Showing 1 words to 3000 words out of 44270 words

Chapter 1 - BA ITA BA CE! Free Books by Nanameera.pdf

11 May 2025

2484

[7/30, 10:00 PM] Nanameera✌: https://chat.whatsapp.com/LVwoOVW31kC9r0d7QRPZhP


*BA ITA BA CE..*



*MIKIYA WRITERS ASSO...*


*Follow my account both arewabooks nd Wattpad.*

*nanameera08*_arewabooks_.
*@Nanameera08* _wattpad_.

*Nanameera*


# *SQUAD 2024*.




```PAGE 01```

مسب* لله نمحرلا *ميحرلا


Wata iriyar tsawa mai firgitar da zuƙata aka yi wacce tayi daidai da sanda jaririyar data haifa ta
tsala wani irin ihuu mai cika kunnuwa, ruwane ake yinsa bana wasa ba ruwan da duk wani mai
hankali zai dinga jin tsoron zubarsa an daɗe sosai ba iya makamancin irin wannan ruwan ba
cikin garin Damaturu, duhu ne mamaye da bukkar da suke ciki domin fitilar kwan gab take da
mutuwa dan ko haskenta ba'a gani sai ɗan kyalli wanda shine zai tabbatar maka da cewa an
kunna fitilar. Shirun da jaririyar ta yi ya yi daidai da ɗaukewar ruwan tamkar ba'a taɓa yinsa ba a
hankali matashiyar matar take sauke wani wahalallen numfashi wanda take jansa dakyar,
tsuroo magidancin mutumin ya zuba idanunsa yana kallon abinda matar tasa ta haifa sosai
kuma ya yi mamakin yin shirun jaririyar. Above 20mins suna cikin wannan halin har sannan
kuma babu wanda ya furta wata kalma a cikinsu, dakyar matar ta yunƙura dan ganin halin da
abinda ta haifa yake ciki daidai lokacin da zuciyarta tayi wata irin kyakkyawar buguwa dalilin
ganin ɗiyar tata da tayi yashe a gefenta ko ba'a faɗa mata tasan itama tabi sauran ƴan uwanta,
runtse jajayen idanunta tayi wasu zafafan hawaye suka shiga zirarowa kan kuncinta tabbas taji
babu daɗi kamar yanda ta saba jin babu daɗi ce eh.' a duk sanda ta haifa ɗa ko ƴa kuma ya
mutu amma ya zatayi? tata ƙaddarar kenan jiki asanyaye ta janye gawar jaririyar bayan ta

yanke cibiyar sannan ta ɗorata akan ƙirjinta bayan tsayin watanni data ɗauko tana ɗawainiya da
cikin tasha wahala kamar yanda ta saba sha kowane lokaci sai gashi yanzu ma Allah ya karɓi
abarsa. Miƙewa magidancin ya yi ya ɗauki wata ƙwarya wacce ke can gefe guda ya yi waje...
Wani irin sanyin ake mai tsara ƙofofin jiki yayinda har sannan yayyafin bai gama zuba ba
yanayin da ya yi wani irin daɗi banda ƙamshin ƙasa babu abinda ke tashi sai kuma kukan kwaɗi
wanda ya samo asali dalilin taruwar ruwa a wajejen, daga can wani gefe inda ruwa ya taru
yanayin wajen kamar pond ya ƙarasa yana tafiya a hankali. Tsugunawa ya yi sannan ya kafa
kan tulun yana tarar ruwan da yake zuba a hankali yake sauke ajiyar zuciya wacce take nuni da
halin da zuciyarsa take ciki saidai tsananin tsoron Allahnsa da kuma yarda da ƙaddara ya
hanashi fallasa asirin zuciyarsa. Tamkar wanda aka tsikara haka ya juya gefensa daga can gefe
guda ya hango wani farin abu mai ɗan faɗi kai tsaye bazai iya cewa ga abinda yake ciki ba.
Ɗauke idanunsa ya yi daga wajen yana ambaton sunan Allah ya miƙe tsaye bayan ya gama
ɗiban ruwan ya ɗora bisa kafaɗarsa. Gaba ya yi batareda ya sake kallon inda yaga wannan
farin kyallen ba, da sauri yaja ya tsaya saboda wata irin bugawa da zuciyarsa ta yi a hankali
kuma ya juyo yana kallon bakin pond ɗin tamkar wanda mayen ƙarfe ke jansa haka ya samu
kansa da komawa wajen sosai sanyin asubar yake shigarsa wanda ya haifar masa da wani irin
masassara mai kamada zazzaɓi, sake tsugunawa ya yi a karo na biyu amma wannan karon ya
tsuguna ne gaban wannan farin yadin sosai ƙirjinsa ke dukan uku uku yayinda wata
matsananciyar fargaba ta ziyarceshi a nutse bakinsa ɗauke da sunan Allah ya ɗora hannunsa
kan yadin amma ga mamakinsa sai yaji wani irin laushi wanda bai taɓa jinsa a jikin wani nau'i
na tufafi ba tamkar auduga saidai kuma yanada wani irin gashi a jikinsa kamar na jikin mage
hannunsa na wata iriyar kakkarwa ya buɗe yadin wanda kai tsaye za'a iya kiransa da bargo ya
subhanallahi!! da sauri ya yi baya sakamakon abinda ya yi arba dashi cikin wannan bargon cikin
ransa yake furta duk wani sunan Allah da yazo bakinsa kuma iyaka iyawarsa kusan 2mins yana
wannan halin kafin kuma ya yi ta maza saboda wata jarumta da yaji ta zo masa a hankali ya
saka hannayensa duk biyun ya ɗauki bargon sannan ya miƙe tsaye kasancewarsa mutum mai
cikar zati ya sanya ya ɗauki tulun da ɗaya hannunsa sannan ya cigaba da tafiya dan komawa
inda ya fito.

Yanda ya bar matar haka yazo ya tarar da ita har sannan kuma jaririyar tana kwancen bisa
ƙirjinta tayi nisa cikin duniyar tunani dan kwata-kwata batasan ya shigo cikin bukkar ba lura da
hakan ya sanya bai kulata ba ya ƙarasa can gefen tabarmar kabar ya shimfiɗar da halittar dake
cikin bargon domin idan har ya ce yasan mene a ciki ya yi ƙarya ganin yanda bargon yake a jiƙe
ya sanya ya yi saurin yaye shi daga cikinsa ya ilahy wani irin daddaɗan ƙamshi ne ya ratsa cikin
hancinsa wanda lokaci ɗaya ya cika cikin ƴar ƙaramar bukkar tasu jinjina kansa ya yi cikeda
al'ajab ya miƙe yana ƙarasawa wajen matar tasa dukda duhun dake bukkar hakan bai hanashi
ganin kyallin hawayen dake fuskarta ba numfasawa ya yi sannan ya sanya hannayensa ya karɓi
jaririyar hannunta sannan ya miƙe ya fice daga bukkar sai a sannan ta saki wani raunataccen
kuka mai tafiya da imanin duk wani mai saurare kuka ne mai fitowa tun daga ƙawon zuciyarta
kuka ne mai nuni da tsananin baƙin cikin da take ciki kanta ta matse tsakanin cinyoyinta ta
cigaba da rera kukanta.

Misalin ƙarfe 5:10am ya dawo cikin bukkar lokacin haske ya ɗan fara shigowa cikin bukkar

da sauri ya ƙarasa wajen da ya yi ajjiya dan a wannan lokacin ji ya yi yana buƙatar mene ne
shigowarsa ya yi daidai da ɗagowar matar a hankali kuma take binsa da idanunta wanda suka
sauya launi daga fari zuwa jaa hannayensa ya sanya ya ɗaga halittar daidai nan kuma ta
ƙaraso gabansa da wani irin sauri kallonsa take sai kuma ta kalli abinda ke hannunsa jaririyace
mace kuma sannan kana ganinta kasan ɗanyen jego ce domin ba zata taɓa shige kwana ɗaya
da haihuwa ba, da sauri ta karɓe yarinyar tana zuba mata idanu fara ce irin tass ɗin irin farin da
ba'a fiye samun ƴaƴan hausawa dashi ba duk da kasancewarta jaririya hakan bai ɓoye asalin
kyawun fuskarta ba idanunta a rufe suke yayinda gashin idanun ya kasance ya sakko har ya zo
wajen kan gefen idanunta hannayenta a dunƙule suke kamar na kowace jaririya wacce take
sabuwar haihuwa danshin da taji a jikinta da kuma lura da tayi kamar bata numfashi ya sanya ta
yi saurin rungumeta kasancewar babu ko wando jikinta da sauri kuma ta kalli mijin nata a karo
farkon bayan haihuwar tata ta ce

"Ki kira sarkin ruwa yaya Gani"

Bai ce komai ba ya miƙe tsaye yana tafiya da ɗan sassarfa ya fice daga bukkar, sake
ƙanƙameta ta yi tana sauke ajiyar zuciya a hankali kuma wasu sabbin hawayen suka ziyarci
kuncinta saidai wannan karan na zallar farin ciki ne duk da har sannan batasan daga inda mijin
nata ya samo jaririya kuma ta tabbatar da cewa ba wacce ta haifa ba ce ba.

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da taji yarinya ta tsala ihu batasan
lokacin da hawaye suke fara fitowa daga cikin idanunta ba sosai tayi murna dunƙule
hannayenta ta yi wanda ke nuni da zallar farin cikin da take ciki miƙa masa yarinya Sarkin ruwa
ya yi sannan cikin sakin murya ya ce"ina maka fatan Alkhairi Ya Gani Allah ya yara maka ita"
tattausan murmushi ya yi sannan ya furta cikin kami'lalliyar muryarsa "Ameen ya rabbil
alameen" fita Sarkin ruwa ya yi ita kuma ta ƙaraso da sauri tana duban kyakkyawar jaririya ta
ce"Ya Gani ki bani shi" sai a sannan nagane ba bahaushiya ba ce domin asalin muryata ta
Fulani ta bayyana cikin kalaminta koda yake daman da zarar kayi ido biyu da ita fuskarta taza
shaida baka hakan kasancewarta kyakkyawar bafulatana sanye take da wasu kayan Fulani irin
blue colour ɗin nan sai murjani wanda ta rataya a wuyanta, murmushi ya yi kawai sannan ya
miƙa mata ita da sauri ta rungumeta a ƙirjinta tamkar wani ya ce zai kwace ta cikin kurɓattaciyar
hausarta ta ce" wacece shi?, ko ɗiyata ne ya tashi?" gyara zamansa ya yi kan tabarmar kabar
sannan ya kalleta a nutse kuma ya furta "*BA ITA BA CE ba!!*" sake kallon fuskarta ta yi ganin
yanda take barcinta yasa ta kalleshi da ƴar damuwa a fuskarta ta ce" to waye shi?, kuma ina ka
same shi?" Numfasawa ya yi sannan ya kama hannunta cikin sanyin murya ya labarta mata duk
abinda ya faru, ya ce"saboda haka na yanke shawarar zamu kula da ita daga nan har ƙarshen
rayuwarmu zamu riƙeta matsayin ɗiyarmu wacce ta mutu, tabbas na tabbata akwai wani
ɓoyayyen al'amari a tareda wannan yarinyar wanda lokaci ne kawai zai tabbatar mana da
hakan" yanayin yanda yake magana zaka gane cewa ba yare ɗaya suke dashi ba domin shi
yana magana ne irin yanda mutanen garin ke magana musamman ma Kanuri wanda hakan ya
tabbatar da cewa shi ɗin ya kasance Kanuri ne. Cikin sanyin murya itama ta ce" karki damu Ya
Gani zan kula da ita kamar ɗiyata dana rasa nima naji ina sonshi sosai kuma ma yana kama

dani kin gani" murmushi ya yi ganin da gaske nuna masa take ya gani jaririyar na kama da ita
ya girgiza kansa sannan ya miƙe ya fice daga bukkar yayinda ita kuma ta ɗago fuskar yarinyar
tana kallonta kallon da yake nuna irin ƙaunar da take mata ita kaɗai kuma take sakin wani
yalwataccen murmushi haka har bacci ɓarawo ya saceta.
*BA ITA BA CE...*

*#Human trafficking*
*#heart touching*
*#destiny*
*#Loyalty*
*#pity*

# *SQUAD 2024*.

*Comments nd like*.
[7/31, 3:29 PM] Nanameera✌: *BA ITA BA CE!...*

*MIKIYA WRITERS ASSO...*

*Follow my account both arewabooks nd Wattpad*

*nanameera 08* _arewabooks_
*@Nanameera08* _wattpad_.

*Nanameera*



# *SQUAD 2024*.


```Page 02```

*Rugar Jama'are*

Durƙushe take gabansa ta zuba masa idanu tana kallonsa ƙaramar yarinya ce ba zata shige 4
to 5yrs ba tana sanye da kayan Fulani Blue colour as usual gashinta dake zube a gefenta
wanda aka kalbaceshi irin manyan kalbar nan guda biyu yabi da kallon a hankali kuma ya sake
lumshe idanunsa shi kaɗai yasan irin tsananin azabar da yake ji, kamar zatayi kuka take kallon
mahaifin nata cikin wata siririyar murya mai Matuƙar zaƙi da ɗaukan hankali take cewa"Papina
sannu zaka samu sauƙi kaji sannu dan Allah" bata rufe bakinta ba aka ɗaga labulen wanda ya
kasance asabari ne suka shigo da sauri kuma cikin ɗaga murya Dada ta ce"Baba kura zo ki

dubashi aradu mun higa uku ya Gani sannu Allah zai tashi kafaɗunki" da sauri wanda take cewa
Baba kuran ya ƙaraso yana zuwa ya zube a gabansa hannunsa ya kai ya taɓa wuyansa sosai
yaji zafi a jikinsa hakan yasa duk hankalinsa ya ƙara tashi a matuƙar razane kuma ya miƙe ya
fice daga cikin bukkar, da kallo suka bisa kafin Dada ta kalleta da idanunta wanda suka sauya
launi ta ce"kai Muhaira ɗebo ruwa a bashi yasha" da sauri ƴar ƙaramar yarinya ta miƙe ta ɗauki
ɗan ƙaramin jallan ruwan tayi waje saidai kafin ta fita ta juya a hankali tana kallon fuskarsa ga
mamakinta sai taga shima ita yake kallo wani tattausan murmushi ya yi mata dukda yanda
bakinsa yake a bushe wanda ke nuni da asalin ciwon da yake ciki a hankali itama ta mayar
masa da nata kyakkyawan murmushi ya ilahy wani irin sihirtaccen kyau ƴar yarinya ta yi tamkar
wata ƴar aljanu haka ubangiji ya yi mata kyau kwayar idonta blue colour ce irin mai hasken nan
sai wani irin sheƙi suke saɓanin na sauran mutane da suka kasance baƙaƙe. Da hannunsa ya yi
mata alama da tazo hakan yasa ta ajiye jallan ta ƙara sa gabansa ɗan ƙaramin hannunta ya
kama a hankali kuma ya buɗe bakinsa wanda yawo yake shirin ƙafewa daga cikinsa ya
ce"Baddon Papi!" da sauri ta ɗaga kanta tana kallonsa wasu zafafan hawayene suka shiga
gangarowa kan kuncinsa da sauri ta saka ɗaya hannun nata tana goge masa kwaɓe fuska ta yi
cikeda shagwaɓa ta ce"Papi kadaina kuka kaji dan Allahhhh" shafa fuskarta ya yi hannunsa na
kakkarwa ya gyaɗa mata kai dan bakinsa ya yi masa nauyi, Bani kura ne ya shigo bukkar shida
wani mutum a bayansa da alama kuma mai magani ne. Bayan sun zauna ya kalli Papi sai kuma
ya kalli Muhaira dake gefensa ya ce"Baddo maza jeki gidana ki karɓon ƙwarya" miƙewa
Muhaira tayi ta fice tana tafiya da a sauri a hankali kuma take waiwayen bukkar tasu.

Tafiya kawai take da sauri da sauri dan ko wasa bata tsaya ba haka har ta baro rugar tasu,
kasancewar su a cikin gari suke ya sanya ta ɗan yi tafiya mai yawa kafin ta ƙaraso ƙofar gidan,
"Wundo!! Wundo!! Wundo!!" turo baki Muhaira ta yi bata ce komai ba har sannan, da sauri
ya'acca ta kalleta cikin ɓacin rai ta ce"ke kam Muhaira bakida mutunci ko?, banda iskanci ki
shigowa mutane gida babu sallama sannan kuma ji ana waye kinyi tsif abinki ko?" sosai
yarinyar ta tsorata da tsawar da tayi mata bakinta na rawa ta ce"unn...uhhhmm...dan...daman
Bani kura ne ya ce a bashi ƙwarya" tsaki ya'acca ta yi ta ce"shine zaki tsaya kina mana
shashanci" sunkuyar da kanta ta yi bata ce komai ba amma duk a tsorace take, shiga ɗaki ta yi
ta ɗauko ƙwaryar ta mika mata, da sauri Muhaira ta karɓa sannan ta juya da gudu tayi waje,
tsaki ta yi tana kallonta ta ce"shashasha kawai".



Da sauri ta shigo cikin bukkar hannunta riƙe da ƙwaryar saidai me?, babu Bani kura wanda
ya aikata haka zalika babu mai maganin da aka ɗauko sai Dada wacce ke zaune gefensa
banda kuka babu abinda take yayinda Papi aka rufeshi da wani tsohon bargon, da sauri ta
ƙarasa wajensa tsugunawa tayi gaban Dada tana cewa"Dadana Papi ya yi bacci?" kallonta
Dada ta yi amma bata ce mata komai, sosai idanunta sukayi jajur ko ba'a faɗa maka ba kasan
ba ƙaramin kuka tasha ba, kuka ta fashe dashi tana murza idanunta da kallo kawai Dada ta bita
dan ita tama gagara magana ganin Dada bata kulata ba har sannan yasa ta kwanta a wajen
tana birgima, Bani kura ne ya shigo shida masu maza a bayansa suna zuwa kai tsaye inda Papi
ke shimfiɗe suka nufa ganin yanda take kuka yasa Bani kura ya ce"Aishatu ke dawa?" daga

yanayin muryarsa zaki fahimci irin damuwar da take tare dashi, da sauri Muhaira ta tashi jin ya
kira sunanta ta ƙarasa wajensa har Sannan kuma kuka take ta ce"Bani koba Dada bace" janta
ya yi jikinsa ya rashe mata hawayen fuskarta sannan ya ce "to kiyi haƙuri zauna anan" shiru tayi
ta zauna a gefensa tana kallon bargon da suka rufe Papi.

Ƙarasawa suka yi bayan sun yaye bargon suka kamashi suka fita daga cikin bukkar duk
wannan abun da ake banda kallo babu abinda Muhaira ke yi dan ita bata gane ba mene ne
abinda ya faru ba, Dada kuwa ƙara sautin kukanta ta yi jikinta na wani irin kyarma, tashi
Muhaira ta yi ta koma kusada ita ta zauna amma bata ce komai ba sai kallon mahaifiyar tata
take, ita kuwa Dada tunanin yadda rayuwarsu zaka kasance take, tunanin rayuwar Muhaira
take, zuciyarta cike take da tausayin tilon ƴar tata, tabbas ƙaddara ta riga fata domin Papi ya tafi
ya barsu a lokacin da suka fi bukatarsa. Tunawa da wannan yasa ta sake rushewa da wani irin
kuka mai tsuma zuciya ita kuwa Muhaira bata fahimtar komai ƙanƙantar shekarunta da kuma
ƙarancin shekarunta sune suka yi tasiri wajen gazawa kwakwalwarta ta fahimtar da ita duk a
tunaninta Papi ɗin wani waje zasu kaishi wanda zasu dawo mata dashi. Amma saidai abinda
bata sani ba shine Papinta ya tafi kenan tafiyarda duk wanda ya yi ta baya taɓa dawowa,tun
tana tambayar Dada ina Papinta har ta fahimci cewa Papinta ya bar duniyar a hankali mintuna
ke komawa awanni awanni ke komawa kwanaki kwanaki ke komawa sattituka sukuma suke
juyewa izuwa wattani wattani kuma ke juyewa izuwa shekaru, tafiya ta tafi a ƙalla Papi zai yi
shekaru uku da barinsa duniya zuwa wannan lokacin kuma Muhaira tanada shekaru 8 a duniya.


Wani irin sanyin ake mai ratsa ɓargon da jijiya sanyinne irin wanda ke haddasa cuttukan
musamman Asthma, pneumonia, sickler dama wasu ciwukan, safiyar ranar juma'a ce gabaɗaya
rugar Jama'are tayi tsit kowa yana cikin bukkarsa da iyalansa, tsugunne take gaban wata
tukunya wacce aka ɗorata akan dutsuna guda uku wanda suka zama sune murhun da take
girkin akai sosai take haɗe jikinta yayinda numfashinta ke wani irin fuzga ita kaɗai tasan azabar
da take ji amma kuma burinta bai shige ta gama damawa Dada kokon ba. Cikin mintuna ƙadan
ta kammala ta juyeshi cikin wani tsohon kofi sannan ta tashi da gudunt ta shige bukkar, tana
nan yanda ta barta a kwance idanunta a rufe suke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login