Showing 21001 words to 24000 words out of 44270 words

Chapter 8 - BA ITA BA CE! Free Books by Nanameera.pdf

11 May 2025

2486

ce"toh ni bazan sha ba?" banza Zaki ya yi
mata ya cigaba da abinda yake aikuwa ta fashe da kuka yana jinta har ya shanye na hannunsa
sannan ya ɗauki ɗayan ma ya fara sha ganin da gaske shanyewa zai yi bai bata ba yasa ta ƙara
volume ɗin kukanta wani killer smile ya yi sannan ya kalleta ganin yanda duk ta ɓata fuskarta da
hawaye ya ce" then you like it?" saurin gyaɗa masa kai ta yi ya dungure mata kai ya
ce"kwaɗayayiya kawai" hannunta ta sanya tana dafe goshinta ta ce"ohhccccc zafi wayyo"
harararta ya yi sannan ya miƙa mata ragowar na hannunsa karɓa tayi tana cigaba da kukanta
har ta shanye sosai ice-cream ɗin ya yi mata daɗi dan yau ne shanta dashi na biyu miƙewa ya
yi yaje wajen swimming pool ɗin ya zauna a nutse ya zura sangalin fararen ƙafafunsa cikin
ruwan a hankali yake furzar da wani zazzafan numfashi gabaɗaya tunaninsa ya kwance
abubuwa nason fin ƙarfinsa rauninsa nema yake ya fito fili wanda hakan ne yake gudu.


Ƙarar ruwan da yaji shine ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi a hankali ya kalli
gefensa ganin yanda wajen yake kwai alamar wanda ya faɗa yana numfashi, da sauri ya juya
inda yabar Muhaira amma sai yaga wayam babu ita da sauri ya mike tsaye yana sake kallon
ruwan, kenan yarinyar cikin ruwan ta faɗa??, Furzar da nunfashi ya yi yana dafe kansa sai
kuma ya juya wajen wani table ya ajiye wayarsa sannan ya koma wajen without second thought
kuma ya faɗa ruwan shima ji kake "tsundummmmm" saida ya fara iyo cikin ruwan sannan ya
hangota can daga ƙarshen swimming pool ɗin kasancewar bashida wani zurfi yana zuwa ya
jayonta ya rungume jikinsa sannan ya fito gaba ɗayan jikinsu sai ɗigar ruwa yake ajiye ya yi
gefen wajen ganin ko numfashi batayi yasa ya matse cikinta da sauri ta fara tari ruwa na fitowa
ta bakinta saida duk ruwan ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya idanunta sun rune sunyi jajur
dasu tsaki ya yi sannan ya miƙe ya ɗauki wayarsa yana kallonta ya ce"tashi" shiru tayi masa
tana kallonsa dan batajin zata iya tashi, ganin tana son ɓata masa lokaci yasa ya sunkuya ya
ɗauketa kamar Baby suka fice daga wajen kai tsaye kuma motarsa ya nufa da ita.


Wani irin sanyi ne ya shiga ratsa duk wata ƙofa ta jikinta sai rawar sanyi take hakan yasa ya
kashe AC motar amma dukda haka bata daina ba, wani shahararren gudu ya shiga yi cikin ƴan
mintuna suka ƙaraso gida. Suna shiga ya kamo hannunta ya fito da ita taka ƙafarta tayi wanda
yasa ta fashe da wani irin kuka da sauri ya kalleta sai kuma ya ce"mene?" cikin kuka ta
ce"wayyo ƙafata zai cire wayyo Allah nashiga uku Papi ka taimakeni" ganin yanda take kuka da
gaske yasa ya sunkuya ya ɗauketa, suna zuwa ya kwantar da ita kan gadon yana kallon
fuskarta ya ce"next time idan kika sake irin wannan shashancin saina zaneki" yana gama faɗin
haka ya juya ya fice daga ɗakin, tura bakinta tayi sannan ta miƙe zaune ganin duk kayan jikinta
a jiƙe suke gashi sun kama mata jiki, dakyar ta iya miƙewa ta shiga toilet tana hawaye saboda
zafin da ƙafar ke mata.

"Zaki mene haka ka aikata?, inata jiranka ka kawomin yarinya amma naji shiru kasan halin
daka sanya ni?, akanme zaki yi haka?, raina ya ɓaci sosai zuwa da safe lallai ka tabbata ka
kawomin yarinyar nan or else..." Kallon screen ɗin wayar ya yi sai kuma ya ajiye yana taɓe baki
ya gyara kwanciyarsa nan da nan bacci ya ɗaukeshi. Wajejen 2am ta farka saboda tsananin
ciwon da jikinta ke mata ga ƙafarta kamar ana sassara mata ita haka takeji ganin bazata iya
cigaba da zama ba yasa ta miƙe zaune tana sakin wani sabon kuka babu wanda zai taimaketa
dan ko tafiya bazata iya yi ba ganin ciwon na neman hallakata yasa ta sauka daga gadon ta
shiga rarrafe kamar Baby haka har ta fito daga ɗakin kai tsaye kuma ɗakin Zaki ta shiga kwance
ta sameshi yana baccinsa batayi wani tunani ba ta hau kan gadon cikin son samun ceto ta
kwanta gefensa a hankali kuma ta shige jikinsa tana sakin wani irin numfashi. Above 5mins sai
kuma wani wahalallen bacci ya ɗauketa tana sake rufe fuskarta cikin naked chest ɗinsa, duk
abinda take Zaki na jinta dan tun sanda ta shigo ɗakin ya farka jin yanda jikinta ya ɗauki zafi
yasa ya rabu da ita a hankali kuma zafin jikin nata ya dinga shiga nasa jikin lumshe idanunsa ya
yi dan shima ba daɗin jikin nasa yake ji ba haka har bacci ya sake ɗaukeshi.



*FCT, ABUJA*

Sanye take cikin shigar atamfa Holland maroon colour ta ɗora veil fari akai dukda ba wani
babba bane amma tayi kyau sosai, kallonta Najeeb ya yi ganin yanda ta haɗe rai ya
ce"Ma'eesha" batareda ta kalleshi ba ta ce"na'am" "naga kamar baki saurarena" kallonsa tayi
da manyan idanunta sai kuma ta tura baki ta ce"ai naga kunnene ki ji kuma ina jinka"
numfasawa ya yi ya ce"shikenan na baki lokaci kije kiyi tunani da kanki ina fatan za ki yanke
shawara mai kyau" kallonsa tayi har zata yi magana sai kuma tayi shiru ta juya tabar wajen
kawai, girgiza kansa ya yi idan ba soyayya ba ai ya shige ajin yarinya ta dinga wulakanta shi.
Kallonta Fateemah tayi ganin yanda take ta haɗe rai ta ce"wai daman Ma'eesha mene haka?,
bakison mutumin nan fine amma haɗe ran na mene ne?" kwafa ta yi ta ce"wlh idan har bai yi a
hankali ba sai na yi masa rashin mutunci nifa banason irin haka ya fara takuramin wlh"
murmushi Zeey ta yi ta ce"nima dai abinda nagani kenan, ni wlh ban taɓa tunanin ma zai yarda
ki dinga yi masa irin wannan wulaƙancin ba mutum mai hankali da aji" a hasale Ma'eesha ta
ce"to ni na kawo shi ai shi ya kawo kansa inda za'a wulaƙanta shi wlh idan bai yi wasa ba saina
yi masa abinda har ya koma da Allah bazai manta dani ba" girgiza kai Fateemah tayi ta ce"to
Allah ya wuci zuciyarki shalele" harararta tayi ta ce"ni dai ku taso muje wajen sir Ahmad na
bashi assignment ɗina" okay suka ce sannan suka tashi.


Zaune suke a main parlon na gidan banda ƙarar cokula babu abinda ke tashi Mommy ce ta
kalli General ta ce"yallaɓai daman inason zan tambayeka idan babu damuwa" ajiye spoon ɗin
hannunsa ya yi ya ce"uhnn inaji" numfasawa tayi sai kuma ta ce"idan babu damuwa inason
zanje gida zuwa gobe" yana riƙeda glass cup ya ce"ohk Allah ya kaimu" murmushi tayi ta
ce"daman idan babu damuwa inason zan tafi da Ma'eesha" kallonta ya yi for some minutes sai
kuma ya girgiza kai ya ce"tana zuwa makaranta saboda haka bazatayi fashin skull ba saidai

idan anyi hutu" Okay ta ce amma har cikin ranta bataji daɗi ba, tura baki Ma'eesha tayi tana jin
haushin General daya ce ba zata jeba dan ita tanason zuwa wani waje kodan tayi yawo.
Mikewa ya yi bayan ya goge bakinsa da tissue ya ce"zanje Villa" okay sukace ya kalli Ma'eesha
wacce take kallonsa ya ce"Shalele zo ki rakani" da sauri ta miƙe tana murmushi ta ce"yawwa
muje Father" girgiza kai Mami ta yi ta ce"ƙafar yawo shige ki ɗauko veil to". Buga ƙafarta tayi
tana ƙunƙuni ta haye sama da gudu dan kada General ya tafi ya barta, murmushi ya yi kawai
tun daga sama take cewa"Father baka tafi baaa" dariya suka yi duka har ta sakko tana haki
kama hannunta ya yi ya ce"ki daina gudu kar wani abun ya sameki dear" gyaɗa masa kai tayi
sannan sukai waje Mommy ta ce"au ko sallama ba zakiyi mana ba?" ɗaga musu hannu tayi
tana dariya, miƙewa Mami ta yi ta ce"Allah ya shiryaki Ma'eesha" Mommy ta ce"Ameen".


*FAROOQ POV*

Murmushi Abeed ya yi ya ce"kai baba kanada sanyawa kanka damuwa wlh, wai me kake nema
da har zaka bari ranka ya dinga ɓaci nifa idan ni ne kai wannan yarinyar tasa zan shiga na fita
na aura sai nayi amfani da ita wajen kwato abinda yake hannunsa karka manta yana mutuwar
sonta sai ka dinga tilastata tana karɓar kuɗaɗe a hannunsa haka har ka ja naka kasan" furzar
da wani irin numfashi ya yi yana ajiye drink ɗin hannunsa ya ce"kai daɗina dake rashin tunani,
idan da zan iya auren yarinyar ai da tuni nayi hakan bama sai kaji ba, ni yanzu kawai neman
hanyar da zan kawar da yarinyar nake idan nayi hakan nayi rabin aikin" dariyar mugunta Abeed
ya yi ya ce"to saika ɗaura ɗamara dan ni ba ɗan kowa ba bazan shiga ba haka kawai ta kwaɓe
azo a kamani ubanwa zai fito dani, kaima kuma zan baka shawara kayi komai a sannu kasan
dai ubanka mahaifi ba kowa bane idan ka jawo abinda soja zai ɗaureka kaga kayi ba wan ba
ƙanin" miƙewa Farooq ya yi yana buga table ɗin gabansa ya ce"kai a wa ka faɗamin magana
wlh har abada nafi ƙarfin a kulleni dan ko a yanzu inada abinda zai isheni rayuwata saboda
haka maintain ur words!" ya ƙarashe maganar yana nuna shi da yatsa, tashi Abeed ya yi shima
yana murmushi ya ce"Farooq kenan idan har da kanada abinda zai isheka kayi rayuwarka so
why kake neman dukiyar wasu?, kayi rayuwarka da abinda ubangiji ya raba ya baka mana
kadaina hangen dukiyar wasu ka zauna matsayinka na agola wanda aka kula da rayuwarsa
kamar ɗan gida, saboda girman Allah wlh sai kayi mamakin yanda zakaci gaba a rayuwarka"
tsaki Farooq ya yi sannan ya ɗauke wayarsa da car key ɗinsa yabar wajen girgiza kai Abeed ya
yi sannan shima ya ɗauki mukullinsa ya yi waje.


*Asokoro Villa*

Sake riƙe hannun General tayi ganin wasu mahaukan jami'an tsaro dukda ta saba ganin na
gidansu amma waɗannan sunfi nasu yawa, har suka shiga main parlon na gidan Ma'eesha bata
saki General ba sai kwaɓe fuska takeyi saida shugaban ƙasa Muhammad Sani Tanka ya fito
sannan suka zauna bayan sun gaisa ya kalli Ma'eesha ya ce"ƴar Baba kin girma ko?"
kasancewar General abokinsa ne tun suna yara yasa sunsan juna sosai murmushi ya yi ya
ce"daman jiya Khaleel ya dawo kije yana second parlon ɗin nan" to kawai ta ce sannan ta miƙe

tana tafiya a hankali har ta buɗe ƙofar parlon. Haɗaɗɗen parlon ne wanda aka kashe iyayen
kuɗi wajen haɗashi ƙamshin turaren Parfums De marley Layton ne ya daki hancinta ta lumshe
idanunta kafin tayi sallama, zaune yake ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya black beauty ne yanada
cute round face da siririn hanci sai beard ɗinsa mai kyau kana kallon fatarsa kasan kuɗi ya
zauna. Ƙasa ƙasa ya amsa sallamar tata kafin ta zauna kujerar dake gefensa waro idanunsa ya
yi ya kalleta sai kuma ya ce"eesha" murmushi ta yi ta ce"ya Khaleel ina yini?" girgiza kansa ya
yi ya dawo gefenta ya ce"ashe dai ban manta ki ba, ykk yasu Mami?" tana wasada fingers ɗinta
ta ce"suna nan klao, ashe ka dawo" ya ce"Eh nadawo jiya shekaru sun tafi eesha kin girma
abinki" rufe fuskarta tayi da hannu tana murmushi ta ce a shagwaɓe"kai yaya ai kaima ka ƙara
girma sosai ji beka fa kafi ya Farooq" haɗe ransa ya yi ya ce"har yanzu wannan guy ɗin na
gidanku?" sunkuyar da kanta tana gyada masa kai dan tasan ko kaɗan basa shiri da Farooq,
ɗaga kafaɗarsa ya yi ya ce"amma mene yake har yanzu a gidan i think ya isa ace ya yi aure ya
bar gidan" ɗaga kafaɗarta ta yi alamar bata sani ba ya ce"then yana shiga harkarki" ji tayi
gabanta ya yanke ya faɗi ta yi shiru bata bashi amsa ba, hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarta
kallonsa tayi taga fuskarsa babu alamar wasa hakan yasa ta fashe da kuka tana faɗawa jikinsa.
Wata nannauyar ajiyar zuciya Khaleel ya sauke yana riƙe da ita above 3mins kafin ya ɗagota
yana kallonta ya ce"baki amsa min tambayata ba eesha" tura baki tayi gaba ta ce" to ai naga a
gidanmu yake kuma..." kallon da taga ya yi mata ne yasa tayi shiru bata ƙara sa abinda zata
faɗa ba shiru ya yi na wasu seconds tuni idanunsa suka sauya kala wani ruwa ya kwanta a
kansu lura da hakan yasa tayi sauri miƙewa tsaye cikin sigar rarrashi ta tsuguna a gabansa tana
haɗe hannayenta biyu ta ce"dan Allah yaya Khaleel kayi haƙuri bazan sake ba wlh dan Allah" ta
faɗa tana shashshekar kuka miƙewa tsaye ya yi bai ce komai ba ya kama hannunta hakan yasa
ta miƙe itama tabi bayansa har suka shiga wani ƙaton parlon.

Parlon ne babba nan ma ya sake buɗe wata ƙofar inda suka shiga wani haɗaɗɗen waje
kamar stadium ko'ina anyi zane duk bangon ɗakin an yi kaca-kaca dashi hannunta ya ja har
gaban wani bango wanda duk akayi zane iri-iri a jikinsa wani ansa Ma'eesha, wani eesha, wani
kuma Khalil wani kuma Tanka wasu kuma heart aka zana a ciki an saka *Khaeesh* batasan
sanda ta rungumeshi ba tana kuka kamar ranta zai fita hannayensa ya sanya ya zagayeta
ajikinsa yana jin yanda duk ta jiƙa masa ƙirji da hawaye saida tayi kuka mai isarta sannan ta
ɗago ta kalleshi cikin kuka ta ce"ya Khaleel meyasa kaci amanata?, ya Khaleel meyasa kayi
aure ka barni?, ka manta sanda kake cewa ni zaka aura Father zai bar maka ni shine kaje kayi
aurenka a wata ƙasar ya Khaleel baka sona ni kaɗai nake sonka kuma nima yanzu nadaina
sonka bana son..." da sauri Khaleel ya haɗe bakinsa da nata yana bawa lips ɗinta wata
amintacciyar tsotsa yayinda hawaye suka shiga gangarowa kan kuncinsa shima sun ɗauki
lokaci mai tsayi a haka jikin Ma'eesha ban rawa babu abinda yake a hankali ya zare bakinsa
daga nata yana kallon kyakkyawar fuskanta wacce tayi face-face da hawaye ya ce"



# *Khaleel*
# *eesha*
# *Zaki*

# *Muhaira*
# *love*
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce!✍️*
[8/8, 11:33 AM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!..*


*NANAMEERA*

*MIKIYA WRITERS ASSO...*


```Page 10```.

# *The war*

"I'm sorry eesha amma ya kamata ace kin tsaya kin fahimci abinda zan faɗa miki wlh isn't my
fault banida zaɓi na auri Ramlah ne saboda babu yanda zanyi ni ne nake kula da ita nd kuma
yanayin lalurarta dole idan ta ce tanason abu ayi mata shi idan ba haka ba za'a ga ba daidai ba
wannan shine dalilin kawai" girgiza kai tayi tana raba jikinta da nasa ta ce"A'a yaya Khalil kaima
kana sonta yasa ka aureta idan ba haka ba bazaka mance alƙawarinmu cikin sauƙi ba, karka
damu nima yanzu inada wanda nakeso kuma nake shirin aure saboda haka..." hannayensa ya
sanya yana rufe mata baki cikin zafin rai ya ce"wlh baki isaba eesha ke tawace ni kaɗai kuma
babu wanda ya isa ya aureki ina raye kuma na barshi nasan kin gane abinda nake nufi"ture
hannunsa ta yi tana harararsa ta ce"da kenan amma yanzu na shige wannan level ɗin kuma har
abada zan cigaba da kallonka matsayin marayaudari wanda yaci amanata" ta ƙarashe maganar
tana rufe bakinta saboda wani kuka daya zo mata da gudu ta fice daga ɗakin. Jingina ya yi da
wall ɗin ɗakin yana dafe kansa gabaɗaya ya ji duniyar tayi masa zafi furzar da wani irin
zazzafan numfashi ya yi sannan ya juya ya fita. Zaune ya tadda ta kan royal cusion ɗin parlon
sai kuka take kamar ranta zai fita, hannayensa zube cikin wandonsa ya ƙaraso gabanta sannan
ya tsuguna ɗago fuskarta ya yi cikin sanyin murya ya ce"eeshana" kallonsa tayi da idanunta da
suka sauya kala zuwa jaa bata ce komai ta cigaba da kukanta cikin son ya rarrasheta ya
ce"now tell me kina sona?" da sauri ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta janye hannunsa daga kan
fuskarta ta miƙe tana kallonsa ta ce"a baya dai na soka yaya Khalil naji kamar bazan iya rayuwa
idan babu kai ba nayi mararin kasancewa matarka kamar yanda ka kwaɗaitamin" numfasawa ta
yi sannan ta cigaba da faɗin"amma yanzu na haƙura dakai na barka kayi rayuwa mai daɗi da
matar daka aura nima ina fatan nasamu wanda zai soni sona har ƙarshen rayuwa"ta ƙarashe
maganar tana goge hawayen kan fuskarta, miƙewa tsaye ya yi yana kallonta zuciyarsa fal
tausayinta ya ce"Ma'eesha nasan nayi kuskure amma dan Allah karki ɗauki haka matsayin
makamin da zaki cutar da rayuwata har yau har gobe ina sonki kuma inada burin aurenki
ƙaddara ce ta rabamu amma nayi miki alƙawarin wannan karan bazan bari ta rabamu ba"

"Aikuwa kayi kaɗan kuma kayi ƙarya domin ƙaddara ta rigada ta gifta tsakaninku babu kai babu
ita har abada matuƙar ina numfashi wlh Khalil bazan bari ka zauna da ita ba ko a baya ina faɗa
maka balle kuma yanzu da ka rigada kayi aure" hankali tashe yake kallon Mommy bashi kaɗai
ba hadda Ma'eesha wacce tazama kamar statue a wajen kenan har i Wannan lokacin Mommy
bata daina tsanarta ba?, har yanzu tana nan akan bakanta na son ganin bayanta?, a baya ta
saba da cin zarafin Mommy a gareta tun bata san tsanarta Mommy tayi ba har tayi girman da ta
fahimci komai amma tsananin so da ƙaunar da takewa Khalil ya sanya bata iya fushi koda
yaushe tana hanyar zuwa inda suke. Bakinsa na rawa ya ƙarasa wajen Mommy yana kallonta
ya ce"haba Mommy i think ai mun shige wannan level ɗin mene haka please?, mene ne aibunta
da kika tsaneta har haka?, ya kamata ace ko dan saboda ni ki daina yi mata irin waɗannan
abubuwan yanzu fa ba da bace Ma'eesha ta girma tasan kanta zata fahimci duk abinda kike
mata dan Allah Mommy stop it" juyowa ya yi da niyyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login