Showing 36001 words to 39000 words out of 65424 words

Chapter 13 - FINI A UBA IN FIKI A MIJI book Complete by Hanne Ado Abdullahi .pdf

bawa Balan ta kudin.

Suka sayar da after guda bakwai da rigunan suma guda bakwai. Kudin su dari biyu da tamanin
haka suka dawo da su cas.
Fatu ta sake saka ta ta dauki tamanin daga cikin kudin. Suka shiga kofar wambai ta sayi
zannuwan gado guda biyu na gwanjo ‘yan dubu bibiyu. San nan suka shiga wajen masu kayan
kicin ta tsintsinci ‘yan kayan kicin dai dai na dubu hamsin har da risho ta saya.
Daga nan suka tsaya shagon mudassir a filin parking. Nan ma ta sai atamfa ‘yar 4500 guda
hudu. Ta sai wata shadda barauniyar bazin ta dubu hudu. Ta sai leshi guda biyu na dubu biyar
biyar..
kwarai ta haura budjet din ta da dubu biyu, amma haka ta dada daurewa ta sai masa shadda
‘yar dubu goma yadi goma da zummar ta sai masa ta daurin aure. Ta kuma saya masa guda
biyu ‘yan dubu biyar biyar yadi biyar. Ta fito bakin shagon ta sai masa hula guda biyu ‘yan 2500.
Suna sauka daga adaidaita a kofar gidan su Fatu, shi kuma yana karasowa a kafa. Suna ta
kakabin sauke kaya ta bayansu suka ji ance “yan mata adon gari inzo in yi dako ne”?
Da hanzari suka juya. Suna ganin shine duk suka saki dariya. Bayan sun gama sauke kaya.
Fatu ta shiga gida ta fito masa da ruwan pure water da mamanta take sayarwa da kuma kunun
zaki. Sai da suka shiga suka yi sallah duk yana jiransu a dakin yayan Fatu, san na suka sake
fitowa. “wai daga ina kuke ne haka na ganku a gajiye”?
Daga wajen mai magani muke ta isheni da kuka za a raba ta da masoyinta, shine na kaita
wajen wani mai magani yace mu samu hawayen kuda da kwan sauro sabuwar kyankyasa da
kuma kafar kiyashi ta hagu zai hada mana lakanin da ruwa da iska ba mai rabaku”.
“saboda Allah Fatu kina ganin halin da muke ciki amma zolayar mu ma kike yi”.
Cikin dariya ta ci gaba da cewa “ina kuwa zolaya kana ganin yadda na dage taya ku neman
magani” ta fada tare da mikewa don kokarin fita daga dakin. Sai da ta fita yace “Putri Salju ina
labari”?
“lafiya kalau. Amma ya na ganka a kafa ina mashin dinka”?
“Ba jiya na sanar da ke zan sayar ba ai har anci kasuwarsa”.
“amma ban so ka sayar da shi ba. Ka ga ai zai taimaka maka zuwa kasuwa da yana nan”.
“kasuwar ba sai a je a kafa ba in dai za a sameki”.
“Allah yayi mana jagora”.
Fatu ce ta shigo da tray din abinci. Tana ajiye wa ta fita ta barsu a dakin. Ita ta bude food flask
din. Birabiskon gero ne da miyar yakuwa.
“Allah ya sa ka iya cin abincin bare bari” ta fada tana mai zuba masa a plate.
Yana ci suna hira. Ya kuma ci da yawa, ko don dadin zancen da take masa. Sai da taga ya ci
sosai, san nan ta fito da kudi daga cikin zaninta ta mika masa dari da sittin. Cike da mamaki ya
kalleta yace “inaa kuma kika samo kudi masu yawa haka. Na fa lura hajiyata kudi gareki.
Wadan nan kuma daga ina”? “kudin kayan da kaki karba ne wannda Abba ya kawo min tsaraba daga Mecca”.
Nan ta shiga lissafa masa yadda ta sayar da su da kuma abin da ta saiwa kanta. Cike da
tausayin irin son da take masa ya ke sauraron bajintar ta. Bata lura da yanayin sa ba, cike da
zumudi ta shiga fitaar da kayan da suka sayo tana nuna masa. Ta kuma dauko shaddar da ta
saya masa da hulunansa guda biyu ta mika masa. Har wata kwalla ce ta subuce masa na tsananin tausayinta. Yanzu ya lura ashe ba mace ta

tsara maka kalaman soyayya ne zai nuna son da take maka ba. A’a sadaukarwarta da kuma
kula da kai shine hakikanin soyayya ta gaskiya. Ji ya ke kamar ya tashi ya rungumeta saboda
tsananin murna.
Ya dago ya kalleta cike da wani irin shauki a ransa. San nan yace “Zainab na gode da irin son
da kike min. ni kuma nayi miki alkawari da iznin Allah ba zaki taba kuka da aure na ba. Zan
nuna miki kauna. Zan baki farin ciki da baki taba tsammanin samun irin sa ba. Yanzu a ina kika
ga ya kamata mu nemi dan gida da zamu zauna”. “tace ka san ni ba sanin gari nayi sosai ba. Amma duk inda zaka nema ka nemi inda ba zaka
sha wahalar zuwa kasuwa ba”
“Ni da ce ma zaki yarda sai mu ci gaba da zama a gidan mu kusa da Ummata. Ina da daki ciki
da falo daga waje da kuma dan bandaki na. In yaso ko daga verender sai an rufa miki kitchen”.
“Amma lalle kuma ina gidan sai Umma ta yi girki, sai kace ban san ciwon kai na ba. Kabar mana
kitchen daya ya ishe mu. Wadan nan kaya kuma ka tafi dasu. Tun da Momi tace kai za ka yi
komai, sai ka tafi dasu wajenka. Amma kayan sawar ka barmin zan dinka da kaina a keken
mama Hajjo”. “Sana’a nawa kika iya. Ban da snacks da kike yi har dinki kin iya”.
“lah aihar zanen lalle da gyaran jiki na amarya na iya. Dama zance idan zaka amince min sai
nima in dan dinga sana’a a cikin gida. Ko dinkin ko gyaran jikin ko kuma snacks din duk wanda
ka zabar min”.
“To putri Salju ni da nake burin mai da ke sarauniya kuma kina debowa kanki aikin wahala”.
A shagabe tace “ni dai kayi min izzni in gwada wata sana’ar kaji mi……”
Bai san sanda ya sa hannu ya lakace mata kumatu ba yace “da wanan muryar taki ai ko duka
na kika nemi iznin zan barki kiyi balle sana’a. amma dai ni complain dina daya kar neman kudi
ya hana a kula da ni.
“Zan maka alkawari daya. Matso kana gida zan ajiye komai in maida hankali na da duk wata
kulawa ta gareka”.
“da gaske matata”.
“Da saura tukun na”.
“A’a wai da na ji kin kira ni mijin ki sai na zama convince of my status”.
Kunya ta kamata ta kasa amsa masa sai ta basar da zance. Ganin haka shima ya kyale
maganar yace “Amma ki bani har kayan sawar taki in tafi dasu. Zan nuna wa Ummana gobe
zan dawo miki da su”.
Nan kuwa taa hada masa har da kayan kicin din data saya. Su kam da niyyar ya barsu a a
gidansu kawai.
Yana shiga ya jibgewa Ummansa kaya a gabanta, yana fadin “Umma kuna tsokana ta na shiga
gwanjo saboda Zainab. Ita ku duba irin abin da take yi sabo da ni”.
Yaya Maryam da ta shigo taji labarin abin da Zainab tayi na kokarin ganin ta taimakawa Albashir
ya aureta, ita ta ba da shawarar a bata duk atamfofin sai da kuwa ta samo original super
kowacce haka ma shaddar ta sayyo ‘yar 40k dinta. Leshi ne aka kasa samun manyan su irin
wadan nan. Zainab ganin ta hada da wan nan ta mai da hankalinta kan saukar da za suyi hankalinta
kwance. Ta san dai kudin nan ko ba su cika dari biyar ba sun kusa. Shi kuwa shi da Mujib duk
abin da aka yi sai sun bugawa mallam Usman watau Abban Hafsa sun sanar da shi.

Ranar jumma’a da misalin goma na safe su Alhaji Usman da kuma ‘yan uwansa suka tunkari
gidan Dr Abdallah Zubair domin nemar wa dansu aure. Ga shi dama suna da daurin auren ‘yar
wajen Alhaji Bashir saboda haka suka nufi gidan da niyyar daga nan sai su wuce daurin auren
wanda ita ma kuma dan wani aminin Alhajin ne zai aureta. [8/8, 21:55] +234 814 948 5104: FINI A UBA
IN FIKI A MIJI
PAGE 25BY HANNE ADO ABDULLAHI
Zainab bata da masaniyar abin dake faruwa, saboda tana gidan su Fatu suna aikin snacks din
da zasu yi sauka gobe. Tabbas Bala ya sanar da ita ko yau da safen nan akan cewa iyayensa
zasu shigo washegari da yamma. Da kanta taje tana kokarin sanar da momi. A dakinta, ta same
ta ce “Mh Momi dama Ya Bala ne yace…..” Bata barta ta karasa ba ta fara sauke mata bala’i. “ya Bala a gidan uban wa. Ke har kin isa ki
aurar da kanki banyi niyyar kiyi aure ba. Shashashar banza marar hankali. Ta shi ki bani wuri ko
in yi ball dake”.
Hakanan ta mike tana mai zubar da hawayen takaici. Ta rasa me zata yi a duniyar nan Momi ta
sota. Laddabi biyayya da kuma hidimar da take mata, ‘ya’yan da ta haifa a cikinta basa yi mata
2% dinta. Amma duk da haka ita ce a hantare ko da yaushe.
Ita dai bata samu sanar da iyayenta zuwan iyayen Bala ba. Ta dai fawwala wa Allah lamuranta
ta kuma yarda idan har mijinta ne shi ba wanda ya isa ya raba su.
Shi ma dai Mallm Usman haka suka yi kundunbala su da kakannin Zaina na wajen uwa da
kuma na uba. Da kuma kannen kakanin nata guda biyu. Shi ya tuko so zuwa gidan Dr
Abdullahi, saboda information din da su Mujib suka bashi akan zuwan iyayensu yau.
Su kuma daga bangaren iyayen Al Bashir sun shirya ke nan saiga gwamna jiha ya iso saboda
halartar daurin auren da za ayi, wanda ya hada dangi da duk wasu abokan arziki. Shi ma Al
Bashir kusan duk abokansa sun zo daurin auren cousin dinsa saboda angon abokinsu ne.
Jiniyar gwamna ita ta tsaida su daga shiga mota domin zuwa wajen iyayen Zainab. Bayan sun
gaisa suke shaida masa inda suke da niyyar zuwa, amma tun da yazo zasu fasa zuwa, su tsaya
a daura auren da dama shi ya tara su.
Allah ya sani His Excellency yana ganin mutuncin Alhaji Usman, watau shi mahaifin Al Bashir,
saboda su suka tsaya masa ya hau kujerar da yake kai saboda sun ganshi a matsayin mutum
mai gaskiya.
Tashin farko ma da zai fara campaing. Naira million 500 ya bashi gudummowa. Kuma da aka ci
zabe ya nuna san ya saka masa da alkhairin ya ki yarda, saboda ko kwangila yaki karab. Ya
nuna masa saboda talakawa suka yi kuma talaka suke so ya ci moriyar dashin da suka zuba.
Ai kuwa His Excellency najin auren Al Bashir za a je nema, yace da shi za aje. Nan kuwa suka
runguda zuwa Hotoro NNDC inda gidan su Zainab yake. Dr bashi da masaniyar kommai sai
gani yayi security sun zagaye gidansa. Kafin chief protocol officer ya gama yi masa bayani, baki
sun iso. Bayan an gaggisa suka sanar da Dr Abdullahi uzirin da ya kawo su. Ka hango ta yadda zai yiwa
governer musu yana matsayin COMMISIONER dinsa? Cike da murna ya karbi abin. Nan kuwa
suka FITO da sadakin da aka yankawa dansu suka mika.
Saboda tsabar rashin gata bai damu da ya tambayi Zainab ko ta na son sa ba ko bata so.
Tun da ai yana sane da cewar Bala mai gwanjo ke neman aurenta ba Albashir Usman Ahmad

Babba ba.
Su dai su Baffa dasuka zo daga Kera sai mamakin wan an abu suke. Shi kuwa Mallam Usman
bai yi mamki ba saboda ya san matsayin Al Bashir. Ana kokarin tashi sai Baffan Nene yace “to
ni kam ranki shi dade da ayi aje a dawo, ga sadaki ga waliyyan ango gana amarya ga kuma
liman na unguwar nan, a daura aure mana kawai shi ke nan”. “haka ne kuwa” da yawa daga falon suka amsa.
Jin haka Alhaji Bashir kawun Al Bashir ya dau waya, ya bugawa babban dansa yace maza a yi
diverting jama’ar da suka taru domin daurin auren ‘yarsa da kuma dan abokinsu shi da Alhaji
Usman zuwa gidan su Zainab, ga wani daurin auren na gagawa ya taso.
Kafin minti talatin kuwa muatane sun cika kofar gidan. Ba shiri mallam ya bude store da aka
jibge tabarmi wadanda aka saya lokacin auren su sakina ya shiga baza su a haraba da kuma
wajen gidan.
Momi na daga cikin gida saboda kasancewar wannan jumma’ar ta kama public holiday ba su je
aiki ba. Kafin ta Ankara kawai sai gani ta yi mutane na ta tududdowa cikin gidan. Baba laure ce,
ke shaida mata ai wadanda suka kawo sadakin Zainab ne suka bukaci a daura aure yau din
nan. Ta lailayo wata ashar da bazan iya rubuta muku ita ba, tace “uban waye mijin, saboda da dai na
san ba wan nan dan iskan mai gwanjon bane’.
Baba Laure dake mata dariya kasa kasa tace “na dai ji kamar ana ko dan gidan gwamna garin
nan, don shi ma ya zo na dauka ma kin ji jiniyarsa”.
“naji jiniya amma ban dauka nan gidan bane, na dauka wucewa su kayi”.
“ai kuwa dai nan suka tsaya”.
Kwasa tayi a guje ta shiga ciki, kamar tababbabiya. Ta buga wayar mijin hayaniyar falon nasa
bata barshi yji ba. Jikinta gabadaya sai rawa yake yi. Ta ce "Yi sauri Hanif falon Daddy ku ka
kira min shi kace masa na fadi bani da lafiya”.
Da sauri kuwa ya nufi falon dadin nasu ya isar da sakon Momi ga Dr Abdullahi. Jin haka kuwa
ya mike da hanzari yana fadin “ina zuwa wani abu ya faru a cikin gida”.
Da sauri Baffan Nene ya riko shi yana fadin “kaga kar ka shiga ciki ko uziri maitsawo ne wakilta
wani kawai ya dauran auren ai kaga ba a bar su mai girma .Gwmana suna jiraba”?
Nan takewa kuwa ya wakilta mahaifin sa a kan ya daura auren Zainba, shi kuma ya shiga yaji
uzurin da ya faru a ciki. Yanda ya ganta shi kansa hankalinsa ya tashi sai sambatu take tana
fadin an munafunceta.
“Kayi sauri ka tsaida auren nan. Ba zai yiwu ba”. Sune kalaman da ke fita daga bakinta. Kokari
yake ya fahimci abin da yake nufi, amam duk ta rude sai Magana daya take maimaitawa.
Kafin su Ankara sai jin sanarwa suka yi an daura auren Zainab Abdullahi Zubairu da kuma
Alhaji AlBashir Usman akan sadakin naira dubu dari biyar, wanda Baffa Nene ya wakilci amarya
His excellency ya zama wakilin ango.
Da Momi da Zainab tare suka shide wacce itama sanarwar ta same ta ta sanadin wan Fatu da
aka daura auren tare da shi.shi kansa Al Bashir bai zaci durin auren a haka ba, a bazata yazo
masa.
Zainab na jin an daura aurenta ba da Balrabe ba, ta kalli yayan Fatu watau Ya Baanaa cikin
firgici da kuma tsoro. Tace “Ya Baana me kake nufi? Da wa aka daura aure na? na shiga uku”.
Tana fadar haka tayi luu ta sume a wajen.

Shi ma daga can kofar gida jin sanarwar daurin aurensa ya san yi shi luu din kamar zai fadi. Su
mujib suka taro shi suna tsoknar sa. Allah ya taimake shi da zai je daurin aure babbar riga ya
saka, ba don haka ba, da hoton daurin aurensa ya fito da karamar riga.
Suna cikin farin ciki shi da abokan sa wadan da ba nashi dauri auren suka zo ba, na Sagir
Inuwa suka zo wanda ya kasance shi ma abokinsu ne sai ga Ya Baana ya nufo su da sauri
daga cikin gida yana neman taimako wai Zainab ta suma.
A miliyan ya zumbuda yafada gidan su Fatu wanda yake bayan na su Zainab. A tsakar gida ya
tarar da ita rungume jikin mama Haajjo tana kokarin shafa mata ruwa. Bai san sanda ya
durkusa ya kamota jikin sa ya rungume ba, sai fadi yake “kar kiyi min haka Zainab. Don Allah ki
tashi idan kika barni bansan yadda rayuwata zata kasance ba” Da kaga yanayin da yake Magana ka san a rude yake. Tana farkowa kuwa ta ganta manne a
kirjinsa yana kuka. Ita ma ba shiri ta saki kuka tana fadin “wayyo Ya Balarabe Momi tayi nasarar
raba mu. Na shiga uku dawa aka daura min aure da shi. Wallahi ban sonsa kai nake so.
Jin kalamanta ya sanya shi dada rungumota jikinsa ya ma mata da wasu mutane a tsakar
gidan. Mama Hajjo ce tasa Fatu ta shiga dasu dakin Ya Baana saboda idon mutane.
Bai ji kunyar kowa ba haka ya daga ta cak ya shiga da ita dakin. Kan katifar dakin ya kwantar
da ita, san nan ya tura kananan kitson da suka zubo har gadon bayanta wanda suka barbazu a
fuskaarta lokacin da aka yaye mata hijabin da ke jikinta lokacin data suma.
Tana kallonsa sai ta sake fashewa da wani sabon kukan. Ya sake rungomata jikinsa kanta na
karkashin habarsa fadi yake “come on Putri is alright. Ki yi shiru ki daina kukan I will explain
things to you”.
“Ya Balarabe ba abin da za kayi min explaining. Ka barni kawai in karashe rayuwata cikin bakin
nciki”.
“in sha Allahu cikin Farin ciki mai tsawo da alkhairi da kuma yakana zaki kare raywarki”?
“Ta ina? Kaine farin cikina, na kuma rasaka saboda haka bani da wani sauran farin ciki”. Ta
sake fashewa da wani sabon kukan.
A cikinn hannuwan sa ya saka fuskarta. San na yace “Putri look at me”.
Ta dago ta kalle shi kamar yau ta fara ganinsa. “kin taba tambayata suna na na asali”?
Gigiza kai tayi alamar a’a. “Putri nine Al Bashir da ni aka daura miki aure. Nine mijinki nine zan
kasance farin cikin ki”.
Take taji wata irin kunya ta kamata. Nan ta ringa tariyo boren da ta yi saboda a zaton ta ba shi
ta aura ba. Hannu ta sanya ta rufe fuskarta cikin jin kunya.
Sake rungomata jikinsa yayi yana fadin “a’a kar muyi haka dake kunya kuma ta ina. Yanzu ki ka
gama suma kina farfadowa akan ba abaki ni ba. Yanzu kuma kin samu sai kuma ki fara yiwa
abin da kike so damage”.
“Ta ina nayi maka damage”?
Yana kokarin bata amsa Fatu tayi sallama. Sai da suka amasa san nan ta shiga tana fadin “ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login