Showing 9001 words to 12000 words out of 65424 words
Chapter 4 - FINI A UBA IN FIKI A MIJI book Complete by Hanne Ado Abdullahi .pdf
nasa ta
jera musu. Ta kwashe wanda suka cire ta wanke ta shanya . Halem da Hanif kuwa har abada
daya na goye a bayanta. Gasu da wata irin kiba kamar mai tallan michelin.
Amma haka nan tutur take fama da su. Ita ba me aure ba amma tafi matar aure hidimar gida da
kuma wahalar yara.
Kwana hudu kawai suka yi Momi da Daddy suka zo daukarsu.
Suna falon mahaifiyarsa suna gaisawa inda a anan baban Daddy ya shigo ya iske su.
Mahaifiyarsa ta kalleshi tace "Dacta ina son ka lura da wani abu idan ita Rumaisa ba ita ta haifi
Zainabu ba kai kai ne mahaifinta. Amma ka kasa yi mata riko irin wanda kake yiwa sauran
'ya'yanka".
"Hajiya wani abu tace an yi mata"?
"Yo wan nan yarinya sai tace an mata. Ai duk mai hankali idan ya dubi yanayinta zai san a
kuntace take rayuwa".
Nan Momi ta shiga matse hawaye tana fadin "ni dai Allah ne shaidata yadda nake rike su Farida
haka na ke rike da ita".
"Wayyo Rumaisa share hawayenki ba yan zu ne lokacin yin sa ba. Ki dai tuna zakaran da Allah
ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi. Nawa aka yi kafin wan nan kuma duk
munga inda suka bulle.
Yarinya gaba daya bayanta a zane kamar jikin alfadari, amma kuce wai ba abin da kuke mata.
To wallahi kaji na rantse maka idan ka sake kai hannu da sunan dukan Zainabu ban yafe maka
ba".
Daga nan kuwa bata sake magana ba ta shige uwar daki.
Nan dai baban Dr watau Baffan Nene ya saka su a gaba duk su biyun da nasiha. Ita dai Momi
har a wan nan lokaci tana ikirarin ba abin da take mata.
Tun da suka dawo kuwa ta dora Daddy akan hana su zuwa kauye saboda a nan ake son lalata
masa zaman gidansa a cewarta.
Zainab dai bata samu karatun ta ya hau turba ba sai da Halim da Hanif suka shiga makaranta.
Suma kuma ba sa tasowa sai biyar saboda har islamiyya a makarantar suke.
Sai schedule dinta yayi mata daidai. Da safe ta yi breakfast ta shirya 'yan makaranta. Bayan
sun fita ta gyara gida. Idan ta taso sha biyu ta wanke kananan kayansu da ta jika ta kuma yi
manyan ayyuka.
Abincin rana an soke yinsa a gidan. Saboda iyayen ma'aikata ne suma sai wajen shida suke
dawowa.
Daga baya Momi ta tura ta wajen wata kawarta ta koyo yin snacks. Shi ke nan ita momi ta fara
sana'ar yin na sayarwa.
Saboda haka tun bayan sallar azahar yarin yar nan zata fara tumurmusar flour.
Ko ta na dani samaosa da spring rolls ko tana murjin meatpie ko kuma tana kwabin cake.
Ga shi Alhamdu Lillah Momi na samun kasuwa ita kuwa Zainab tana ji a jikinta.
Ita zata je kasuwa ta sayo kayan aiki ta murza ta soya ko ta kwaba ta gasa ita kuwa uwar dakin
sai dai ta caski kudi.
Amma duk da haka ko ladan aiki bata samu. Saboda ko da sallah ko irin Allah ya isa tallana ba
zata samu a dinka mata ba. Sai dai kannenta su bata kwancen nasu.
[8/6, 23:13] +234 814 948 5104: FINI A UBAí ½í±¨â€í ½í±§IN FIKI A MIJIí ½í²‘
page 8
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Haka nan rayuwar Zainab ta ci gaba da kasancewa. Momi ta rabata da uwarta ta cusa rashin
jituwa tsakanin ta da mahaifinta ta kuma raba ta da sauran dangi.
Bata shaku da kowa ba sai dai aikinta da kuma baba Laure matar Mallam mai gadinsu.
Dakuna shida ne a gidan kowanne da bandakinsa ga kuma falo uku. Amma kullum sai ta share
na sharewa ta kuma wanke na wankewa. San nan ta bi ko ina ta goge.
Idan Farida ta nuna kokarin taimaka mata yanzu uwar zata kora ta akan maza ta koma kan
karatunta.
Saboda haka daga 'yanmatan gidan anti Sakina da anti Bilki zuwa kannenta Farida, Farisa,
Khalil, Halim da Hanif ba wanda zai iya rayuwa idan bata taimaka masa ba.
Ko kayan sawarsu ba su iya tsarawa ba sai ta hada musu.
Kusan ko yaushe ka ganta a cikin wata hidima take. Kullum ita ke karshen kwanciya misalin sha
dayan dare kuma dole ta tashi hudu.
Jikinta ya saba da wahala. To ita da haka suka kyale ta ma ba kyara da hantara da kuma cin
mutunci da ta ji dadi.
Inda kawai take samun sauki wajen Farida da kuma Anti Bilki. Amma sauran sai dai wahala. Su
din ma suna sata ayyuka amma ba cin mutunci da wulakanci. Kuma sukan yi hirar arziki da ita.
Inda ta dada tantance matsayinta a gidan wata rana ne tana kwashe tuwon semo. Khalil yana
zuwa ya sa cokali ya debo tuwon nan ya bude rigarta ya sakar mata shi a ciki.
Habawa! Ba ta san sanda ta mike cikin jin zafi ba tana ta rawar radadin zafin tuwon da ke kona
ta a gadon bayanta.
Haka ta dinga rawa da tsalle saboda zafin da take ji.
Su kuwa sauran yaran sai dariya suke ta tintsira mata. Bayan nan ya dade yayi ja, abinka da
farin mutum.
Nan aka mai da abin wasa. Kuma har da Momi a wajen. Itama sai ta kulli aniyar ramawa tun da
taga wasane.
Sai ta sayo rayuwar ruwa a makarantarsu. Wasu animals ne da objects na roba. Idan ka siyo
shi yana karami. Kana jika shi a ruwa sai ya yi ta shan ruwa yana kumbura.
Ta san shi da tsoron kadangare sai ta sayo mai suffar kadangare ta jika shi wajen kwana uku.
Yayi girma sosai kamar kadangaren gaske. Ta lallaba ta wurga masa cikin jakar makarantar sa.
Yana zazzago litattafansa habawa yayi arba da katon jan gwala gwada ya fado.
Tsalle ya daka da ihu a lokaci guda.
Su Momi duk a ka yo kansa. Shi kuwa kamar zai shide sai nuna musu kadangare yake yi.
Zainab tasa hannu ta dauke shi tana fadin "nima na rama"
Wani irin barin makauniya Momi ta rufe ta da shi. Tana dukanta tana fadin "shegiya tsinanniya
mayya. Kashe min da zaki yi"?
Tana zaginta tana duka a lokaci daya. Farisa da Khalil kuwa sai dariya suke.
Sai da tayi mata lilis san nan ta tsallake ta ta barta a wajen.
Khalili ya kalle ta ya mata gwalo yana cewa "gobe ma ki kara tabani sai na sa Momi ta yi miki
duka banza boyi boyin gidanmu".
Tun daga wan nan lokaci ta dada janye jikinta daga garesu. Saboda kome suke so idan taki yi
musu yanzu zaka ji suna fadin "ko yi ta girma da arziki ko yanzu musa kuka . Kin kuma san idan
mun digar da hawaye digo daya ko na karya ne sai kin zubar da cikin jug na gaske".
Sai ya zamana bata da wani da take mu'amala daxshi a cikin gidan idan ba baba Laure ba.
Ita ma din kuma Mallam mai gadin su ne ya dora mata nauyin kula da Zainab. Saboda ya lura
da taken taken matar gidan so take ta watsa rayuwar yarinyar nan gaba daya.
Ba abin da ya dameta da tarbiyarta. Za ta iya aikenta shago siyo abu komai dare ba abin da ya
dameta. Kasuwa kuwa ko wacce iri ce turata takeyi kuma da kashedin lalle ta samo araha.
Mallam sai ya fassara hakan da taken taken lalata rayuwarta. Shi ma kuma sai ya dauki aniyar
tsaya wa a kan lamuranta.
Shi ya hana ta fita da daddare. Idan an aiketa ya ja mata kunne kar ya kara ganinta taje shago
shi ta ba shi ya sayo mata.
Lokuta da dama kuma da uwar take tura ta kasuwa sai ya tabbatar da matarsa suka tafi. Balle
da suka yi sa'a ba yini suke a gida ba.
Haka zalika ya dorawa matarsa larurar kula da tarbiyyar yarinyar tare da nusar da ita harkokin
da suka danganci tarbiyarta.
First period dinta ita ta nuna mata yadda zata kula da kanta.
A wata rana mallam yazo wucewa sai ya ganta ta kawowa direban gidan abinci. Shi kuma ya
rike hannu ta yana mata wasa. Yana cewa "zo nan matata. Zo ki bani a baki in koya miki wasan
masoya. Kin san Momi ta ce ni zaki aura".
Dama kullum haka Momin take gaya mata cewar tun da ta ki karatu sai dai ta auri Sale direban
gidan.
Kuma inda zaka san da gaske take. Ita ta dora mata dokar duk sanda ta gama abinci ta kai
masa dakinsa.
A wan nan ranar da Mallam yaji kalamansa ba karamin tashin hankali ya shiga ba.
Da fushinsa ya karasa wajensa yace "sakar mata hannu karamin shakiyyi".
Ba shiri ya saki hannunta cikin tsoro. Ko ba komai yana shayin mallam mai gadi saboda yana
kallon mai gidan ma ko bukatarsa ta tashi a wajen aiki wajen Mallam yake zuwa ya taimaka
masa da addu'a. Gashi kullum ka ganshi da Qur'ani a hannunsa yana karatu ko kuma wani
littafin addini. Hakan yasa yake masa kwarjini. Mallam ya juya ya kalleta ya daka mata tsawa yace "me ya kawoki dakinsa"?
Cikin tsoro da rawar murya tace "momi ce tace in kawo masa abinci".
Ya dan sassauta muryarsa cikin tausayin yarinyar yace "daga yau ki dinga ajiye masa a bakin
baranda kar ki sake zuwa dakinsa".
"ToMallam "ta fada da saurinta. San nan ta juya ta wuce cikin gida. Sai da yaga ta shige san
nan ya juya wajen Sale yace "kai kuma naga take taken ka. Ta ka saurareni da kyau. Na rantse
da girman Ubangiji idan ka kara taba yarinyar nan ni kuma na maka alkawarin kai da mace a
duniya har abada. Network naka zan dauke gaba daya. Idan kana ganin karya nake ka gwada
ka gani".
Kwarai Sale ya tsorata da barazanar Mallam. Saboda haka ya kashe wan nan boss din.
Ita kuma Baba Laure ta shiga nusar da ita duk abin da ya kamata diya mace ta sani a
rayuwarta.
Allah ya basu hahihuwar yara biyu duk maza. Basu samu mace ba, sai suka mai da ita kamar
'yarsu. Ita ma kuma haka ta mai da su makwafin da iyayen da Momi ta hanata ba don Allah ya
raba ta da su ba.
Kawarta daya a islamiyya Fatima. A nan bayan layinsu take. Su ba masu sukuni bane domin
babanta masinja ne a kotu yayin da babarta take awara. Amma ita take taimaka mata. Ita take
bata abincin break.
Ba tare data sanar da ita komai ba ta fahimci halin kuncin da ta ke ciki a gidansu.
Ba ta cika zuwan gidan ba sai ta tabbatar momi da ahalinta ba sa nan.
A haka rayuwarta ta ci gaba har suka fara zama 'yanmata ita da sauran kannenta.
[8/6, 23:13] +234 814 948 5104: FINI A UBAí ½í±¨â€í ½í±§IN FIKI A MIJIí ½í²‘
Page 9
BY HANNE ADO ABDULLAHI
A haka Zainab ta dinga cukurkudar rayuwarta. Ta koma baiwa a gidan ubanta. Ta samawa
kanta lafiya ta zama mai hakurin dole. Idan an sakata tayi. Idan ance tayi laifi ta bada hakuri
komai gaskiyarta.
Tayi developing wani robotic attitude a rayuwarta. Bata da ra'ayi sai na 'yan gidan. Abin da duk
suke so haka take biye musu.
Amma duk da haka bata tsira daga masifa da kuma kyarar Momi ba. Abin da bata sani ba Momi
hassada take yi da baiwar kyau da Allah yayi mata.
A yanzu ne ma ta daina aske mata gashin ta. Da bini bini zata dauki almakashi ta mai da mata
shi saisaye a sunan wai taga kwarkwata aciki.
Amma gashin nan da yake ba shi da zuciya bashi sati uku zuwa hudu zaka sake ganinsa
kwance lamban a gadon bayanta. Gashi baki mailaushi gaske.
A haka kuma ba gyara ya ke samu ba. Da kyar take iya shafa masa vaseline sau daya a wata.
Shima Baba Laure ce ta sanya mata dokar duk sanda zata yi wankan tsarkin al'ada ta tabbatar
ta tsefe shi ta wanke da sabulu.
Suna fara zama 'yanmata kuwa surar jikinta ta nuna mai kyawu ce lamba daya. Fuskarta kuwa
dama tun da ta taso kasan kyakkyawa ce.
Ba abin da ya rabata da mahaifiyarta har hasken fatarsu iri daya ne. Wan nan kyau nata shi ke
dada bata ran momi.
Kar kuma ku dauka nata basu da kyan. Suma kyawawa ne bama ya Farisa da ta ke fara kal. Ita
ma kuma Farida kamarsu daya sai dai haskenta bai karasa na Farisa ba. Zasuyi kala daya da
Zainab. Sai dai ita kuma jikinta ne ba mai kyau ba saboda she is busty.
Amma zamani na gayu. Da yake kuma ta iya parking din su da kyau sai suka zama abin
sha'awa.
Ita kuwa borar 'ya'ya ba ma wanda yake tunawa da saya mata undies. Jikin ne Allah ya sanya
ya zama mai tsayawa da kansa. Sam bata bukatar sanya bra. Skirt ne da pant idan sun bata ta
zubar ta zabi masu dan dama dama.
Shi ma idan Farisa taso wulakanci tayi kararta wajen Momi akan ta satar mata undies. Hakan
kuma ba zai sa Momin tayi tunanin sai mata ba sai da ta ci dan banzan duka Farisa kuma ta yi
ta dariyar jin dadi.
Tana da shekara sha bakwai Farida na sha shida Farisa kuma bata karasa sha biyar ba suka yi
kandi.
Anti sakina da anti Bilki kuwa kannen Momi lokacin suna BUK 300 level. A lokacin ne kuma
suka tsayar da samarin da suke so. Anti Bilki ta samu Sulaiman mai aiki da wani attajiri da ke da
kamfanin yin atamfofi a China. Yayin da Anti Sakina ta hadu da Kabir. Shi kuma ma'aikaci ne a
DPR. Tun da kuwa suka samu samarin da suke so sai dawainiya ta karar wa Zainabu.
Ga shi yanzu sun shiga ajin sauka a islamiyya. Saboda haka basa tasowa sai uku da rabi.
Kuma ya zama dole bayan ta girka abincin dare ta bata lokacin wajen yi wa samarin aunties
dinta better na musamman. Ta gyara falon baki inda suke zama. Bayan nan ta kashe lokaci
wajen yi musu kwalliya da daurin dan kwali. Haduwarta da Fatima ya sanya ta koyi abubuwan gayu kamar su make up dauri da kums lalle.
Har da gyaran jiki.
Da wajen babar Fatiman suke zuwa lalle da gyaran jiki. Dan raka sun da take yi sai itama ta
koya. Shi ke nan kuwa suka daina zuwa ko'ina.
Ita ke musu komai. Amma fa ita bata da lokacin yiwa kanta. Hatta gyaran farce ita take zama
tayi musu.
Mahaifinta dai duk yadda Momi zata yi ta sa shi yaga bakin ta ta iya.
Idan har yana gida zata saka Farida ko Farisa wani a cikinsu ya hada masa abincinsa a dining.
Wacce ta girka daban amma mai serving ita ake nunawa uban ita ta girka.
A hankali sai da ta sa yayi mata shaidar hatta aikin gida kiwa take masa.
Bari Momi take bayan ta saka ta ta gyara dakinsa da su bandaki ta wanke. Sai an daidaici ya
kusa shigowa sai a tura 'yan gata da turaren wuta su saka masa.
Za kuma a tabbatar ya gansu saboda ya yarda su suke hidimarsa. Yayi ta jin dadi yana sa musu
slbarka.
Ita kuwa tsakaninsu sai dai zagi da fada.
Kuma ko waye zai ji haushinta.
Ke ba karatu ba kuma ke ba aikin gida ba ai dole uba yaji haushi.
Baba Laure da Mallam sai kuma Mama Hajjo watau mahaifiyar Kawarta Fatima su ka dai ne a
tsaye a lamarinta. Ko pad idan wani a cikinsu bai sayamata ba to kuwa sai dai tayi amfani da
tsumma.
Ana haka auren Sakina Da Bilki ya tashi. Daddy shi yayi musu komai na 'yan gata.
Zainab ta samu an dinka ankon bikin da ita. Kwatsam sai ga kawar Farisa ta zo daga Lagos
ziyarar gidan uncle dinta. Nan kuwa Momi ta karbe ankon Zainab aka bawa bakuwar Farisa.
Kaf snacks din da aka ci a bikin nan da kuma wanda aka kaiwa amare gidansu ita tayi shi.
Duk da bata da anko. Ranar dinner ta ci kwalliyarta da less din da Farida ta bata. A keken
Mama Hajjo ta gyara rigar da skirt din suka dawo size dinta. Saboda tsabar karbar kunce kamar
sai da takoyi gyara a dole.
Ko ita Fatiman da keken dinkin ke gidansu bata iya dinki kamar Zainab ba.
Ga dai babarta Mama Hajjo mai ciniki goma ce.
Banda awara tana gyaran jiki da lalle tana kuma taba dinki. Amma ita Fatu kamar yadda suka fi
kiranta da shi a gidan bata damu da ta koya ba.
Kawancen su da Zainab ta fara tabawa saboda ganin ita Zainab din ta dage tana yi.
To a wan nan rana itama ta ci kwalliyarta da kwancen da aka bata. Tana ta sauri ta biya ma
Fatu su tafi tare.
A barandar fita waje Momi ta hadu da ita.
"Ina zaki je"? Ta tambayeta a wulakance.
"Mh gidan party". Itama ta amsa mata a tsorace.
"Idan kin tafi party uwar waye zata gyara gidan "?
Shiru bata amsa mata ba. "Come on juya ki je ki tattare gidan nan kafin in hada miki gajiya".
Kafin ma ta dire maganarta ta juya da sauri ta koma ciki.
Kaf gidan nan sai da share kowanne daki ta goge ta kuma wanke ban dakinsa da falukan gidan.
Ita kanta Baba Laure bata san Momi ta hana ta zuwa ba da kuwa ba za ta tafi a motar farko ba.
To ita ta tsaya sai da ta yiwa sauran 'yan matan kwalliya san nan ta shirya.
Bayan ta gama tattaro ciki ta dawo kicin shima ta gyara ko ina nasa san nan ta dumfari wanke
wanke.
Ta wanke plate da kofuna sama da dari biyar.
Tun da farko tukwanen da akayi girki ta fara jikawa.
Bayan ta goge plate da kofuna da kuma cokula ta maidasu ma zauninsu, sai ta dawo kan kuloli.
Suma sun kai goma runduma runduma kamar za a sata a ciki. Haka ta wanke su ta kife.
Ta dawo kan tukwane suma ta dirje su tas.