Showing 39001 words to 42000 words out of 65424 words
Chapter 14 - FINI A UBA IN FIKI A MIJI book Complete by Hanne Ado Abdullahi .pdf
na gaya maka lakanin da malamin nan ya bani kamar yankan wuka yake. Amma ba yanzu zan
karbi ladan aiki na ba sai nan gaba, da kuma tarar kin sanar da mu sunanka na asali har kana
sakamu suma”. Hararar wasa ta sakar mata. Ita kuma ta ci gaba da fadin “ai yanzu ka gano matsayin da kake
mitar an ki a nuna maka. Tun da yau dai ka tabbatar in ba kai ba sai kabari. Tun da rijiya ma
idan an shiga a iya fito da mutum da rai”.
“Ni dai bani da abin cewa sai godiya”.
“za dai kazo godiyar amma ba yanzu ba. Ku zo daddy ya aiko a kira ku”.
Hijabin ta ta mika mata suka fito suka nufi gidan su Zainab cike da farin ciki.
Anan kuma suka tarad da iyayensu da kuma Alhaji Bashir da Alhaji Usman, wadanda sakon
kiran uban amarya ya same su lokacin da suka fita za su raka his excellency, wanda zai wuce
wajen dayan daurin aren wanda shine ya fito da su dukkansu.
Sai da motarsa ta tashi san nan suka koma cikin falon, inda suka samu hajiya Rumaisa tana ta
gursheken kuka da ikirin dole a raba wan nan aure. Baffan Nene ji yake kamar ya tashi ya rufe
ta da duka. Shi Alhaji Bashir ne yace a bata damar ta fadi dalilin ta na son raba auren
Tace ba zata fada ba sai an kira Al Bashir yazo. Ana wan nan takaddama shine aka tura
kiransu. Suka shigo cikin farin ciki wanda ya gaza boyuwa a fusakarsu duk su biyun.
Alhaji Usman ne yace “hajiya gasu sunzo fada mana dalilin da kike son sai an raba su”.
A razane duk suka dago idonsu su ka kalleta watau ango da amaryar da ba su san kiran na
meye ba. Allah ya sa tare suka shigo shi da Mujib. Kamar daga sama yaji muryar Momi na fadin
“saboda ya yaudari ‘yata, shi yasa nake son a rabasu”.
“Wacce yaudara yayi mata”? nan kuma Baffan Nene ne ya fada cikin bacin rai.
“Ya san shi ba namiji bane ya yaudareta ya aureta”.
Dukkan su na falon haka suka ji saukar zancen Momi kamar dukan guduma
[8/8, 21:57] +234 814 948 5104: FINI A UBA
IN FIKI A MIJI
PAGE 26 BY HANNE ADO ABDULLAHI
Dakin ya dauki shiru na dan wani lokaci. An rasa mai abin cewa. Shi kuwa Al Bashir sai
kwankwasar daben kasa yake yi da knuckles din shi. Mujib da ya san shi tun suna yara, ya san
alamun kurewar bacin ransa ke nan. A hankali ya dora hannayensa a kan nasa ya dan matsa.
Ya dago ya kalle shi idanuwansa jawur kamar an zuba masa gauta a ciki. Girgiza masa kai yayi
alamar yayi hakuri. Ga wani uban gumi da ya wanke shi sharkaf duk da sanyin falon.
Ita kuwa amarya dago kanta tayi ta kai kallonta zuwa angon, tana mamakin furucin Momi.
Tunani ta ke a zuciyarta “to in ba namiji ne ba shi menene? Mutum ga saje ga kira irin ta maza
murya irin ta maza sutura irin ta maza kuma ace ba namiji bane”?
Wan nan shine tunanin da zuciyarta ke wassafa mata. Bata san sanda wata karamar dariya ta
subuce mata ba, saboda sakarcin Momi da take gani. Tayi saurin kunshe dariyarta kar iyayenta
da kakanninta su jiyo ta. Amma tabbas bata ga ta inda za a ce ya balarabenta ba namiji bane.
Dogo mai kyakkyawar kira ta mazan kwarai, kuma momi ta kalle shi tace ba namiji bane. Shine
abin da zuciyarta ta ci gaba da wassafa mata. Tana cikin wan nan tunani taji muryar Baffan
nene yana cewa “Rumaisa kiji tsoron Allah. Ta yaya kika san wan nan maganar”?
“Baffa tsoron Allah ne yasa na furta wan nan maganar a gabanku sabo da bana son cutar da
Zainab”.
Muryar Al Bashir can kasa yace “na nawa kuma”?
Mujib ne ya yi saurin sakin gyaran murya wadda ta dakushe kalaman Al Bashir ba wanda yaji
mai yace sai shi kadai. Hanakalinsa bai dada tashi ba sai da yaji muryar mahaifin sa yana fadin
“Balarabe kaji tsoron Allah. Idan har ka san ba ka da lafiyar sauke hakkin auren yarinyar nan ka
shaida mana tun da wuri kar ka cuce ta”? Dago idonsa yayi ya sauke su akan mahaifinsa, wanda shima ya hango tsananin bacin ran da
ke tare da shi, amma ba ya son ya zama mai son kai a tsakanin ma’auratan yafi son kowa a
bashi hakkinsa.
Baffa ne ya sake cewa “Rumaisa ke muke jira muji dalilin ki na cewa shi din ba namiji bane”
“Mh ai Baffa zancen ya zaga garin nan, tun da ba wanda ya taba ganinsa da wata yarinya ya
nuna yana sonta, shi ne nima na samu labari”.
“ita ke nan iya hujjar da kika dogara da ita”?
“ka ga baffa bari muji daga bakin yaron, kar a cuci yarinya” Alhaji Usman ya dada fada.
“Haba Alhaji saboda kawai yaro ya kame kansa baya shiririta sai a dau kazafi a lankaya masa.
Kai AlBashir ka kare kanka mana. Tun da ita bataji kunyar zargin ka ba, kai ma kar kaji kunyar
maida mata martini”.
Ya dago kansa ya galla mata harara kamar zai tashi ya rufe ta da duka saboda tsabar takaici.
San nan murya can kasa yace “Baffa ni bani da abin cewa sai dai a bani lokaci shi zai tabbatar
da gaskiyata ko karyata”.
“Wan nan hakane” in ji Baffan Khadija.
“ai kuwa wallahi ba zai yiwu ba. Ba zan zauna ina gani a cuci yarinya ba. Dole ne ya sake ta”.
Ta fada cikin muryar kukan da ban san ko na karya bane kona gaskiya.
Baffa Nene ne ya sake harzuka ya mike tare da fadin “Allah ya sa kin gane ba wanda ya isa
sakin auren sai mai shi da kansa ba. Bani ba. Ba ke ba, ba kuma shi kansa mahaifin yarinyar da
ya zuba miki ido kina ciwa mutane mutunci ba”.
“Don Allah Baffa kayi hakuri. Duk maganar bata bacin rai bace kayi hakuri”. Alhaji usman ya
fada.
Take ya juya harshe cikin fulatanci yake fadin “kin so nakasa yarinya Allah ya kareta shine kika
bullo ta nan”. Ya juya inda AlBashir ke tsugunne yace da shi “kai mike kadauki matarka ku bar
gidan nan. Aure ni na baka shi, ba kuma wanda ya isa ya karbe shi daga wajenka. Wuce ku
tafi”. Yana fadin haka ya nufi hanyar fita. Har ya kai kofa ya dawo inda Zainab ke tsugunne ya daga
ta ya fita da ita ya dago hannuta ya hada dana Al Bashir yace ban yarda ka tafi ka barta a nan
gidan ba. Yanzu ku kama hanya. Kaje duk inda Allah ya hore maka ka ajiye matarka”.
Aikuiwa yana mika ta, caraf ya sa hannu ya damke nata. Shi kuwa yayi ficewarsa daga falon
yana fadin “ina Mallam Usmanu yazo ya mayar dani in rabu da ganin wanan bakin cikin”.
A tare duk suka fice daga falon, suna jiyo muryar Momi tana tashin hankali. Su dai suka fita
suka barta da mijinta wanda tun da aka fara Magana bai ce komai ba, saboda tsoron kar
Baffansa ya tsinka shi idan har ya goyi bayan matarsa. Shi ma kuma wannan lokacin ba zai goyi
bayan nata ba. Saboda ko banza His Excellency ne madaurin aure. Wanda hakan ya sa zai
dada samun kusanci da shi.
Shi wannan aure na Zainab ai an taki sa’a. wadan nan dalilai suka sa shi yaki siding da kowa.
Shi ma a nan ya tafi ya bar Momi tana ta hargowarta.
AlBashir rike da hannun Zainab cikin rakiyar Mujib suka nufi motarsa Mercedes benz G63. Sai
da ya zaunar da ita a kujerar baya san nan ya zaga daya gefen ya zauna, yayin da Mujib ya
shiga mazaunin direba.
Ba wanda yace da kowa komai a cikin motar sai sauke zazzafar ajiyar zuciya da Al Bashir yake
yi. Zainab ta saci kallonsa sai kawai zuciyarta ta raya mata wai gashi nan daure da dankwali da
zani da riga irin na mata. Picture in her mind is so funny saboda haka ba ta san sanda dariya ta
kwace mata ba.
Sai a san na shi ma ya saki ransa ya shako wuyan ta cikin wasa yana fada “dariyar me kike
min”?
Muryarta can kasa cike da dariya take fadin kayi hakuri, hotonka na hasko da gwaggwaro da
high heel shine dariya ta kamani”.
Tare suka dago ido suka kalli juna shi da Mujib sai a nan suka fahimce Zainab ba ma ta san
accusation da Momi tayi masa ba. Ita kallon physical halittarsa kawai ta ke and not something
else. Dariya suka bushe da ita a tare.
Mujib yace “yaya ina zan kaiku for your honey moon ko mayi saurin proving Momi wrong”.
Kafin ya bashi amsa, wayarsa tayi ringing sai da ya daga wayar san nan ya tuna da
appointment din da yake da shi da wanda ya kira. Ya na dagawa yace “yi hakuri ranka dade.
Shaf na manta I was coming to see you, wani lamari ne ya sha kai na”.
Ya dan yi jim alamar sauraro san nan ya sake cewa “a’a gani nan zuwa yanzun ma kuwa”.
Ya kashe wayar ya maida cikin aljihunsa. Yana murza hannun Zainab dake rike a hannunsa ya
ce da Mujib “please lets go to immigration office I need to get a passport done”
“Amma na dauka yau public holiday they wont be around”?
“no suna nan because of hajj operation they work round the clock”.
Mujib zai sake Magana ya hango Al Bashir ta cikin madubi yana rada wa matar sa wata
Magana wadda ta sata dariya, sai kawai ya fara waka yana kida, da steering motar. Yana fadin
“ranar muke jira yau
'nima da tamburana gani na zo’
'ango muke yiwa shi
'Muyo rawa da murna anyi aure’
Gaba daya dariya suke masa na ganin ya daddage ya na ta zuba waka. A haka suka isa farm
center inda passport office yake. Duk da wajen a cike amma an kaisu VIP room dinsu. Ita dai
biye take da su tana mamakin yanzu hoton passport kawai sai an zo wani waje. Da sun yi
Magana da ko a nan unguwarsu an dauka. Amma sabanin yadda tayi tunanin wannan hoton daban ne, saboda har su yatsun hannu aka
dinga daukar hotonsu. Bayan an gama sun fita sun shiga mota Mujib yace “ango har yanzu
baka sanar da ni inda zan kaiku ba. Kaga dai auren da muka taru domin sa kayi hijacking, tun
da dai ni da kai ba za mu iya attending ba”. “You know what, da nayi niyyar mu wuce gida, but on second thought why should I deny may
deer and her mother the right to enjoy and cherish this moment. So I think mu wuce Garko
kawai’”.
“kaga idan kai da Zainab murnar angwancewa ta sa kun mance komai. Ni yunwa nake ji,
saboda haka kafin mu wuce find me some thing to eat please”.
A wani haddaden restaurant suka tsaya. Nan fa ya sha daga da Zainab akan taci abinci amma
ganin sa da kuma idon Mujib ya sa ta kasa ci. Ya juya ya kalli Mujib yace “please dan bamu
privacy mana”.”
"yanzu kuwa” ya fada yana mai mikewa domin kuwa shi dama ya gama .
Yana fita ya jawo kujerarsa daf da tata wadda har kafadarsu tana gogar juna. Ya debo abinci a
spoon yace “Ha’ ta so ta noke,amma bai bata damar yin haka ba, sai dai ma threat din dura da
yayi mata. Sai da ya tabbatar ta ci yadda ya kamata san nan ya kyaleta. Kuma har ya tabbatar
ta koshi bai daina bata da hannunsa ba. Ita kam kunya ce ta lullube ta na ganin wani Balan da
bata san da shi ba.
Suna shiga mota taga sun dauki hanyar Maiduguri. Da sauri ta kale shi tace “ba gida zaka mai
da ni ba”.
“a’a garko zan kai ki wajen umman Hafsa”.
“Wai gashi ban taho da kaya ko daya ba. Da zaka yi hakuri kayana da na dinka suna gidan su
Hafsa da naje na dauko”.
Wani irin kallo ya watsa mata. San na yce “saboda ni kuma bani da wayo. In koma filin dagar
yakin da na sha da kyar. Yau dai kiyi managing da na Hafsa, gobe in sha Allahu zan kawo miki.
Haka nan suna hirar su cikin annashuwa suka isa gidan mallam Usman. Nan kuwa suka shaida
masa akan cewa kawo Zainab suka yi wajen mahaifiyarta ta yi mata irin bikin da ta ke so.
Kwarai daga shi har hajiya Khadija sun ji dadin abin da suka yi musu. Nan dai suka yi sallama
suka juya saboda suna son halartar bikin da dama shi suka taru domin sa.
Washe gari kuwa sai gashi da kayanta da Fatu da Kuma Mama Hajjo wacce ta hado kayan
gyaran jiki rankatakaf da turarurruka masu kamshi domin gyaran amarya. Anan kuma mallam
Usman ya sanar da shi shawarar da suka yanke ta kai biki kera.
A gida kuwa Momi kamar wata zautacciya ta koma saboda tsabar bakin ciki. Balle data gano
waye mijin asalinsa da matsayinsa sai da taji kamar ta hadiyi zuciya ta mutu. Su dai masu aure
sun samu an zarga musu shi ita kuwa mai bakin ciki sun barta da abinta.
[8/8, 21:58] +234 814 948 5104: FINI A UBA
IN FIKIN A MIJI
PAGE 27
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Zainab na ganin Fatu da mama Hajjo ta taso ta rungume su cike da murna. Sun tsaya zasu fara
kaudi Hafsa ta shigo da sakon Al Bashir yana son ganin Zainab. A babban falon Abbansu ta
same shi, ya zuba kwalliya sai tashin kamshin yake.
Da sallama ta shiga, yana jin sallamarta ya dago suka kalli juna. Bai sani ba ko idanunsa ke
masa gizo amma sai yaga ta kara wani kyau na fitar hankali ga kuma wa ni irin serenity in her
face da ba zai iya describing ko na meye ba. But to him she look more at peace.
Abin da bai sani ba, kwanciyar hankali yanzun nan take bayyana a yanayin mutum kamar
yadda tashin hankali yake bayyana. Duk da kunya ta dan fari dake tsakanin Khadija da Zainab,
amma tabbas sun ji dadin dan kankanin lokacin da suka samu sakewa da juna.
Ajiyar zuciya ya saki, san nan ya mika mata hannunsa alamun suyi masabiha yana fadin
“assalamu alaikum”.
Ita ma nata hannu ta mika masa alamun amsar musabihar tasa tare kuma da amsar sallamar
da yayi mata. Yana damkar hannunta ya jawo ta jikinsa ya rungumeta tsan tsan a kirjinsa. Duk
da dai Zainab na da tsayi dai dai misali, amma tsayuwar su tare sai ya mai da ita wata gajera a
gabansa. Ta fara kokarin zare jikinta daga gare shi ya kara rike ta tsam, yadda ba za ta iya kwacewa ba.
Yace “haba amaryar Bala Mai gwanjo, ina zaki gudu ki bar Balanki”?
Ita ma muryarta can kasa kamar mai rada kuma cike da jin kunya tace “wan nan ba Ya Balarabe
na be. Ni nawa kawaici gareshi da kunya”.
Dada rungumeta yayi yana dariya, san nan yace “ahaf manta da shi shi a lokacin ba a halasta
masa yin hakan bane shi yasa ki ka ga yana wani kamewa wai shi ala dole ga mai kiyayen
hududullah”.
“amma ai dai ya tsaya inda aka umarce shi din ko”?
“ni kuma ina ne iyakata”? ya tambaya tare da tsare ta da idanun bayan ya dan sassauta rikon
da yayi mata. Shiru ta kasa ba shi amsa.
“ba ki da amsar hakan to ni ina da ita”. Ya sa dan yatsansa dan ali ya shafo tun daga goshinta
zuwa hancinta ya dangane da bakinta zuwa habarta wadda ya dago ta da yatsansa ta kalle shi
sosai ciki idonsa. Sai da ya dan yi kissing bakinta, san nan yace “Putri Salju Al Bashir da aka
aura miki bashi da iyaka a kan ki”. Kunya ce ta kamata sai kawai ta boye kanta a cikin kirjinsa. “a’a kar muyi haka mana, daga na
kawoki garin Fulani sai kuma ki kama al’adarsu”.
Ta samu ta dan zame kadan san nan tace “dama nima tawa ce ala’adar”.
Tafi yayi mata yace “eyeh Putri saya. That’s more like it. Na fi son duk maganar da nayi ki bani
amsa”.
Take ta canza topic tace “yaya gajiyar bikin da kuke yi”? “gajiya tabi lafiya zamuje mu kai
amarya Kaduna an jima kadan. Na dai bar su Sa’ad sun dauko wani choreographer wai ya
koyar da su rawar Fulani, saboda sun rantse biki zasu yi da gaske a Kera”.
Dariya ta saka a hankali tace “haba wasa dai suke yi. Ina su ina bikin kauye:?
“ashe kuwa zaki sha mamaki. Baki san friends dina da son challenge ba. Already har sun yi
oder costume da zasu yi amfani da shi. So gwanda ma ki sanar da su Fatu they should get
ready for a duel”.
Nan dai ya zauna har kusan azahar suna ta hirarsu cikin annashuwa da jin dadi. Kuma duk abin
nan da ake hannunta na cikin nasa bai saki ba. Ita kanta yanayin da ta ji na wani nishadin da
bata taba jin irinsa ba, sai ya sanya ta daina kokarin kwace hannu ta bar shi yana wasa da shi.
Da kyar ya iya mikewa bayan 12.30 shi ma sabo da nacin wayar su sa’ad ne da su Mujib ya
hakura. Har bakin mota ta raka shi, anan ne kuma wata wayar ta sake shigowa. Ganin angon
ne da kansa ya sa a speaker. Daga can banagaren aka ce “wai kana ina ne. ka san so muke by
1.30 latest mu bar garin nan, amma kai an neme ka an rasa”? “kai jiya da aka neme ka aka rasa waye ya dame ka da cigiya? Ba kyale ka aka yi ba. I beg give
my space. You know the feelings that iam experiencing so why are whining like a wounded cat”.
“yi hakuri mutumina. Da zaka yi dabara ma kawai ka