Showing 63001 words to 65424 words out of 65424 words
Chapter 22 - FINI A UBA IN FIKI A MIJI book Complete by Hanne Ado Abdullahi .pdf
dai ban san nawa ta sata ba”.
“kai jama’a. yanzu Ya Balarabe don zaka taimaka min sai ka ci min fuska”?
Sa’ad ya jiyo muryarta ta speaker da Albashir ya danna. “Kin ga madam kyale shi. Bani nan da
five minutes zan kiraku”.
Minti biyar din ma bata karasa ba ya kira ya ke sanar dasu abin da ya faru. Kudi ne suka fitar ita
da ogan ta har miliyan hamsin. Amma unfortunately five million kawai taci a cikin kudin saboda
ogan ne ya karbe sauran. Sai dai kuma sa hannunta ne a voucher so ba ta inda zata fita.
Sa’aad ya ci gaba da cewa “idan so samu ne a samu a yi refunding ko da ten ne daga cikin
kudin sai a samo guarantor da zai sa hannu a sake ta. In yaso daga baya zan ga yadda za a yi
ayi dropping all charges against her”.
“kana maganar 10 mill. Ni ina ga kudin da zan biya”?
Da mamaki ta juya tana kallonsa. Mutumin da don ya ginawa talaka gida ya bashi jari mai kauri
ba wani abu bane a wajensa amma yana kukan bashi da as little as 10m.
Tana cikin kuka ta duba balance din account dinta. Kudin ba su kai ba. Saboda bata dade auren
Sajida da kuma Faruk kannenta ba. Duk da dai 90% Albashir ne yayi komai. Ga kuma Hafsa da
ta itama auren nata ba hustling saboda kanin abokinsa Mujib shi ya aureta, amma dai duk da
haka an dan ji jiki. Saboda har gida suka gina masa. Yinin ranar sam ta kasa sukuni. In ban da kuka ita da Farida ba abin da su ke yi. Ita farida tana
da albashi mai dan tsoka, amma kaf hidimar anti Sakina da yaranta a wuyanta suke, saboda
haka kafin wata dan abin da aka samu ya kare.
Zainab tayi rokon tayi lallashin amma sam Albashir ya kekasa kasa yace shi ba abin da zai iya
yi. Daddy kuwa ko guarantor ma yace ba zaiyi mata ba. Farisa tace ita kuwa she cant waste her
money on Momi saboda ita ta jawa kanta.
Albashir ya shiga wajen Umma take tambayarsa yinin yau gaba daya bata ga zainab ba, kuma
bata kirata a waya ba. Kwanciyarsa yayi a kan doguwar kujera san nan yace “kyaleta umma
rigima take ji shi yasa ma na fito na barmata gidan”.
“haba dan uwana. Don tana ji rigima kuma ina ce ba rarrashinta zaka yi ba. Ita fa mace ba
girma take da shagwaba a gaban mijinta ba”.
“umman ba rarrashin take so ba. Wai fa matar gidansu taci kudin gwamnati shine ofis din su
Sa’ad suka kamata. Kuma wai ni take so in taimaka in fito da ita”.
Da mamaki Umman ta sake cewa “baka da abin da zaka fito da ita din ne ko kuwa tsiya kawai
kake ji”?
Shiru ya kasa baiwa umman amsa. “Anya dan uwana yaushe ka koyi riko haka”.
“Allah Umma don dai baki san irin muguntar da ta dinga yiwa Zainab bane. So tayi kwata kwata
rayuwarta ta lalace. Hatta makaranta kin ga sai da tayi mata sanadinta”.
“Kuma da tayi mata sanadin nata sai me ya faru. Yanzu kai ilmin da Zainab take da shi ba
daidaikun mata ne suka samu sa’ar yin sa ba. Ina ce ran nan kace min ERC sun nemi ta basu
littafin data buga na easy fiqhu akan zasu saka shi a IRK syllabus na makarantu. Kuma duk
wan nan daukakar har ace ana bakin ciki bata yi karatu ba. Ashe akwai abin da yafin ilmin
addini dadi”.
“umma ni kawai haushin matar nake ji”.
“To ka daina saboda Maryam ta taba tambayarta dalilin da yasa take iya yiwa Momi alkhairi
lokacin da ta kai Khalifa karatu Saudiyya. Amsar da ta bata ni kaina naji dadin ta. Tana budar
baki tace idan har ta ci gaba da kullatar Momi to tabbas ba ta yi wa Allah godiya da ya hada ta
zama da mu ba. Kaga kuwa idan ita tayi wan nan tunani kai ma irinsa nake so kayi. Saboda
haka, kaje dan uwana in dai baifi karfinka ba, ka taimaka a fito da ita”.
Suna falonta zaune ita da Farida sun yi jigum jigum, saboda ance idan ba a zo bailing Momi ba
tsakanin yau da gobe tabbas jibi kotu za a tura ta. Shigowarsa yana waya inda suka ji yana
neman ticket na mutum uku zuwa Abuja, ya sanya suka saki ransu.
Sun sami jirgin karfe daya. Kafin uku suna ofis din Sa’ad. Albashir ne yayi komai, ya kuma tsaya
a guarantor, amma fa yana yi yana mitar idan Momi ta gudu aka kama shi, ita ya shafa. Saboda
umma da Abba suna da wasu ‘ya’yan ita kuwa shi kadai ne mijinta.
Sa’ad yana dariya yake ce masa “kar ka damu ba inda zata je. Kuma ma ina ga zan yi closing
din case din yau din nan. Nan da nan asarar 10m ta hau kan Albashir. Saboda ba shi yayi niyya
ba ya sa mata suna asara. Mutumin da riba ke shiga account dinsa bayan kowacce awa daya.
Ko sati zai iya hada ribar 10m din. Inda Allah ya takaita Farida bata tare dasu da ba karamin kunya zata sha ba na mitar da mijinta
ke yi. Sa’ad kuwa ya taimaka matuka, saboda a ranar aka gama case din Momi.
Tana fitowa daga inda aka tsareta taga Zainab, har kasa ta durkusa tana yi musu godiya ita da
Albashir. Zainab ta dago ta rungunme ta a jikinta tana bata hakuri. Abin mamaki wai yau ita
Momi ke shiwa albarka.
An gama case. Sai dai kuma an sauke ta daga aiki. Tare suka juyo zuwa kano washegari. Dadi
kuma yayi tsallen arziki yace ba gidansa ba. Ba irin rokon da ba su yi masa ba yace shi kam ba
zai maida ita ba.
Akwai wasu kananan gidaje da Albashir kan gina masu dauke da dakuna uku a jere sai falon a
karshen dakin farko da kuma kitchen da tsakar gida suna kallon dakunan daura da falon ke nan.
Sai kuma daga karshen dakunan akwai dakin waje da toilet dinsa da kuma shago dan
madaidaici. Ko wacce shekara ya kan gina irinsu guda goma ya bayar sadaka. Zainab ta bude daya tasa
aka wanke shi. Take ta sayo kayan gida har da su Ac aka gyara gidan sosai. Ba ita ta gama ba
sai kusan magariba. A ranar momi ta tare a sabon gidan da Zainab ta bata.
“Eh haka kawai saboda mutum yaga ba a iya fushi da shi sai ya dinga min hawa kawara. To
bulukutu maragatan”
Ita dariya ma mitar ta Albashir take bata sai kace Ammace take fada da Amir. Jawo shi tayi
jikinta sai da ya samu daidaita natsuwarsa ya fara manta a ina yake san nan tace “kayi hakuri.
Ba zan iya ganin Farida cikin tashin hankali in kyale ta ba. Momi kuma ai uwace a wajena”.
Cike da shauki yace “tsokanarki nake yi Putri. Kin san I can do koma meye for you”.
“Alhamdu lillah. Yanzu sauran ka abu daya. Yadda ka sama wa su Hafsa mazan aure nagartattu
ka taimaka Ita ma Farida ka samu wani mai hankali cikin jama’arka ka hada ta da shi”.
“kai Putri akwai ki da naci. Kusan shekaru takwas ke nan kullum sai kin yi min maganra in aurar
da farida. Yaya ki ke son in yi. In lokacin auren ta yazo ai za ta yi ne”.
To Momi dai daga babbar ma’aikaciya ta dawo zaman shago. Dan provision Farida ta zuba
mata take sayarwa tana dan samun na batarwa. Duk da dai Zainab bata barta haka ba. Yadda
ta sauke a gidan mahaifin ta haka take saukewa a gidan Momi. Amma yau da gobe sai Allah.
Sai daga baya Farida ta samu auren wani nurse in charge ne a asibitin su . Yana da kirki sai dai
matarsa da uwarsa ba bayani. Masifaffu ne na nuna wa sa’a. da sun yi zai barta ta kama gidan
ta, amma daga baya matar ta zuge uwar tace mata “inna idan kika barsu suka kama gida su
kadai dadi zasuje suna ci mu su bar mu a anan tun da ance babbar likita ce tana da kudi. Ki sa
shi ya kawo ta nan ayi komai akan idonmu”.
Haka kuwa akayi. Daki ciki da falo aka bata a gidan sa. Duk tarin da momi tayi na auren ta ya
tashi a banza. Momi taso taki auren ita kuwa she is being practical tace “mh mh Momi kyale ni
iam not getting any younger. Iam almost thirty”.
Haka ta lallaba tayi auren da take ganin zai zamo mata rufin asiri, sai dai fa abin da kamar
wuya. Ba a raba tunuya ba. Haka dole take cefane na mutum goma sha biyar. Inna da kanne
mijinta hudu. Mariya da ‘ya’yanta bakwwai. Ga kuma bazawarar kanwarsa da ‘yarta duk a gida
daya. Ba wani cikakken privacy a gidan. Duk wanda yaji ko da sartse ne ita zata kai shi asibiti ta kuma
sayo magani. Cefanen gidan ita ce. Shi nasa albashin sai Innar ta karbe ta bawa useless
kannensa. Dama shi kadai ne responsible a gidan. Ga ‘yar banzar rashin kunya da suke labta
mata. Ga sata. Yanzu haka ta hakura da sayen waya mai tsada ta koma nokia mai torch light.
Saboda in dai ta saya yau gobe kuwa zata neme ta ta rasa. Ba kuma ta isa tayi cigiya ba.
Saboda ko ganin ta tayi a gidan za ace ai ba ita kadai nasara yayi wa wayar ba.
A haka ta haifi diyarta mai sunan Momi. Lokacin da ta tashi zata saka ta anursery aka ce sam
ba za a raba musu makaranta da sauran yayyen ta ba. Saboda tana son Iman ta samu karatu
mai kyau, haka ta hakura ta dau responsibility yaran takwas ta hada da tata tara.
She works for like sixteen hours daily just to meet her financial abligations. Ko motar hawa ta
kasa saya. Duk ta tsofe kamar ba ita ba. Ranar da Zainab ta haifi ‘yarta ta hudu Khadija, taje
mata barka. Haka ta tantsa yaran nan a adaidaita sahu, saboda ta dauko su daga makaranta ke
nan, don ta san idan ta koma gida ba zata samu fitowa ba. Zainab na zaune a falo ta ga yara sai fitowa suke daga adaidaita. Sai da mutum goma suka fito
daga cikinsa. Take hankalinta ya tashi na ganin kanwarta ce cikin wan nan situation din. Sai da
sukaci abincin dare san nan suka tashi tafiya. Ta fito raka ta driver zai ajiye ta agida, sai kawai
ta tuna da sienna LE2004 dake zaune a gidan wai saboda ko da za aiki driver. Bata san sanda ta shiga daki ta dauko key ba. Har sun gama duruwa cikin motar ta range rover
tace wa “Farida sauko ungo wan nan ai dai zata kai ki point A to B. cike da murna ta shiga gida
da sabuwar motar da yayarta ta bata.
Washe gari har da maigidan aka fito ana ta murnar samun sabuwar mota. Aka lalauba babu
mota babu dalilinta. Ana kakabin an sace sai ga waya daga police station yazo an kama
kannesa sun buge wani mutum da mota.
Haka mijin Farida ya nufi police station din. Ashe wai ta window dakinta suka shiga tana wanka
suka dauke key din da daddare. Yayi belinsu Farida ta tsaya kan medical treatment din wanda
suka buge. Daga ya dawo gida yana musu fada, kishiyar farida Mariya tace tana jin san da
Faridan ta zuga shi. Nan kuwa suka tarar mata. Duk da kokarin da yayi na hansu sai da sukayi mata ligif da jikinta
san nan suka kyaleta. Shi ya kaita asibiti yana bata hakuri kamar yadda yake mata ko da
yaushe. Shi ai yana sonta. Family shi ne wasu bunch of hooligansa.
Zainab da danyen jego ta je ta ga yadda kanwarta ta koma saboda dukan dangin miji. Ba yadda
bata yi da Dadi ba yace ai shi ya fitar da hannunsa akan Rumaisa da ‘ya’yanta. Da kyar ta samu
ta lallaba shi. Tare suka je gidan mijin su Farida. Nan kuwa tadage takardar kanwarta za a bata,
ko kuma a raba musu gida. Shi dai kabiru yana son zama da matarsa, saboda haka ya samu ya lallaba uwarsa akan cewa
idan suka bar farida ta bar gidan yara sun daina zuwa makaranatar kudi saboda ita take biya,
haka kuma dan dadin da suke ci da kuma ‘yar sutura mai kyau duk zata gagare su saboda ita
ke tallafawa. Da wan nan ya samu ya dora ta ta yarda akan Farida ta koma gidanta, amma sai tayi alkawarin
zata ci gaba da dawainiyar yara ta makaranta. A nan unguwar Zainab ta samu dan gida
madaidaici ta saya mata. Aka kuma yi mata iyaka da kannen mijin. In dai suna son ganinsa sai
dai su kira shia a waya, amma ban da shiga gidan Farida.
A haka ta samu ta kwato mata ‘yancin ta. Ta kuma ci gaba da tallafa mata, saboda albashinta
ba zai dauki nauyin dake kanta ba. Ga Sakina da yaranta biyar ga tata ga na mijinta guda
bakwai da kuma ‘yar kanwarsa duk ita ke biyan school fees dinsu. Tayi aikin gwamnati tayi
private duk don ta rufwa kanta asiri. Yau shekarar Zainab da Albashir goma cif da aure. Ba tare da saninta ba ya shirya mata
hadaddiyar dinner. Ya sa ta shirya ita da ‘yanmatan ta cikin wani hadaddaen lace yayin da shi
da Amir suka hade a shadda suma anko babbar riga.
Sai da ta zauna a matsayin guest san nan ta fuskanci ita ce host na taron. Ba abin da ya dada
birgeta irin yadda Albashir ya dada tababatar mata da soyayarrsa a gaban mutane. Allah yasa
ma su yasu ne kawai matasa. Wakar da aka musu ta shimfidar fuska ranar bikin aurensu, ya
zauna yayi miming da kansa ya rera mata a cikin bainar jama’a. Ai kuwa bata san sanda ta shiga fili ta dinga falle ‘yan dubu dubu tana lika masa ba. Shi kuma
ya riko hannunta yana taka rawa da ita a hankali. Nan kuma sauran abokansu suka kewaye su
ana ta zuba masa kudi.
Mujib ne yayi jawabin godiya inda yake cewa “lokacin da muka je neman auren a’yan gwanjo
muka je. Yau kuma mun koma mawaka after ten years. Ban sani ba nan da wata ten years idan
har muna raye ban san wacce sana’a zamu fara ba. Amma dai kam iam sure of one thing. The
circumstances might change but the love of Albashir and Zainab will remain where it was
yesterday”.
ALHAMDU LILLAH