Showing 27001 words to 30000 words out of 65424 words

Chapter 10 - FINI A UBA IN FIKI A MIJI book Complete by Hanne Ado Abdullahi .pdf

mamaki amma sai na tuna zancen wani malami
da ya ce duk wanda ya iya harshen larabci, koyon ko wan ne irin yaren a duniya ba ya masa
wahala. To itama advantage din data samu ke nan. Zainab dai na samun attention amma aikinsa Allah
ya sa yana da mataiamaka na kwarai da an samu matsala. Amma Alhamdu Lillah kwalliya tana
biyan kudin sabulu, saboda kuwa dan dai turanci daya biyu na kare yawa yana samuwa. Haka
zalika rubutu ma ana samun ci gaba. Ga kuma jajircaccen malami ga kuma daliba maikwazo sai
komai ya tafi daidai.
Yau su Momi sun dauki sama da sati hudu basa gida. Ba abin da ke hada su illa idan an kira
Momi a waya ana bukatar snacks ta yi wa Zainab waya ta bata instruction din abin da ake
nema.
Damuwarta kadan ce saboda da dama ko suna gidan ba wata mu’amala da ke hada su in dai
ba wani abu za a sakata ta yi ba. Farida ce kawai dama dama, domin ita har hira tana zama tayi
da ita. Ga kuma yawan alkhairin da ta ke mata. Domin ko wan nan shopping din da suka je sai
da ta sayo mata roll on na sure guda biyu da kuma body spray din su. Ta hado mata da turaren
splash na VICTORIA SECRET GAEDEN.
Da zata tafi kuma ta bata kayan sawa wadan da ta cire zata bayar saiti shida kuma duk masu
kyau da tsada, haka nan ba su ji jiki sosai ba. Da kuma wasu designer turararruka da kadan
suka yi kasa da rabin kwalbar, guda biyu.
Ita ma kuwa haka ta dage da kanta ta tambayi Momi kaji aka sayo tayi musu dambun nama mai
dan Karen dadi. Ta yi mata fura wacce baba Laure ta koya mata ta shanya ta bushe. Ga su

tankwa da busasshen attarugu duk ta hada musu. Har da yajin daddawa aka sayo kayin hadi
Mama hajjo ta hada mata. Ita kuma ta kai inji nika ta tankade musu shi.
Saboda haka ba wani kewar su tayi ba da ba sa nan. Balle kuma yanzu da take cloud seven
watau duniyar masoya. Ba karamar kewa Balan ta mai gwanjo yake dauke mata ba.
Kullum sai ya kawo mata ziyar da safe da kuma yamma, san nan da dare su sha waya da shi.
Ita ba sayen katin waya take ba, saboda haka bata san tsadarsa ko arahar sa ba. Sai kuma ya
kara da yi mata wayo, inda ya sanya mata dubu hamsin a wayarta, yace da ita tayi ta waya ko
yaushe MTN ne suka bata bonus na dubu hamsin din. Haka kuwa ta yarda. A wan nan rana da ya shigo da safe ya sanar da ita zai kawo abokanan sa su gaisa da ita.
Bayan ya gama koyar da ita karatu yayi sallama ya tafi da alkawarin zuwa shi da abokansa
bayan la’asar.
Nan take ta shiga tunanin me zata basu idan sun zo. Kudin da Momi ta bata ta dinga sayen
abinci tana ci ta duba taga saura dubu biyar da dari shida. Saboda dama tun da ta duba taga
lissafin kudin sai ta daukarwa kanta, da safe ta sha ruwan bunu. Da rana ta ci a gidan su Fatu
ko kuma ta karbi tuwon BabaLaure. Da daddare kuwa sai ta ci bread na sittin ta sha ruwa. Balle
kuma dama ita gwanar azumin litinin da alhamis ce. Idan tayi bude baki sai ta sayo indomie
super pack guda daya. Taci da magariba, sai ta rage kadan tayi sahur ta sha bakin shayi. Shike
nan.
Saboda ta fitar da shi kunya tayi abin da samari kance ‘a wajen gayu da girma ya fadi gara jari
ya karye’. Itama haka tayi kuddumus mutuwar kazar kuku, ta dauki kudin nan. Ta sayo kazar ta
guda daya ta dubu daya. Ta sayo mince meat rabin kilo da flour rabin kwano da kuma sauran
kayan meatpie da samosa. Ta sayo lemon bawo na dari uku, sai man gyada rabin kwalba. Sai da ta kashe dubu uku da dari
takwas. Ta duba taga abin da yai saura mata baifi dubu daya da dan wani abu ba. Amma a yau
ba abin da ya dameta irin ta farantawa Al Bashir rai.
Ta zauna ta murza meatpie.ga shi kwaben yayi kyau, sai da ta samu guda goma sha hudu.
Samosa guda ashirin. Da ta ga man ba zai ishe ta suya ba. Sai ta gasa meatpie din a murhun
gawayi saboda dan guntun gas din dake gidan kwanan su Momi biyar da tafiya ya kare.
Itama kazar tayi musu gashi mai kyau da kuma dadi. Lemon kuwa barewa tayi ta nika ablender
ta mai da shi juice.
Kafin la’asar ta kammala komai. Ta samu plates masu kyau ta saka a ciki. Kazar kuma ta zuba
aflask. Ta samu jug mai kyau ta zuba lemon. San nan ta debo ruwan sha a dispenser gidan ta
sa a wani jug din. Komai dai can a can. Balle dake ta samu sake ba wanda zai hana ta daukar
komai. Ta share verender bakin falon babansu. Ta dauko carpet ta shimfida. Bayan ta idar da sallar
la’asar ta rangada wanka. Acikin kayan da Farida ta bata wadanda ta gyara, ta dauko riga da
skirt na wani cotton lace mai kyau ta saka. Kayan suka yi mata cif kamar dama daidai jikinta aka
dinka. Ita kanta ta yaba da kyan da tayi.san nan tabi jikinta ta feshe da turare. Tana jinkiran
wayarsa ta yi murmushi ta saka hijabinta mai hannu ta nufi waje.
Su hudu ta gani, har da shi. Har kasa ta durkusa yadda ta saba gaishe shi haka tayi musu.
Suma cikin fara’a suka amsa mata. Tayi musu jagora har bakin falon. Sai da suka zauna ita
kuma ta shiga cikin gida domin hado dan entertaimaent din da tayi musu.
“where did you find this clean item” ? daya daga cikin su ya tambaya.

“kyauta daga Allah” in ji AlBashir.
“Amma fa mun wahala. “inji Mujib. “can you imagine we had to spend the whole day a kasuwar
gwanjo. Ai I promise duk sai na kai ku kun ga wajen. It was just awful”.
“For such classy babe I can spend ten years in prison”. Shi ma dayan ya fada.
“Ina ga gwara in sallame ku, ba wani amfani da zaku yi mun anan” Al Bashir ya fada.
Gaba daya dariya suka saka ganin kishinsa kiri kiri. Dayan zai bashi amsa Zainab ta fito
hannunta dauke da katon tray. Shi ya tashi da hanzari ya karbeta yana fadin “putri salju ba sai ki
kirani in dauka ba”.
Ba ta bashi amsa ba sai dan murmushi da tayi. Sai da ta zuba musu ruwa da lemo kowanne
san na aka sake sabuwar gaisuwa. Ya kuma nuna mata abokansa tare da introducing dinsu. Ya
nuna na kusa da shi yace “wan nan shine Mustapah,ga kuma Sa’ad. Sai kuma”.
Ta katse shi da fadin da cewa “ai shi na gane shi. Ba Ya Mujib bane”?
“shine ashe kin gane shi”?
Ba tayi Magana ba sai murmushi da ta dada yi. Mustapah na gutsirar meatpie yaji wani irin dadi
ya ratsa shi. Bai sanda yace "Amma dai wan nan daga Madina aka kawo shi ko”?
Gaba daya suka tuntsire da dariya. Ita dai bata shiga cikin zancen zolayar da sukewa junansu
ba. Sun taba hira kadan duk da dai ita bata cika sa musu baki ba. Balle lokuta da dama da
turanci suke Magana. Duk da bata ji duka ba, amma tana fahimtar wasu zantukan nasu.
Da ace tana da exposure, to da kuwa ta lura da yanayi jikinsu da kuma suturar da ke sanye a
jikinsu da ta gane masu kudi ne na gaske. Amma bata da wan nan ilmin. Sai da sukaci suka
koshi domin kuwa sun cinye kusan komai data kawo musu.
Mustapha ne ya sanya hannu a aljihunsa da niyyar debo kudi. Idon Al Bashir kir a kan aljihunsa
ya ganshi yana kokarin zaro dollars daga aljihunsa. Da sauri yace
“chill bro. the case is low profile”.
“but the object is classy and worth it. It is supposed to be a high profile case”. Inji Sa’ad.
“forget it it’s a long story. Thats why we had to spend a day at bend down and pick boutique”.
Duk iya kokarinta bata fahimci zancensu ba. Ta dai dauki sabbin kalmomi a kanta da niyyar idan
sun kebe ta tambaye shi fassararrsu. Ita tana tunaninta su kuma suka ci gaba da tattauna
maganganansu.
“amma duk da haka we cant leave with out giving any percuma for her”
“Yeh a I agree but make it kacik”.
Sa’ad ne ya ciro dubu goma daga aljihunsa ya ajiye mata. Suka mike tare da yi mata
sallama.shima ya mike domin rakasu.
“Putri ina zuwa”.
Tare suka fita. Sai da sukaje yaga wata katuwar thundra a fake a kofar gidan kusa da mashin
dinsa. Yace dasu. “Amma you guys almost flop my plan. Data fito ta gan ku da wan nan motar
fa. Me zaku ce “?
“very simple sai ince ni driver ne a wani gida na dauko motar gidan na fito raka abokina zance.”
Mustafa ya amsa musu.
Dariya suka saka duk kansu. Sai da suka shiga zasu tafi Sa’ad ya leko yace “When you are
done, call us so that we can come and pick you”.
“kar ku damu. Sai na dawo I will call you back”.
Inda ya tafi anan ya tarar da ita zaune a gefen verender. Shima gefenta ya zauna a gefen

carpet din da ta shimfida. Suna hada ido dukkansu murmushi ya subuce a fuskarsu. Shi yasa
hannu inda kudin suke ajiye ya dauko yace “ga sakonki, ko kin bani”.
“da kai kaya duk mallakar wuya ne”.
“Kin san me ina jin dadin duk sanda kika nuna min I have right over you dadi nake ji”.
“Ni kuma yin hakan shine babban burina a rayuwa”.
Zai yi magana tace me ake nufi da profile. Na san dai high sama ke nan. Amma ban san
fassarar case da profile ba”.
A dan firgice ya juya ya kalleta. Amma sai ya dake yace “forget it. Amma a ina kika sayo snacks
din nan ba karamin dadi suka yi ba. Kina ganin mun yi abin kunya, sude kwano a gidan surukai
harda tauna kashi”.
“Na ji dadi da kunyi enjoying abin da na kawo muku. Amma ai snacks a gidan nan ake yinsu,
saboda Momi tana na sayarwa. Kusan kullum sai nayi”.
“amma naga bata nan” ya fada cikin dan bacin rai”.
“Eh ai ko bata nan ana placing order kuma tun da dama ni nake yi, duk da haka anayi tun da
dama……” sai kuma ta kasa karasa abin data fara fada.
“Tun da dama ke kike yi. Ke ba kya gajiya ne na lura kullum cikin hidima kike”.
“Lah a ai bashi da wuya. Don dai in yi samosa da spring rolls guda five hundred kowanne in a
day”.
Bai ce mata komai, saboda ji yake ransa na suya. Ita ‘ya’yanta na karatu ta maida ta wata
baiwa. Bai dai ce komai ba, sai ma kudin ta da ya mika mata. Fir taki karba, sai da ya nace san
nan ta zari guda biyu daga ciki, san nan tace “rike sauran a wajenka”.
“Kyauta ko ajiya”
“kayan Allah ai na Annabi ne ko kuwa”.
“naji na yarda,amma please ki karbi kudin nan”.
“kayi hakuri ba na son in na maka musu, amma ka taimaka ka ajiye su a wajenka.
Washe gari kuwa wani mutum yazo akan yana sallama da ita. Bayan sun gaisa ya fada mata
cewa maigidansa ne ya aiko shi sayen snacks a wajenta. Da sauri ta gaya masa kudin ko wane.
Tana jin sa yabuga waya yake fada. Bayan yayi sallama ya ajiye ya juya wajenta yace “maigida
yace shi ga yadda yake saye kuma haka zai saya amma in har zaki sayar”. Tayi mamakin price din da ya ambata saboda abin da zai saya sai da ya ninka kudin kowanne
sau uku. Baba Laure ce ta sanya ta ta karba. Ta kuma nuna mata tayi wan nan order kanta ce
bata Momi ba. Tun daga ranar kuwa kusan kullum za a zo sayen snack. Kuma kullum tayi ciniki
bata samun kasa da ribar dubu ashirin. Ita dai bata san me saye ba. Sai dai saboda kudin da ya kara sai ta kara masa girma da kuma
yawan fillings din ciki. Amma duk da haka kudi take caska ba na wasa ba. Sai ta shiga tarasu a
wajen mama Hajjo saboda saukar da take burin yi wan nan shekarar. Da kuma tunanin saka
kanta a LEGal kamar yadda kawarta tayi. Haka zalika tana burin idan sun yi aure sai ta
taimakawa Bala ya kara jari.
Shi kuwa Bala mai gwanjo /AL Bashir, shi ke dibga mata wan nan ciniki ba tare da sanin ta ba.
Kuma da yazo bata boye masa komai ba na sabon customer da tayi da kuma cinikin da yayi
mata.
Shi kuwa a bangarensa, idan ya sayi snacks ya kan kaiwa Ummansa da kuma sisters din shi.
Kuma ko bai saya ya kai musu ba zasu tambaya, saboda a cewarsu ba su taba cin mai dadin

wanda yake sayowa ba. Shi dai bai sanar da su daga ina yake sayowa ba.


[8/7, 21:33] +234 814 948 5104: FINI A UBA
IN FIKI A MIJI
PAGE 21
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Haushi bai kara kama Al Bashir ba sai da ya ga irin garar abincin da Zainab ke shirya mishi.
Abin da ya faru, wata rana ne ya je wajenta suna hira. Ta lura da hamma da yake ta dokawa. ta
kalle shi ta ce “kamar kana jin yunwa”?
“wallahi kuwa” ya amsa mata. San nan ya ci gaba da cewa “kin san sana’ar tamu. Yau da ciniki
gobe sai godiyar Allah. So nake ma in fara daukar dealer tawa ta kaina, in daina tsinta, saboda
yin haka yafi riba. Hmmm” wata hammar ta sake katse shi.
“ina zuwa “ kawai tace da shi. Ta juya ta shiga gida. Dama ta dan tsinto kayan abinci da ribar
cinikin da ta ke yi. Tana shiga cikin sauri ta dafa masa jollof din taliya wadda ta wadata da
busasshen kifi da kuma alabasa. Sai da ta dakko dahuwa, san nan ta nika dan attarugu ta da
sweet pepper ta zuba a ciki. Ta kara kayan kamshi kadan ta rage wuta ta barta ta karasa a
hankali.
Ta yanka gwanda kanana, ta hado ta doro komai a tray. Nan dai bakin vereander Mallam inda
suka saba zama ta kai masa. Tana bude flask din wani daddadan kamshi ya bugi hancinsa. Sai
da ya shaki kamshin abincin nan san nan ya hadiye yawu.
Nan kuwa ta zauna tana zuba masa yana ci tana dada wata daga gefen plate din domin tayi
sanyi. Kafin ya gama da ta gabansa ta sake tura masa wadda ta fifita masa. Yaci abincin nan
sosai. Sai da ya gama ta zuba masa ruwa ya sha.
Ta tura masa plate din gwanda, yana sha sannan tace “kuma dealer da kake son dauka da
tsada”?
“Kai tsadar ma. Tana kaiwa dubu saba’in zuwa da biyar”.
“idan nayi wani abu kayi alkawarin ba za kayi min musu ba”
“come on don’t trick me ki sani yin abin da yafi karfina”.
“Allah nayi alkawarin ba zai fi karfin kaba”.
“To shi ke nan nayi”?
Kudi ta ciro daga cikin hijabinta kashi kashi. Tace “taya ni kirga wan nan”.
Ya dinga ware su yana hadawa. Sai da ya gama hada su tsaf san nan ya kirga. Dubu dari da
sittin da shida da dari biyar ya samu. Ya gaya mata san nan ya mika mata.
“barsu dai a wajenka. Lissafi zamuyi. Bani twenty daga ciki”.
Ya kirga ya mika mata. San nan ta sake cewa. “ka sake ware min sha biyar din ka bani”. Ya
sake yin yadda tace.
Yana bata yana fadin
“lallai hajiyata ashe kudi gareki haka. Shine baki aika an kawo miki security ba”?
“meye security”.
“sorry tsaro nake nufi. Ko da yake kina da masu tayaki zama a gida saboda haka ba wani tsoro
ma da zaki ji.
“Ka manta ne amma tun farko na sanar maka ni bana jin tsoron zama ni kadai. Na saba zama ni

kadai a gidan nan, ba tare da kowa ba”.
Da hanazari ya maida kallonsa wajenta. “ban gane kin saba zama ke kadai ba. Kina nufin da su
Momi suka yi tafiya ba wanda ya zo tayaki zama? Da ki ka gaya min hakada farko na dauka
tsokanata ki ke yi, ko kuma za a turo masu tayaki zama daga baya".
Ba tare da nuna damuwa ba tace
“Mh mh ni kadai ce”.
Sai da ya daga ido ya kalli gidan san nan yace “yanzu duk girman gidan nan ke kadai ce, ba
kowa a cikinsa”?
“lah to meye ai na saba. In dai nayi addu’a ba tsoron da nake ji”
Muryarsa can kasa yayi zagin da bai san sanda ya kubuce ya fito daga bakinsa ba. “bloody
awful people” ya furta.
“Sorry Magana kake ban ji me kake cewa ba”.
Nan da nan ya waske yace “mh mh ina mamaki ne kawai saboda ni har yanzu na kasa rabuwa
da mamana. Ga dakina ga nata. In fita kofar gida ma na kasa, saboda tsoro”.
Dariya tayi tace “wan nan kuma ba tsoro bane shakuwa ce”.
“eh amma ni kin yi min laifi. Tun da nake zuwa baki taba bani ummanmu a waya mun gaisa ba”.
Nan da nan yanayin ta ya canza alamun damuwa kadan ya bayyana a fuskarta. Ta sunkuyar da
kanta tana wasa da yatsun ta. Tace “kayi hakuri nima bani da numberta shi yasa”.
“yaya zaki ce baki da number mahaifiyarki”?
“eh to dalilin ne ya faru. Rabona da ita na kai ten years. Ba ita ba rabona da inje Kera ma haka”.
Wani irin tausayinta ne ya tsirga masa. Nan ya dinga bugar cikinta cikin wayo har ta sanar da
shi inda kakanninta da kuma Umman ta suke.
Sai da ya gama digesting wan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login