numfashi da sauri ta riƙeshi tana sauke wani irin numfashi saida ya yi mata haka wajen sau uku
sannan numfashin nata ya dawo zare bakinsa ya yi daga nata yana kallonta har sannan wasu
hawayene suka shiga sakko mata na zallar azabar fitar numfashi, sosai ta bashi tausayi dan
yasan azabar cutar numfashi dan har yanzu idan Asthmarsa ta tashi sai ya yi kamar ya rasa
ransa. Saukar numfashinta ya ji a ƙirjinsa hakan yasa ya kalli fuskarta gani ya yi tayi bacci ya
shafa kanta sannan ya miƙe da ita ya shiga bedroom ɗinta yana kwantar da ita ya juya tayi
saurin riƙe masa hannu cikin wata iriyar murya ta ce"karka barmu ka zauna a nan tsoro muna ji"
kallon fuskarta ya yi yaga ta kwaɓe fuska hakan yasa ya zauna gefen gadon ya zuba mata
idanu yana kallonta wata iriyar ƙara ta saki sai kuma ta miƙe zaune tana sauka daga kan gadon
da sauri cikin zafin nama ya riƙota ya haɗata da ƙirjinsa ya rufeta ruf yana jin yanda take ƙoƙarin
guduwa ya sake rufeta yana haɗe face ɗinsu waje guda cikin wata iriyar murya mai amo tashiga
furta" mu ka kyalemu tafiya zamuyi da ita ka rabu damu ka daina riƙemu" shiru ya yi yana sakin
ajiyar zuciya ya ce"au kune?" sake yunƙurawa tayi ya yi saurin rungumeta yana sakin murmushi
ya ce"meyasa zaku tafi da ita to?" ta ce"saboda ita ɗin amanarmu ce babanta ya barma
amanarta kafin ya mutu sbd haka dole sai ta bimu ka rabu damu" haɗe ransa ya yi yana
dungure mata kai ya ce"ƙarya kuke" "mu ba ƙarya muke ba munsan Allah ai" murmushi ya yi ya
ce"au da gaske?" gyaɗa masa kai ta yi ya ce"shikenan muyi abu guda, naji ku tafi amma ku
barmin amanarta ni zan riƙe muku nayi alƙawarin bazan bari wani abu ya cutar da ita ba" tura
baki tayi gaba ta ce"kayi alƙawari?" gyaɗa kansa ya yi ta sake cewa"to amma bazaka bari kowa
ya taɓa ta ba, duk randa wani abu ya sameta to ka karya alƙawarinmu kuma zamu zo mu tafi da
ita" numfasawa ya yi ya ce"na yarda" murmushi ta yi tana miƙo masa hannunta ta ce"to kayi
mana alƙawari" girgiza kansa ya yi sannan ya ɗora hannunsa akan nata, waya sassanyar ajiyar
zuciya ta sauke sai kuma jikinta