Showing 12001 words to 15000 words out of 65424 words
Chapter 5 - FINI A UBA IN FIKI A MIJI book Complete by Hanne Ado Abdullahi .pdf
Tun misali tara na dare tafara aikin nan har shabiyu
saura kwata bata gama.
Nan suka dawo suka tarar da ita tana kokarin share wajen da tayi wanke wanke.
Suna shigowa suka ganta jakwane jakwane da ita sai Farisa ta tuntsire da dariya tana fadin "wu
kallo ya bar wata yarinya. Mun je dinner mun more boyi boyi tana wanke wanke".
Ita dai bata kula ta ba. Ganin ma zata takura mata data gama sai kawai ta dauki zanin baba
laure dake rataye a igiya ta cire kayan jikinta ta shanya su ta lulluba da hijabinta tayi
kwanciyarta a sito din kicin din.
[8/6, 23:14] +234 814 948 5104: FINI A UBAIN FIKI A MIJI
Page 10
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Washe garin biki aka kai amare. Bilki matar Sulaiman gidansu yana Ribado road. Yayin da anti
Sakina ke karkasara.
A tunanin Zainab raguwar yaran gidan zai sanya aiki ya ragar mata, amma ina sai ma kari data
samu.
Ga shi dai kowacce da mai aiki aka kaita, amma hakan bai sa sun rangwantawa Zainab ba.
Kullum tana zaryar hanyar gidajensu. Daga baya ma Momi ta saka mata dokar idan gari ya
waye ta yi kokari ta gama gyaran gidansu san nan ta wuce zuwa nasu gidajen ta zauna kar ta
dawo sai biyar na yamma.
Tayi kukan takaicin rasa karatun ta na islamiyya gashi sun shiga ajin sauka. Baba Laure ce ta
kwantar mata da hankali akan tayi hakuri ta bi yadda aka sata. Allah yana tare da ita. Ta kuma
karfafa mata gwuiwa da fadin idan ta dawo sai baba Maigadi ya dora mata.
Allah cikin ikonsa sai ma kuma wani sauki ya billo mata.
Ganin idan taje ma kusan kullum ta kan samu aunts din nata ba su tashi ba. Sai da daina zuwa
sai ta tashi daga karatun safe wanda take tashi sha biyu.
Daga nan sai ta hau dan sahu ta wuce karkasara. Za kuma tayi kokari duk abin da zatayi mata
zata gama shi kafin karfe biyu.
Tana yi azahar sai ta wuce gidan Bilki.Ita kuma idan tayi la'asar sai ta dawo gida ta fara hidimar
abincin dare kafin masu gidan su dawo.
Haka ta koma kullum tana hanya. Shi uncle Sulaiman da ya ke a kamfanin wani babban dan
kasuwa yake aiki a matsayin accountant dinsa. Goma na safe ya ke fita ya dawo biyar na
yamma. Da safe matar zata lallaba ta sama masa shayi da burodi.
Amma abin mamaki idan ya dawo zai tarar da abinci mai rai da lafiya an ajiye na rana ga kuma
na dare shima lafiyayye da shi.
Bai kuma cika haduwa da ita a gidan ba. Saboda ranar jumma 'a ne kawai da yake dawowa
zuwa masallaci ya kan hadu da ita.
Shi kuwa mijin Sakina Kabir yana DPR.
Shi ma dai bai san sirrin matarsa ba ya dauka ita ke zankado masa hadaddun delicious din da
yake diba.
Domin ko dakunan mazajensu sai ta zo zata gyara ta sa musu turaren wuta ta wanke
bandakunan tas.
Ga shi har injin wanki a saya musu amma sai dai ita ta hada wankin ta zuba masa ko kuma idan
ta zo ta tafi da kayan gugarsu gida. Idan kuma an goge ta dawo dasu ta shirya kowanne a inda
ya dace. Idan kuwa ba ita tayi ba, to kuwa sai dai kayan su zauna haka.
'Yan boko ne na karshe amma fa ba abinda suka iya a domestic responsibilities dinsu.
Su kuwa sauran kannenta ko da sun kaiwa aunties nasu ziyara su tarar aiki kamar zai kasheta
to ba abin da zasu kama mata da dashi.
Haka nan ta zama kamar machine kullum cikin hidimar kannen mominta take.
Gwanda ma anti Bilki ita da mijinta suna da kirki. Amma Anti Sakina ba abin da ta rage na
wulakanci da
kuma toxarta Zainab. Ga mijin nata wani irin wawa mai barin zance.
Haka nan tana ji tana gani sauran 'yan ajinsu sukayi sauka banda ita.
Saboda tana zuwa normal lesson amma karatun rana na mura'ja ar saukar bata zuwa saboda
hidimar amare da ta hau kanta.
Da suka samu ciki kuwa sai komai ya dada kacame mata. Hidimar ta karu mata.
Hakan kuma bai sanya Momi ta rage mata hidimar gidansu ba.
Dole tayi na safe ta kuma gyara gida. San nan ta tafi wajen su Sakina. Suna da masu aiki
amma ba za su iya tsayawaa a kansu su yi abin da ya kamata ba.
That is idan ma sun san abin da ya kamata su yi din su da kansu. Sai Zainab tazo. Anti Sakina
ce ta fara haihuwa. Saboda haka kacokam Zainab ta koma gidan da zama. Saboda kusan kowa
na gidansu a nan yake yini. Amma fa ba abin da suke yi sai dai zaman hira da kuma zan ci kaza
zan sha kaza. Ita kuwa tayi ta fama da dafawa da kaiwa da kwashe kayan da aka yi smfsni da
su.
Wata rana tana tsaka da wankin toilet din Uncle KB ashe ya shigo gida bata sani ba.
Hijabinta na rataye kan murfin kofa jikinta sanya da skirt da riga sun yi mata das a figure 8 dinta
kawai taji an banko kofar tailet din.
A tsorace ta juyo domin ganin waye.
Tana ganin Kb ta dafe kirjinta cikin sakin ajiyar zuciya tace "wai uncle ka bani tsoro".
Wani irin yawu ya hadiya makwat san nan yace "amma an dade ana boye kyawawan kaya a
nan. Dama haka kike da kyau shine kike nade jikinki a wan nan yadi marar kyan gani. Bala'i
gaskiya an zuba kyau a anan".
Bata rai tayi ta sha kumu. A iya saninta babu wasa tsakaninsu tunda ita ba kanwar matarsa
bace. Hannun ta mika zata jawo hijabinta yayi saurin dauke shi yana fadin "kin ci karya yarinya.
Ai ba zan sake yarda ki rufe min wan nan blockbusyer din da na samu an yi realeasing dinsa a
yau ba". Kamar zata yi kuka take masa magiyar ya bata hijabinta. Ya nade shi a hannunsa sai ma
matarsa da ya shiga kira.
"Sakina zo ki gani".
Da sauri ta karaso inda suke. Ganin su a haka ya sa taji ranta ya baci saboda macece mai
tsananin kishi. Ga mijin nata kuma da shegen son mata. Muryarsa ce ta katse ta yana fadin
"taimaka min ki bani 'yarki in aura ni kuwa na yi miki alkawarin na daina zuwa ko ina daga
wajenki sai nata". "Kaga Kb bana son irin wadan nan stuid jokes din naka".
"You think iam jocking. Ai ba namiin da zai yi wasa a neman mace irin Zainab. Da gaske na ke
yi miki. Kin ga kin huta da yawona ni kuma in huta da mitar ki na ina neman matan banza".
"Ke get out of here kafin in babbalaki" ta fadawa Zainab cike da bacin rai.
Da dan gudunta ta fito daga cikin taoilet tare da rakiyar wani uban fito da Kb ya saki, mai nuna
alamun yabawa da abin da ya dada gani.
Bai daddara ba ya sake mai da hankalinsa wajen matarsa yace "yaya do we have a deal? Kara
min da ita ni kuma na miki alkawarin na daina yawo".
Bata bashi amsa ba sai ma fizge hijabin da ta yi daga hannunsa ta fita a fusace.
A kicin ta samu Zainab tana tsaye cike da rudani ta wurga mata hijabin ta.
"Don ubanki kama hanya ki bar min gida kafin in canza miki halitta yanzu yanzun nan".
Jiki na bari ta karba ta saka ba tare da tace komai ba.
A kafa ta taka tun daga karkasara har NNDC quarters na Hotoro inda gidansu yake.
[8/6, 23:14] +234 814 948 5104: FINI A UBA
IN FIKI A MIJI
Page 11
BY HANNE ADO ABDULLAHI
A gajiye tikis Zainab ta iso gidansu saboda ga gajiyar aiki ga kuma ta hanya da ta sharo ta a
kan takalminta.
Amma ganin motar Sakina a gidan ya sanya taji gajiyar tata ta wartsake.
Ta kofar baya ta zaga tana kokarin sulalewa ta gudu dakinsu saboda bata san abin da ya kawo
Sakinan gidan ba.
Tana kokarin hawa benen karaf Farisa ta hango ta.
"Momi ga munafuka ta dawo. Na kamata tana kokarin gudu ta buya".
Farisa ta fada cikin daga murya.
Kafin ta gama hada da kuma fassara maganar Farisa sai kawai taji Momi ta rufe ta da duka
tana cewa "shegiya tsinanniyar karuwa. Idan tambadewa kike sha'awar yi ba sai kin je kin nemi
mijin Sakina ba ki shiga kasuwa da gaske har da kudi zaki samu".
Ranar ta sha duka da zagi. Sabo da daga kafar bene Momi ta jata har falon gidan inda suka
zauna ita da 'ya'yanta suka kare mata cin mutunci bana wasa ba.
Ita dai in ban da kuka ba abinda take yi.
Shigowar Halim da baby Amra 'yar wajen Sakinan shi ya katse taratsin masifar da ke saukarwa
Zainab.
Sai kuka yarinyar take tsandarawa kamar za a cire mata ido.
"Kai Halim ina ka dauko Amra"?momi ta tambaye shi.
"Uncle KB ne ya kawota yanzun nan yana waje ".
Momi tabayar da umarni a shigo da shi.
Daidai zai shigo Sakina ta dada narkewa ita als dole an cuce ta a bi mata hakkinta. Cikin gatsali
ya gai da momin san nan ya juya wajen matarsa yace "ke kuma da kika fito ki ka barta yaya
kike son in yi da ita".
Itama cikin tsiwatace "ai na dauka ka samu inda zaka kaita".
Dariya yayi san nan yace "aiwai ke nan yaji kika yo. Wan nan kuma ya rage nake. Dama
alfarma zan yi miki saboda korafin da kike min na yawo amma tun da kin fi son haka sai mu ci
gaba".
Momi ta katse shi da fadin "yanzu Kabiru a gabana kake fadin irin wadan nan maganganun"?
"Ah to Momi ni meye laifina. Idan dai macen bata kai ta rikeni ba ai ni kuwa zan nemawa kaina
mafita. Na ga wanda zata iya rikeni tace ba haka ba sai kuwa tayi hakuri da yadda ta sameni".
Kafin Momi ta gama hadiye mamakinta ya mike yana fadin idan kin sauko kya iya karasawa
gida idan kuma kin san ba zaki koma yau ba nima in nemi wajen kwana".
Daga nan bai kara cewa komai ba ya mike yayi tafiyarsa.
Da farko Sakina taso itama ta dan ja ajinta amma Momin ta nuna mata shi wan nan gabon mijin
nata sai dai su bi shi a hankali. Saboda ko ba komai akwai shi da sakin hannu. Mutunci ne
kawai ba shi da shi.
Haka ta dauki borin kunyarta ta koma. Wan nan abu da ya faru bai kuma sa ta ragewa Zainab
duk wata hidima tata ba. Sai dai fa akwai close marking. Duk yadda zata hana Zainab haduwa
da Kabiru tana kokarin yi.
Ita ma kuma Zainab din ba son haduwa da shi take ba. Saboda indai zai ganta sai ya yaba wani
abu a jikinta.
Ga shi dai a lullube take amma hakan bai hana shi rike memory da ya gani ba.
Ana haka Farida ta samu tafiya Sudan ita da Farisa. Ita Farida ta samu medicine yayin da aka
bawa Farisa computer scince. Ita kuwa jakar gidan tana nan.
Shekarar farko da zasuyi sauka zaman gidan Sakinna ya hanata. Bayan wata shida aka sake
yaye wasu daliban da suka fadi screening na farko aka basu damar sake maimatawa aka saka
da ita shi kuma daddy ya hana ta kudin sauka a dalilin Momi ta ce masa yasayyadin ne
saurayinta shi yasa ya saka sunanta amma ba abin data sani. Haka tana ji tana gani ta sake maimaita wata shekarar.
Ga kawarta Fatu ita har ta samu shiga Legal ita kuwa tana nan tana fama da hidimar Momi da
ta su Sakina.
Raguwar 'yan gidan ya dan rage mata aiki balle da su Halim ma sun girma suma ba sa tasowa
sai biyar na yamma.
Hakan ya sa Momi ta dada habaka sana'arta ta snacks.
Shekarar su Farida daya a sudan, Momi ta debe duk yarsn gidan suka kai musu ziyara daga
nan ta dauke suka karasa Saudiyya suka yi Ummara san nan suka je Turkey da England yawo.
Saboda Momi ta kwashe wajen wata bata gida sai hakan ya bawa Zainab dama shiga wajen
Mama Hajjo watau mahaifiyar kawarta Fatima.
A nan ta dada karuwa da darussan rayuwa. Saboda Mama Hajjo macece mai hikima cikin wasa
da dariya take nusar da su abin da ya dace da rayuwarsu kamar irin su mu'amala da iyaye da
kuma dangin miji da shi kansa saurayin idan an same shi har kuma ya zuwa lokacin da zai
zama miji. Ha ka zalika nan ta sake kwarewa da gyara irin su lalle da halawa da dilka.
Ita kanta ba ta san ta tana da talent na zane ba sai da ta zanawa Fatu lallen rasma idan kagani
sai ka dauka a saudiyya aka zani shi.
Haka nan ta ci gaba da kasancewa lokaco lokaci Momi zata debi sauran yaranta har su Bilki
dake gidajen mazajensu su kaiwa 'yan sudan ziyara daga nan su wuce yawo kasashen duniya,
amma banda Zainab.
Saboda idan ta tafi da ita harkar cinikinta zata tsaya.
Kuma yadda ake cinikin snacks tana nan haka ake yinsa ma in bata nan.
Kusan in bata nan ma kudi sun fi taruwa saboda babu mai ci sabanin idan yaran gidan suna
nan.
Sai da su Farida suka dauki tsawon shekara uku a Sudan san nan suka zo hutu saboda IT da
za suyi a kasar nan.
Biliki ce ta sake haihuwa ta biyu ke nan. Dukkan su suna gidan. Yan boko na kwance a kujerun
falon suna ta latse latsen wayoyinsu yayin da ita kuma take ta kai da kawowa na ganin tsaftar
gidan da kuma abincin da za a ci ya kammalu.
Uncle Sulaiman ne ya fito daga dakinsa da hanzari rike da waya yana amsawa a dan firgice
yana fadin "gani nan zuwa yallabai".
Sai da ya kashe wayar san nan ya ya juya wajen Bilki yace mata "mai gida na ne ya zo mana
barka".
San nan ya fice da hanzarinsa ya shigo da shi.
Yadda suke kwance a kujera ko zaman su ba su gyara ba.
Haka zalika rawar jikin da Sulaiman yakeyi ta kokarin martabar bakon bai shalle su ba.
A yangace kowacce ta dago kai ta kallashi.
San nan aka yi masa gaisuwar ya kake. Shi ma da lafiya kawai ya amsa musu san nan ya mai
da hankalinsa wajen gaisuwar ban girman da Bilki da Sulaiman suke masa.
Ita Bilkin ce ta sake mikewa ta shiga kitchen Farida da Farisa su na nan a yadda suke. Sai
faman latse latsen waya suke ta faman yi.
Ba ta fi minti biyu da shiga ba Zainab ta shigo falon dauke da dan madaidaici tray wanda ta
dora jug da kananan kofuna guda biyu da kuma robar ruwan swan. Sai daga gefe dan side
plate ne data rufe da foil paper. Kamar ko da yaushe sanye cikin dogon hijabinta wanda ya kusa
rufe idon sawunta. Cike da natsuwa ta karasa kusa da shi ta jawo side table ta dora tray a kai san nan ta russuna
daga gefensa tace "barka da yamma".
Sautin muryarta kawai ya sanya yaji duk wata jijiya ta jikinsa ta amsa. Take adduar da yake
korawa baby Musty ta makale a bakinsa.
Da kyar ya daure ya amsa mata da cewa "barka kadai".
Bata lura da yanayinsa ba ta jawo tray gabansa ta zuba masa ruwa a kofi daya dayan kuma ta
zuba masa matsattsen lemon zaki san nan ta dan kware gefen side plate din da ta rufe da foil
samosa da meat pie suka bayyana.
Wai tas Mallam Al bashir ya manta da azumin litinin da alhamis da yake yi ya kaiwa abincin nan
attack saboda kawai ya manta da komai in ban da kyakkyawar fuskar Zainab.
Yatsun hannuta zara zara su suka dada mantar da shi komai sai kokarin shan lemu da ta zuba
da su.
Ba tare da ta lura da yanayinsa ba ta mike ta koma kitchen ta ci gaba da aikinta.
Sai da ya cinye meatpie biyu da samosa uku ya kuma sha lemu kofi biyu san nan ya tuna yau
ya dau azumi.
Yaran nan suna kallo tunda bakon nan ya shigo maigidan yake mazari a gabansa amma hakan
bai san sun gane darajar da bakon yake da ita ba.
Shi dai Albashir yayi musu barka. Amma fa rabin hankalinsa na ga son sake ganin baiwar Allah
nan da ta shayar da shi lemon da bai taba jin mai dadinsa ba a rayuwarsa.
A lokacin da ya shigo masu gidan basu dade da yin lunch ba saboda lokaci ya nuna wajen karfe
biyu da rabi.
Zainab tana shiga kitchen tayi sauri ta dora nama da busasshen kifi da stock fish a pressure
pot.
Ta dauko kazar gidan gona guda daya ta wanke ta mutssuke ta da kayan kamshi da su maggi
ta dora mai ta hau suya ba tare data tafasa ta ba.
Da ta gama da jar suyar ta kwashe ta zuba a food flask.
Zuwa lokacin abin da ta dora a pressure pot ta san ya nuna ta bude ta zuba jajjagen attarugu
kadan da tumaturin leda sai da ta bari ya dan bararraka san nan ta wsnke ganye ugu da bitter
leaf kadan ta zuba a kai ta kuma watsa agushi a ciki ta rufe tukunyar.
Ta dauko guntuwar doya. Miya na sauka doya ta dahu ta buga masa sakwara.
Duka duka bata fi 40 minutes a kitchen ba sai gata da wani tray din da su plate da serving
spoon ta dora kan dining.
San nan cikin san yin murya ta juya wajen Bilki tace "Anti na gama".
Nan dai maigidan ya ja bakonsa dinning. Shi kuwa bakon yayi wa abincin nan ci mara algus.
Da kyar bayan la'asar shi ma don kar masu gidan su kosa ya hakura ya bar gidan.
Ya kuwa tafi zuciyarsa cike da tunani 'yar kyakkyawar budurwar da ya gani wadda ta sa shi
karya azumi da kuma