Showing 51001 words to 54000 words out of 65424 words

Chapter 18 - FINI A UBA IN FIKI A MIJI book Complete by Hanne Ado Abdullahi .pdf

da kuma son zumunci haka suka ciko
bus biyu manya. Daya cike da mata sama da goma daya kuma maza.

Babu kuma wanda ya san da zuwansu. Duk iya kokarin mutum ba zai iya wadata mutum sama
da ashirin da abincin da bai san da zuwansu ba. Ita dai tana ganinsu ta zare jikinta ta koma
gida. Industrial kitchen dinta ta shiga. Allah yasa tana da ajiyayyun snacks wanda tayi wa yaya
A’I ba ta zo ta dauka ba. Shi aka fara soyawa aka gabarta musu da ruwan lemon kanakana. Ko ba komai ta san zai iya
rike su kafin dai awa daya ta gama abinci. Kafin awar nan kuwa ta cika, ita da masu aikinta
guda biyu sun sauke tuwon shinkafa da miyar danyar kubewa wacce ta sha naman rago.
Gefe guda kuma ga ferfesun kayan ciki da aka hada da shi. Ba su gama ba sai gata ta shigo da
katon tray dauke da yankakkun kayan itatuwa. Nan ta zauna aka fara gaisawa. Caraf kuwa
facalar Umman matar wan Abbansu ke nan mai suna baba kulu ta ce “hm sannu isasshiyya sai
yanzu kika ga damar zuwa gai da mutane”? To dama kowa ya san ta da neman Magana da kuma sa ido. Umman ma sai da suka kwashi
adashin tsiya taga ba abin da zata dauka a wajenta san nan ta samu lafiya.
Ita dai ba tayi magana ba ta sunkuyar da kanta kawai. Bata hakura ba ta sake cewa da umman
“dama haka surukar taki bata san darajar mutane ba aka ishe mu da matar auta mai hankali.
Ina hanakalin yake iyayen mijinki suzo sama da awa biyu amma ki kasa shiga ki gaishe su”.
Ta sake juyawa ta kalli Zainab ta ci gaba da cewa “ki bar ganin daga kauye muka zo, mune dai
asalinsa”. Ita Zainab tun da tazo gidan ba wanda ya taba yi mata ko da kallon banza balle a kai
ga fada. Rabonta da jin fada tun a gidan momi, sai kuma yau da wan nan azababbiyar baba
Kulun ta dasa nata. Umman Al Bashir na kai kallonta wajen Zainab taga yadda take share hawaye. Mikewa tayi
daga inda take zaune ta karasa wajenta. Ba ta ji kunyar kowa ba ta jawo ta jikinta tana goge
mata hawaye tana fadin “yi shiru matar auta. Kar ki bari wani abu ya bata ranki har dan uwana
ya shigo ya tarar da ke a yanayi na bacin rai. Kin san ko yaya ranki ya baci shi ma kasa sukuni
yake”.
San nan ta maida hankalinta wajen baba kulun tace “kin san mutane kowa da irin tunaninsa. To
ita Zainab nata tunanai na in taga baki sun iso ta yi iya iyawarta ta wadata su da abin da su ci
su sha, kafin ta zauna luguden lebe. Ai kema dan kin koshi ne da kabakin data kawo miki shi
yasa har kika samu damar aibata ta”. “au Allah akan matar danki kike nema ki gayan min bakar Magana. In dai surukan zamani ne
gaki ga su. Idan kin dawo kina kukan an janye miki da ke kika jawo wa kanki. Ko da yake naki
ma sunan sa janyayye kamar yadda kika janye dan wata dole kema sai an janye naki”.
Dariya Umman tayi saboda ta gane abin da take son fada Kenan. Ta ce “ai ni kowa a dangi ya
shaida tsakanin na da surukuta mutuntuwa ce da kyautatawa. Kuma yadda ta rike ni haka kuwa
zan rike wacce aka kawo min”.
“aikin banza kamar ba mu san komai ba. Ba asiri kikayi musu ba ita da dan nata suke fifita ki
sama da kowa”.
“kash yaya Kulu kin sha fadar maganar nan na kuma ce ki shirya in raka ki wajen malamin da
yayi min aiki a akansu ko kema kya samu yayi miki”.
Wata ce a cikin matan dake zaune a wajen tace “Don Allah Hajiya kyaleta. Shi zaman duniya ai
kowa da halinsa yake yinsa. A danbatta gaya min gidan da bakiyi fada da su ba. shi yayanmu ai
don mai hakuri ne da kuma Dadan data hana shi sakinki shi yasa kike ganin kamar kin fi karfin
kowa. Kin fi so yadda kike sa in sa da naki surukan itama ta dinga yi da tata”.

Ita dai Zainab jiki a sanyaye ta miki daga wajen ta koma sama wajen Meena.Wan nan kuma
shine abu na farko da ya taba mata rai a gidan mijinta daga shi kuma bata sake haduwa da
wani ba. Yadda suke son Al Bashir kusan itama haka suke nuna mata.
Amma fa gidan Dr Abdullahi Zubair ba haka abin yake ba. Saboda dai dadi ya gaji da kazantar
da kuma kwaben abinci da ake yi a gidansa. Ashe itama Momin ko ta manta ne ko kuma dama
can girkin da sauki oho. Amma ko ita da kanta tayi abinci ba dadi yake yi ba.
Baki kuwa ya daina gayyato su, saboda idan ya kawo su kunya yake ji. Gida kaca kaca ba
gyara. Ransa bai kara baci ba, sai ranar da ya fito daga masallaci suna gaisawa da malamin
islamiyyar su Zainab, yake masa godiyar abin arzikin da mijin Zainab ya aika masa. Shima yana
murna ya ke ce masa “ai mallam zainab kam abin na ta akwai albarka a ciki. Kaga dai da uwar
ta so taki auren saboda wata jita jita da taji amma yanzu ga shi nan Alhamdu Lillah komai nata
yana tafiya daidai”.
Shi ma yasayyadin ya dora da fadin “biyayyar Zainab da kuma kwazonta ba zai tashi a banza
ba”.
“kayya mallam Auwwalu. Allah dai ya shiga cikin lamarin. Amma Zainab ai na sha wuya da ita a
gidan nan. Kullum sai an kawo min kararta, ga kuma dakikanci da ta dorawa kanta. Ba yadda
ban yi da ita ba tayi karatu amma sam yarinyar nan taki”.
Da mamaki yasayyadi yace “ita Zainab din”?
“Ita kuwa wallahi. Sam bata son karatu ba kuma ta son taimakawa a gidan. Kullum tana dakin a
kwance”.
Mallam Awwalun ne yace
“ai mu kuma abin mamaki kusan tun kafuwar makarantar nan ba mu taba samun daliba mai
kwazo da hazaka da kuma ladabin ta ba”.
“Ahaf a makaranta take muku haka. Amam mu a gida ai wahalar ta muke sha. Kullum a cikin
fada take da uwar goyonta. Ga bakin cikin kannenta da take yi. Allah dai ya sa ta samu mijin
kwarai”
Yasayyadi ya dan yi tsai san nan yace “Alhaji kayi hakuri da wata Magana da zan sanar da kai.
Ka san kannena dukkansu biyu kawayen ta ne. haka zalika mahaifiyata tana shiga wajen hajiya.
Amma labarin da ke fitowa daga gidan ka akan zainab ba mai dadin ji bane. Ka san su
al’amarin mata akwai daure kai a ciki. Amma zan sanar da kai abin da na lura baka sani ba. Kaf aikin gidan ka har ma da sana’ar matarka Zainab ce mai yin su. Makaranta kuma ba kokari
ne bata da shi ba. Amma hajiya da kanta, ta rantse sai ta lalata rayuwar Zainab saboda bakin
cikin mahaifiyar ta da ta ke yi.
Zainab na iya diban kawan uku na kowanne sati bata samu zuwa makaranta ba. Ko tana
hidimar gidan ka ko kuma ta kannen matarka, wacce har gidajen su ake turata taje tayi musu
boyi boyi.
Ba aje makaranta ba ta yaya za a samu karatu ya tsaya. Ai rufar ka akayi. Abin da take yi wa
Zainab shi ya hada su da mahaifiyata saboda tayi mata nasiha. Zani wan nan sai dai idan
sauran ‘ya’yanka sun ga dama sun bata kwancen nasu. Shin ko ka san a gidan ka Alhaji,
Zainab bata taba kwanciya a kan katifa ba. A kasa take kwana. Zainab ai ta sha wahala. Kuma ni Wallahi da na san bada sanin ka abubuwan nan suke faruwa
ba da na yi karambani sanar da kai, saboda zagi dai kam ka sha shi a unguwar nan a kan
Zainab”.

Dr in ban da zufa ba abin da yake sharewa daga fuskarsa saboda bacin rai. Sai yanzu ya gano
dalilin da ya sa tun da Zainab ta bar gidan komai ya daina tafiya daidai. Ashe dama ita ke
aiwatar da komai. Shi yasa momi ta fito da dabarar yin kyauta idan kaci jarrabawa kawai,
saboda ta san ta toshe duk wata hanya da zata sa Zainab ta samu wan nan kyautar. Yasayyadi ne ya katse masa tunanin da fadin “kayi hakuri Alhaji na san azarbabi na ya zarce
misali. Amma a musulunci an fi son idan kaga dan uwanka na aikata kuskure to ka yi kokarin
sanar da shi ya gyara, ba ka tafi kana gulmar sa ba. Ni ma kuma nayi ta neman sanadin da zan
gaya maka naka kuskuren amma na rasa. Kasan yadda muke da hakki a kan ‘ya’yan mu haka
suma suna da hakkki a kanmu”.
“ba komai mallam Auwalu. Na gode da wan nan nasiha taka da kuma fahimtar dani da kuskure
na da kayi. Na gode kwarai da gaske”. Ya fada yana mai mika masa hannu domin suyi sallama.
A fusace ya shiga gidan sa nan kuma ya tarar da momi ta ci kwalliya za ta kamu. Dama kuma
ita aladarta tana tsananin son buki. Saboda dinner ko ta waye sai ka gan ta a garin kano. Akawi
randa ta kasa samun katin halartar wata dinner saboda jarabar son zuwa saboda ta hadu da
haddaun mata, satar katin tayi ta kai sabon gari aka buga mata irinsa. A falo suka yi kicibis da shi tana fadin “dama kai nake jira ka shigo sauri nake yi fita zan yi”.
“ba inda zaki je azzaluma macuciya mayaudariya”.
“dr ni kake zagi? Ko dai ka sha wani abu ne”?
“ba abin da na sha ido na ne ya bude daga nannauyan bacci da kika sakani. Ashe yarinyar nan
zaluntar ta kika dinga yi ban sani ba”.
“wai wacce yarinya kake magana akai ni ban ma gane me kake nufi ba”?
“maganar Zainabu nake yi. Ashe ke kika cuce ta kika hana ta makaranta ban sani ba. Ashe
baiwa kika mai da ita a gidan ubanta./ ashe kas kantar da ita kikayi a gaban ‘yan uwanta data
girma. Amma ba komai ai kinga yadda Allah ya mai da ita”.
“Oho sai yanzu na gano inda zamcen naka ya dosa. Kace dai yarinya ta auri mai kudi kaima
zaka shiga ayi da kai. Shi yasa kake ta wan nan rara gefen. Yo kuma in ban da abinka kwantar
da hanaklinka. Auren masu kudi ai yanzu aka fara shi a gidan nan. Farisa da zata auri dan
senator ashe ita goya ta a baya zaka yi saboda nuna kauna da kuma soyay…….” Bai san sanda ya wanke ta da wani zazzafan mari ba wanda tun da take ba a taba yi mata
irinsa ba.
“Dr ni ka mara”?
“An mare ki din idan kina da abin yi ki zo kiyi”.
Har zata ci gab da zazzaga masa masifa, take sai tunanin ya shigar mata na cewar duk yadda
akayi asirin karya tambaya data yi masa ya karye ke nan. Saboda malamin da yayi mata aikin
ya tabbatar mata ba zai taba tantamar abin da ta gaya masa ko yayi shakku akan duk abin data
fada. Tuna haka yasa tayi shiru kar zancen ya dada kwabe mata. Amma fa wata irin tsanar Zainab ce
ta dada shiga cikin ranta. Shi kuwa bai ma kula da yanayin da take ciki ba, ya fita da sauri ya
shiga motarsa. Har ya sanya ribas zai fita sai kuma ya fito ya tambayi mallam ko ya san gidan
Zainab. Ya dai kwatanta masa. Kuma da yake ma ba boyayye bane mai gidan bai sha wahalar samun
gidan ba. A baking gate suka yi kicibis da Al Bashir yana yiwa maigadi bayani wajen wacce
yazo. Da hanzarinsa ya karasa wajensa. Har kasa cike da girmamawa ya tsugunna ya gaishe

shi.
Shi da kansa ya wangale masa gate ya karaso ciki da motar sa. Tun daga harabar gidan ya san
cewa Allah yayiwa Zainab sakayyar kuntatawar da sukayi mata shi da matarsa. Da kyar ya
daurewa kwallar dake barazanar zubo masa.
Shi kuwa AlBashir kamar zai kwanta a kasa ya takashi saboda ladabin da ya ke a gabansa.
Babban falonsa ya shiga da shi. Shi da kansa kuma ya bude fridge ya dauko ruwa da wani lemo
na cucumber ya hada ya doro a jug. Ya kuma shiga kitchen da kansa ya debo danbun nama da
kyar ma ya gano shi sai da shamsiya mai aikinta ta nuna masa inda yake. Yana jiyewa ya tuna da wani dabinon ajwa da basa rabuwa da shi. Ya sake zabura ya dauko ya
dire masa. A gefen kafarsa ya zauna aka sake sabuwar gaisuwa. Sai sa masa alabarka ya ke yi
yana amshewa.
“dadi Bisimillah sha ruwa bari in kirawo zainab din”. Ya fada yana mai mikewa domin haurawa
sama.
‘yar hutu kuwa tana zaune ta tsala ado da wani dan Karen leshi mai laushi da kuma tsadar
gaske. Ita dai ta san sun yi sallama da shi akan zai fita sai kuma gashi ya shigo. Cak ya daga ta
daga kishingidar da tayi ya mikar da ita tsaye.
“Putri yau idan na baki wani albishir wanne goror zaki bani”?
“sai da ta dan sumbance shi san nan tace “kai da ka mallakeni kuma ai komai nawa naka ne,
sai dai in tayi maka salatin Annabi in yi tawassali da shi Allah ya yafe maka kura kuranka.
“Godiya nake Putri. Muje innuna miki albishir din”?
“Allah ya sa ba mota ka sake sayo min”?
“Wan nan yafi duka wani kyalkyalin duniya da kika sani daraja”.
Tare suka sauka saka. Hango Dadi da tayi ya sanya ta karasa sauka matattakalar benen da
sauri cike da ihun “dadiiiii”.
Sai dariya yake ya na fadin “yi a hankali Zainabu”.
Sufa tayi a gabansa ta tsugunna tare da damke hannayensa duk biyu a cikin nata.
“Dadi da gaske kaine”?
Shi ma cike da dariyar murna ya fara tsokanarta yana fadin “ke kuma haka akeyi, saiki gudu
sama ki bar mijinki da hidimar saukar baki”.
Shi ne yayi saurin cafewa lokacin da ya zauna a gefenta yana fadin “Dadi ba laifin ta bane. Ka
san akwai bakon da ya zarce saukar matar gida sai ta maigidan kansa”.
Dariya suka saka dukkansu. Sai lokacin Zainab ta samu sukunin gaishe da mahaifin nata amma
har a wan nan lokaci tana rike da hannunsa taki saki, kamar yace guduwa zai yi ya barta.
Al bashir ne ya mike tare da fadin “let me see if Umma is around”.
“da ka barta sai mu shiga”.
Bai bata amsa ba ya mike yace da Daddy yana zuwa. Yana fita ya mai da hankalinsa kan
Zainab. Muryarsa kamar zai yi kuka yace “ashe har turanci kina ji yanzu”.
“gaskiya Dady ba laifi. Although it is not that fluent amma dai i can converse effectively”.
Cike da murna yace “da kyau Zainab. Ga kuwa turancin nan radau”. Sai kuma ya dada
marairaice fuska, yace “zainab”. Ta dago ta kale shi ba tare da ta amsa ba saboda jin
seriousness din dake muryarshi. Tana sauraron kalaman da zasu fito daga bakinsa sai kawai
taji muryarsa tana cewa “Zainab rokon gafarar ki na zo nayi akan irin wulakantanciyyar rayuwar
da na barki ki ka yi a gidana. Ni da kaina na nakasa ki saboda haukan kishin mahaifiyarki da ya

rufe mini do, da kuma wan nan munafakar uwar taku da ta ringa ingiza ni ina zaluntarki”.
“Don Allah Daddi kar ka sake cewa in maka gafara. Bani da wata afuwa da zan maka illa kai ne
ma zan dawwama neman yafiyarka ko na kuskure maka”.
“sam Zainab baki taba bata min ba. Tun da nake dake ko musu baki taba yi dani ba komai
gaskiyarki. Nine dai na dinga take hakkuwanki da suka wajaba a kaina”.
“Don Allah Daddy kayi min afuwa ka daina maimaita Kalmar cuta da ka ke ganin kayi min. har
abada bani da wani mahaifi sama da kai. Abubuwan da suka gifta na kuskure sun wuce har
abada”.
“Kin san Allah ba da sanina na dinga yi miki abin da nayi ba. Wan nan uwar taku ita ta ringa
ingiza ni. Kuma na miki alakwarin sai na dau mummunan mataki akanta”.
“Don Allah Daddy itama kayi mata afuwa. Duk duniya bani da ‘yan uwa da suka wauce su
Farida. Tabbas kuma idan ka bata wa Momi zasu ji ba dadi. Ni kuma rashin jin nasu dadin zai
saka ni nima inji ba dadi. Saboda haka afuwa ga kowa ita ta kamance mu”.
“Madalla na gode da fahimtar ki Zainab. Makaranta kika koma ne ko yaya”?
“A’a dadi ya Al Bashir ne yake koya min a gida. Nan kuwa ta takakrkare tana bashi labarin irin
lesson din da take dauka a wajen maigidanta. Sun sake suna hira sai kawai jin sallama suka yi
Al Bashir yaje ya tattago Abba da Umma domin su gaisa da mahaifin Zainab.
Da sauri ya mike ya isa ga Abban domin suyi musabiha. Bayan sun gaisa suka zauna. Ita ma
umma ta rusunu har kasa ta gai da shi. Hakan kuwa ba karamin dadi yayi masa ba. Shi yaushe
ya isa Rumaisa ta gai da bakinsa a ladabce? Ai kawai kallon contenporaries take yi musu.
Sai da suka gama gaisawa yace “kai kuma Albashir me yasa ka tattago su alhaji. Dama niyya ta
daga nan ka kwatanta min gidansa in karasa mu gaisa”.
“Ai Dadi main house din is adjacent to nan gidan “in ji Zainab.
Umbola yayi musu da hannunsa yana fadin “kun ci gidanku daga ke har mijin naki. Kuma shine
tun da na shigo ba zaku sanar da ni ba”.
Dariya kawai suka yi. Ganin sun ware da hira ya sanya umma mikewa ta koma gida yayin da
Zainab ta shiga kitchen. Bayan ya raka umma ya dawo kuwa a nan kitchen din ya sameta. Run
gomota yayi jikinsa yace “yaya surprise din nawa how much is it going to be worth”?
“hajj da Ummara”
“Na riga naje na sake zuwa”?
“sabuwar mota latest”.
“not interested”.
“a delicious meal”.
“not good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login