Showing 45001 words to 48000 words out of 65424 words

Chapter 16 - FINI A UBA IN FIKI A MIJI book Complete by Hanne Ado Abdullahi .pdf

jikinsa kamar za a sace ta. Haka lokacin da za a fita zuwa Minna a
karamar motar suka tafi kuma ta wani titin daban wan da duk travelling agency su ne ya yi musu
organizing as part of their VIP package. A nan din ma a Camp A ya kama musu tent su biyu kawai sai kananan gadaje guda biyu a ciki
da kuma dan karamin bandakinsu attache to the room. Babu wata wahala data fuskanta,
saboda ba kananan miliyoyi Al Bashir ya saki ba domin ta samu easy and comfortable Hajj.
Ranar da suka yi jifa na farko ranar babbar sallah ke nan ranar suka shiga Macca domin yin
dawafin aikin Hajj da kuma sa’ayi. Bayan sun kamalla jifa na biyu da na uku suka dawo hotel
din su dake daf da harami a Zam Zam towers.
Da magariba suka shiga ka’aba suka yi sallah. Sai da suka yi isha da shafa’I da wuturi. Ya kuma
kara da wata nafila da ita dai ba ta san ta meye ba. Ya dade yana addu’a wacce ta fuskanci
rayuwarsu da ita yake tayi wa wan nan addu’ar a gaban dakin Allah. Bayan sun fito suka nufi
inda zasu ci abinci. Abu daya ta lura dashi yau wata irin annshuwa yake ji a cikin ransa. Bayan sun koma masaukinsu, ita ta fara shiga tayi wanka san nan shi ma ya shiga. Sabanin
lokutan baya yau wata irin silk negligee ya ajiye mata a kan gado. Ita data daga ma ta dauka
shimi ce. Ba ta san ta meye ba ta mayar da ita ta jiye, ta dauko zulumbuwar rigar da ta saba
sakawa ta saka. Tana gyara gashinta ya fito daga wanka. “ya haka”? ya tambaye tare da kai kallonsa wajen rigar da ya ajiye mata.
Bata kula shi ba ta ci gaba da abin da take yi na kokarin gyara inda zata kwanta, wanda tun da
suka zo Saudiyya kullum a kan couch din dakin yake kwana ya bar mata gadon.
Ta ci gaba da kokarin shimfida masa quilt da kuma pillow domin yaji dadin kwanciya. Ya dan
daure muryarsa alamun ba wasa yace “ke ba dake nake Magana bane kin yi banza da ni”.

Ta dan tsorata jin yayi mata Magana da muryar da bata taba jin yayi zance da ita ba.
“Wai da shimfida nake kokarin yi maka”.
“ban saki ba, ba kuma naso. And kafin raina ya baci ki cire wan nan buhun da kika zuba ajikinki
ki dau kayan da na ajiye miki ki saka”.
Ta kai kallonta kan rigar amma ta kasa dauka. Tsawa ya sake daka mata “wai ba Magana nake
miki ba”.
A firgice ta dau rigar ta shiga bandaki a guje. Dariya ya saki kasa kasa ganin yadda ta tsorata,
amma ba ya son bata fuskar yi masa musu sai ya dada shan kunu. Ta sa riga amma ta kasa
fitowa, saboda haka da taji alamar murda kofar yana fadin “ba zaki fito bane” a tsorace ta dau
bath robe din data cire ta zurma ta dora a kan night gown din data saka, wacce ta bi ta lafe a
jikinta ta fitar da duk wani asirin kyau da ta boye cikin hijabinta.
Yana ganinta haka bai san sanda dariya ta so kubuce masa ba. Shi ya karasa inda ta tsaya yan
fadin “to karaso mana, na rasa wan nan sanyin naki na yau na menene. Ni ne fa Balarabenki ba
wani ba”.
Ta bayan ta ya tsaya ya rankwafo ta bayanta. Hannayensa ya saka ya cire nata daga rikon rigar
wankan da tayi. Ya salube ta, san nan ya tsaya ya na kare mata kallo, wanda bai taba yi mata
irinsa ba sai yau din nan.
Allah ya sani da kyar ya iya karasa alkawarin bakacen da yayi wa ubangiji na cewar idan har
Allah ya sa ya auri Zainab zai daurewa zalamarsa har sai ya kawota gaban dakin Allah san nan
komai zai kasance tsakaninsu.
Haka ya faru ne sakamakon wata hira da suka taba yi shi da ita. Tambayarta yayi yace “Putri a
duniya wacce kasa kike da burin zuwa a rayuwarki”?
Da wani irn excitement a fusakar ta tace “ai ni ba inda nake son zuwa irin kasa mai tsarki. Ranar
da duk na ganni a garin macca da Madina ban san irin farin cikin da zan yi ba. Kullum idan su
Farida suka je suka dawo suna bani labara sai in ji kamar in yi tsuntsuwa in je”.
“Amma ya akayi suka je ke ba ki samu zuwa ba bayan kece babba”.
Kasa tayi da murnarta and all the excitement left her voice. Cike da rauni tace “saboda ni bani
da kokari bana cin jarrabawa”.
Ya tausaya mata matuka. Ganin yadda take da ilmin addini da kuma yadda take jin larabci ya
san kawai muguntar matar gidan ce ta hana ta zuwa. Wan nan shine dalilinsa na yin wan nan
bakace.
Ni da na ga shiru ba a fara honey moon ba, har na tsorata na dauka ko maganar MomI ce ke
son tabbata, ashe shi baka ce ne kansa. Ya kai minti uku yana kare mata kallo. Wata irin kirar
jiki gareta da shi dai a iya yawonsa bai taba ganin perfection irin nata ba.
Da yake ganinta cikin hijabi, ya dauka flat take, ashe all the curves are in the right places.
Jikinta so beautiful. Da ya kai hannunsa kuwa ya taba skin din jikinta, sai da ya saki wani irin
numfashi. So soft and silky. Taushin hannunta ya dade yana bashi mamaki. Ga shi kullum cikin
aiki take, amma hakan bai sa hannayenta tauri ba, saboda bata rabo da shafa man kadanya a
hannu nata.
Ya saba da jin kamshin jikinta, amma hakan bai sa yana jin ya gaji da shaker sa ba. Wajen
wuyanta ya tsaya yana shinshinarta. Ya kuwa shaki kamshin ta sosai, kafin ya sauke labbansa
akan nata. Take jikinta ya dauki rawa na abin da taji da bata taba jin irinsa ba.
Ta saba da dan light kiss da yake mata, amma wannan French kiss din is different. Take jikinta

ya dauki rawa. Kafafunta suka kasa daukarta. Jin zata zube a wajen ya dauke ta kamar
karamar yarinya, ya shimfideta a kan gadon, shima ya bita .
To alhamdu Lillah kazafin Momi ya tabbata karya, saboda a wan nan rana ya tabbatarwa da
Zainab cewa shi lafiyayyen namiji ne mai tsananin kwazo kuwa. Saboda asuba ita dai ta kasa
ko motsi, amma shi ya daure a gaggauce ya samu raka’a daya a masallaci.
Sai da ya dawo san nan ya taimaka mata ta gyara jikinta tayi wanka. Sallah dai bata samu ba
sai bayan shida na safe. Ita dai duka tayi sanyi saboda bata tsammaci haka daga gareshi ba.
Yayin da shi kuwa murna kamar ta zautar da shi. Gaba daya ya rude mata sai rawar jiki yake.
Ga shi ya hana ta matsawa ko nan da can kamar za a sace ta. Kwana biyu kawai suka kara a Macca suka shiga Riyadh wajen wani abokinsa da suke
kasuwanci tare a nan kasar. Na ma dai amarcin da suke ragargaza ya fi komai. Da zasu tafi
kuwa kyautar sarka babba da awarwaron gwal guda shida suka bata.
Daga nan suka wuce China saboda shi kansa ya san yayi neglecting aikinsa. Gidansa na
zhoungou anan suka sauka. Bilkisu taji dadin ganinta. Shima dai nan din aiki rabi da rabi ne.
saboda baya sama da awa uku a factory bai zo inda take ba. Ta dai sha tsokana wajen Bilkisu.
[8/8, 22:27] +234 814 948 5104: FINI A UBA
IN FIKI A MIJI
PAGE 29
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Soyayya dai ana rangada ta tsakanin Al Bashir da Zainab. Ga karatun ta na koyon turanci da
suka dage dashi. Kullum kafin ya fita zai koya mata newa words da spelling da pronunciation
dinsu. Haka zalika zai bata example yadda zata yi constructing sentence da su.
San nan zai ba da dokar lallai kafin ya dawo ya tarar ta haddace su. Kuma hakan take yi. Ba ta
shara bata wanke wanke ba wanki ba guga. Saboda haka sai ta samu enough time to face her
studies. Tana kuma da wani web site wanda ita ta lalubo shi da kanta, bai ma san ta kai wayon
haka ba. Duk abin da ya kakare mata a wajen za ta duba ta ga yadda zata gyara. A yau da ya fita bai dade ba ya dawo, saboda yana son suje shopping. Tare suka shiga mall din
suka nufi wajen kayan mata. Bawan Allah nan ya sai mata kayan mutunci , yaki sai su dogon
wando da su three quarter and other revealing out fits yake zabar mata.
Da kyar ta samu a wani shagon larabawa ya saya mata dogayen riguna masu kayan gaske.
Suka shiga wajen undies. Kunya ce ta kamata ganin shi da kansa yake duba inner wears. Ya
gane yanayin data shiga amma sai ya share kamar bai gani ba.
“Putri wane size zamu dauka”? ya tambayeta lokacin da ya dakko wata shudiyar rigar ciki mai
dan banzan kyau kamar ka saka ta a saman riga. Kudinta ba zai kasa dubu ashirin ba kudin
Nigeria.
“putri I am talking to you tell me your size”.
Ringin din wayarta ne yayi saving din ta daga embarrassing situation data shiga. Tana dubawa
taga number Fatu. Wata ajiyar zuciyar ta saki da ta tuno mastalar da take ciki. Ta fara mata
zolaya, ta tsai da ita ta kuma juya harshenta cikin larabci tace “ke ki tsaya akwai matsala”.
Daga can ta amsa mata “wacce irin matsala me ya faru ina fatan ba ke da bala bane”.
“ni da shine mana. Ya kawo ni sayen kaya yanzu muna shagon undies yake tambayata size din
na. Kin san kuma kullum kwance ake bani saboda haka lambar duk ta koke ban san size din ta
ba. Ni kuma kunya nake ji in sanar da shi hakan. Kuma kin ga na gwanjo ma da muke saye

suma ba lamba a jikinsu. Ban san yadda zan yi ba”.
Dariya tayi sosai san nan tace “na tuna size dinki kin tuna a lefen kawarmu Salma da aka baki.
Ki ka ce baki taba jin dadin saka ta irin ranar ba saboda kin samu perfect size dinki”.
“Wai Allah na gode maka. Size nawa ne”?
“kice masa 38B’.
“Shi ke nan na gode zan kira ki idan na koma gida”.
Tana juyowa suka hada ido da shi ta saki murmushin wanda ya katse lokacin da ta ji muryarsa
cikin larabci yana fadin “da ma baki tona mana asiri wajen Fatu ba. Mu shiga fitting room in
gwada miki da kaina”.
Da sauri ta juya zata fita daga shagon saboda tsananin kunya data kamata. Dankota yayi yana
kokarin tura ta cikin fitting room din wanda ke kusa da su.
“ka yi hakuri zan fada da kaina”.
Yana mata cakulkulin wasa yake fadin “zaki kara gulmata da wani yare”?
Ita kuma tana dariya tana fadin “a’a kayi hakuri ba zan kara ba”.
Haka dai a shiririce kamar wasu kananan yara suna tafe suna wasa a haka aka gama shopping
din. A wajen sayen takalmi kuwa shi ya tsuguna a kasa kusa da ita. Duk takalamin da aka kawo
ya dora kafarta akan cinyarsa ya gwada idan ya ga yayi masa su saya.
Amma fa sun saya da yawa. Domin yadda take da karuwan jiki haka take da karuwar kafa. Duk
wanda aka sa sai kaga yayi mata kyau. Har mai shagon ya tambaye shi da turanci saboda ya
naji akan wai ita din model ce.
“yeh a very expensive one. But only I get to see her in her modelling outfit”. Ya amsa masa.
Farkon zuwanta har mamaki take ita kanta da yadda mutane ke tanka kyawunta. Ga shi dai a
cikin after dress take, amma hakan bai hana kyawun ta fitowa ba.
Shi da kansa in ya zauna ya dinga mata kirari ke nan. Ya kalleta ya ce “my beautiful princess.
Elegant while covered, appealing idan ta sauke abaya, idan kuwa a ka zarce haka, you drive
me crazy”.
Sai da suka huta suna cin abinci tace “yanzu sabo da Allah ashe ka iya larabci amma kana jin
mu ni da Fatu kaki nuna mana. Da ma zaginka muka yi fa ai da ka bar mu da jin kunya”.
“haba putri kin kasa gaya min kina sona, sai kuma na yi sa’a kin iya gayawa wata da harshen
da kike tsammani banji, and you expect me to disclose my secret no way. Yau ma sa’a kika ci.
Maza ku canja wani yare mu gani ke da ita”.
“a’ai an gama wan nan game din”.
Bayan sun kwanta da daddare yake shaida mata gobe zai fita da wuri kuma zai dade a factory.
Bayan ya fita ta dauki sugar da lemon tsamin ta ta dafa ta saka a fridge yayi sanyi, saboda tana
son yin halawa.
Sai da ta shiga sauna bath din da ke bandakin gidan ta turara kanta san nan ta fito bayan ta
goge danshin turiri ta fara dana wa jikinta halawa nan tana fizgewa. Sai da kuwa ta dauke duk
wani gashi dake jikinta banda na gira da kai. Bayan nan ta dauko dilka cream da ta sayo a
shagon larabawan nan ta muttsike jikinta da shi. Duk bata fi tara na safe ba ta gama da wan nan. Sai ta dakko sole tape din data yanka jiya da
daddare akan chopping bord dinta. Sai da ta saki murmushi da ta tuna yadda ya dameta da
tambayar me zata yi da razor da sole tape da ya ga tana masa wani yanka kamar bille.
Murmushi kawai tayi bata ba shi amsa ba. Na kafarta ta fara sakawa san na ta dawo hannu ta

saka wanda tayi wa yankan hula daidai saman faratunta na hannu, da ga nan kuma ta nada shi
siri siri kamar spring. Shi ma ta yabe da lalle
Ta sa leda tadaure ko ina saboda kar yayi saurin bushewa. Barcci tayi ba ta farka ba sai bayan
uku. Ta cire lallen wanda tun daga saudiyya tayi dakonsa shi da mahallabiyar da ta sa masa.
Dau kuwa ya kama. Hakan ya dada fito da asirin kyawun hannaye da kafafun nata. Lokacin
data shiga wanka kuwa saboda santsi da jikinta yake yi, haka nan ruwa ya dinga gangarewa
daga jikinta.
Tana idar da sallah ta tsantsara kwalliya da daya daga cikin kayan da suka sayo. Dogon wando
jeans da kuma T-Shirt wacce ta dada kawata mata figure dinta. Bai shigo ba sai bayan
magariba, tana zauna a kujera ta dora kafarta kan center table tana kallon TV.
Yana bude kofar cike da gajiya yaji ya wattsake saboda arba da yayi da wata jar kafa da aka yi
wa wani rodi rodi kamar kwale. Sakin jakarsa yayi ya dumfare ta. Dagota yayi tana rike a
hannunsa yana juyata saboda ya karewa kwalliyarta kallo.
“woh! My putri gaskiya kin biya ni. Nawa za a caji wan nan kwalliya haka”?
“idan ka bani kyautar zuciyarka, ka biya ni”.
“kin dade da samun wan nan putri, nemi wani abu daban”.
Da kyar ta lallaba shi yayi wanka sukaci abinci. Ko shi abincin akan kafarsa ya dora ta yana
feeding dinta. Lokacin da suka je bacci kuwa sai da ya kusa zaucewa saboda santsin jikinta
kawai.
Allah ya sani zainab tana tsananin alfahari da kaunar da Al Bashir ke nuna mata. Bata taba
sanin somebody can give so much love ba sai a wajensa. Sai da suka dauki wata biyua China
ya samu ya rage ayyukan gabansa, san nan suka biya ta England can ma dai dan wani abin na
sana’arsa ya dai daita. Suka shiga Turkey suka kwana biyu, san nan suka yada Zango a Dubai.
Wanda suka yi kwana goma kacal.
Sama da wata uku ba sa Nigeria, san nan suka dawo gida. Ba wani ba ita kanta idan ta kalli
madubi bata yarda itace saboda wani irin beuty data kara, balle shi uban gayyar da ko barci
take birge shi take yi.
Driver ne ya dauko su daga airport inda bai ajiye su ko ina ba sai gidan su Al Bashir. Amma
maimakon su shiga gate din main house sai taga sun shiga a smaller version of the main
house.
Duk da bata kwana a gidan ba, amma she has a good memory of the environment. Inda gidan
yake yayi kama da filin da aka yi yinin bikinta. Ganin kamar tana tunani, ya saka shi cewa “sorry
putri I remember cewa kin ce zaki iya zama da mamana shi yasa na gina gida gefenta, because
having the two of you very close to me zai sani in kasance cikin farin ciki, amma ba zan takura
ki if you have any reservation sai mu canza waje”?
A dage ta juyo ta kalleshi. San nan tace “ashe kai har zaka ga darajar matar da zata ki zama da
mahaifiyarka. Ni Ya Bala ne alkawari muka yi zai ajiye ni kusa da ummansa. Idan nayi laifi tayi
min fada. Idan na kuskure ta gyara min. ni kuma in dinga binta sau da kafa ina mata ladabi da
kuma koyon lamuran rayuwa a wajenta, saboda ko ba komai ta zama role model a idona ko don
Haifa min mijin mai cike da tarbiyya da halin kwarai da tayi”.
Ganin driver ne kawai ya hana shi rungomata jikinsa.
Itace ta ce da driver “mu fara shiga main haouse tukunna”.
Ai kuwa su Umma na jin takun motarsu duk suka fito ita da yayyensa gaba daya cikn murna, sai

fadi take “ga bakin China sun dawo. Kuma dan uwana ba sai ku karasa da ita gida ba ta huta
tukunna”.
“umma is not my fault ita ta fada akan sai tashigo nan san nan zata gida”.
Nan dai aka zauna gaisuwa ta musamman. Ruwa kawai umma ta barsu suka sha a wajenta ta
kora su gida.
Sai da hawaye ya zubo a fuskar Zainab da taga dankareren gidan da wai nata ne.
Dan wani zaure suka shiga daga tsakiya, wanda ta nan kofa biyu ce daya ta shiga dakin baki da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login