Showing 24001 words to 27000 words out of 65424 words
Chapter 9 - FINI A UBA IN FIKI A MIJI book Complete by Hanne Ado Abdullahi .pdf
da minti goma ba, sai ga Farida ta iso wajensu. Ita kam sun yi
gaisuwar mutunci don har ta yi introducing kanta a matsayin kanwar Zainab. Ya dan ji dadin
ganin yadda ta mutunta ta. Amma shi ma abin takaice ta kalleshi tace “sorry to intrupt you.
Amma Momi tace kizo ki kwashe plates a dining ki gyara kitchen”. Tana fadar haka tayi masa sallama ta koma ciki. Daga ido tayi tana kallonsa, kafin ma tace
komai yace “kar ki damu Putri jeki zan kira ki anjima”.
Tayi masa sallama ta dauki jug dinta ta shiga gida. Tana bada baya, AlBashir yace “mallam
haka Zainab take fama da ku a gidan nan”?
“Ai kuwa haka take fama kullum”, ya amsa masa. Sallama suka yi ya karasa bakin mashin din
Sule ya dauko leda mai dan girma ya mikawa Mallam yace “don Allah mallam kar ki karba. Kayi
hakuri”.
Sai bayan ya tafi Mallam ya bude yaga kykkyawan yadi mai laushin gaske da kuma turmin
atamfa duk da bai san kudin su ba, amma tabbas ya san masu dan tsauri ne.
[8/6, 23:25] +234 814 948 5104: FINI A UBA I
N FIKI A MIJI
PAGE 19
BY HANNE ADO ABDULLAHI
kusan tun da suka rabu da Al Bashir cikin tunanin sa take. Da ta tuna wata Magana da suka yi
shi da ita sai ta saki murmushi kamar wata sakarya. Ita Kanta bata san sanda murmushin yake
kwace mata ba.
Baba Laure na hankalce da ita, har ta kasa daurewa tace “uwata yau wane irin nishadi kike ciki
ne. ni dai ina ga Balaraben nan ne sanadin wan nan farinciki naki”.
Kunya taji matuka na yadda ta bari har baba Laure ta gano yanayin shaukin da ta ke ciki. Ba ta
dai amasa mata ba. Amma fa duk da haka yanayin fuskarta bai canza ba.
Yau bata da aikin snacks, amma Momi ta sanar da ita da safe da waina da ganda zasu karya a
gidan. Kuma ta tabbatar sun dahu kafin bakwai da rabi na safe. Ganin ba pressure pot garesu
ba, ya sanya ta hada gawayi a makubur din su, ta hada gandar ta dora ta barta tana dahuwa a
hankali. Niyyarta data gama hada kullin masa, sai ta kwanta. In yaso ta samu bacci ko na awa hudu,
san nan ta tashi tayi kokarin yin nafilar da ta saba, sai ta hau danin wainar.
Kirrrrr karar waya ta katse mata tunani. Tsayawa tayi tana kallon fuskar wayar kamar fuskar mai
kiran zata gani a ciki. Sai da tayi ringing uku san nan ta sa hannu ta latsa kiran.
Sansanyar muryarta ce ta doki kunnensa wanda ta aika masa sallama da ita.
Shima cikin shauki ya amsa mata. San nan cike da zolaya yace “ina fatan yau tunani nane ya
hana ki bacci”.
“idan yin hakan laifi ne ayi min afuwa, zan daina”.
“haba putri salju. Abin da nake addu’a ya kasance sai kuma ince an yi min laifi. Ai fatana in
shiga zuciyarki in yi kane kane, yadda ba wanda zai samu shiga, wanda yake cike kuma in
hankido shi waje ya fada kwata”.
Dariya kawai tayi san nan tace “kar ka wahalar da kanka. Barka da dare”.
“barka kadai putri salju”.
“sai dai ka san ban san ma’anar sunan da kake kira na da shi ba. Kar ko ce min kake zainab
mai katon baki”.
“Akwai madubi a tare da ke”?
“a’a me kake so ayi da shi”?
“So nake kije ki tsaya ki karewa kanki kallo. Ki gaya min meye bashi da kyau a fuskarki, kama
daga goshinki mai kyalli kamar watan dan dare sha hudu. Wanda ya fito da kyawawan dara
dara kuma fararen idanunwanki. Su kuma suka hadu suka kara fitar da kyakkyawa siririn hanci ,
wanda da ya taso bai tsaya a ko ina ba sai da ya iso inda kyakkyawa bakin ki mai dauke da
siraran labba, wanda cikin sa yake cike da kanana, hakora farare tas da su. Af nayi mantuwa
akwai wata siririyar wushirya da ta dada kawata su. Kamar yadda fuskarki ta kawatu da
dimples.
So ki duba a madubi kiga ina na kuskere ban fasalta ba. Ko kuma ina kike jin na fadi da daidai
ba”.
Murmushi kawai tayi ta kasa bashi amsa. Sai shine ya sake cewa putri salju yana nufin
coolprincess, kuma wani yare ne na wani gari dana taba zaman ci rani”.
Bata gane me cool proncess din ke nufi ba, amma dai ta daure bata nuna masa ba. Ya sake ci
gaba da tambayarta. “mu dawo maganar dazu, me kike yi baki yi barci ba”?
“waina nake kokarin hadawa. Ko zaka ci”?
“idan an bani mai zai hana. Ko yanzu sai in biyo in karaba”.
Sai da ta sake dariya mai cike da nishadi san nan tace “a’a ba zaka samu yanzu ba, sai dai da
safe idan zaka iya zuwa”.
“wanda yace zai zo da tsakar dare ta ina kika ga safiya zata wahalar da shi? Karfe nawa ki ke
son in zo in karba”?
“Idan zaka iya zuwa takwas zuwa tara zaka same ni. Idan ka wuce haka kuwa zaka daki gurbi”.
“in sha Allahu kuwa zan zo. Ke dai tanadar min waina ta. Yau ba kya jin labarai ne, ko dai hira
dani tafi labaran dadi”?
“kai yaya b………” bata san yadda akayi ba taji ta kasa kiran sunansa. Nan dai hira ta barke a
tsakaninsu, duk da shi ke fiye da rabin zancen. Amma ga mamakin ita kanta zainab din kusan
shine bakon mutum na farko da ta ji tana iya sakewa da shi har tayi musayar Magana da shi
din. Washe gari kuwa zainab tayi abin da bata taba yi ba. Tana sauke naman nan ta debi parts masu
kyau guda hudu, ta samu dan karamin flask ta zuba a ciki. Kafin takwas da rabi ta gama gyara
ko’ina.
Al Bashir na ganin motar Momi data dadi sun fita daga gidan, ya karasa ya shiga ciki. Kamar ko
yaushe mallam ne yayi sallama da ita. Sanye cikin shudin uniform wando da riga da kuma
cream colour hijabi na yadin makarantarsu ta fito. Hannunta dauke da flasai guda biyu.
Bayan sun gaisa ta gabatar masa da wainar da tayi masa alkawari. Lomar farko da ya kai
bakinsa sai da ya lumshe idanuwansa saboda dadin abincin nan. Bai taba cin waina mai laushin
ta ba, haka zalika shima dahuwar jelar san tayi dadi matuka. Ga kamshin kayan kanshi yana
tashi wanda daka bude kwanon shi zai maka sallama. A wajen Mama Hajjo ta koyi dabarar sa spices sau biyu a girki. Ta zuba kadan domin fitar da
karnin daga farko san nan idan girkin ya dauko dahuwa ta kara kadan saboda ya fitar da
kamshi. Haka zalika bata daka spices ta ajiye. San da zata yi girki san nan take daka su,
saboda sun fi kamshi a haka. Yana ci suna hira yake tambayarta wacce makaranta take zuwa.
“umar bin Khattab, ta’alimul Qur’an” ta amsa masa.
“iyeh ashe mutuniyar tawa ya sayyada ce. Yanzu izunku nawa”?
“mun yi sauka da biye shekara uku da suka wuce. Yanzu kuma saura mana bai fi izu goma ma
mu gama da hadda ba. Wanda muna san ran nan da wata uku zamu hattama, saboda kasa ne.
kuma tun lokacin muna biye mun samu haddar sama da izu talatin ku san yanzu maimaitawa
ake”. “ma sha Allah. Ni kawai kice in sayo allo ga malama har gida. Ba bulala ba kudin laraba”.
Dariya kawai tayi bata bashi amsa ba. Sai da ya gama cin abincinsa wanda ya cinye tas duk da
yawan sa, san nan yace “thank you putri salju for a wonderful meal. Na san abin da naci will
carry me for most of the day”.
Tana jin yana tsaro turanci taga ya kamata ta sanar da shi cewa ita ba ‘yar boko bace, saboda
kar yazo ko mai jin turanci yake so ita kuma ta yaudare shi.
Sai da ta dan saci kallonsa san nan cikin sanyin murya tace masa “kayi hakuri ni bana jin
turanci”?
Shima cikin sanyin murya yace “Me yasa ba kya jin turanci”?
“Saboda bani da kokari aka cire ni a makarntar boko daga primary na tsaya. Sai aka mayar da
ni islamiyya”.
“shekararki nawa Zainab”?
“ashirin’ ta amsa masa a sanyaye.
“kar ki sake cewa kanki baki da kokari. Haddar Qur’ani tafi ko wane karatu wahala. Duk kuwa
wanda ya same ta, to ba wani karatu da zai gagare shi a duniya. Turanci kuma ba lalle ne kowa
sai ya iya shi ba. Idan kikaje kasashe da yawa musamman yankin Asia da Europe duk da
yaransu suke karatu da gudanar da harkokinsu na yau da kullum. A nan kasar ne kawai idan baka iya turanci ba mutane suke ganin ka koma bayan al’umma”.
“ai kuwa ba dadi kowa ya iya abu ya zamana kai kadai ne baka iya ba”.
“fine and good. In dai turanci ne mastalarki ni kuwa nayi miki alkawarin koyar da ke”.
Take kuwa fuskarta ta kasa boye farin cikin da take ciki. Sai da ta shiga ta mayar da kwanukan
da ya ci abinci san nan ta fito dauke da school bag dinta. Tare suka fita, shi yana tura mashin
dinsa ita kuma tana gefensa suna tafe suna hira. A nan ya samu ya sanar da ita asalinsa da na
iyayensa da kuma labarin yayyensa da family dinsu. Duk da dai ya rufe mata level of affluence
dinsu, da kuma shi matakin karatun sa.
Ya nuna mata shima iyakarsa secondry school daga nan ya shiga kasuwa. Tsoron kar ya
kwafsa ya saka shi bai bata detail story na kasuwar ta sa ba.
Sun fi minti arbain suna tafiya, kafin suka iso makarantar tasu . tabbas ya jinjina mata nisan
makarantar da gidansu, amma ya lura yaga ita ko a jikinta hakan ke nuna ta saba da nisan.
A bakin kofar makaranta ya sa hannunsa a aljihu ya dakko wrapper daya ta dubu goma sababbi
ya mika mata. Bata amsa ba tsayawa kawai ta yi tana yi kallonsa.
“Don Allah kar kice min bazaki karba”.
“don Allah kar kace sai na karba. Kudin sun yi yawa”.
“ba abin da yake da yawan da zan kasa baki shi. Kuma trust me kasuwar tamu yanzu akwai
alkhairi. Please ki karba ko kudin break kya yi da su”.
“Duk da haka mu bi komai a sannu. Kar mu durkusar da kanmu”.
Yana kokarin yi mata magiya ta karbi kudin daga hannunsa ta zari guda biyar daga wrapper ta
bude aljihusa na gabar rigarsa ta zura sauran a ciki. Yana kokarin yin Magana, tace “Please
nima na roke ka mu bar maganar haka.in dai kyautar ce wan nan ta ishe ni. Shima dan kar kace
naki karba ne”. Tana yi masa sallama ta shige gate din makarantarsu. Ta bar shi yana kallonta cikin tsan tsan
tausayi. Yarinyar is so humble yet classy. Ita bata san da kyar ya daure ya bata dubu goman da
ya dauko ba, saboda ko driversa ya kan bashi haka a kyauta kawai,balle ita da yake jin zai iya
mallaka mata duk abin daya mallaka a rayuwarsa, [8/6, 23:26] +234 814 948 5104: FINI A UBA
IN FIKI A MIJI
PAGE 20
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Kusan kullum sai AlBashir ya kaiwa Zainab ziyara da safe kafin yaje office.
Wahalar mashin dai yana fama da ita, amma sam ko ajikinsa. Idan Mujib yayi masa tsiya sai
yace masa “muna bata lokaci ne kawai zuwa gym, but this is a better exrcise”.
Shi dai Mujib tun zuwan su na farko sau daya ya kara rakiyar zance, saboda ya koma
portharcourt in da yake aiki a kamfanin SHELL. Shi kuwa kullum sai ya kai ziyara gidansu
saboda haka fahimtar juna na dada wanzuwa a tsakaninsu.
Ya kuma fi son zuwa wajenta da safen saboda ya lura ba a interrupting dinsu sabanin zuwan
yamma da kuma na dare, da bata minti biyar a tare da shi wani bai zo yakirata ba. Haka suke
hirar a tsintsinke, har dai ya hakura ya tafi.
Amma yau da yazo da safe lokacin da ya saba sai ya ganta tare da su Momi da duk sauran
yaran gidan ana ta loda kaya a mota. Guri daya ya samu ya labe ya kuma yi sa’a ba wanda ya
lura da shi.
Tas suka loda kaya cike da but, mota biyu. Daddy da Momi a daya, yayin da yaran gidan suka
shiga Venza. Gaba daya suka tafi. Shi har ya tsorata ya dauka ko tafiya suka yi zuwa wani gari,
Zainab bata shaida masa ba. Amma Mallam na kokarin kulle gate sai ya hango ta cikin uniform
dinta. Wani irin farin ciki yaji ya lullube shi. Domin kuwa ya san da tayi tafiya, zai yi kewarta ba kadan
ba. Tana kokarin shiga gida sai muryarsa suna gaisawa da mallam ta tsai da ita. Shi ma kuwa
da hanzari ya karaso in da take, ya bar mallam na kokarin kullo gate din.
“ai yau hawan jini ya kusa kamani”.
“don Allah yayi hakuri kar ya kamaka, ko don ya tausawa min”.
“Ashe har kina tsorona da ciwo, amma ni ban kai ga gane hakan ba. Kin barni sai rara gefe na
ke yi”.
“Hm kai baka da dama”. Ta durkusa sosai tare da fadin “barka da safiya”.
Ba karamin nishadi yake ji idan tayi masa irin wan nan gaisuwar ba. Sai yaji shi kamar wani
basarake. “Barka kadai” shi ma ya amsa mata. Ya karasa ya zauna a wajen da ya saba zama.
Itama ta karaso ta zauna a gefensa.
“Mu dawo maganar dazu. Ki na tsorona da hawan jini, amma ba kya kareni daga shi”.
“Gaya min abin da zan maka in hana hawan jinin kamaka”.
Sai da ya dan nisa san nan yace “Idan na fada kin yi alkawarin yi min abin da nake so”.
“In har bai fi karfi na ba, nayi maka alkawarin yi maka duk abin da ka ke so”
“Ki kwalli cikin idona kice min I love you my sweet heart.yin haka zai saka ni inji sanyi a cikin
raina. In kuma daina kokwanton matsayi na a zuciyarki”.
Kasa tayi da idonta san nan cikin sanyin murya tace “ba kullum baki kan furta asalin abin da ke
cikin zuciya ba, amma idan mutum ya lura halayyar dan Adam kan iya yi masa nuni da abin da
ke cikin zuciyar”.
Sai da ya dan yi tafi san nan yace “yarinyar nan ashe wayo gareta ban sani ba. Amma hakan
ma ya gamsar da ni. Tun da kullum cikin kykkyawan yanayi na ke ganin ki. To amma ina mutan
gidanku suka tafi dukkansu kika yi saura sai ke kadai, ko da sauran mutane a gidan”?
“Su farida ne zasu koma makaranta shine duk suka yi musu rakiya”.
“A wane gari suke karatun”?
“A sudan”.
Cike da mamaki yace “Sudan? To ke me ya hanaki tafiya Sudan din”?
Fuskarta ta dan nuna damuwa, san nan tace “Tun farko na sanar da kai bani da kokarin boko.
Kaga Farida Medicine take yi. Farisa kuma computer”.
Cike da haushi yace “and they left you to be their maid”.
Ta dago ta kalle shi san nan tayi murmushi tace “ina ga kana mantawa na gaya maka ban iya
turanci ba”.
“aikuwa in sha Allahu zaki koye shi. Yaushe zasu dawo”?
Ta daga kanta alamar tunani. Ta tuno da lissafin da Momi tayi mata, in da ta bata dubu goma a
kan ta dinga sayen abinci a ciki. Amma fa ta hada da gargadin idan anyi ciniki kar ta taba mata
ko kwabo, ta kuma lissafa mata yadda tafiyarsu zata kasance, san nan tace “eh to watakila suyi
wata biyu, saboda sunce idan sun je Sudan suka gama ko ragisrarashin, sai su wuce Saudiyya
suyi ummara. Daga nan kuma su kaiwa anti Bilki ziyaraa can kasar sin”.
“yanzu ke da waye a gidan”.
“daga ni sai Baba laure ko da yake ita tana wajenta a baskwata”.
Sai da ya daga kai ya kalli girman gidan san nan yace “kuma ke ba kya tsoron kwana ke kadai a
cikin gidan nan”?
Ta dan yi murmushi san nan tace “ni bana wani jin tsoro.kuma ma na saba suyi tafiya su barni ni
kadai”.
Take yaji ransa ya baci. Tabbas matar nan is wicked, ba abin da ya dameta da safety ko
tarbiyyar yarinyar nan. Amma ya danne bacin ransa yace “me ye ragisrarashin”.
Abin da dalibai suke yi idan zasu koma sabon zangon karatu”.
“OK you mean registration”.
“Eh shi”.
“ok repeat after me re-gis-tra-tion”
Sai da ta maimaita wajen sau uku kafin ta samu ta fade shi daidai.
Sai da yaga ta samo wan nan yace “to daga yau idan nazo zamu yi English lesson na atleast
one hour”.
Ta gyada kanta alamar ta gane. Amma duk da haka sai da ya saka ta ta fahimci ma’anar
kowacce kalma da ya fada.
Ganin gidan bakowa sai suka samu sake. Washegari da zai zo ya taho mata da wayar
TECHNO irin ‘yar dubu hamsin din nan. Da yake ba sanin darajar waya tayi ba, bata fahimci
mai tsada bace. Haka zalika ya jibgo mata tarin litattafan koyon turanci da kuma spelling.
Kullum kuwa yazo haka zai kashe lokaci yana koyar da ita turanci. Bayan nan ya dauki sarar
yawaita Magana da turancin a tsakaninsu, kuma zai bata lokaci ya bata dama tayi ta canka har
sai ta gano ma;anar abin da yake nufi.
Haka zalika yana yawaita encouraging dinta data yi simple sentences da turancin. San nan ya
bata lokaci wajen koya mata amfani da wayarta ta yadda zata shiga dictionary ko kuma google
ta gano ma’anar kalmomi da kanta.
Haka nan kullum idan yazo zai sakata, ta koyi spelling at least 10 new words da kuma meaning
dinsu. Ba shi ba ni kaina na yaba da kokarin Zainab. Saboda dai simple sentences ta iya
constructing din su da kyau. Haka nan ta na fahimtar zancen da ya kan yi mata da turancin.
Haka kuma dan chatting din da ya koya mata suke yi lokuta masu yawa shi ma ya taimka mata
wajen fahimtar yaren turancin. Abin ya so bani