Showing 21001 words to 24000 words out of 65424 words

Chapter 8 - FINI A UBA IN FIKI A MIJI book Complete by Hanne Ado Abdullahi .pdf

ki
ba”. Ta sake fashewa da dariya “san nan tace ki wuce kije yana jiranki. Amma ki tabbatar kin
shigo gida nan da minti ashirin saboda bar ganin zaki wajen saurayi ba uban da zai dora miki
abinci dare. Su Farida karatu ya sha musu kai, saboda haka idan kika haura hakan zaki hadu
da ni”.
Ita dai saroro tayi tana kallonta saboda tama kasa fahimtar abin da Momi take nufi. Sai da ta fita
san nan Baba Laure tace “wuce kije kin ji uwata”.
Sanye cikin hijabinta wanda ya kusa rufe dunduniyar kafarta ta nufi wajen bakon da bata san
shi ba.“
[8/6, 23:22] +234 814 948 5104: FINI A UBA
IN FIKI A MIJI
PAGE 17
BY HANNE ADO ABDULLAHI
A nan wajen Mallam ta same su tsaye. Tun da ta dosu su suka tsaya da zancen da suke yi. shi
dai Mujib mamakinsa ya tafi ne akan yadda take spreading wata irin aura even though ko ina na
jikinta a lullube yake. shi kuwa sarkin masoyan duniya nurnar ganinta ce ta saka shi ya kasa ci
gaba da zancen da su ke yi. cikin zazzakr muryarta ta durkusa har kasa tace "barkanku da yamma"
"barka kadai gimbiya" inji Mujib. "Da fatan mun same ki lafiya kalau"?
"lafiya kalau ". kunma har a wannan lokaci tana durkushe bata mike ba.Mujib ne ya sake cewa
"to gimbiya Zainab mike mana ai mun gama gaisawa".
"a'a ba komai hakan ma yayi" ta sake fada. A tare bakin nata suka hada ido sai kawai suka
zube a gabanta suma suka durkusa. cike da mamaki tace "lah ya haka kuma"?
"Tun da gimbiya na durkushe ai kuwa ba mu ga ta tsayuwa ba". Bata san sanda wata 'yar
gajeriyar dariya ta subuce mata ba. san nan ta mike tsaye. mikewar tata yayi dai dai da zuwan
Mallam wanda ya karaso wajensu dauke da kujerun roba guda biyu. hakan ya sanya su suka
zauna a kujerun yayin da ita kuma ta zauna a dan dakalin dake bakin varender gate din. Bayan nan suka sake sabuwar gaisuwa. mujib ne ya nuna mata Al Bashir ya ce "kin gane shi"?
ta dan dago ta saci kallansa sai kuma ta girgiza kanta alamun a'a. cike da zolaya yace "da
gaske Zainab baki gane ni ba. ni kuwa tun randa na fara ganinki na yi printing din fuskar ki a
zuciyarta". murmushi ta sake yi cike da jin kunya san nan tace "Allah da gaske nake kayi hakuri
ban gane ka ba”. “Amma dai ina fatan daga wan nan haduwar zaki gane ni ba tare da na sake introducing kai na

ba”.
“In sha Allahu” ta amsa masa tana mai nuna jina kunya.
Mujib ne ya sake gyaran muryar tare da cewa “to malama zainab ni dai suna na Mujib Sani shi
kuma wanda kika kase ganewa sunan sa Bash. …” mintsinin da ya kai masa shi ya hana shi
karasa sunan da ya fara fada.
Nan take ya gane me yake kokarin shaida masa. Take kuwa ya gyara kuskurensa yace “shi
kuma sunansa balarabe. Kuma shi ya ganki yaji kuma yana da ra’ayin ki zamo abokiyar
rayuwarsa idan har kin aminta da shi”.
Shiru ita dai bata yi Magana ba sai wasa da take da hannayenta ta cikin hijabinta.
Kiran sunanta da Mujib yayi shi ya sanya ta sake dago kanta. Tana dagowa kuwa suka hada ido
da AlBashir wanda ya kura mata ido. Itama ta dan yi tsai da idanuwanta cikin nasa san nan ta yi
kokarin kau da nata idanuwan.
Nan dai Mujib ya yi ta kokarin ganin ya dasa bishiyar kaunar Al Bashir a cikin ranta. Duk da dai
basu sami tartibiyar amsa ba, amma sun gamsu da yadda ta yi musu.
Shi kuwa AL Bashir duk da ba wata Magana mai yawa ya samu yayi da ita ba, Amma tsayuwar
ta kawai kusa da shi ya sanya shi jin wani nishadi.
Khalil ne ya karaso inda suke tsaye cikin gatsali yace “ke kizo momi tace ki zo ki dora abincin
dare”.
Bata jin dadin yadda ya tsinka ta a gaban bakinta ba. Kuma tabbas suma sun gane bata ji dadin
hakan ba. Da yaji shiru bata bashi amsa ba ya sake cewa “ko in je ince ba zaki zo ba. In kuma
na fada kin san sauran jikinki ne zai gaya miki”.
Ya juya zai tafi, Mujib ya yi sauri janyo shi yana fadin “yi hakuri abokina. Yanzu zata zo kaji kar
ka gaya wa Momi komai”.
Ya kalleta cike da tsiwa. Yace “kin yi sa’a. da yau na kalli kukan yaya babba tana shan duka”.
Yana fadin haka ya juya ya bar wajen.
Al Bashir ya lura da kwallar da ta ke kokarin sharewa cikin dabara tana kokarin kar su ganta.
Yayi ajiyar zuciyar na takaicin abin da aka yiwa Zainab dinsa. San nan yace “waye wannan”?
“kanina ne” ta amsa masa a takaice.
Ya sake ajiyar zuciya y ace “shi ke nan Zainab shiga gida. Sai gobe idan na sake dawowa”.
Ta sake durkusawa har kasa tace “na gode ku gai da gida”. San nan ta juya ta bar su tsaye a
wajen su kuma suka rakata da kallon tausayi. Ba su tafi ba sai da suka yiwa mallam sallama.
Shi kuma ya sanar da shi lambar wayar Zainab, wacce itama Baba laure ya sa ta dauko masa
wayar. Ba ko kbo a cikinta saboda haka sai please call me yayi zuwa wayarsa san nan ya samu
damar kwafar lambar tata.
Suka fita mashin kuma yaki tashi haka suka hakura suka tura shi suna tafe suna tattauna yadda
suka samu Zainab.
Albashir ne ya fara tambayar Mujib yace “yaya is she worth the trouble”?
“She is worth more than that. Ta bani tausayi matuka. And from yadda kaninta yayi embrassing
dinta a gabanmu is a clear indication na bata da wani galihu a gidan. Amma fa gaskiya abokina
tayi. Such rare beauty is very scarce”.
“Ok fine kaima daga yau bazan kara zuwa da kai ba. Dama ai zancen farko ne kawai aboki
yake rakiya. Daga yau kagama”.
Dariya ya saka san nan yace “ai kaima ka san ko ba serious relationship bane once ka furta ni

kuwa na haramta kaina zuwa wajen. So just trust me. Kuma kasan na gaya maka ni Meena
nake jira ta gama secondary ka bani ita”.
“au wai da gaske akan wan nan small girl din”.
“shi yasa na ga wadda muka baro wajenta is over thirty five. Ita ma wan nan ta girmi Meenan
ne”?
“Fine kaje neman auren Meena. Amma bani zan raka ba. Don bazan je gaban ‘yata ina wage
baki da sunan na rako abokina zance wajenta ba”.
“Ai tunda na shigar maka kasuwar gwanjo zaka iya yi min duk wulakancin da kaga dama. Nima
bance zan kiraka rakiya ba”.
Haka suna hira suna tura mashin din nan basu yi realising ba sai ganin su suka yi daga Hotoro
NNDC gidan su Zainab har sun iso round din Ahmadu Bello Way. Wanda su kuma Alu Avenue
zasu shiga inda gidansu yake.
Sule mai mashin dai Allah ya taimake shi, saboda suna isa gida aka bashi kudi ya sayo sabon
mashin su kuma ya gyaro musu wan nan saboda zuwa wajen Zainab.
[8/6, 23:24] +234 814 948 5104: FINI A UBA
IN FIKI A MIJI
PAGE 18
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Da misalin sha daya na dare, zainab zaune a kicin din gidansu. Kowa yayi bacci banda ita. Yini
tayi ta na murjin meat pie guda dari biyar da Momi ta samu odar sa. Da karfe bakwai na safiyar
washe gari tayi alkawarin masu shi su zo su dauka. Kunnenta sanye take da ear piece tana
sauraron radio ta cikin wayarta. Duk wanda ya santa, ya san ta da wan nan dabi’ar. In dai tana aiki to kuwa sauraron radio take
yi. Da haka take saurare direct daga radion, sai ranar da Farisa ta ringa yi mata masifa akan
tana damunsu da jiye jiyen radion ta, wanda ita kuma itace abokiyar hirar ta. Hakan ya sanya
take manna ear piece a kunnenta. Ta san programmes din kusan kowacce tasha da kuma lokutan yada su. Amma yau abin da ya
bata mamaki, ringin taji a wayarta ta, wanda ya katse mata shirin duniya labari da take sauraro
a tashar freedom.
Da sauri ta matsa amsawa a tunaninta Momi ce zata bata wani sakon.amma tana sallama
kamar yadda ta saba sai taji bakuwar murya ta amsa mata sallamar da tayi.
“me kike yi har yanzu baki yi bacci ba”? aka tambaya daga daya bangaren. Sai da ta dago
wayar daga inda take ajiye a kasa saboda ta ga waye mai kira da wan nan tsohon dare. Bata ga
suna ba sai bakuwar lamba da ta gani.
Ba shiri ta maida hankalinta kan wayar tace “yi hakuri wa kake nema ne”?
“wacce nake nema na samu. Ko ba Zainab ce nake Magana da ita ba”?
“itace ,amma don Allah kayi hakuri ban gane wa ke Magana ba”.
“Allah ya sani Zainab zaki sa zuciyata ta buga, ina nan na kasa sukuni da tunaninki amma ke
har kin manta da ni”.
Ta dan yi ajiyar zuciya san nan tace “ka yi hakuri da gaske ban gano waye ba”.
“na yarda Zainab. To bakon dazu ne Balarabe”.
Murmushi tayi mai sauti wanda har sai da yaji sautin sa ta cikin waya, san nan tace “kayi hakuri
ban dauki muryarka ba. Barka da war haka”.

“barka kadai Zainab” shi ma ya fada cikin jin dadin yadda yaji alamun murna da jin sautin
muryarsa.
San nan ya ci gaba da cewa “mu dawo maganar mu ta dazu. Me ya hana ki bacci har wan nan
lokaci”?
Tabbas tayi murna da jinsa , saboda tsayuwarsu yau daya taji shi a cikin ranta. Ta kuma kasa
daurewa har sai da ta sanar da baba laure bakon da ya zo mata da la’asar. Ita ma kuwa ta taya
ta murna, ta kuma nuna mata cewar kar taji komai in dai har tana sonsa, saboda ta kan Mallam
suka biyo. Ta fada mata haka saboda shi ma Mallam din iya abin da ya sanar da matarsa ke nan. Take
kuwa ba ta san yadda akayi ba sai jin muryarta tayi tana cewa “idan na mayar da wan nan
tambayar kanka zan samu amsa”?
“Me kuwa zai hana Zainab”?
“To na tambayi abin da ka tambaya’
Kai tsaye yace “tunanin santaleliyar yarinyar dana hadu da ita shi ya hanani bacci. Kin ji amsa
ta ni ma kuma ina sauraron taki amsar”.
“Ni labarai nake ji”.
“kai Zainab. Ni nan na rasa sukuni saboda ke amma ke kin ma saka ni a kwandon shara. Kin
ma manta da ni gaba daya”.
Ba ta san san da ta dada kasa da sautin muryar ta ba, tace “kayi hakuri ba haka bane. Amma
idan kaji ba dadi kayi hakuri. Ka san komai sai a hankali”.
Kwarai ya yaba da hikimarta. Ga shi dai bata fito kiri kiri ta nuna tana ra’ayinsa ba. Amma kuma
yaji dadin yadda ta karbe shi.
Saboda haka yayi ‘yar karamar dariya yace “hakane Zainab. Na yarda da maganar ki. Amma
yanzu duk da haka ki taimaka mini inji kwakkwarar bayani. Shin kin amince dani kokuwa. Ki
taimaka min Zainab inji Magana daya daga bakinki”.
Kunya ce ta kamata kamar yana ganin ta. Ya ji alamun haka saboda haka yace please Zainab ki
taimaka min ko na samu kwanciyar hankali idan naji Magana mai dadi daga wajenki”.
Cike da kunya tace “Allah ya tabbatar mana da Alkhairi”.
Daga inda take tana jin alamun murna a sautin muryarsa in da ya ci gaba da cewa “na gode
Zainab. Hakika yau kin faranta min raina yadda ba kya tsammani. Allah ya tabbatar mana da
alkahiri”.
Kwarai ta shagala da jin dadin hirar da suke yi shi da ita. Gaba daya taji nishadi na shigarta. Aiki
take yi amma bata taba jin dadin aiki irin yau ba. Kafin kiransa a gajiye take matuka, saboda
Allah Allah take ta karasa ta kwanta. Amma sam tun da ya bugo wayar ta gane wake Magana
taji gajiya ta bar jikinta. Cike da nishadi taci gaba da danne meat pie din da ta zubawa nama.
Tana yi tanajera shi a cikin kwalin da zata sanya a freezer kafin masu shi su zo dauka
washegari.
Cikin sassauta murya yace “bani labarin abin da kikaji a cikin radion”. Nan kuwa ta shiga bashi
labarin duniya dalla dalla.
Ya yaba da knowledge dinta a a current affairs. Ku san duk abin da yaji a tashar CNN da BBc
world shi ta maimaita masa.
Sai da ya nisa san nan yace “you are very current. Ina ga alamar jourrnalist zaki zama . sam
bata gane me yake nufi ba saboda haka tayi shiru bata bashi amsa ba.

Nan dai ya dinga janta da hira, har ta gama aikinta ta karasa gyaran kicin din. Ba shi ya daure
yayi sallama da ita ba sai wajen sha biyu da rabi. Ya rabu da ita da alkawarin washe gari zai
kawo mata ziyara.
Momi na barin gida washegari tayi sauri ta shirya ta shiga gidan su Fatu da kokarin ta sameta
kafin ta wuce makaranta. Ta kuwa sameta ranar bata da lecture sai bayan goma. Cike da
zumudi ta zayyana mata labarin dan kyakkywan bakon da ya kawo mata ziyara jiya da kuma
wayar da suka kwashe lokaci mai tsawo suna yi da shi. Feelings da ta ke ji a tare da ita bata taba jin makamancinsa ba. Ji take yi kamar ta janyo
lokacin da yace zai sake zuwa wajenta. Ranar dai a anan ta lalace bata je islamiyyar safe ba
haka nan bata bar Fatu taje tata makarantar ba. Domin suna ta tattauna batun Balarabe sai
dubawa suka yi su kaga sha biyu tayi. Da sauri tayi wa mama hajjo sallama ta koma gida.
Kamar yadda yayi alkawari. Ta na kokarin karasa hada abincin dare bayan sallar isha Mallam
da kansa ya zagayo inda take a kicin tana aiki ya shaida mata cewar Balarabe ya zo.
Da sauri ta karasa abin da ta keyi. Ta canza hijabin jikinta san nan ta nufi wajensa. Sai da ta
dauki jug ta zuba matsattsen lemon zaki a ciki, san nan ta nufi bakin gate wajensa.
Yau shi kadai ne. tun kan ta karaso daddaan kamshin turarensa ya bigi hancinta. Ba tare da
saninta ba ta ja numfashi ta shaki kamshinsa sosai. Tun da ya hangota fitilar gidan ta haske ta
ya kura mata ido. Bai taba ganin macen da ta iya taku irin na Zainab ba. Ga shi dai da dan
hanzari take tafiya, amma sai ka rantse rawa take. Sai da ta iso gabansa san nan ya saki ajiyar zuciya. Shi ya sa hannun ya karbi jug din yana
fadin “barka da fitowa gimbiya”.
A kunyace ta dago ido suka hada nata da nashi. Dan duster da ta riko ta cikin hijabinta, ta saka
ta goge bakin verander tace “Bissimmillah zauna”.
“ni in zauna ke kina tsaye, ai kuwa haka bazata yiwu ba”. Tana kokarin zama gefen verender da
sauri yace “kai kai dakata”.
Da dan firgice ta juya tana kokarin tambayarsa abin da ya faru. Kafin tayi Magana sai gani tayi
ya sanya gefen shaddarsa wacce da ace ta san kudinta to ta haura dubu dari. Amma haka ya
sanya bakin rigarsa ya goge mata gefen da ta goge masa.yace “kema zauna my putri”.
Ba ta san me yace da ita ba amma dai ta fahimce wani suna ne na jin dadi ya kira ta da shi. A
wajen da ya goge mata ta zauna. Shima ya zauna a dan nesa kadan da ita suka saka tray da ta
zubo masa lemo a ciki a tsakiya. Ta dan rankwafa ta gaishe shi kamar yadda tayi masa farkon
zuwanta, san nan ta zuba lemon a cup ta mika masa. Cike da jin dadin abin da ta yimasa ya dauki lemon nan. Ya sha rabi ya na kokarin ajiye sauran,
kawai bata Ankara ba sai jin muryar Khalil tayi yana cewa “eyeh lallai. Zainab kin rika. Jug din
da Momi ta ware wa bakinta shi kika dauko kika kawo wa Bala mai gwanjo saboda kin raina
Momi. Yau kuwa zaki gane kurenki”. Gaba daya ji tayi wutar kanta ta dauke saboda takaicin wulakancin da Khalili ya yiwa bakonta
da ita kanta. Amma ta san babban ganganci ne ta nuna masa hakan. Kafin ta yi Magana yace
“kin ga save your breath. Momi ce ta ce ki zo ki hadawa bakinta abinci, saboda su Farida da
Farisa are very tired kin san su ba NFAs bane sun dawo daga IT sun gaji. A jiya Zainab tsakannin shabiyun rana zuwa na dare sai da ta dana samosa 500, spring rolls ma
haka, da kuma meatpie shi ma same quantity, hakan kuma bai sanya ta ragi aikin gidan da take

da komai ba, amma wai masu zuwa IT ten na safe su dawo 1 na rana sune suka fita gajiya.
Khalili kuwa sauri yake yaje ya gayawa Momi labarin jug din data dauko, saboda haka ya na
gama fadin haka ya yi gaba abinsa. Ganin haka ya sa ita ma ta mike da sauri ta ce da Al Bashir
“yi hakuri ina zuwa”.
Kafin ma ya amsa mata ta bi Khalil da sauri. Shi dai mamakin wan nan yaro yake. Ji yake kamar
ya tashi ya rufe shi da duka, saboda wannan ne second time yana wulakanta masa Zainab
dinsa.
Tana jiyo sautin muryarshi yana sanarwa Momi labarin jug dinta na acrylic da ta kaiwa bakonta
waje. Tana kuwa kokarin hada musu abinci Momi na caccakar ta tana masifar jug din da aka
kaiwa bako ruwa a ciki. Bata tanka mata ba ita dai kokarin hada abincin take yi a dinning. Sai da
ta gama komai su kuma suka zauna suka fara ci wanda ta dauki minti ashirin, san nan ta koma
a tunaninta ma zata tarar ya tafi, amma ga mamakinta tarar da shi tayi zaune suna hira da
Mallam.
Ta zauna sun dan fara hira bai fi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login